Furar 2Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 17

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣

______________

*3 DAYS CLASS*

Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni

Class ze fara ranar jumaa insha Allah

WhatsApp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA

WhatsApp 08144147273

_________________

……..Bayan anyi gaishe-gaishe da taya juna murnar samun lafiyar Baban kai tsaye ya jehoma Uncle Yousuf tambaya kamar jiya. Uncle Yousuf da tunda suka shigo bai kalli inda Daddy yake ba, ko gaisuwa sama-sama yay masa kansa tsaye ya fayyace komai kamar yanda ya faɗama Baba Garkon a dare jiya. Jikin Dada tuni ya jiƙe da zufa, amma tsabar makirci sai ta fashe da kuka wai Uncle Yousuf ɗin ya haɗa mata harda sheri dan ya baƙantata kawai. Ita koda ta ɗakko Lulu dan bata da lafiya ne ta ɗakkota…..” tsawa Baba Garko ya daka mata da cewar, “Yima mutane shiru mutuniyar banza da kullum bata sanin ta girma a rayuwarta. Bance miki ki fita cikin al’amarin auren yaran nan ba tun farko? Rashin lafiya shi mijin nata ne yay dake bazai iya kula da ita ba? Ko kin fishi sanin abinda ya dace yayi akan iyalinsa?!.”.
“Ka gaya min. Kuma ni naga shi ba wani kuɗin da zai iya kulane da ita ga resa ba”.
“Mtsoww zancen banza kenan. To raini ne da son tozarta ni da nunama duniya ban isa ba ya saki zuwa ki ɗakko yarinya a ɗakin mijinta har ki kaita wata ƙasa?”.
“Bafa haka bane sam Alhaji ka fahimceni, yarinyarfa da bakinta ta fayyace min gaskiyar manufar auren …….” nanta ta kwashe komai da komai da Lulu ta sanar mata ta faɗa musu. Karo na farko Uncle Yousuf yay murmushi, yayinda Uncle Muneer ɗanta dake bima Alh. Sulaiman cikin son danne ɓacin ransa da taushin murya kamar yanda ya saba girmamata matsayin mahaifiya ya ce, “Amma Dada duk da a ta gaya miki haka a matsayinmu na wanda muka fita hankali nazata zamu taimaka mata ne ta hanyar kwantar mata da hankali ta haƙura ta zauna a ɗakin mijinta dan yaron nan mutumin kirki ne da duk wasu iyaye na ƙwarai zasu so haɗa zuri’a da shi”.
Harara Dada ta ɓalla masa, yayinda Baba garko ya amshe da “A’a ina zatayi haka ga matar ƙaruna ƴar ƙaruna kuma da hankali bai gama game mata jini ba, ai Mawaddat ɗin ma ta fiki hankali. Wai Hajarah mi kika ɗauki rayuwa ne? Mi kika ɗauki dukiya ne? A zatonki dan ALLAH ya yomu a haka mun zama mafifitane a cikin mutane har a wajensa? Kamar yanda talauci yake jarabawa itama dukiyar da kike gani jarabawace. A wani fanin ma babbar fitina ce ga bawa. Shekara nawa ya rage miki a wannan duniyar da har kike jin wai dukiya har zata cigaba da zame miki abin tinƙaho. Ba tonon silili ba naga ai kema ɗiyar talakawance amma na aure ki, ƙarewa ma mahaifinki masinja yake ga mahaifina mutuncinsa da sanin Yakamata yasa mahaifina cewa na auri ƴarsa. Ban yi musu ba kuma na aureki nake zaune da ke har tsawon shekarun nan matsayin ke kaɗai matata Ashe albasa batai halin ruwa ba….”
Sosai Dada ta daburce dajin kalaman mijin nata irin wanda koda kwatance bai taɓa yinsu gareta ba tun aurensu. Su kansu yaran sai da sukaji shock su dukansu. Dan basu taɓa sanin wannan tarihin ba kasancewar a sanin da sukaima mahaifin mahaifiyar tasu hannunsa a jiƙe yake, sosai Baba kema Dada cin mutunci da ya sakata kuka rurus, agaban ƴaƴan nata ya kuma turketa saita gaya masa inda suka kai Lulu koya bata mamaki da hukuncin da bata taɓa zato ba. Ganinfa ruwa ya ƙarema ɗan kada dole Dada ta fayyace komai game da kai Lulu Canada ita da Alh. Sulaiman harma da yunƙurin zubar mata da ciki da sukayi amma bai fitaba sai da ga bayan nan kuma suka gane hakan, sai kuma kiran da Sulaiman yay mata a jiya cewar ya nema su Lulu ya rasa wai wani ya sacesu, amma yasa ƴan sanda na bincike. A yau da safe kuma yake turo mata text message akan yana zargin Yousuf ne da Smart. Da matuƙar mamaki Uncle Yousuf ke kallonta cikin nuna kansa ya ce, “Ni Yousuf ɗin ko wa?”.
“Inba kaiba waye Yousuf anan, munafuki algungumi. Ai dama kana biye damu tunda muka ɗauke ta kai da shegen yaron nan mara kunya dan bakinku ɗaya ne dama. Dan haka saiku fito da ita tunda ankai ga yanda kake so”.
Tuni fa falo ya hargitse, dan sai kawuna kuma suka nema rabuwa. Yayinda Daddy da tunda ya shigo falon baice komai ba ya zuba musu ido kawai. Hakama Baba Garko. Cikin ɓacin ran yin shirun Daddy Uncle Yousuf ya tashi ya fice a falon dan zuciyar ƴan maza ta motsa da gaske a yau. Ganin bazasuyi shiru ba Baba Garko ya katse hayaniyar tasu da faɗin, “Hajarah kije na sakeki saki biyu, kuma ki barmin gidana a yau har sai kun maido Mawaddat idan da yiwuwar ki dawo sai ki dawo”.
Waɗan nan kalmomi masu dukan zukata na Baba Garko ne suka saka falon yin tsitt, yayinda ya miƙe abinda ya shige cikin bedroom ko waiwayen su bai yi ba. Dada kam da taji kanta na juya mata sai ganinta kawai sukai a ƙasa babu numfashi. Cikin tashin hankali sukai kanta. Duk hayaniyar da ake Baba na jinsu amma har suka kwasheta zuwa asibiti bai ki leƙo ba.
Wannan shine sanadin kwanciya Dada a asibiti na tsawon sati biyu tana jiyya, dan hawan jininta ne yay masifar motsawa. Koda ta samu sauƙi kuma Baba yace duk wanda ya kawo masa ita gida a cikin ƴaƴan nasa wlhy sai ya kwashe masa albarka. Duk kuma wanda yazo yay masa maganarta a gidan nan ma sai ya kwashe masa albarka. Wannan ya saka yaran tsorata matuƙa dan sun san wanene mahaifin nasu akan zuciya, balle yanzu ya sake birkice musu irin yanda basu taɓa gani ba. Gashi sunata kiran Alh. Sulaiman dake matsayin babba garesu kuma silar wannan tashin hankali amma sam sun gagara samunsa. Dole dai aka wuce da Dada gidan Uncle Muneer aka gyara mata sashen baƙi….

