Bakar Ayah Book 2

Bakar Ayah Book 2 Page 47-48

Sponsored Links

Page 🖤 47••48🖤

Zilliyyah wacce take kwance a cikin kogonnasu sai ganin bombee tayi a kanta tsakar dare.
Tashi tayi ta zauna tana kallonta,dan tasan ba abin daÉ—i ne yakawota wajenta ba,tana mamakin duk shu’umancinta wai Æ™aramar yarinya tasamu ganin damarta.
“Me……me kuma kikazo nema wajena,ba kince inna faÉ—amiki abinda na’imah tayi zaki rabu damu ba?”
“Ahah ki sanja zancen,bazan rabuda ke badai,zan rabu da É—anki nace,amma kekam ko a mafarki aka ce zan barki ki tafi hannu rabban ai yakamata kiyi maza ki farka.
Yau mai kankat ƙareki nazoyi daga duniyar nan,aje can a tarar da sabuwar rayuwa kafin muma mu ƙariso.
Ke hilyan tanÆ™wasomin ita ki fitomin da ita waje ina jiranki”
Bombee ta faÉ—a tanayin hanyar waje,domin amsa wayar da khmees yayi mata.
“Hello ina jinka,ka karbi takardun ka tabbatar sune……..okay to shikenan,barina gama da wannan ,amma kafin sannan ka taho yanzu muna jiranka,saboda bansan mai zai faru ba”
Tana ajiye wayar hilyan ta jeho Zilliyyah a gaban bombee,wacce ta bushe tayi baƙiƙƙirin tana riƙeda ƙirjinta inda bombee ke gana mata azaba,wanda zai hanata yin katabus balle ta ɗau mataki.
Nishin take sauƙewa ɗaya bayan ɗaya kaman wata mutuniyar arziƙi,wani banzan kallo bombee ta aika mata daga ita har ɗan nata,wanda fuskarsa take sunkuye,ta takwaikwaye kaman dodo.
“Wai don tsabar mugunta da son kai,wannan Æ™azamin dodon É—annaki zaki aurawa innayi,inda bangano ki ba Allah ne kaÉ—ai yasan inda zaki tsaya kenan….hmmmm”
Duk abinda bombee take faɗa Zilliyyah tana jinta ko tari batayi ba,sai rawar ɗari take kikir kikir.. Suna cikin hakanne khmees ya iso wajen da motar bombee,takardun hannunsa ya miƙamata da gama dubasu,kafin ta bashi ya saka a mota.
“Hilyan madannin na hannunki bani nan na gama da ita mubar wajen”
Ɗan Zilliyyah ne ya rarrafo yana son roƙon bombee,da wata murya mai kamada gwaranci.
“Ohhh abin yayi yawa,bayan sauya kamanni ko magana ma bakayi,to shikenan kada ka damu bazan kasheta ba,abu É—aya kawai zanyi shine maida komai data tabayi kanta,ta hanyar fasa madubinta…….hilyan hakan yayi koh”
Cikeda mugunta hilyan ta É—aga kai tana dariyah,da sauri kuwa tashiga cikin gidan ta É—auko madubin,wanda yasha fenti da jini.
Zilliyyah wacce ta rufe ido tana jiran ta inda zuciyarta zata tarwatse,da sauri ta buɗe idon jin abinda bombee ke shirin yi,wanda yafi mutuwar dazata bata tashin hankali,domin tariga ta basu ruhinta kafin su dunga yimata aiki,idan aka fasa madubinnan shikenan tata taƙare,rayuwa zatayi ita ba,a mafarki ba ita ba a zahiri ba,sannan kuma cikin azaba da ƙazanta.
“Ahah ahah bombee kada kiyi haka naroÆ™eÆ™i,aradu gwara kasheni daki fasa madubinnan kafin na mutu,gwanda ki kashemu nidashi gabaÉ—aya,inkika fasa madubinnan……”
Hannun ta haɗa taba roƙon bombee,jikinta har rawa yakeyi,wanda kuma hakan yasaka zuciyar bombee yin fari tass kaman farin goro.
Madubin ta ƙarba a hannun hilyan ta ɗagashi sama,saida tasakewa Zilliyyah murmushi,wacce take jijjiga kai kafin tasakeshi ta bashi waje a ƙasa,jin yabar hannunta kuwa gravity na ƙasa yaji izuwa fashewar sa fassss a ƙasa.
