Furar Danko Complete Hausa Novel

Furar Danko 81

Sponsored Links

 

81

 

………Washe gari gidansu ya wuce bayan ya sauketa, anan ne yake samun Abba da Ammah da batun shifa yana zargin Mawaddat ce tayi koma miye. Dan an sanar masa taje gidan a ranar monday. Mamaki sukaitayi suma da tunanin to mita faɗa ma maman Sa’id da har ta risina haka da sauri. A gefe kuma ƙaunar yarinyar na sake shigar musu zukata. Kamar yanda akace sati ɗaya cikin satin Hawwah ta fara shirin komawa sabon gidanta danƙarere. Hankalin Umma ya sake tashi, da bin ƙwanƙwanto ta gano Lulu ce tamayi koma miye har komai ya dai-daita. Hankali a tashe ta nufi gidan Hajiya Naqiba ƙawarta. Acan suka baje faifain zagin Ammah da bata san sunayi ba da Ƴaƴanta suna neman mafita dan abubuwa fa nata faman kufce musu a hannu, sai dai gaba ɗaya hankalinsu da mugayen ƙudirinsu sun tattara ne ga Lulu yanzu. Dan sun fahimci shigowarta gidan abubuwa da yawa ke neman taɓarɓarewa. Duk da su basu fahimci cewar asirin jikin Smart ma ya gama warwarewa gaba ɗaya ba. Ga aikin Malam na-zuru yaƙi yiwuwa, dan kayan Lulu da Smart dai sun gagara ɗakkuwa. Hajiya Naqiba ce cikin dogon tunani ta ce, “Aminiya anya bazamu canja taku ba?”.

 

“Kamarya? Fito kimun dalla-dalla, kin san bana son kwana-kwana fa”.

 

“Ina nufin ba asiri bane kaɗai yanzu ya kamata musa gaba dole mu haɗa da makirci da kissa. Kamar dai yanda nai akan shegun yaran can na baƙar dagar tawa.”

 

“In dai wannan ne ai mun jima munayi Aminiya, yanzu ko ita akan wannan shegiyar da zata koma Hawwah ai kinga sai da muka haɗa da makirci waccan shegiyar da bamu san mitaje tayi ba ta ɓata mana komai.”

 

“Kwantar da hankalinki karki damu, murnarsu zata koma ciki ne. Yanzu mu fara kai wannan baƙuwar hauren ƙasa tukunna dai. Dan wannan ƴar iskar amaryar da aka jajubo muku na fahimci da ƙarfinta tazo, gashi yarinyar nada ilimi fiye da tunaninki kuma goyon turai, ga kuɗi a gida, kuɗi a mota, kuɗi a Office, kuɗi a banki. Idan mukai sake fa komai zai koma wanwarne, ni ko da kishiya da yaƴanta su ji daɗin duniya ko komawa sama dani gara ace kowa ya mutu a ƙasar, ke ama busa ƙaho”.

 

Dariya Umma tayi da faɗin, “Hajjaju ke bala’i ce ai, shiyyasa nake sake tausayin Matar gidan nan naki. Yanzu ke miye shawararki?”.

 

“Dole ne muyi bincike akan yarinyar mu samo wanda zamu shiga jikinsa nata mu mata rugu-rugu”.

 

“Tab babbar magana ta yaya kenan? Bayan kin san daga wane gida ta fito, gate ɗin gidan su ma taɓa shi ba masifa bane balle shiga gidan”.

 

“Kwantar min da hankalinki. Akwai matar nan mai min ƙunshi ranar ana labarin dukiyar da aka zubar a auren ita yarinyar da aka kai gidanku take cewa ai ita taga zahiri dan itace kema matar Alhaji Garko ƙunshi shekaru kusan shidda kenan, shiyyasa tasan abubuwa da yawa a gidan nan ko shagalin bikin nan duk akan idonsu akai komai. Ita kanta taci rabonta dan tayi ƙunshi sosai a gidan, sai dai ta fahimci kamar matar Alhaji Garko bata son auren fin ƙarfinta akayi, yarinyar da ɗan uwanta aka saka mata biki lokaci guda ta birkice wai sai yaron gidanku”.

