Furar Danko Book 2 Page 21
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣
……..“ALLAHU akbar, ALLAH mai rahama mai jin kai, Sarki gagara misalin masu misalai. Isashe mai iko da koman da ke iya kallon kansa a iko. Dama anga ɗiyar tawa?”.
Kai Uncle Yousuf ya jinjina mata, da ga ita har Abbah da farin ciki ya sashi jin yama kasa motsawa, sai sunayen ALLAH yake ambata a jajjere. Cikin nutsuwa Uncle Yousuf ya zayyane musu komai ta yanda zasu fahimta. Wato gano inda Lulu take dama abinda ya faru akan cikin har zuwa haihuwarsa a yanzu. Sai dai suna roƙonsu da su ɓoye wannan sirrin dan basa son asan inda Lulu take a yanzu har sai abubuwa sun dai-daita domin koyama Alh. Sulaiman da Dada hankali bisa kuskurensu. Da ga ƙarshe suka sanar musu sunan yaro Aliyu kamar yanda Lulun ta saka aka masa huɗuba da shi. Sosai su Ammah sun gamsu da wannan dabara, tare da mamakin wannan baƙin hali na su Dada. Ga kuma Umma a gefe itama tana nata yaƙin, duk da dai Ammah ce kaɗai tasan da wannan. Yaro yasha addu’oi shi da mahaifiyarsa Lulu na fatan samun lafiya a gareta. Da ga ƙarshe Daddy yace musu su shirya domin sama musu visa dan yana son suje su gano Jariri. Da farko Abbah yaso ƙi, acewarsa bazasu sakasu wahala ba. Duk randa suka dawo Nigeria ai zasu ganshi. Amma sai Daddy da Uncle Yousuf sukaita roƙonshi. Da ƙyar dai ya yarda ya amince. Inda tun a ranar suka fita da su domin yin passport. Abinka da harkar kuɗi, an gama musu duk abinda ya dace cikin ƙanƙanin lokaci saura jiran result kawai.
Kowa ya kalla Abba da Ammah a wannan yinin yasan suna cikin farin ciki mai tsanani, sai dai ba’a san kona minene ba. Dan hatta su aunty Bilkisu Ammah bata sanarmawa ba sai Gwaggo Sa’adah kawai saboda ita ɗin sirrinta ce, ai ko sai ga Gwaggo Sa’adah itama da hawayen farin ciki, da yammacin nan bata iya haƙuri ba sai da tazo gidan taga hoton jariri. Ita Umma dama bata gidan, tana can wajan biɗar baƙar tambayarta. Bata dawo gidan ba sai yamma lis. Sannan su Abba har sun dawo da ga fitar da sukai. Amma sai Mama ta sameta har ɗaki da gulmar wai yau surukan Smart sunzo gidan, kuma sun fita da su Ammah tana ganinfa akwai matsala. Sai dai kuma su Ammah tunda suka dawo sai faman washe haƙora sukeyi da ga ita har Abba. Dan Ammah harda su sadaka tayima yaran anguwa da maraicen nan. Sosai wannan magana ta tsayama Umma a rai, dan sabon malaminta da sukaje wajensa a yau ɗin nan dama ya sanar musu akwai wani babban al’amarin farin ciki da ya samu Smart ɗin, sai dai ya gagara gane ko minene anata nuna masa haske kawai babu komai. Amma taje gida duk abinda taji gobe ta dawo. Sai kuma gashi da ga dawowar tata taji sabon zance a wajen Mama macijin sari kanoƙe. Cikin matsanancin tashin hankali tai kiran Hajiya Naqiba suka tattauna, sai dai duk iya hasashensu sun kasa canko komai ilai tunanin ko Lulu zata dawo ne. Amma dai sun tsaida matsaya Umma taje ta zunguri Abbah akan batun. Wannan shawarar ta rika, dan haka a daren dan ta kasa nutsuwa ta nufi ɗakin Abba da nufin su gaisa tunda yau bata yini a gida ba. Lokacin Ammah ta baro ɗakin da kwanikan da yaci abincin dare. Zaman dirshen Umma tai suna hira da Abba bayan sun gama gaisawa, inda cikin salon makirci ta fara zungurarsa da batun Smart duk da bata fito fili ta ambaci sunansa ba. Dai-dai nan ALLAH ya kawo Ammah, tsaf ta fahimci manufar Umman, dan haka ta zauna a falon dan tasan halin maza wani lokacin sai addu’a musamman idan suka haɗu da makirar bace. Zuwan Ammah baima Ummah daɗi ba sam, dan tasan halin Ammah da shegen tsartar tsiya. Dan haka ta tashi ta fice cikin jin takaici tana ƙwafa. Da kallo kawai Ammah ta bita tana girgiza kai, inda bayan sunbar falon zuwa makwanci cikin hikima ta sake nusar da Abba muhimmancin ɓoye al’amarin haihuwar nan kamar yanda su Daddy suka roƙa, Abba ya fahimceta sosai, sannan bai zargi tayi hakane saboda Umma ba dan Ammah mace ce mai hikima da dattako. Kawai dai dan ba fitinanniya bace da lallai su Ummah sun kaɗe a gidan nan…..