“Tsawon rayuwarki kina cutar da al’ummah,yau lokacin naki hukuncinne,kinsan kin shiga gonar bombee a yau,in baki mutu ba yazamemiki gargaÉ—i”
Wani ihu tasake mai cike da kama zuciyah,iska ce tafito daga cikin madubin tana ƙugi tana jan ƙafafun Zilliyyah,wacce take neman taimakon abinda zata kama,babu abinda yake kusada ita sai hannun ɗan ta,wanda kuwa tariƙeshi gam suna shirin shigewa tare.
Hilyan ce takalli bombee tareda cewa.
“Anty maryam shiÉ—in mu ceceshi,tunda babu abinda yayi?”
“Ahah koda kin ceceshi yazakiyi dashi,shikansa naga alamun ba cikekken mutum bane,sannan bakya ganin shine yakeson binta,barsu suje kawai gayyar tsiyah”
Bata gama rufe baki ba Zilliyyah taƙarisa shigewa cikin madubi itada ɗanta,wani haskene yafito mai ƙarfi wanda ya tarwatsa madubin kashi kashi..
Hakan a tare ya wakana da zubewar bombee ƙasa sumammiyah.
*** ***
Yauma kamar kullum yana tashi daga aikinsa yanufi gida,sashen lubnah ya nufa yacire kayansa yayi wanka.
Sallar la’asar ya haÉ—a da kuma magriba,ko Addu’a bayyi ba ya tashi ya naÉ—e sallayar,saboda lubnah tace masa kada yasake yayi Addu’a idan yayi sallah,ita kanta sallahr sa’a yaci bata hanashi ba.
Abincin daya shigo dashi a waje ya buÉ—e yaci,daga nan yasamu waje ya zauna.
Aikin da bayyi ba ya É—auko yafarayi har lokacin isha,yana sallah yacigaba har cikin dare yana zaune.
Can kaman a sama yaji ana ƙiran sunansa da ƙarfi,bai amsa ba sai waiwayawa dayakeyi domin ganin mai ƙiran,bayan ƙirna yayi shuru sai yaji an kwaɗa masa wani abu a tsakiyar kansa,mai makon yaji zafi sai yaji tamkar ana warware masa wata igiya.
Riƙe kan yayi da hannyensa biyu,daga nan ya bingire a wajen sumamme.
*** ***
Tun safe har dare ya shiga brr na’imah bata zauna ba,yanzu ma zirga zirga take a cikin talatainin dare,saiga Gen abdu manga yashigo shida su lubnah,da sauri ta taresu tana duddubasu ko anyi musu wani abun,ganin komai sumul yasa ta maida ajiyar zuciya.
“Sannu maza muje ki wanke jikinki ki ci abinci ki huta,hmmm ai Lailah ta É—ebo ruwan dafa kanta,dani take zancenne”
“Mommy Lailah kuma,wacce lailan?”
“Wacce ta É—aukeki mana?”
“Ba Lailah ce ta É—aureni ba,maryam ce fah matar Jabeer,wacce nake faÉ—amiki muna sa insa da ita,tantiriyace ta bugawa a taro,domin bata tsoro ko kaÉ—an”
“Maryam kuma,to itakuma menene nata na kamaki”
“Uhm da alama tasan nayi wanannan aikin,dan cewa tayi bazata sakeni ba sai nayi wata guda,saikuma gashi wai ta sakeni a sati uku.
Ƙaƙƙarfa ce naji wasu yaranta hilyan da khmees sunace mata captain dai,yawwa akwai wani sunanta ma Bombee”
Zaro ido su brr na’imah sukayi a tare,wayarsa ya ciro ya danna wani hoto ya miÆ™awa lubnah.
Hoton bombee ne da kayan sojoji ta sara,kanta da jar hula irinta captain.
“Lahh itace ai,ya akayi na ganta da kayan sojoji,no wonder nake tunanin kaman na taba ganinta a barrack mana”
Wani duka brr na’imah ta kaiwa lubnah,dukkuwa da halin da take ciki.
“Nikam mai yasamu rayuwata na haÉ—u da dolayen Æ´aÆ´ane?
Tsohuwar maÆ™iyarki kina zaune da ita amma baki sani ba,har saida tagama dake kaff,Tazo da daÉ—i ma da bata barki kinyi watan ba,saikije ki wanke wannan dauÉ—ar kana kici abinci.”
Cikeda takaici ta wuce ɗakinta,ko ammar bata kalla ba wanda yake zaune akan kujera ya mimmiƙe ƙafafu.
