Bakar Ayah Book 2 Page 55-56
Page 🖤 55••56🖤
Su ukune yanzu kacal a falon,daga Jabeer wanda yake kan wheelchair sai haidar dayake ta wasa da motocinsa,bombee kuma tana kitchen,lokaci lokaci takan zo ta wucesu a falon.
Idonsa akan tv yake inda ake labarai,sai haidar yayi ƙarane ya juya ya kalleshi,ko kuma in bombee zata wuce yabita da kallo.
Duk sanda zata wuce idan suka haÉ—a ido murmushi take sakar masa,dan har cikin ranta tanajin daÉ—i yanda yake samun lafiya akan lokaci..
Yanzu har yana iya laluransa a banÉ—aki ya fito batareda taimakonta ba,duk da cewar har yanxu babi wani yanayi dayake nuna wa a fuskarsa bayan kallo.
Mutane gidan kusan kaff a sashenta suke yini idan ka É—auke Hajiyah Zeenah da su Lailah sai kuma iya sayyada,sai yamma tayi kowa ya kama gabansa.
Gidan data siya inda su innayi suka zauna yanzu ta tamƙawa baban ta shi. Sjn samu kuma ya karba ya zauna bayan an kai ruwa rana.
Yana cewa da yarasa yaransa yanzu gashi allah yayi masa kyauta da guda huÉ—u russ mata,wato hadda su hilyan.
Ya riƙesu kuma gam tamkar mahaifinsu lokacin dayaji labarin rayuwarsu,inna Danejo ta warke yanzu kaman ba itaba.
Yau ma kamar kullum É—in dare yayi kowa ya tafi saisu kaÉ—ai a gidan.
Su Jawaheer ma tun lokacin daya dawo daga asibiti ta koresu,dan karma ya gansu hankalin sa ya tashi.
Abincin ta kawo ta ajiye akan dinning,haidar yana gani ya jefar da abin wasan ya taho da tafiyarsa irinta yara.
Dariya bombee tayi tareda cewa.
“Tun É—azu nake magana kaÆ™i kulani saida kaga abuna koh?”
Zaunarshi tayi akan cinyarta tareda jawowa kujerar Jabeer ma ya matso kusada itah.
Ɗebowa tayi a cokali ta miƙawa Jabeer a baki,haidar yana gani yafara darun yara yana kuka,ala dole shine farko,dan hakan har yazamar mata tamkar jiki a iya sati biyu datayi tanayi.
Kaiwa bakinsa tayi tasakamasa dan dama nasanne.
Tana cikin hakanne tatsaya cakk da abinda take ganin bakin Jabeer ya na motsawa,da alama murmushi yakeson yiwa yaron.
Ita tana kallonsa shikuma yana kallon yaron dayake kan cinyarta.
Batace komai ba haka ta gama basu abincin kafin ta hau aikinta na Company,wanda É—azu khaleel ya kawo mata da zai wuce,dan yau batasamu zuwa wajen aikinba.
Can wajen misalin sha É—aya na dare ta rufe system tana shirin kwanciya sai taji kaman alamar dirowar mutum ta bayan windownsu.
Kallon Jabeer tayi wanda yake kwnace da haidar a gabansa,sai kuma fili a gabansu wajen dazata kwanta.
Bakin windown ta nufah da sanɗa tareda leƙawa..
Duk da cewar akwai duhun dare,amma hakan bai hanata ganin wulgawar mutum ba da baƙin kaya.
Saurin dawowa tayi ta baya bayan ta rufe windown..wind
Zuwa da dawowa take a ɗakin na wasu daƙiƙu,don tarasa ma mai zatayi.
Kasancewar bata kashe hasken É—akin ba tana kallon Jabeer wanda shima yake kallonnata,da alama yaji motsi kenan.
Wajen wardrop ɗin ta ta nufah ta ɗauko dogon wando ta saka,doguwar rigar baccin dake jikinta tayi saurin cirewa tasaka ƙaramar riga..
Ribbon ta É—auka ta É—aure gashinta ta baya tareda komawa bakin gadon ta zauna.
Saitawa tayi a bakin ƙofar ɗakin tana jiran shigowar wani,dan zuwa yanzu tana jiyo muryarsu a kusada ɗakinsu..
Shidai Jabeer yana nan kwance yana kallonta.
