TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 63

Sponsored Links

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/1, 11:07 AM] +234 903 973 1553: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣3️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Na samu taji dama tana zaune ta idar da sallah nagaida ita
tare da tambayanta karfin jikin nata tare da kokatin nemanshi a layin wayan
shi.

    Yana dauka na mika
mata ta karba suka fara gaisawa dashi yake tambayanta karfin jiki naji tace
dashi naji sauki ai  dama bata fadama ba
jikin nawa ai kullunne ni.

    Banji me yace mata
ba sai tace zan mata magana idan jikin ya matsa min tayi mai godiya tare da
adduan neman tsari agareshi ta miko min wayan na karba.

   Na mayar a kunnena
yake fada min na fada mata idan jikin yakiya tayi maki magana kuje asibiti don
Allah da ita ko ki kaita chemist abata magani nasan baki rasa kudi har in dawo
ai ?

   Zamu anjima idan na
gama girki su bata maganin daya dace yace shine daidai don haka zatayi ta fadin
taji sauki amma jikin na nan.

    Sai kuma ya koma
tambayan badai matsala komai ko bayan tafiyana nace ba komai wallahi saidai
wani brother dina dake zaune USA yayi waya dazun yake fadin na hadoma shi civic
din ka akwai wani aiki da zasu dauka na tsunci bakina yana fadin haka.

   Yaya Musa ko ya
Jafar ya tambaya da sauri nace a,a brother Bisi na lagos dake can zaune makwabtan
mune inda muka zauna a lagos muka zama kamar yan uwa dasu lokacin har yanzu
kuma ana zumunci dasu sosai.

   Shine ya kira dazun
yana fadin na turo takardun ka ko nawa saidai ni ban gama karatu ba a yanzu sai
a fara turo naka idan suna complet   sai
naji yayi shiru na dan lokaci.

  Itako Dije dake
gefen mu sai faman fadin take madallah madallah Allah abin godiya Allah maji
rokon bawansa Allah mungodema.

    Kina dakin Dije
har yanzu ke nan na amsa maida eh ok idan kin koma part din mu zamuyi magana
sai ya kashe wayan nabi wayan da kallo don dama na zaci hakam tunda ban taba
bashi labarin Bisi a cikin yan uwan mu ba.

     Dijeko sai fadi
takeyi madallah wanan dan uwa naki Allah ya saka mai da alheri abinda yake nema
na alheri Allah ya bashi na amsa da amin tare da fadin tuwo zan maki kici ko
Dije ?

   Tace to tuwon naso
tunda rana amma wa yanan makiyautan sunki girka min sai hanjin bature da suka
sulala wai shine abincin gayanan na kasaci tundazun ma.

  Na kalli roban da
suka zubo mata taliyan a ciki har ya fara bushewa gashi hankade da dan jajage
kadan a sama nace zakisha shayi mai zafi yanzu in fara hada maki ?

   Tace idan na samu
zansha tun kunun safene a cikina sai naji ta bani tausayi sosai naga harda
sakacina a cikin barinta da yunwa tunda ina gidan nima ai da sauri na mike na
hado mata shayi mai zafi da kauri da guntun bread din da mukai amfani dashi da
safe.

   Na kawo mata nadan
zauna na fifita mata saiga Asmau ta leko tana gani take fadin a a a yar tsohuwa
dama ciwon kwadai kikeyi ashe shayi kika samu haka da kauri Dije.

  Shayi na samu wurin
yar arzikin data san ciwona ba irin ku masu nema su kwace min ba sukayi ta
musayan baki ina masu dariya.

   Ta tafi na bata
tasha saiga zufa ya karyo mata a raina nace kila harda yunwa ke damun
tsohuwarma lokacin nan na mike na fito ina mata sannu ina saka takalmana a kofa
naji muryan inna na fadin.

    Mu ina zamu samu
muna yar dangote a gida duk wani nema nasa yanzu ai can yake karewa wurinta
yaushe zai tsaya bamu wani kayan shayi can yanzun ma kafin ya tafi da yaya ya
hada muna abincin da zamuci ?