Tana tunanin tasan kan matsalar ashe duk ba haka bane,koda yake itama bombee bazata gagareta ba,abinda yafi bata mamaki shine ya akayi taje gidan Æ´ar ta a matsayin kishiyarta batareda tasani ba,yarinyar da shari’a take nemanta itace take cikin garin hankali kwance,kuma harda sace mata Æ´aÆ´a,duk yadda akayi fansa takeson dauka ta hanyar katse mata burinta na mallakar JAAN Company’.
Ihun da lubnah ta kwarara da safene yasakata firgit tatashi ta nufi dakin nata da sauri,bata ganta a dakin ba dan haka ta shiga banÉ—aki inda take jiyo kukannata.
A tsaye take a bakin sink tana kallon wani ruwa mai kauri da wari kalar ruwan ɗorawa,wanda yake fita daga ƙasanta.
Itama brr na’imah wacce take bayanta saurin toshe hancinta tayi tareda girgiza kai.
“Ba haka bane,hakan bazata sabu ba,ai baki cika wata gudan ba,bahaka mukayi da Zilliyyah ba,mai yasa haka zata faru”
Komawa dabaya take tana maimaita duk abinda yazo bakinta,har bata saniba tayi tuntube ta drawer gaffo.
Miƙewa tayi batareda duba gurdiyar datayi ba tayi hanyar ɗakinta.
Gen abdu manga ta tarar a zaune a tsakiyar gado yayi haɗa kai da gwiwa yana kuka tamkar ƙaramin yaro.
Magana brr na’imah tayimasa amma ko kulata bayyi ba,abinda ya faÉ—ane taji tamkar notin kanta ya kunce.
“Na’imah kincuceni duniya da lahira,Allah ne kaÉ—ai zaimin hisabi dake ranar gobe Æ™iyama,kin zalunceni,kin rabani da aminina Bello,kinsaka naci amanarsa na zalunceshi na kashe masa É—an sa,yarinyar da bataji bata ganiba kinsaka na É—ora mata laifin da bata aikata ba,aminina yariÆ™e ta amana,amma saida kika saka ya koreta daga gareshi a matsayin wacce ta kashe masa dansa.
Hakan bai isheki ba saida kika sakani farmakar dukiyar surukina Na’imah,nikuwa mai nene bakimin ba,Allah saiki innata saida tace kada na aureki tun farko,amma nayi kunnen uwar shegu da ita,ni a dole inasonki,yanzu mai gari ya waya damai na amfana a zamana dake.
Wannan iya abinda nasani kenan,wanda bansani ba bila adadinne nasan”
Komawa tayi da sanÉ—a da bar É—akin batareda tayi magana ba,dan batada amsar waÉ—annan maganganunnasa,tabbas akwai gagarumar matsala indai aikin kansa ne ya kwance.
Ɗakin data ajiye madubinta ta nufah,tana yaye ƙyallen dayake jiki da kalli hotonta a tsaye a ciki kamar kowanne sauran madubai.
Sab’anin da dazata ga duhu baÆ™iƙƙirin,inata saka hayaÆ™i sai Zilliyyah ta bayyana.
Bata daddara ba hayaƙin da dauka ta banga,saida suka kare tass batareda madubin yayi komai ba.
Wani duka takai masa da ƙafa saida ya tawarwatse gabaɗaya.
Kaman lubnah itama zaman durshan tayi a wajen tana nata kukan,zagi kuwa sa tsinuwa babu wanda batayiwa Zilliyyah ba,gashi banda ƙaiƙayi babu abinda jikinta yakeyi,saidai ba kamar wanda zai zautata ba.
“Mommy ni……nikam zan koma gida wajen Jabeer….inaga idan naganshi komai zai dawo daidai”
Tana kukanne take maganar.
ÆŠan tsayawa brr na’imah tayi da kukan tareda cewa.
“Yakikayi da ruwan dayake zubowan ya daina?”
“Ahah bai dainaba Æ™unzugu nayi,idan naje gida saina wanke nasake saka wani,in yaciba a haka nashiga uku mommy nikam duk yadda za’ayi ma kiyi wannan masifar ta daina fitomin”
Bata maida mata martanin maganar ba,dan intace tanada abincewa ma tayi ƙarya,maida gabanta tasakeyi inda madubin yafashe yanzu,tanajin lubnah ta tada mota tabar gidan.
Cikin sanɗa ta fita daga motarta tashige sashenta,lokacin data shiga ɗakin Jabeer yana kwance a falo yana bacci,mamaki abin yabawa lubnah,saidai bata ce komai ba zage tashiga banɗaki,domin cire ƙunzugun dayake jikinta.
