Bakar Ayah Book 2 Page 15-16
Page 🖤15••16🖤
Mutane da dama a wajen idonsu na kanta,musamman ganinta da Kayan sojojin rasha É—in,kuma ga idonta ya nuna daga can É—in take.
Taxi tazo tara,tana saka hannu zata shiga motar taji anyi mata magana a bayanta.
Security su uku maza. Turanci suka farayimata dan a tunaninsu batajin hausa.
“Am madam daga ina haka,shin zamu iya ganin katin Visa ki?”
“Eh akawai visa amma akwai wannan ma”
Ta mayar musu magana da hausa tareda miƙamusu ID card ɗinta na Shaidar ɗan ƙasa.
“Ko kunfi buÆ™atar visa kai ba ID card ba”
Taƙarisa magana a zuciye,shuru sukayi cikeda mamaki,wanda hakan yasa itakuma ta juya tashi taxi ɗin.
Kwatancen inda zai kaita tayi masa,tareda kwanciya a jikin kujerar motar tana sakin ajiyayyen numfashi na gajiyah.
Kaman ance da Nu’aimah ta É—aga kai,tana taimakawa mai aikinsu bawa shuka ruwa,ido biyu sukayi da Bombee wacce take a tsaye a gabanta ta naÉ—e hannu tana kallonta.
Mitstsika idanuwanta tayi domin shin taga dagaskene Bombee ce a gabanta kowa.
“Addah Bombee dagaske kece nake gani kuwa”
“Uhm ko kin taba ganin wata aljanar dama mai kama dani?”
“Ummah addah Bombee tadawo,wlh dagaske nake kin ganta a waje.
Hajiya Zulaiha ce suka fito a tare itada Farouq.
“Ƴa ta wannan tafiyar kuma fah,ko matsala aka samu a makarantar kika dawo yanzu?”
“Ahha ummah na gama,jiya akayi bikin yayemu ma,a sannan na hau jirgi na taho gida”
Ƙarisowa wajen tayi tareda kama hannun Bombee ɗin
“Naji daÉ—i danaji cewar kin gama cikin sa’a,saidai banji daÉ—in yanda kika É—aukemu ba,tunda har za’ayi bikin gamawarku ki taho batareda munsaniba”
ÆŠora É—aya hannun nata tayi akan na Hajiya Zulaiha kafin ta É—ora da cewar.
“Ahah ummah banason É—oramuku nauyine dayawa a kodayaushe,inada kuÉ—in dazanyi amfani dashi na taho shiyasa kawai ban damu abba ba,nasan idan na faÉ—a zai iya cewa ma shizai É—akkoni,bayan busy yake da aiki. Karki damu komai lafiya tunda na dawo zance wuce ummah”
Bombee taƙarisa maganar cikin sigar neman afuwar abinda tayi.
“To shikenan,amma kinyiwa kanki saidai ki zauna a É—akin Nu’aimah,tunda naki kam baa gyare yake ba,babu wanda yasan da dawowarki”
Daga haka Hajiya Zulaiha tajuya ta shiga cikin gidan suma suka bita a baya,tun a hanya Nu’aimah tafara bata labarin abinda tayi missing.
Bayan taci abinci tayi wanka lafiyar gado tabi,bata daÉ—e da kwanciya ba su Haidar suka dawo daga waijen aiki shida Abbansu,Hajiya Zulaiha ce ta sanar dasu dawowar Bombee É—in. Suma sunyi mamakin hakan,duk da zuwa yanzu sunsan halin kayarsu.
Deciding sukayi kan bazasu tasheta ba,gwanda ta huta tukunna.
Hakanne yasa basu haÉ—uba sai a wajen cin abincin dare.
Hirar yaushe gamo aka fara bayan an gama cin abincin dagannanne kuma magana mai muhimmanci ma tashigo na gameda matsayin Bombee a yanzu,dakuma abinda yadace tafarayi a lokacin.
“Toh maryam yanzu dai tunda kin dawo lfy É—auke da sakamakon da ake so shine abin farincikin.