Bankaɗo ƙofar sukayi da ƙarfi,maza ne guda uku ƙarti dasu sun sha baƙaƙen kaya,hannun kowannensu ɗauke da pistol ƙarama.
Kallon ƙananan shegu bombee tayi musu amma kuma bata nuna a fuskarta ba,saima tashi tsaye da tayi jikinta yana rawa,alamar batayi zaton shigowarsu ba.
Babban ne ya kalli na kusada gefensa tareda cewa..
“Wow Kalli wata jar cika hadaÉ—É—iya,ai da hajiya saitace bayan ganimar kuÉ—i akwai kuma na mata.
Kai mai kake kallo riÆ™emin ita nan,shin na fara ta kanta ko kuma na fara da kashe wancan gutun gawar kai?”
“Ogah duk wanda ka zaba zakayi,amma inaga ka fara da ita,kaga inka bari muma saimu lasa kafin kacika aikin koh?”
“Ahah ogah inaga ka gama dashi tukunna,sanin kanka ne sati guda mukayi muna tsara yanda zamu kawo farmakinnan mu gama dashi,bai kamata mu tsaya bi takan mace ba”
“Kai dallah ana za’a kwashi romo kai kuma kana wani zancen aiki,dare fah bai kusa Æ™arewa ba akwai ishashshen lokaci”
“Ya isheku haka wannan surutun,kai riÆ™emin ita ka ciremin kayanta,kai kuma wancan É—akkomin shi daga kan gadon can,Hajiyah tace dama babu abinda yake sai yanda akayi dashi”
Wanda bashi umarnin riƙe bombee ne ya nufi wajenta,ja da baya take tareda kallon wanda ya nufi inda Jabeer yake.
“Wai ku suwaye waye kuma ya aikoku,kada ku kuskura ki tabashi mai yayi muku”
“Sai yayi mana wani abu Æ´an mata? Matar Æ™anin babansa ce ta aikomu da kuma uwar matarsa,sunce suna sonsa a mace yakike so muyi banda mu aikata abinda suke so,tunda muma zasu bamu abinda muke so”
“Ahh ogah ya kake faÉ—amata wanda ya bamu aiki”
“Saboda babu yadda zatayi,a gabanta zan kashe shi kuma na tafi da ita,itada ta Æ™ara taka Æ™asar gidannan har abada,tazama tawa”
Yana gama faɗin hakan ya nufi inda Jabeer yake kwance yana kallon su da wuƙa.
“Tun har kayi yunÆ™urin taba iyalina to you leave me no choise,dolene kaga wacece ni”
A kausashe tayi maganar,tana gamawa ta bawa wanda yake riƙeda hannyennata ƙafa a fuska,kafin suyi wani yunƙuri ta kashe wutar ɗakin.
Gab gab kake ji na lokaci ƙalilan kafin wutar ta dawo..
Bombee ce zaune a bakin gadon tana haki,ƙasanta kuma ogan nasune ta ɗora ƙafarta a wuyansa,goshinsa kuma ta saita shi da bindigar datake kunkuminta.
Sauran kowa yana angle guda na ɗakin,wani yana riƙeda ciki wani kuma yana riƙeda kai.
“Shugaba dama kece?”
“Miye to idan nice,dana faÉ—amaka nice wato babu abinda zakayi,idan kuma wata ce da yanzu ka kashe mata muji kuma kayi mata fyaÉ—e ko,daka cemin ka shiryu ashe Æ™arya kake koh.
Uban me ma yakawoka garinnan tunda ga gembu?”
“Na……nazo neman kuÉ—ine,tunda kika tafi mun daina karbar kuÉ—in Æ™ungiya shikenan muka rasa sana’a”
“Da cewa aka faÉ—amaka a rayuwata Æ™arewa zanyi ina zama maka hanyar sana’a,ubana ne kai iyeee,faÉ—amin ku nawane kuka zo kuke wannan É—anyen aikin?”
