M SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan Ko Mazan 3

Sponsored Links

 

MATAN??? Ko MAZAN???đŸ’«

 

 

âœđŸ»M SHAKUR

 

 

EPISODE 3ïžâƒŁ

 

 

BONUS💃

Sosai kirjinta yabuga da sauri ta sauke hannayenta kasa tadaina rawan tasauke kanta kasa shima daga kallonshi gabanta nafaduwa dumdumdum.

Wucewa Nura yayi dasauri sama zuwa dakinshi yakasa daina ganin fuskan Ummi dana yaranshi how happy all of them were, yanda itada Aman kema Amal rawa, bayi yafada dasauri ya watso ruwa yafito yashiga shiryawa dan yafita meeting din dayake dashi is by 2, cream yadauka zai shafa saikuma ya tsaya maisa ya kalleta haka smiling ya tambayi kanshi? He was lost dayana kallonta, yar aikinsu ce fa but he was finding all abubuwan datakeyima yaranshi super cute, dan ijiyan zuciya yasauke saikuma yacigaba da shafaman.

 

Ummi daduk takasa natsuwa itama a kitchen ta tambayi kanta maisa yake kallonta, tun yaushe Alhaji yaganota tana rawa haka? Duk wani kalan kunya kunya da nauyi nauyi taji tanaji, IPad din Aman tadauko ta kunnamusu anan kitchen din dan bazata rabu dasu ba tashiga gyaran gidan duka tanaso tana gamawa tamusu wanka, itama taje tayi saita daura abincin dare.

 

Shiryawa yashigayi cikin suit dan dawasu representative na China company zai hadu dasu yanaso yabasu contract nayin titin cikin estate  dayakeyi, yana cikin daura agogo wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Sis yasa yakai hannunshi ya danna call din batare daya daga wayanba yacigaba da saka agogo daga ta dayan bangaren akace “Ya Nura ina yini” “how are you Aminatu ya jikin Hajiya kunje asibitin”? Kasa magana tayi sai bakinta yahau rawa, dasauri yasa hannunshi yadauki wayan gabanshi ya mugun fadi yakai wayan kunnenshi dasauri yace “what happen jikin Hajiya ne meya faru?” Cikin kuka tace “dazun nan tafadi abayi yanzu haka muna asibiti” bugawa kirjinshi yahauyi sosai anatse yace “Dr Tanimu ne ke ganinku”? Dasauri tace “eh shine” dan ijiyan zuciya yasauke yace “daina kuka ya isa babu abinda zai sami Hajiya kinji” kaman yana gabanta gyadamai kai tayi, cikin dan taushin murya yace “is okay, zanyi magana da Tanimu I think zan muku booking flight gobe kutaho nan Abuja taje babban asibiti anan don’t cry again hankalinta zai tashi, akwai kudi awajenki”? Dasauri tace “eh akwai” ahankali yace “to stop crying bari nai magana da Dr Tanimu” nan da nan ya katse wayan yakira Dr sunyi magana da dadewa sannan ya katse wayan dakanshi yamusu booking first flight na gobe da safe sannan yasake kiran sister nashi yace zasu biyo jirgin safe gobe suzo koya ake ciki tadinga gayamai yatashi ya idasa shiryawa duk mood nashi ya chanza sannan yafito anan falo yaga Aman da Amal suna kallon cartoon a iPad nasu duk an musu wanka sunyi kyau gwanin ban sha’awa kaman ya debesu yafita dasu Amal kaman ba itane mara lafiya ba karasawa yayi inda suke ya duka yamusu peck agoshi yace “Dady zaitafi aiki” dasauri Aman yace “Dady zan bika office” shiru yayi kaman mai tunani yana shafa kansu yace “shikenan zanje daku amman sai ranan Saturday jibi kaga gobe akwai school yau bakuje ba dukanku” Dasauri Aman yace “hadda Anty Ummi zamu itama taje taga Daddy’s bigggggg office” ya ware hannunshi biyu yana nuna how big office na babban shi is, dan murmushi yayi yana kallon Aman din kafin ahankali yace “yes Son hadda Anty Ummi” dasauri Aman yace “love you Dady u the best Dad ko Amali? Dadyn mu is the best” dasauri Amal yace “yeeeessssss Dady is the best” murmushi yayi yace “my princess and my Aman are the best nima” harzai tashi yace “ina take?” Aman yace “Anty Ummi”? Gyadamai kai yayi dasauri yace “itama taje tai wanka adakinta” jinjina kai yayi yamike yace “to natafi bye” bye sukamai yawuce yafice.