 

“Kai haba da gaske wai? Anya ba asiri suka mata ba ma kuwa”.

 

“Wlhy haka tace, babu abinda Hafsatu bazata iyaba wlhy, wama ya sani. Shiyyasa nake ganin ya kamata muje gidan Alhaji Garko mu kunnowa Hafsatu wutar da zata ƙoneta ƙurmus har ƴaƴan nata a wannan karon. Ba suna murna sun samu ɗiyar biloniya ba. Zasuci ubansu ne”.

 

Dariya suka kwashe da ita suna tafawa……

 

_____________★★

 

Kwanaki sun ƙara shiɗawa, dan a lissafin Lulu dai next week ne rabuwarsu da Smart. A week ɗin daya wuce ya kaita gidansu da gidan Uncle Yousuf, daga nan ta samu ƙafar zuwa duk bayan kwana biyu haka idan ta fita aiki takan leƙasu duk da dai daga Daddy har Uncle Yousuf ɗin ma dai sunyi tafiya basa ƙasar ma. A ranta a duk sanda ta ƙiyasta tana jin farin cikin komawarta free dan ta fara jin ƙosawa da tsakurarsa musamman ta saka hijjabi da tafi cimata zuciya da rai fiye da komai. Sai dai wani sashe na zuciyar tata na mata kamar babu daɗi musamman idan ta tuna Ammah da ƴan uwansa. Takan faɗa dogon nazari akan hakan, amma idan taje duba jikin kakanta Alhaji Garko da har yanzu dai babu lafiya suna ma shirin fita da shi ƙasar ne duk da yana turjewa sai da Dada taita mata fanfo da zugeta. Wani lokacin Lulun kan nutsu ta saurareta, wani lokacin kuma tace “Kai Dada dan ALLAH wai miye matsalarki da Aliyu ne? Miyay miki?”. Dadan kan zazzageta wani lokacin ko balbaleta da faɗa dan masifaffiyar mata ce. Wannan faɗan da take takura mata da shi yasa kwana biyu Lulu bataje gidan ba, sai dai tai kira a waya taji yaya jikinsa. Hakan sai ya fara damun Dada, dan a ganinta wani asirin Smart ya sake tafkawa Lulu…

 

A ranar Juma’a da Lulu ke cika kwanaki uku rabonta da zuwa gidan Smart ya wuce Legos, Maryam da Asma’u aka kawo mata su tayata kwana, sai Mubarak da zaizo da dare, sai su Afrah suma da taje da kanta ta ɗebo. Nan fa shafta ta buɗe. Wucewar su Maryam ya ƙara zafar Umma, tai shiri ta nufi gidan aminiyarta Hajiya Naqiba rai ɓace. Bayan ta gama labarta mata Hajiya Naqiba tace tashi muje yau ayita ta ƙare. Sun je gidan mai ƙunshi da tace zatai musu rakkiya. Daga can suka tafi gidan Alhaji Garko. Sosai Umma ta sake girgiza da dukiyar waɗan nan mutane, nan fa zuciyarta ta ƙara ƙaimi wajen ƙulle-ƙulle na ganin auren Smart da Lulu ya gundile. Sunyi zama fin na awa ɗaya kafin hamshaƙiyar tsohuwa mai ji da kuɗi da hutu ta fito cikin isa da izzarta. Ai sai su Umma sukai saƙale suna kallon ikon ALLAH, dan Dada ta tsufa sosai kawai dai abinka da jin daɗi ne. Cikin girmamawa suka gaisheta tana amsa musu da ƙyar a yamutse. Mai ƙunshi ta mata bayani duk da dama ta fara sanar matan. Amma tsohuwar nan saita dubi su Umma a watse cike da isa ta ce, “Ku tabbatar duk abinda zai fito bakinki bazai zama wuƙar yankaku ba, dan bana son munafunci ni da kuke gani na anan”.