*_UK LONDON_*
Sosai yake cikin farin ciki mara misali, yaso yay amfani da ɗan hutun da suka samu yazo gida Nigeria sai dai hakan na neman gagara saboda kara kainar da manyan clubs keyi akan al’amarin sa. Duk da dai abin bai fito fili duniya ta fahimta ba Coach ɗin sa shi da komai ke a garesa da Manager ɗin sa Uncle Yousuf suka ce ya dakata dai aga inda wasan zai tsaya. Wannan shine dalilinsa na haƙura da zuwa gida Nigeria ya cigaba da bama kansa hutu a gidansa. Sai motsa jiki da yakan fita da ɗan yawata gari idan yaso a wasu lokutan.
Yau ma yana gida kwance a binsa, sai dai idanunsa biyu yana zaune ne a falo idonsa a tv yana kallo sai popcorn da ke gefensa yana jefa ɗaya-ɗaya a baki (Su Smart an zama an gayu😂😜🚴). Gift da wani ɗan lutin yaro ke buɗewa a film ɗin yana tsalle ya sashi tunawa da saƙon da aka kawo masa jiya da yamma da ko buɗewa bai yi ba. Hasalima tunda ya amsa ya ɗora shi a inda takalmansa suke farkon shigowa falon bai sake bi ta kai ba dan yasan dai bai wuce irin gift da fans nasa kan kawo bane takanas garesa. Miƙewa yay a hankali zuwa corridor ɗin farkon shigowa, saƙon na’a inda ya barsa, dan haka ya ɗakko ya koma falon. Kiran Ahmad da ya samu na shigo masa a waya ya sashi ajiyewa ya ɗauki wayar. Kamar yanda suka saba cikin barkwanci suka gaisa da juna, Ahmad ya sake masa congratulations da tabbatar masa da next month yana tafe fa, dan yana son yazo ya masa hutu. Sun ɗan ja lokaci suna hirarsu cike da nishaɗi da ƙaunar juna kafin suyi sallama. Har ya sake shagala da batun saƙo zai koma ya kwanta sai kuma idonsa ya sake sauka a kai. Tashi yay ya jawo brown envelope ɗin ya buɗe tare da zira hannu a ciki ya zaro kayan ciki. Hotuna ne har guda biyar, sai flash drive guda ɗaya da kwalin haɗaɗɗen turare designer ɗan ƙarami sai masifar ƙamshi. Hotunan dake a kife ya fara ƙoƙarin dubawa, haka kawai ƙirjinsa na wani irin harbawa, saukar idanunsa akan hoton farkon sai da zuciyarsa ta motsa da ƙarfin gaske a cikin ƙirjinsa. Tsigar jikinsa ta shiga wani irin ya mutsawa. Tabbas wannan duk wanda ya sanshi a jinjiri yaga hoton nan yasan shine, sai dai shi da kansa yasan bashi ɗin bane ba saboda dalilai da yawa idan aka auna, musamman yanayin hoton da inda aka ɗauki hoton da suturar jikin yaron duk da yasan duk za’a iya editing, cikin tsumar jiki yaje ga hoto na biyu, nan ma dai yaron ne again. Hoto na uku ma haka, sai a na huɗu ne fuskar da bazai taɓa mantawa ba ko’a magagin barci ce rungume da yaron a saman ƙirjinta tana da ga kwance jikinta ɗaure da zanin asibiti, ga ƙarin ruwa a hannunta, sai rabin jikin mace da ke gefenta ta dafe mata yaron sai dai ba’a ganin fuskarta. Hajijiyar da yaji tana neman kwasarsa ta sashi komawa a kujerar daɓar ya zauna. Da ƙyar harshensa ya iya motsawa wajen furta, “Mawaddat da jariri ta yaya?”. (Ta yanda kowa ke samu mana) zuciyarsa ta bashi amsa kai tsaye. Rawa lips ɗinsa ya shigayi da illahirin jikinsa, dan sam ya kasa furta abinda ma yake son furtawar. A dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Da ƙyar ya iya juyawa ya duba wayar. Uncle Yousuf ya gani ɓaro-ɓaro. Cikin zallo kuwa ya caɓi wayar dan gani yake kamar mafitace ALLAH ya kawo masa na warwarewa da ga ruɗanin da ke neman zauta masa ƙwaƙwalwa tamkar a mafarki…
“Congratuletions angon ƙarni”.