 

 

Wani babban shago ne girmanshi zaiyi wani super market din sama da kasa ne, kasan abayoyi ne irin na yan millions din nan designers dan babu abayan yan 100 ashagon saikuma sama asalin designers bags da shoes ne latest collection ma kuwa, zaune take cikin wani office dake nan sama babban office ne na gaske dawasu mata guda biyu suna hira, daya daga cikin matan biyu ne tadaura tissue kan idanunta tana kuka Hadiza taje tsaki tace “kodai nazo nai magana da mijin nan naki ne Baraka”? Dasauri Baraka tazare tissue dagakan idanunta takalli Hadiza idanunta sunyi jazur tace “so kike ya koreni? Not everyone is as lucky as u are kinada miji kaman Nura mai hakuri da share magana, idan nama Ubale abinda kikema Nura saiya lakadamin duka halan saiya korani gida” wacce ke kusa da itane ta tureta tace “dallachan ai gashinan saisa sai gallaza miki azaba yake waya cemiki anama maza good girl yanzu??” Dasauri Hadiza tace “ahh tohh tell her ooo my dear, tell her Zee cus good girl no dey pay again, kima miji good girl ya tattakaki yayi using naki do dambu yaje ya watsar a shadda, ai yanzu zaman Auren fire for fire ake yana baki kada kibari yakai kasa give him back gbasgbos kawai saikaga yasha jinin jikinshi yasan keba kanwar lasa bace, kinga Nura ko giyan wake yasha yasan bai isa ya tunkareni da nonsense nashi ba cus bana ma dauka ne kuma gashinan nasama ma kaina lafiya I do duk abinda naga dama duk abinda raina yaso agidana to waima tsaya idan nai aure banyi whatever naga dama agidana ba yo menene fa’idan auren? Menene banbancin gidan mijina da gidan iyayena? Abeg ke waye Ubale yana cemiki kule kicemai chass wlh zakiga kun zauna lafiya” dasauri Zee tace “Allah yasa ta dauka, itane kullum yamata ihu kaman ubanta, fita saiyaga dama yake barinta, yahanata business ya kulleta agida kullum ciki yake duramata won’t you speak up kinuna mishi kefa duk lokacin dakikaga dama fita zakiyi ki kwatarma kanki yancinki, ki nunamai kedashi are equal sabida yana namiji baya nufin zai dinga juyaki, munafa zamanin feminism ke duk inda namiji yau yataka aduniya kema zaki iya takawa to akanme zaki maida kanki slave dinsa? Jibemu kawayenki yanda muke more rayuwa muncigaba ke kinachan kina bautama mijin dake hanaki fita sana’a, yakuma miki ihu” tissue takara dauka dan maganganun su nasata jin badadi datasan hakane da da Zee tazo daukanta batabita ba, tace “nidai kubarni duk randa nazo wajenku saikun sani ina feeling bad inajin kaina kaman banda sa’a aduniya, kaman I’m the unlucky one, Ubale na sona ina sonshi kuma ya isa yace nayi nayi karnayi karnayi ya is

.” Mtswwwww Hadiza taja tsaki dayasa Baraka tai shiru takalleta Hadiza tace “takuraki dai baya bari kiyi yanda kikaga dama, imagine yaranki uku har yanzu kece ke komi agidanki, girki, kula da yara uku fa da sauransu ke jakace Baraka? In nice ai sai na mutu, Idan yana sonki bazai sama miki yar aiki ba haba akan mene zaki dinga shiga kitchen kina girki awan nan zamanin da masu kudi ke hiring intercontinental chef yana musu girki agida that’s my next plan ma ni nadauko professional Chef daman na share zancen ne bayan na sami wannan current yar aikin nawa Ummi but still zan dauko” dan murmushi Baraka tayi tace “Allah baki sa’a, kowa nada abinda works for him, ninaji naga kuma zan iyane ne, mubar maganan please kona tashi nayi tafiya ta gida daman Zee takawoni, I don’t have to be like you ladies, tundadai ba dukana ko wahalar dani mijina keyiba ko neman mata Alhamdulillah” dasauri Hadiza tace “to abar maganan amman wlh sabida kawai ke kawarmuce duk tare muka taso da tuni mun rabu dake danni banga dalilin dazaisa kene ke duka aikin gidanki ba mijinki na miki ihu kaman wata jak

.” Karan da wayanta yayi yasa takasa karasa maganan takalli screen din ganin Nuri yasa tai murmushi sosai tajuyo da wayan tace “kun gani” tanuna musu screen din wayanta tace “tsakanina dashi kar tasan kar ne amman jibi yanda yake bibiyana maza fa saida hash treatment kana musu taurinkai ki nuna musu ke fire for fire ce cus sun iya raina mace kai mai sanyi irinsu Baraka” Zee tace “kwarai kuwa Aminiyata”.