Wasu kayan ta sanja tasake fitowa falon,har sannan yana nan kwance a inda tabarshi,matsawa inda yake tayi tareda bubbuga bayansa.
“Honey lafiya kake bacci anan,duk saboda kana jirana na dawo koh,gani na dawo tashi ka ganni”
Tashi Jabeer yayi yana mutstsika ido tareda ƙarewa inda yake kallo.
“Anan nayi bacci?”
“Uhm yanzu nadawo naganka a wajen a kwance,common i miss you”
Lubnah ta Æ™arisa maganar tana Æ™oÆ™arin rungume Jabeer”
Saurin tureta yayi daga jikinsa yana mata kallon bakida hankali.
“Ya isa haka lubnah,duk abinda kikayi bai isheki ba har yanzu,kijira dawowata ki karbi sakamakonki,abin yatsaya kuma iya haka”
Miƙewa yayi tsaye ko kallonta bai sakeyi ba yashiga part ɗinsa ta falonnata.
BanÉ—aki ya shiga ya dauro alwala,yana share hawaye ya tada sallahr asubar da bayyi ba,bayan yagama yadaÉ—e yana kuka akan sallayar kafin ya tashi.
Babu abinda ya faɗo masa a rai sai Jaleelah,gwanda ma Jawaheer ita gidan ba baƙonta bane,amma ita fah babu wanda tasani a gidan saishi,amma haka ya ɗauke kansa tamkar bai santa ba sanadiyyar lubnah,koya takeji oho?
Yasan a yanzu tana matuƙar jin haushinsa ba kaɗan ba.
NaÉ—e sallayar yayi da sauri ya nufi sashenta,ko kulawa da neman abinda zai saka a cikinsa bayyi ba,gashi rana tayi sosai sha biyu takusa.
Murɗa ƙofar sashenta yayi ya shiga,rabonsa da taka wajen tun wata uku dasuka wuce.
Zaro ido yayi yana sake mutstsikawa,ko har yanzu bai farka daga mafarki bane kai?
Domin shidai yasan bahaka yasan falonnata ba,wanda a yanzu yake dauke da wasu danƙara danƙaran funitures da ba iya a nigeria bama anaji dasu.
Ma’aikata kusan ukune suke kai kawo a falon,kaman sansanin Æ´ar sarki,wata nasaka turaren Æ™amshi,wata na gyara labulayen falon,wata kuma sai mopping É—in falon take da wata na’ura mai matuÆ™ar tsada.
Basu taba tsammanin wani zai shigo daga ƙofar dayake tsaye ba,dan haka ko kulada shi basuyi ba saida yayi gyaran murya tukunna.
Dukkansu zubewa sukai suna gaisheshi,duk da kana ganin mamaki ƙarara akan fuskarsu na ganinsa a sashen.
“Jaleelah fah tana ina,kota sanja sashene?
“Ahah Hajiya Jaleelah tana sashen Jawaheer yau”
“Sashen Jawaheer kuma?,mai tajeyi can kuma?”
“Uhm idan suka yi kwana É—aya anan washagari kuma can suke zuwa ranka ya daÉ—e”
Abin yasha masa kai,saidai bai sake tambayarsu ba ya nufi sashen Jawaheer É—in.
Yanda na Jaleelah yake itama hakan nata yake sakk iri É—aya,kala ne kawai ta bambamtasu,saidai nan tsitt kakeji babu alamar sawun masu aiki.
ÆŠakinta ya nufah,batareda yayi magana ba ya buÉ—e,dan duk a zatonsa hade kai sukayi suna mutunci,tunda ya É—auke musu Æ™afah,duk sai yaji yanajin haushin kansa gameda abinda ya faru…….
Tunanin dayakeyi yatsayar dashi cakk sakamakon abinda yayi arba dashi a É—akin.
ÆŠakin har yafi falon Æ™watuwa da kuma kaya masu tsada,wannan shine abin burgewar É—akin,abin takaicin kuma wanda ya riski Jabeer dabai taba tunanin sa a mafarki ba shine ganin amarennasa a gado É—aya tsirara haihuwa uwarsu suna masha’a.
Sun wani kanannaÉ—e tamkar macijai a waje É—aya,deep kiss suke aikawa junansu,sai bayan sun raba bakinsu kafin Jawaheer ta shafi fuskar Jaleelah.