 

Muryar Umma na rawa ta ce, “Wlhy Hajiya a duk abinda mukazo miki da shi nan babu munafunci. Yaron nan asiri yayma ƴarku. Idan kuma baki yarda ba kisa malamai su bincika muku zaki fahimci gaskiyarmu. Amma kuyi da sauri dan yanzu haka yayi tafiya wai Niger da abokinsa kin san kuma yanda suka iya asiri bana raba ɗayan biyu wani bala’in zai sake haɗo muku (😂 Niger akacema su Umma Smart ya tafi raka Ahmad sayen shanu).

 

Mai ƙunshi da yake itama makirar mace ce tana kuma son sake samun fada a wajen Hajiya Dada sai ta sake taƙarƙarewa tana taya su Umma. Harda cewa zata raka Dada wajen wani malami a duba musu ɗan uwanta ne a Zuru yake. Amma batai maganar hakan ba sai da su Umma suka fito bayan an sallamesu. Hankalin Dada ya tashi, dan haka ta sallami su Umma tace mai ƙunshi tazo ta sameta gobe idan ALLAH ya kaimu bayan an wuce da Alhaji Garko dan zasuyi gaba ƙasar London ita sai nan da sati ɗaya zatabi bayansu. Cike da farin ciki su Umma suka fito da ƙyautar naira dubu ɗari kowa hansin-hansin. Mai ƙunshi kuwa ma basu san mi aka bata ba. Ta kumace dole su cire mata kasonta a ciki dan bazata rakosu a banza ba. Da ƙyar suka bata goma-goma suna ƙunƙuni. Tace oho dai shegu ai ni kunzo min da hanyar samun kuɗi, naci a wajenku, naci a wajenta, naci a wajen malamin da kukace aje.

 

Washe garin asabar aka wuce da Alhaji Sufi Garko ƙasar London dan likitoci anan gida Nigeria sun tabbatar poising ɗinsa akayi. Ba’a fahimci hakan ba kuma sai a tsakanin kwana biyun nan da gubar ta bayyana kanta, dan sun bashi wadda bata bayyana kanta da wuri har sai tayima jiki illa ne. Duk da wannan tashin hankalin da ake ciki hankalin Dada nakan Lulu da itama dai yau tazo gidan har da su Asma’u da su Afrah. Sai dai taƙi yarda ko sau ɗaya su zauna da Dada har sanda ambulance ta ɗauki Baba itama sai taja ƴan rakkiyarta suka bisu har airport. Basu baro ba sai da jirgin da za’a ɗauke sa a ciki shi kaɗai sai yaransa maza biyu ƙannen Alh Sulaiman da zasuyi gaba ya tashi. Kowa ya bisu da addu’a kafin yaje. Suna baro airport ɗin jirgin da ya ɗakko Tajuddeen da Alhaji Sulaiman (Tsule🤣) ya sauka shi kuma. Ya samu sauƙi sosai koma muce a zahiri ya warke, sai dai a zuciya kam babu abinda ya ragu na soyayyar da yakema Lulu. Ya samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyane kawai bisa alƙawarin da mahaifinsa yay masa na sai ya mallaka masa Mawaddat ya kwantar da hankalinsa. Wannan dalili ne ya sashi jin ƙwarin gwiwar biyosa suka dawo. Manyan aminansa na yanzu duk da dama can aminan nasa ne matsaloli suka rabasu Alhaji Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau ne sukaje tarbarsu. Dan kaf Family na Garko babu wanda yasan da dawowar tasu a yau…….✍️

 

(🤔Tofa! Alhaji Sufi Garko ya tafi jiyya a dalilin poising nashi da akace anyi. Alhaji Sulaiman Sufi Garko ya dawo tare da ɗansa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko daya tashi a jiyyar soyayya babu wani damuwa tattare da al’amarin su. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa? Humm kumu dai je zuwa to🚴).

Leave a Reply

Back to top button