Kalmar farko da Uncle Yousuf ya furta masa bayan sallama da ta daki ƙirjinsa. Da ƙyar ya iya furta, “Angon ƙarni Uncle?”.
“Yes of course Son. Ka zama Daddy mana, na kuma san saƙon yaya zuwa yanzu ya isa zuwa gareka sai dai in baka duba ba”.
Wasu irin hawaye ne da masifar gudu suka shiga biyo kumatun Smart. Muryarsa na rawa ya furta, “Uncle kana nufin da gaske ne Mawaddat nada ciki kuma ta haihu? Sannan kun san inda take”. Uncle Yousuf da ke murmushi da ga can ya ce, “Hakane Aliyu, ALLAH ya azurta Mawaddat da samun ciki, kuma an mata cs a jiya an ciro yaro mai kama da kai, sai dai muma da ga baya duk muka san hakan. Tsaf ya kwashe labarin su Dada dana Daddy ya sanar masa har yunƙurin zubar da ciki bai ɓoye masa komai ba. Ya ɗora da bashi haƙurin cewar an ɓoye masa maganar ciki ne a lokacin dan kar a tada masa hankali tunda basu san takamaiman ina Mawaddat take ba a lokacin ɗin sai Daddy shi kuma ya ɓoye ne dan tsaron lafiyarsu, tare da manufarsu ta son a ɓoye yanzu har sai an wajiga rayuwar Alh. Sulaiman. Ɗari bisa ɗari Smart ya yarda da wannan shirin, yayinda zuciyarsa ke masa kai-kawo akan sakkowar Daddy da sauri haka. Sai dai baicema Uncle Yousuf komai game da wannan ba. Ya daiyi murmushi da cema Uncle Yousuf batun Alh. Sulaiman wannan wasan nashi ne. Jin wai Lulu kuma tace a sakama yaron sunansa ya sakashi sake yin murmushi da lumshe idanunsa, dan harga ALLAH baiyi tunanin hakan daga gareta ba. Irin farin cikin da Smart ke ciki yau da banne a rayuwarsa, dan ko randa sukaci nasarar cin ƙwallon nan baya jin farin cikin sa yakai koda kwatar haka. Ya kira Abbah da Ammah cikin zumuɗi, inda suma suketa tsokanarsa cike da farin ciki tare da masa barka da arziƙi. Ya ce, “Ammah shiyyasa kullum sai naita mafarkin yara, ashe takwarana yana isarmin da saƙon ya kusa zuwa duniya ne”. Dariya Ammah keyi, cikin tsokanarsa ta ce, “Oh ni Hydar ko irin ƴar kunyar ɗan farin nan babu ma?”. Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da rufe fuskarsa da fillon kujera kamar yana gabanta, ya ce, “Ammah sai anjima to nayi shiru”. Itama dariyar ta shiga yi masa sosai cike da jin shauƙi da tarin ƙaunar tilon ɗan nata namiji……..✍️
_🚴🚴🚴Yau fa dangin Smart an cika mu da iyayi, to ɗa dai bara mu bada ba ehe dan zufarmu ce😏_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*