    Raina ya baci
ranan na bayar da amsa nace ba diyar dangote nake ba amma yar babana nake shayi
kuma ba a gidan nan na koyi shanshi ba da abina ya ganeni bama na wahala irin
wanan ba.

  Don ko yaushe kaje
gida  mu zaka samu kayan shayi zube saman
dining table don babu mai kula dashi ban karban kudin daki ko na hanashi ya sai
maku abu amma inna kin dauka nice ke hanashi baki abinda kikeso gareshi.

    An fada ko bakiso
na fada auren kine yake kokarin juya min baya a yanzu bani gane kan dana amma
ke gidan ku ai yana kai masu don a yabeshi.

   Kadin nayi magana
naji muryan Dije na fadin ke kan Rashida kinji kunya tun yar nan bata baki amsa
har yau an wayi gari ta gaji da halinki takai ga baki amsa daidai dake.

   Dama ke zaton ki
shi dan naki yana iya daukan duk lalurantane kome ki rabu da So sone kawai ke
aikinsa nan amma ko kallon yar nan kikayi kinsa ba kalan danki bane ita.

  Sai kuma ta juyo
gareni tana fadin yi tafiyan ki ki kyalesu da ita mara tausayin wace taje ta
fada masu din dan kin tausaya min kin hado min ruwan zafi nasha naji karfin
jikina Allah ne maganin su.

  Marasa godiyan Allah
kawai in kina da kunya ke har kyayi wanan maganan don ta taimaki uwarki ina
zaki san ta taimakeni kina daki da diyan ki tun safe kuma shewa zan mutu ku
kwashi ganima.

    Nikan ganin abin
zai rikice masu naja kafana na koma part dina cike da bacin rai na barsu ina
jin hayaniyarsu daga part dina ina mamakin hali na inna da zata tsaya tana
sa,insa da mahaifiyarta haka.

   Yanzu nagane da
danta be kula al,amarinta ashe yasan halin abinshi har ina ganin laifin farkon
shigowana gidan sai yanzu na fahinci inna irin mutanen nan ne da basu danne
zuciyarsu subar abu a cikin su komai kankantanshi.

    Hakan yasa na
manta da wayana dake kuryan daki ashe yayi ta kirana ban sani ba saidana gama
aiki na dauko waya naga six misscall din shi a wayan.

   Ban kirashi ba don
raina yana bace sai gashi ya kira banyi saurin daukan wayan ba saida ya kusa
katsewa na daga murya ciki ciki nake amsa mashi.

   Naji yana tambayana
kina inane waya nata rinngin baki daga ba ina kitchen na bashi amsa a dakile
yace banace inkin dawo part din mu zamuyi magana ba na sake fadin aigani yanzu.

   Jin hakan yasashi
fadin wai meke damunkine princess ina magana kina bani amsa wani iri ba yadda
kika sababa sai naki yin magana a lokacin.

  Da sauri yace min ko
wani abu ya farune kuma nace gaskiya nagaji da irin yadda inna ke min don kawai
na hadawa Dije tea shine zai zama wani magana har tace aurena dakai yasa yanzun
baka kulawa kana kwasan kudin ka kana kashewa a kaina ni har, , , , ,

   Cool down my dear
ba sai kin kai karshe ba don nasan kina hakkuri da zancen inna dama yau daine
tayi maki fiye da kullun don Allah zahra ki kara hakkuri da inna tunda kinsan
halinta.

    Naji nace amma
kawai don Asmau ta fada mata magana sai ta dinga zuba min arashi kamar sa,anta
nake mahaifiyarta fa na taimakawa.

   Kin gani ba nan
zaki gane abinda nake fadi da farko kina fada kina ganin laifina nace kai
dantane ai dole ka bita ko yaya halinta yake .

   Wai Asmau bari yar
kam uban nan da nadawo zasu koma gidan dagin ubansu su zauna na gaji nagaji
wallahi da yan iskan yaran nan dako sharan gida basu iyawa saici da tsegumi.

    Ka hada takardun
ne na katseshi da fadi naji yaja tsuki yace barin loda kudi na sake kiranki ya
kashe wayan a cikin takaici.