Saura kuma aiki,nayi magana da gen captain É—in dake division É—ina,Zai adding sunanki da É—aya daga cikin Captain din dake Æ™arÆ™ashinsa,idan kinje saiki ga yanda abin yake,domin za’a baki wanda zasu kasance a Æ™arÆ™ashinki”
Murmushi Bombee tayi kafin da É—ora dacewar.
“Nagode abbah da duk karramawarka a gareni,inshaaallah zanyi aiki da gaskiya kaman yanda nayi maka alkawari,bazaka taba samuna da wani mungun nufi ba”
“Yawwa naji daÉ—i hakan,kisake zuwa ki huta kafin zuwa goben to,akwai kyautar dazan miki na wannan gagarumin jarumta da kikayi”
Dare yaɗan raba an daɗe da isha,baccine yagagareta duk yanda taso da tayishi,hakanne yasa ta fito filin gaban gidannsu tana kalle kalle,dama ga farin wata ya haske ƙasa daga sama.
Riga da wandone a jikinta,amma basu kamata ba,sai ƙaramin hijabi data saka ita kafaɗa.
“Ka fito najika”
Fitowa haidar yayi daga inda ya labe yana ganinta,nufar ta yayi yana murmushi na ganinnata,dan dama yaso tunda ta dawo suyi magana amma basuyi ba.
“Ke ma kinkasa baccin koh,hmm har yanzu horon rashin bacci da daddare nima baibar jikina ba,inaga kuma yake?”
“Haka fah,dan ni nafijin daÉ—i bacci da rana akan dare,ganinsa nake kaman shine lokacin aikina,musamman dama daya zamo ni basuda wani banbanci sosai a wajena”
“Oh wanann ganin darennaki koh,shin ne Dagaskene abinda mutanen garinku ke fada akan idonki ko kuwa”
Ƴar karamar tsukar takaici Bombee tayi kafin tace.
“Hmmm Æ´an ranin hankali ba,naje nayi bincike akan hakan,matsalar aljanuna bata shafi idona ba,kowanne zaman kansa daban,kuma kowanne nasan dalilinsa”
Zaro ido haidar yayi tareda cewa
Kina nufin dagaske suke ba kalau kike ba”
“Kana tsoron karna cutar dakaine wata rana?”
Jijjiga kai yayi cikeda jin kunyar zaburar dayayi.
“Ahah idan cutarwane ai da kin cutar dani tun a baya,sannan kuma nine dakaina na tunkare ki ai,duk da nasan kinsha banban da sauran yaran danake gani a lokacin,musamman a cikin mata. Amma yaya idonki kuma menene dalilin dayasa aka haifeki dashi a haka”
Yafaɗa tareda ƙoƙarin kauda wancan zancen.
“Ka fiye tamabaya Haidar,inka matsu kaje kayi bincike akai kaman yanda nayi,shin mai yasa idona ya kasance a haka.”
Ta ƙarisa maganar tana ɗaga masa gira,alamar tana challenging ɗinsa,da haka ta bar wajen ta kyaleshi.
Jijjiga kai yayi tareda cewa.
“I love this nature of you maryam,you are amazing”
Washagari da safe tare dukkansu suka nufi barrak din,karon farko tun a ganin level É—in aikinta ta samu matakin captain batareda matsala ba,zabi aka bata na ta karbi gida ko kuma zata zauna a side din captain dake dorm É—in mata.
Da farko gen Muhammad yaso ta zauna a gida ta dunga zuwa,musamman dan haka ya bata sabuwar mota dalleliya a matsayin kyautarta,amma haka taja ta tsayah akan a barrack zata zauna,dan haka dole ya ƙyaleta,saita dunga zuwa musu da yawo.
Kayan jikinta ta cire,daga ita sai towel mai adon zanen kakin sojoji,banÉ—akinta ta nufah na cikin dakinnata,kira ta jiki ba’a magana,musamman kuma jikin daya samu fitaccen workout yanda ya kamata.
Minti biyar ma basu cikaba ta fito daga wankan.
