Hausa MusicLatest Musics

[Music] Zugson – Ni Da Ke Mun Dace

Sponsored Links

Zugson
Song Title: Ni Da Ke Mun Dace

Singer: Zugson

Album: Single

Producer: Zugson

Song Size: 3.0MB

File Type: Mp3

Release Year: 2022

Song Description: Ku sauke wakar Zugson ta farko, mai taken “Ni Da Ke Mun Dace” mp3 download. Wakar dai soft music ne ba wani duma ne a cikinta ba. Ku sauke ku saurara.

Waka ce na yi ta soyayya, amma fa sabun shiga ne abina, ba wani salo, kidan ma ba wani mai zaki bane. Kuma lokacin da na yi wakar muryata a murance take.

Hakikanin gaskiya yadda suka min kidan wakar nan bai yi min ba, ko-da-ya-ke ba yadda na iya, hakan ya sa na ga ya dace na kokarta na je studio na rera ta biyu.

Ga Kadan Daga Baitukan Wakar:

_Ni da ke mun dace.

 _Ko da ‘yan’uwa sun tace.

_Zuciya ta nace.

_A duniya na dace.

_A fagen kauna ban kauce.

Babu kida mai dadi, kuma da ya ke ni kaina wannan shine farkon rera wakata, ban yi wasu salo ba.

Kai ba ma wannan ya karaci tsiyar ba, ranar sai da ruwa ya ban kashi kafin na isa studio, muryata ta disashe, ina rera waka ina tari ko na ji makogwarona ya saki.

A karshe bayan na gama, ga sakamakon, ita ce wakata ta farko, kuma ita ce wacce na fara ji na tsana. A wurina ba ta yi dadi ba, amma za ku iya saurara domin jiyewa kunnuwanku.

Leave a Reply

Back to top button