 

 

Tashi Zee tayi takalli Barakan tace “muje mu duba abayoyin to” tashi tayi tabita suka fice ba walwala kan fuskanta, Hadiza na kallon kiran sai murmushi take dake kara fito da kyawun fuskanta saida wayan yayi gab da katsewa ta dauka takai kunne ayangance tace “ka gama nunamin matsayina menene kake kirana kuma yanzu”? Dan shiru Nura yayi yana jinta ba sallama bakomi kafin yamace wani abu tai magana, yana addu’a duk wani namiji dabai Riga yayi aure ba to Allah yarabashi da auren mai baki kaman na Hadiza, saikuma chan yace “Hajiya tafadi abayi yau an kaita asibiti but hankalina bai kwanta ba namusu booking flight na safe gobe zasu taho nan da ita da Amina zan kaita hospital taga kwararren Dr, specialist” wani abu Hadiza taji ya tsaya mata arai zai cigaba da magana ta tareshi tace “wai Nuri what gives you the right kadinga making decision regarding our family on your own eh? Wai meke damunka ne zakace Hajiya bama ita kadaiba harda kanwanka suzo gidana bazaka fadamin ba kaji me zance kafin nan kai kadaine agidan? Kodon kaga gidanka ne? Koma da gidanka ne ai nima ba zaman banza nake agidan ba aure ne yabani gidan dan haka u have no right to invite koma waye into my home without telling me, without seeking my approval” tunda Nura yake baitabajin urge na yadaga hannu ya mari mace ba sai yau wlh he feels kaman yadaga hannu ya kifama Hadiza marin da saiya maida fuskanta keya, keyanta yadawo fuska, mahaifiyarshi ba lafiya bama ta tambaya yaya jikinta ba or anything sai maganan gida, menene agidan? What is house? Me Hajiya zatayi agidan? Yau shekaransu nawa da aure Hajiya bata taba zuwa Abuja bama ballema gidanshi so menene abinda matan nan ke fadi? What can a sick old woman zata possibly iya miki agida tana fama da kanta fisabilillahi?Yanada mahaifiya mara lafiya da zatazo garin abuja for the first time yaje yakama mata hotel ne sabida matanshi batason wani yazo wajensu???

 

Daurewa yayi yarike zuciyanshi yana controlling anger yadan sauke ijiyan zuciya Hadiza tabugamai ihu da tsawa tawaya. “Ina maka magana kamin banza are you deaf ne or what Nuri? What gave you the right to invite a third party to my house baka fara sanar dani ba” shi Hadiza ke kira deaf??? Innalillahi, cikin wani irin murya datai sanyi sosai tsabagen bacin rai yace “mahaifiyata ce third party Hadiza? Maman mijin dakike aure uban yaranki, kakan yaranmu itane 3rd party”? “Well u can translate it duk yanda kaga dama is none of my business just listen to wat am about to say” tadan gyaran murya tace “first of all bada yawuni aka kawota ba don’t expect anything from me babu abinda ya shafeni da dawainiyan ku, sabida Hajiya bazan fasa fita aiki na ba, kuma bazan shiga kitchen ba, kuma bani acikin tafiyan zuwa asibiti ko rakiya kai infact banda any business with anything dazai faru daga goben nan zuwa harta bar gidan, dan haka kaika sani ni please sai anjima I am busy with work, I don’t have time for ur unnecessary demand” ta katse wayan Nura yadade yana kallon wayan kafin ya fuzar da iska kaganshi dole kai saluting nashi dan namiji ne mai hakuri dayay composing kanshi bai duramata zagi ba, dama kiranta yayi yaroketa kada taje aiki gobe sabida su Hajiya sannan kuma ya tambayeta me da me babu agida amman jibi abinda tayi rasa abinda zaiyi yasa yayi dialing number Gardner na gidanshi ruwa ringing daya ya dauka anatse Nura yace “Amadu banda number Ummi danje ka buga kofa ka bata wayan” dasauri Amadun yace “gasuchan inajin muryansu a garden takai yaran suna buga kwallo bari nakai mata” anatse Nura yace “ok”.