“Wlh babu ni kaÉ—ai ne,waÉ—annan ma a gidan yari na haÉ—u dasu an sakomu tare,shine muke aiki,kuma dama mun yi aiki tareda su da a wajen Hajiyah lailan,mune wanda tasa muka kwancewa ubansa ma tayar mota,shekara goma da suka wuce,bayan munyi wannan aikinne tasa muka bar garin,ni saina na nufi can hanyar taraba,to shine bayan lokaci da muka dawo tasake bamu aikin kashe É—ansa,saboda idan yana raye koba ya motsi to kece zaki cigaba da kulada Companyn injita,amma idan ya mutu kuma tunda bayada magaji to dole alhj Abdullahi ne zai riÆ™e Companyn”
“Wonderful naji wannan,to itakuma Hajiyah rabi mai ya tsomota cikin aikinku”
“Iyee ita kuma zata taimaka musu da nata ikon,idan sukayi nasara to É—anta ne zai zama babban director na Companyn,tunda hajiya Lailah sun tabbatar mata da Jabeer bazai haihuba”
Dan tsabar takaici wani duka bombee ta kai masa a hanci saida ya rasa hankalin sa.
Suma wanda suke É—akin dukansu da dungayi da bakim bindiga saida taga basa motsi..
Kuka tasaka mai cin rai dan tarasa ma mai zatayi.
“Yan…,yanzu da ni watace da shikenan ta kashe shi kohh?”
“Mar…..rrryaam”
Saurin goge hawayen tayi tana kallon inda sautin dushashshiyar muryar ta taho.
Jabeer ne a yake ta ƙoƙarin tashi ya zauna da kansa,hannayensa dukka rawa suke amma kuma bai daina ƙoƙartawa ba.
Tashi tayi da sauri ta nufi inda yaken,hannayenta tasaka a ƙasan nasa ta zakagayeshi ta baya tareda ƙanƙameshi a jikinta.
“Ka Æ™ira sunana,kafara magana……..yanzu da tuni ta kasheka kenan,ta daÉ—e tanayin abu ina Æ™yaletane saboda matsayinta,amma tasaka Æ™afah ta take shi ta tsallaka matsayinnata.
She will pay for touching my family,dole ne saita gane kuranta na taba iyalin bombee,wannann alƙawarine danayi.
Sun daɗe a haka bombee tanata sambatu,shidai kawai jinta yakeyi,dan bashida ikon maida mata doguwar magana,shikansa sunan nata Allah kaɗai yasan iya ƙoƙarin dayayi wajen jawo hankalin ta gareshi,a tsawon zamansa da ita koyaushe takan kasancewa dashi a duk lokacin daya buƙaceta,hakanne yasa shima yayi ƙoƙarin zama a gefenta a wannan yanayin,duk shima shikaɗai yasan mai yakeji gameda abinda suka faru a rayuwartasa,saidai buɗar ido dayake yana kallonta a gefensa yasa yafara daina damuwa da abinda suka faru dashi a baya..
Kamasu tayi ta É—auresu tamm tasakasu a cikin store kafin safiya..
Da safe ta tashi kaman babu abinda ya faru jiyah,saida tayi wanka ta tayiwa haidar ma,shima Jabeer ta haÉ—amasa nasa kafin ta nufi É—aura musu abinda zasuci..
Bayan tagama aikace aikacenta misalin 9:00 maleekah tashigo gidan.
“Morning anty maryam ya jikin bro”
“Jiki da sauÆ™i yama fara magana jiya”
“Really wow”
“Yawwa kinga riÆ™emin abincinnan barina je na tayashi wanka”
“To shikenan”
A bangaren bombee kuwa data shiga banÉ—akin taimaka masa tayi ya hau kujerar suka fito,saida yagama saka kaya tass kafin ta tsugunna a gabansa.
“Am ka É—an yi haÆ™uri zanyi wani acting show a waje yanzu”
ÆŠaga mata kai yayi kawai,duk da bai san mai zatayi ba..
Hannu tasaka tashafi gefen fuskarsa cikin kulawa kafin tabar É—akin.
“Maleekah maza ki Æ™ira kowa da kowa yanzunnan kiyi sauri kowa fah”
“Anty maryam mai ya faru ki faÉ—amin……?”
“Kedai ki Æ™ira kowa nace yanzunnan,hatta abba shima da matan Jabeer dukka suzo yanzunnan”
Ganin yadda bombee ta kiɗime yasa maleekah ƙiran kowa da kowa ba bata lokaci,duk da batasan mai ya faruba amma har kowa yafara shirin tahowa,dan dama ta ƙware a hakan.
Cikin lokaci ƙanƙani kowa da kowa ya hallara,daga kan matan gidan da iyalansu harma da dana gidan suma da ƴan uwansu..falon bombee saida ya cika danƙam da mutane.