   Nima na jefa wayan
gefena inna son zuwa in duba tsohuwar da jiki saidai kuma takaici ya hana inje
part din nasu don nasan inna na nan sun baza tabarma da diyanta a lokacin.

  Sallama naji daga
kofa na amsa Aishan shice ta shigo wurina a cikin rashin sakin fuska na amsa
mata ta shigo tana fadin ashe baki barci ba na dauka harkin kwanta ai.

   Nace ban kwanta ba
Aisha ta zauna tayi shiru na dan lokaci kafin tace Anty Zahra banji dadin
abinda ya faru tsakanin ku da inna ba dazun.

    Duk Asmau ce ta
kawo zancen nan duk dai bata dauka itama zancen zaiyi tsawo haka ba don ta
shigone tanawa Dije sheri shine inna ta karbe maganan ta juyeshi ya zama haka.

  Don Allah kiyi
hakkuri kin saba da halin inna ai yanzu kibar tankawa don Allah kada ajiku da
ita nasan idan yaya yaji hakan ba zai masa dadi ba.

  Kinga ni yanzu na
gane tana kallo ko yanzu na shigo nan din don ba zata rabamu ba muna gida daya
kina muna alherin da zakiwa kannen ki don haka kika daukemu muma.

   Asmauce ta shigo
itama tana fadin nikan na wuto wai innace ke kwala min kira na dawo naki matan
yaya kallo zaki kuna muna a waya muyi dama don yaya na nan ne bamu zuwa.

    Mamakin halinsu
naji nikan na jawo wayan na kuna masu wani film din tan Philippines da muke
kallon season film tana fadin mun wuce nan ai yana kiran wayan.

    Hakan bai hanasu
yin surutunsu ba yace keda suwaye a dakin nace su Aisha ne ya kunduma zaki dame
sukazoyi yan kaza uba ?

    Kasa kudin ke nan
na fada na kawar da zancen a lokacin yace eh yanzu na sayi a banki kin saka
loudspeaker ne ko kuwa nace ban saka ba yace tambaya dama zanyi yaya akayi guy
din nan zai bamu aiki.

    Kai tsaye nace
idan zancen bai kwanta maka bane a barshi don Allah ni j  nagama zan nemeshi yabani tunda niya sani
yace haka zakice min nace naga kana son fassaramin zancen ne da wani manufa
banji yayi magana ba ya kashe wayan.

    Na kunna masu na
mike ina fadin zan dubo Dije in gaida ita da jiki suka amsa da sai kin dawo nan
na fita na barsu zaune suna kallo can na iske inna tayi bakin mata masu zuwa
sayen kayanta.

   Na shiga wurin Dije
muka gaisa na samu tana cin abinci lokacin yasa na dan jata da hira tanaci muna
taba hira tana ban hakkuri kan abindaya faru nace ai ya wuce yanzun ma su Aisha
na wurina na barsu suna kallo.

   Ban jima ba na mike
zuwa part dina na kwanta ina fadin in sun gama su tayar dani in rufe kofa
Asmauce tayi saurin fadin ni a nan zan kwana barin tashi in rufe gida dayani.

   Inna nada baki a
cikin gida na fada tace zan fada mata ta rufe don yaya yaja muna kunne sosai
kan rufe gida wai barayi ke yawo a unguwa.

   Ta mike zuwa cikin
gida bata dade ba ta dawo tana guna guni ta fadin wai inna kada mu kwana nan
yau don dama idan baya gari a yan kwanakin nan da muka fara shiri dasu sukan kwana
a part dina saboda kallo.

    Ai basu koma a nan
din suka kwana dukkan mu falo muka kwana tare dasu nayi sammakon tashi zuwa
school inda daga can gidan mu zan tafi in duba maijego sai dana shirya na shiga
sallaman su nake fada masu sai da yamma zan dawo zan tafi gidan mu daga can in
duba mai haihuwa .

   Asmau tace dani
aida daga nan zaki tafi da mun tafi tare ina son zuwa gidan ku wallahi mutum
baj fitowa ba a bashi wani abin karuwa ba gashi kuma kaci ka koshi farat inna
tace to yar mayunwata fada mata gidab ku gidan tallakawane.