 

Bata wayan Amadu yayi yace “gashi Alhaji yakira zai magana dake” sa wayan tayi a kunne kaman yana gabanta ta duka tace “Alhaji ina wuni” baisan what just happen ba amman har cikin zuciyanshi yaji sanyi aranshi na muryanta, dan ijiyan zuciya yasauke ahankali yace “Ummi mahaifiyata da kanwata zasuzo gobe  dasafe Mamana bata da lafiya zataga likita agarin nan” da zuciya daya Ummi tace “Subhanallahi Allah yakara sauki, Allah yasa kaffara ne, Allah kuma ya iso dasu lafiya ya tsare hanya” Wallahi he cannot even explain wani kalan dadin addu’an ta da sanyinsu dayaji aranshi, jin yanda yayi shiru yasa Ummi tace “Alhaji kanaso na gyara musu wajen kwanan su ne namata abincin da marasa lafiya keson ci”? Harga Allah ta dauka abinda takira yafada kenan cus ana bata wayan abinda yafara fada mata kenan mahaifiyarshi ba lafiya kuma gobe zatazo. Yarinyar nan is not just good with kids tanada great sense of humor tanada hankali tasan meyakamata and tanada natsuwa, though abinda yakira was yanaso ya tambaya menene babu agida but tambayanta made hum wanna talk to her more, ahankali yace “menene abincin marasa lafiya Ummi”? Kai tsaye dan babu komi aranta tace “meke damun Mama Alhaji”? Yanda tafadi Mama ba Hajiya ba dan yasan batasan Hajiya ake kiranta ba wani sanyi yaji aranshi baisan lokacin dakaman wani dan karamin yaro yace “ciwon sugar da hawan jini ke damunta” dan shiru Ummi tayi kafin ahankali tace “abincin dayakamata tanaci abinci ne da babu sugar aciki, babu Gishiri kuma dan Gishiri yana kara hawan jini, zan mata tuwon Alkama ko tuwon garin plantain dabai nunaba amman duka biyun bamu dashi agida, da miyan ganye, Gwaggo na a kauye nada hawan jini da ciwon sugar duk nasan irin abincin datake ci dake taimakamata bata cika ciwo sosai ba, idan Mama tazo itama zan dinga dafa mata zakagani zata ji sauki da izinin Allah” dan murmushi kadan yayi a tsane yace “nagode Ummi kituramin sunan abubuwan da zan sayo dakuma abubuwan da babu agida, saiki gyara musu wajen kwanan” Ahankali tace “to” dan shiru yayi itama tai shiru tana jiran taji ko akwai wani abun jin shiru yayi yawa yasa tace “hello” batare daya amsa ba yace “inaso naci tuwon shinkafa da miyan taushe ki dafamin kinji” yanda yayi maganan ataushashe saida taji wani iri dasauri tace “too” yasake shiru itama tai shiru tana sake jiran maganan shi maganan su Aman da Amal dayaji suna Anty Ummi come come let’s continue yasa yace “to saina dawo ko” ahankali tace “too Allah dawo dakai lafiya” lumshe idanu yayi tareda zare wayan daga kunne he just wish da matanshi yayi dis dogon magana wlh babu abinda yake craving yanzu aduniya irin kwanciyan hankali, Allah ya azurtashi, yakuma bashi yara, kwanciyan hankali ne kawai yarasa, yesterday yafara magana da yarinyar nan why is he enjoying conversation da ita haka?.

 

See y’all Saturday đŸ„°

 

 

 

 

Let’s keep HADIZA in one place, one of the major abu dake kawo matsala agidan miji is shigowan baki, guest ko visitors aturence.

 

Mata will always say ban isa nakawo baki batare dana sanar dakai wane ko wance zatazo ba.

 

Maza kuma sai sun gama cema mai zuwa Allah kawoshi lafiya za’a cemiki babe wane ko kaza na hanya fa zaizo ko zatazo tamana kwana biyu hakan na batama Mata dayawa rai.

 

My question is, is it okay for mijinki ya yarda kowa yazo kafin yazo yafada miki daga baya wane ko kaza zaizo?

Koko yakamata yafara neman yardanki ne kafin wane ko kaza yazo?? Cus I keep wondering gidan aure belongs to waye exactly??

Does it belongs to the wives ne sabida ai cewa ake za’a kaiki gidanki ko it belongs to mijin kadai ne koko gidan aure belongs to the TWO OF YOU???

 

To idan gidan na dukanku ne biyu maisa ba’a making decision kan wanda zai shigo tare???

 

Mata ayanzu daku nake ko sabida maza sunsan mun tsani ace wane ko kaza zaizo ne koda an gayamana bazamu yarda ba saisa gwara suyi accepting wane yazo kafin asanar damu cewa wane zaizo rana kaza????

 

How do you think za’a iya magance yawan issues da ake samu idan za’ayi baki agidan miji??

 

Let’s discuss thisđŸ‘‡đŸŒ

Leave a Reply

Back to top button