Kowa idan yashigo maleekah yake tambaya mai yafaru,wanda itama saidai ta kalli bombee,dam batasan mai yake faruwa ba.
Saida bombee ta tabbatar kowa yabar abinda yake ya taho kafin tayi gyaran murya.
Kallon Lailah take wacce tayi É—an murmushi,dan lokacin da taji ance kowa yazo da saurinta ta taho itada nata familyn,dan tasan Jabeer ne ya mutu.
Itama Hajiyah rabi tare suka taho itada Jawaheer,Jaleelah ma tasan mai yake faruwa a wajen Jawaheer dan haka batayi gaddamar zuwa ba,dan tasan idan Jabeer ne ya mutu ti bawanda kuma zai kulada abinda sukayi kenan.
“Kin Æ™iramu maleekah mai ya farune?”
“Uhm nima bansaniba,anty maryam ce tace na Æ™ira kowa akwai abinda yake faruwa”
“Ina….”?
Tun kafin Hajiyah Zeenah ta rufe baki sukaga tafito daga ɗakinta tana riƙeda ƙafadar Jabeer wanda yake takawa a hankali.
Kujera suka matsa masa ta zaunar dashi ya jingina,kowa babu wanda bayyi mamaki ba daganinsa,wasuna farinciki wasu na razana wasu kuma suna baƙin ciki.
“Ba dalilin Jabeer na tara kowa a wajennan ba,dalilin tara kowa shine jin jawabi daga bakin waÉ—annan.
Zaku iya fitowa yanzu”
TafaÉ—a cikin É—aga murya.
ÆŠaya bayan É—aya suka fito daga cikin store É—in kai a sunkuye,da bindigoginsu a hannunsu,sakk kana ganinsu kaga Æ´an fashi.
“Na tara dukkan mutanen nan wajen domin kuyi musu bayanin abinda kuka faÉ—amin”
“Daamus,mai kuma kake anan?”
Khmees da hilyan suka faÉ—a a tare suna kallonsa da mamaki.
“Mai kukeci na baka na zuba,duk yanzu zayyi bayani ai”
Kaman kuwa jira yake tiryan tiryan yafara bayanin abinda su Lailah suka sakashi ya aikata,tundaga na shekara goma baya harna daren jiya.
Furgaga laila tafara tana wani fige fige.
“Ƙaryane wannan zancen Æ™arya kike,ni ban sanshi ba sam,komai daya faÉ—a ke kika sakashi faÉ—ansa,tunda gashi nan yaranki yana fitowa suka ganeshi”
“Lailah abin basai yakaimu ga haka ba, tunda na shigo gidannan babu wanda yasan wacece ni,duk da cewar Ba hajiya zeenah bace ta tunkareni ita kaÉ—ai,nima na tunkareta domin cimma wani kuÉ—irina a gidannan da kuma garinnan.
Maida kallonta tayi kan Jabeer wanda ya kafeta da ido.
“Tunda nazo gidannan kakeson sanin koni wacece,saidai naÆ™i faÉ—amaka saboda wani dalilina.
Babu abinda kasani gamedani daga garinsa saikuma sunana,a yau zakaji komai”
Labarin rayuwarta tafara bawa ɗaukacin falon,tundaga labarin gidansu haihuwarta da tashinsu da ƙanwarta,harda halinda ta tsinci kanta na rayuwa, da barinta gida harma da kuma riƙonta da gen muhammad Bello Yayi,dakuma irin sharrin da akayi mata.
Kowa a wajen dayaji labarin saida ya jinjina abin,musamman yanda tayi tsara abubuwa a gidan na maganin lubnah da danginta,harma dakuma wanda Lailah tayi itada mijinta da kuma Hajiyah rabi.
“Ba iya ga haka abin ya tsayaba,nasan dukkanku babu wanda yasan dalilina na yiwa su Jaleelah hukuncin tsare su a gida dasakasu aiki,wanda kuma har yanzu basu faÉ—awa kowa suma abinda ya faru ba.
Da farko naso barinsa shi mijinsu dakansa yafaÉ—i abinda sukayi masa wanda yayi sanadiyyar shiga halinda yake ciki a yanzu,saidai kuma a yanzu yabani izini na nasanar dakowa abinda suka aikata.