  Ji inna meye yanzu
matar yaya bata sani ba game damu saidai idan mutanen gidansune basu sani basu
ni dai na fita na barsu da shirmen su.

   Ina mamakin yadda
Ahmed ya fito cikin cikin wanan matar haka halinshi ya fito daban shi kodan bai
tashi tare da ita bane oho don dana biye mata ko da safe da mun kwasa tana fada
da yaranra kan sun kwana part dina tana fadin wai ana dauke masu hankali da
kallon banza da zai lalata masu tarbiya

   Kai haba inna wani
irin bata tarbiya mutanen dako yarensu bamuji kuma ba irin tufafin mu suke
sakawa ba don Allah ya horewa yaran nan ta baki basu da kwabo ko kadan.

    Shiru yayi yana
sauraren abokin nasa har yakai karshen magana kafin ya dago ya kalli sauran
dake saurarensu sukace kwarai kuwa don ko gaskiya Alh jauro ya fada.

  Duk yadda mukaso
muzo kusa dakai a lokacin matarka dama kai kanka baka yarda da hakan saidai
aimu bamu kika ba don ko yaushe muna tare dakai don munsan hakan bayin kanka
bane.

    Duk abinda kake yi
alama ya nuna muna ba a cikin hankalinka kake muna mun so mu share zancen ka mu
zauna a inda Allah ya ajemu saidai a yadda muka taso dakai mun kasa hakan
gareka.

   Badon komai ba sai
sanin cewan da mukayi cutar dakai zasuyi a karshe don badon Allah suke tare
dakai ba kuma gashi duk yan uwanka sun kawo ido suma sun saka maka duk da
sunsan gaskiyan zancen suma sunyi fushi dakai a yanzu subar zancen ka.

   Idanunshine ya ciko
da hawaye lokaci guda don jin zantuntukan da abokan nasa suke fada a yanzu
yaushine mace ta mayar hakan a cikin yan uwasa da abokanan sa lokaci guda.

   Yanzun dai mu
godewa Allah dayasa ka gane hakan da wuri tun lokaci bai kure maka ba don da ka
mutu a cikin halin gaskiya akwai matsala babba.

    Aishi mutum mai
alheri Allah baya barinsa haka dama don ko sun hanaka komai basu hanaka alheri
ga mutanen makwabtanka ba.

    Wanan ma ya isa ya
taimaka maka ka fito daga kanginsu don ba haka sukaso gani a gareka ba sunso
suga sun rabaka da kowa a garin nan.

   Yanzun dai ba wanan
ba yaya zancen da muka fara dakai a waya na yaron nan don ya kamata ace zuwa
yanzu kasan matsayin da yaron nan yake ciki.

   Fuskanshi ya shafo
don maganganun nasu sunyi masa yawa a kai duk da dama yasan dasu abaya amma
yanzun da yake kara jin hakan a bakunan su sai yake jin zancen kamar sabo a
gareshi.

   Sun dauki lokaci a
tare dashi har zuwa magariba kafin zuwa sallah bayan sun fito kowa ya nufi
wurin iyalinshi akan da safe zasu fito su rakashi zuwa wajen yan uwan nasa na
haihu.

    A cikin gida kuma
itama hjy mariya mamakin abubuwan dake faruwa sai take ganin abin yau kamar a
falki yake zuwa mata ba gaskiya bane yau mijin nasune yazo gareta shi kadai ba
tare da matarshi wani lokacin da yaransu da basu da kwabo ko kadan.

  Zasuzo su mayar da
ita kamar yar aiki agidan sai sun tafi take samun sa,ida a rayuwanta don
hakanema bata kaunan zuwan nasu saboda cin fuskan da ake mata din idan sunzo.

   Ya shigo gidan bata
saba idan yazo ta sameshi ba kamar yadda ko wace mace ke samun freedom da
mijinta idan yazo sai gashi ta kasa zuwa gareshi.

   Sai shi din ne daya
fahinci hakan ya taso zuwa gareta sai taga abin wani irin bambarakwai a gareta
don haka lokaci guda ta rude da ganin shi kai duniya.

 

Leave a Reply

Back to top button