*_CANADA_*

Labarin Ummita da Lulu taji ya ƙara musu shaƙuwa matuƙa, yayinda Lulu ta fara tunanin buɗe ƙungiya domin taimakon yara marasa zuwa makaranta dan al’amarin yaron nan data taɓa amsar Number a wajensa bisa titi har yanzu yana ranta bata manta ba, tana jin babu daɗi kuma da bata sami ziyartarsa ba. Ƙungiyar zata riƙe abubuwa uku ne. Karatun yara da rashin galihu ya hanasu yi, sai harkar fyaɗe da kuma shaye-shaye. Ɗari bisa ɗari Ummita ta bama Lulu goyen baya game da wannan ƙyaƙyƙyawan ƙudiri nata. Dan haka suka hau tsare-tsaren su kamar waɗanda akacema gobe zasu bar wannan wajen. Lulu ta cigaba da rainon ciki yayinda Usman ke zuwa dubata da bata magungunan ƙarin lafiya ita da abinda ke cikinta. Alh. Sulaiman kuwa na tunanin allurar gubar da zata ruɓar da tayin cikin Usman ke mata. Akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su Lulu da Usman, dan shi ke kawo musu duk wasu bayanai akan Alh. Sulaiman, sai dai a rubuce yake basu, a zahiri kam babu wata alamar dake nuna ko kallon arziƙi sunaima junansu. A haka a haka dai har ALLAH ya kai cikin Lulu haihuwa. Inda ta koma zama da ƙyar tashi da ƙyar. Gaba ɗaya ta canja kamanni saboda kumburin da taɗan yi, dan ma Ummita baiwar ALLAH tsaye take a kanta yanda ya kamata, bata gajiya da yima Lulu da abinda ke cikinta addu’a. Ga Usman na iya bakin ƙoƙarin sa akan komai nasu ciki harda fara shirya musu hanyar guduwa daga tsibirin. Lulu bata taɓa kiran lambar kowa ba tun sanda ta gwada Alh. Sulaiman ya ɗaga. Tunda aka kawosu gidan bai zo ba ko sau ɗaya, hakan ya sasu fahimtar kodai duk cikin takune ko kuma baya ƙasar ne…..