Jaleelah da Jawaheer kun sani nima nasani inada videon abubuwan da kuke aikatawa a wajena,saboda saboda kunci albarkacin ina daraja ni mata bakaman yanda kuka watsa taku kimarba,bazan saka aikin dakukayi kowa anan wajen ya kalla ba,dan haka yanzu ku fito ku sanar dakowa abinda kuke aikatawa,ko iyayenku zasu daina tsinemin suna ganin laifina da cewar na rabaku da mijinku”
Jiki na rawa ido ya raina fata suka fito zuwa tsakiyar a falon..
A tare suka zube ƙasa suna kuka kaman ransu zai fita,kana gani kasan rana ce tazo musu ta ƙin dillanci.
“Kuyi haÆ™uri sharrin shaiÉ—anne,Baba da inna dan Allah kuyi haÆ™uri,haÆ™iÆ™a kunyi iya Æ™okarinku wajen ganin kun bani tarbiyya dakuma karemin mutuncina,amma saboda Æ™yamatar talaucin da muke ciki,da kuma son kuÉ—i irinnawa da daula yasa na fara Æ™azamin abu a boye da dalilin Æ™awaye,wato neman Æ´ar uwata mace”
Itama Jawaheer É—in nata labarin ta bayar babu yadda zatayi.
Dukka wajen kowa salati yafara da sallallami,babu ma ya mahaifin Jaleelah wanda saida matarsa innarta ta riƙeshi ta zaunar dashi,wacce itama take ta kuka.. Ko kallon inda take basuyi ba suka nufi ƙofah suka bar gidan.
Ko uffan basu ce mata,dan a halinda suke ciki basuda abinda zasuce mata.
“To ku mungama da babinku saura kuma Hajiyah rabi da Lailah da kuma alhj Abdullahi,wanda zasu karbi nasu hukuncin a gaban kotu a gobe tareda su brr na’imah,wanda suma lokacin za’a yanke musu abinda suka shuka suyi ta ci”
“Hee aikin banza,bar ganin kin tona aikin kowa kuma kin samu nasara kiyi tunanin ke kuma zaki zauna a gidan kiji daÉ—i.
Kaman yadda sauran basu haihu da Jabeer ba kema bazaki haihunba,haka zaki zauna kiyi ta kashi,dan an riga an rabashi da samun nasa É—an,gadon dukiyar gidannan badai daga jininsa ba saidai Æ™annensa”
Murmushin takaici bombee tayi tareda cewa
“Lailah kenan,a tunanin ki wai maganin dakikayi Æ™oÆ™arin bashi yasha yayi aiki?wanda kika bawa tayi aikin zatonki ta aikata? Andai cemata tace ta aikata dai..
Dan kinga cikin matansa babu wacce takeda ciki sai akace miki aikinki yayi?.
Jaleelah da Jawaheer dama sun bada mahaifarsu ga ƙungiyarsu,lubnah kuma uwartace ta bada tata domin samun abin duniya,nikuma babu abinda yahaɗani dashi. Kinji inda lissafinki yake?.
Kuma koda bazan haihu da Jabeer ba ni naji na amince,amma ki daina sakawa a ranki cewar Jabeer bashida É—a a raye,Jabeer yanada É—a a raye,kuma a yanzu duk duniya ko a addini ko a shari’a nice nakeda matsayin uwa a wajensa.
Dan inajin son haidar a raina tamkar É—an da na haifa a cikina,domin a kaf abinda uwa takeyiwa É—anta abu É—ayane banyiwa haidar ba,shine haihuwarsa.
Shine babban dalilin dayasakani shigowa gidannan,domin haÉ—ashi da mahaifinsa da kuma danginsa.
Na boye matsayinsa ne kuma badan komai ba sai dan irinku Lailah wanda kuke jagaye a duhu,dama wannan lokacin nake jira,idan nagama shafeku sannan zan bayyana matsayinku,ta hakkanne É—ana zai zauna lafiya a gidan ubansa batareda fargabar taba lafiyarsa ba.
Wannan kaÉ—ai abinda zan iya masa a matsayina na mahaifiyar sa mai Æ™aunarsa da kuma muradin kareshi……
Toh fah mu haÉ—u a chapter gaba Æ´an uwa……
Labari yakusa zuwa Æ™arshe inshaallah…..😂😂😂
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________