“My reddish slender i love you,ina sanki fiyeda komai nawa,ni nafi ganinki a ja maimakon baÆ™a……..bantaba tunani ba ko a mafarki wai zan haÉ—u dake ido da ido kuma a waje É—aya”
Hannun Jawaheer da kama tasaka a bakinta tana tsotsa,saida tacire kafin ta É—ora da cewar.
“Uhmmm nima haÉ—uwa ta dake is my blessing,saboda a lokacinne na koyi yanda zanfito da maÆ™udan kuÉ—aÉ—ena nayi facaka dasu,abinda yafi bani dariya dake,shine yanda kike nuna kishina a dubai idan Jabeer yajani É—aki.
Wow i love this side of you my lady,shifa yayi zaton sonsa nake koh???”
Dariya suka saka a tare,kana suka sake haÉ—ewa waje daya.
GabaÉ—aya basu kulada Jabeer ba wanda yake tsaye akansu jikinsa yana rawa.
Jijjiga kai yake saboda wani duhu dayake gani,lokacin daya samu kallonsa ya dawo daidai É—akinsa ya koma da gudu.
Drawer dayake zuba magunguna ya buÉ—e,amma babu koÉ—aya a ciki,da alama bombee ce ta É—ebesu..
Gwauron numfashi yaja mai zafi yana murza kai,ganin abin bazai kaishi ba ya dauki makullan motarsa yanufi waje dasauri.
Ko gama bawa motar wuta bayyi ba yafigeta ya fice a gidan.

*** ***
Da farin silin ta haÉ—a ido lokacin data farfaÉ—o akan gadon asibitin.
Tashi tayi ta zauna tareda fige ruwan dayake shiga cikin jikinta.
Hilyan ce ta taso da sauri daga kan kujerar tanufo inda take.
“Anty mar….”
“”Karfe nawa ne yanzu?”
“Uhm 12:30 ne”
“Ina inna tatashi kuwa?”
“Ahah bata tashi ba har yanzu,amma itama daidai lokacin dakika faÉ—i sanann ta suma”
“Maza tayarmin da motata yanzunnan barina gyara nafito mu tafi gida,nasan tana wajen da za’a kulada ita,Jabeer yana gida maybe zuwa yanzu nasan shima yatashi”
Daga kai kawai hilyan tayi tareda fita waje,abinka da jinin sojoji koda ya daskare,tun kafin tagama fitoda motar a wajen parking harta shiga wajen drivern ta karba a hannun hilyan.
Figar motar tayi da gudu zuwa gida,daidai zuwa shigar motar taga mota ta fita a gidan a guje kaman mai shirin tashi sama,bata kulada da waye ba tasaka kan tata motar zuwa ciki.
A bakin sashen su tayi parking,bata shiga part É—intaba don tasan koda yajema to zaiga bata nan,lubnah kuwa tayi zaton tana gidansu,dan tasan zuwa yanzu taga sakamako.
Sashen Jaleelah ta nufah da sauri ko yaje can.
Masu aiki ta tarar suna ta goge,gaisheta sukayi,bata amsa ba saima jefa musu tambaya da tayi.
“Jabeer yashigo nan kuwa yanzu?”
“Eh yashigo ranki ya daÉ—e,saidai da mukace masa Hajiyah Jaleelah tana sashen Jawaheer to ya tafi can”
‘Tabb Allah yasa bayyi mugun gamo ba ameen’
Tafada a ranta,cikin sanyin jiki ta nufi sashen Jawaheer ɗin,abinda take gudu shiya faru,domin tun a daga falon ta hango ƙofar ɗakinta a buɗe yanda ya barta,ga nan center table ya goce inda yayi hanya yabar falon.
Waya da ɗauka ta ƙira Security office na bakin get.
“Hello motar danayi clear da ita a bakin get wanene a ciki?”
“Ranki ya daÉ—e ogah Jabeer ne a ciki,kuma da alama baya cikin yanayi mai dadai,domin a zuciye ya bamu umarnin bude get É—in”
“Kuma da kukaga haka babu wanda kuka Æ™ira koh?”
“Kiyi……”
Ƙitt ta kashe ƙiran tareda jan zuciya.
A zuciye ta karisa ɗakin da su Jawaheer tareda jingina a jikin ƙofar tana kallonsu.
Ganin basu san ma tana tsaye ba yasata yin tafi guda uku da hannunta.
“Hii less ladies the plessure has stopped,everything you did is on the camera”
(Barka yan mata,daɗi ya ƙare,komai kukayi yana cikin camera!!!)

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button