*_UK (LONDON)_*

A ɓangaren Smart wasannin link sun cigaba da tafiya cike da nasarori harma da ƙalubale, inda ALLAH ya ɗaga darajar team ɗin su suka ƙare da maki tamanin da shida, Smart ya jefa ƙwallaye ashirin da bakwai. Hakan ya sashi zama best player na wannan kakar wasa ta bana a ƙasar England, inda ya samu ƙyautar takalmin zinare, team ɗin su kuma ya samu damar shiga babbar gasar premier link na england. A randa su Smart sukai wasan ƙarshe ne ya kasance dai-dai da randa Lulu ta wayi gari da naƙuda. Hankali tashe Ummita tai kiran layin Alh. Sulaiman, amma sai ya amsa mata a daƙile cikin halin ko’in kula. Sai da yaga Lulu na neman rasa ranta sannan yay kiran Usman akan yazo ya dubata, a kallo ɗaya Usman da yay mata ya tabbatar da Alh. Sulaiman cewar dole fa akai Lulu asibiti, dan theatre ya kamata ai mata tilas. Da farko Alhaji Sulaiman ya ɗauki abun babu wasa, sai da fuskanci zai iya rasa damarsa sannan ya amince aka a wuce da Lulu asibiti can cikin gari dan shi tunaninsa mutuwar ɗan a ciki ta jawo hakan. Dai-dai ana shiga da Lulu ɗakin theatre Smart da gabansa keta faduwa ya zira ƙwallo a minti ɗayan ƙarshe da ya rage a tashi wasan. A take garin ya ɗauki ihu, yayinda ya kai ƙasa yay sujida hawayen farin ciki na ziraro masa. Gaba ɗaya teammate ɗinsa sukazo kansa aka rungume juna, suna mai ɗunbin farin cikin shiga a jerin manyan team na duniya da zasu buga primier link kenan, abinda ko’a mafarki ba’a taba kawo musu ba. Amma Alhamdullah sai gashi a dalilin ɗan baiwa kamar yanda suka sakama Smart sun shigo cikin jerin masu nasara. Sosai London City take a hargitse yau anata selebration, su Smart na cikin wata irin doguwar mota mai masifar ƙyau da ɗaukar hankali hannunsu rike da kofin da suka ci suna ɗagawa masoya. Wasu a cikin teammate nashi har cire riguna sukai suna jefama fans. Shi kam dai murmushin sa yake mai ƙayatarwa cike da nutsuwa yana mai ɗaga hannayensa duk biyu, yayinda idan idonsa yakai kan yara yakan ma hannun nasa kiss ya hura musu, sai kaga yaran na maido masa da kisa ɗin suma, jin farin cikin yake tamkar ya zarce na cin ƙwallo a zuciyarsa yau, dan fargabar ɗazun nan da faɗuwar gaba duk ta gudu saboda addu’oin da yake ta yi. Haka suka dinga zagaye cikin London City a wannan mota, inda ta ko ina suka gitta imasoyane ƴaƴa da iyaye harma da kakanni da suka fito domin kallonsu. Sunan Smart Mawashi yasha kira a wannan rana tamkar zai ƙare duk da yanda suke kiran Mawashin abin dariya, sai yaji har hawaye na cika masa ido da wannan al’amari da rahama ta UBANGIJI. A rayuwa ai babbar rahamace ma kaga mutum ɗan uwanka na nuna maka irin soyayya balle kowa yasan Bature akan ƙyamar baƙin fata a zahirance.
Wannan fa nasara ta Smart ta saka hankalin manyan club na ƙasashen turai gaba ɗaya irinsu Italy, Spain, Germany France etc… dawo wa kansa, yayinda aketa kaikawo da cecekuce akan al’amarin yaron a wannan yini, kowacce kafar yaɗa labarai kaje a ƙasar ta England musamman a fanin ƙwallon ƙafa zancen kenan dai Smart Mawashi, Smart Mawashi.. Al’amarin kamar busa usir na alƙalin wasa. Cikin ƙanƙanƙanin lokaci manyan clubs ɗin suka fara ƙwaɗayin nuna zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa……..✍️

_To insha ALLAHU dai mun kusa zuwa gaɓar da komai zai cigaba da tafiya a buɗe, ina zazu ɗin nan ne ɗan can mu samesa yanda muke so🥱 dan nasan kunfi kauri acan😜🚴🚴🚴_

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button