Sharp sharp tasaka kaya ta nufi kitchen É—inta dake cikin side É—inta na dorm É—in.
Omlett ta haÉ—a na kwai gashashshen biredi sai ruwan tea.
Cikin ƙanƙanin lokacin ta gama komai tayi niyyar fita.
Mai yi mata aiki ce tashi tafara,dan ta faÉ—amata kan cewar sai tagama komai kafin tazo ta gyara.
Kai tsaye division dinsu ta nufah,inda zata ga ƴan team dinta da suke karƙashinta.
Mutane biyar ne,mata uku maza biyu,wanda Haidar ne yazaba mata da kansa,da alama dama yasansu kenan,itace baƙuwa a cikinsu,daga yanda suke magana da dashi kafin ta iso.
Ɗagowa yayi ya kalleta tana tsaye ƙiƙam tasaka hannun a aljihun wandonta.
“Haidar sannu da aiki,da abokanka ka haÉ—ani ko kuma da waÉ—anda zasu tayani aiki?”
“Da dukka biyun na haÉ—aki,kuma zasu taimaka miki fiyeda yanda kike tunani,wannan abokina ne munyi wata shida dashi tare,Shine second captain Wato Khamees ,sai sauran Mabiyan a hankali zaki sansu dukka”
Ƙaremusu kallo Bombee tayi na dan lokaci,kaman yanda yafada kam basu da matsala daga ido,amma dai lokaci ne zai bayyana komai.
Tundaga wannan ranar Bombee takama aiki haikam babu kama hannun yaro,wanda har takai tayi shekara guda tana aiki. A iya cikin wannan lokacin tayi aiki na bajinta da dama,wanda hakan yasa gen Muhammad yakeji da ita da kuma alfahari da ita.
Lokacin tantance Field marshal yayi,za’a dauki É—ayah tsakanin Gen Muhammad da kuma gen Abdu manga.
Kowa a yanzu iya ƙoƙarinsa yake wajen ganin ya kai abokin takararsa ƙasa,shikuma yayi nasara,domin tsawon lokaci aikinsu a kunnen doki yake tafiyah,dole ana buƙatar zakaran dafi.
Harbi ne yake tashi a ta kowanne sako a cikin dokar daji,inda aka tura su Bombee aiki wannan karon.
Ƙirane ya shigo wayar Bombee ta sojoji,saurin dannawa tayi taji muryar Khamees.
“Hello Captain An samu matsala fah,maza kuyi gaggawar barin wajennan muma gamunan tahowa”
“Mai yafaru captain Khamees?”
“Makamanmu dukkansu basuda,mutanenmu da dama sun rasa ransu,ciki harda yan team É—inmu guda biyu,Saikin kai hari kiji bindigar taki harbawa,kokuma kayan mu ba bullet protection bane mai kyau,idan bullet biyu suka sameshi yagewa yake,akwai matsala sosai,muyi gaggawar juyawa da wuri,Fitilar ma É—aukewa suke na goshinmu kum…….”
Tun kafin yagama magana wayar ta katse,zaro ido Bombee tayi tana kiran sunansa amma shuru bai amsa ba.
Kallon Sojan dayake gefenta tayi,yana da ƙoƙarin saita kunamar bindigarsa amma taki yin aiki,ga fitilar sa ta mutu.
Wani ta gano a nesa ya saita shi,da sauri tayi super a kansa suka faÉ—i tare.
Hularsa ce ta cire taga wanene.
“Hilyaan dama kece,ina sauran suke,sannna mai yasamu bindigar kika saka harbi”
Saita ji muryar kafin tace.
“Captain inaga da matsala,fitilunmu duk sun mutu,bindigogin ma basa aiki fah”
ÆŠaga ta Bombee tayi tareda runtse ido kana ta buÉ—e,maza ki koma da baya ki faÉ—awa saura su koma maboyarsu,bari zanje na taho da Tawagar su Captain khamees.
“Ammma captain maryam bakida fitila a hannunki,taya zaki bani taki”
“Dama riketa nayi ba amfani nake da itaba,kedai kiyi yadda nace kawai,maza ki koma”
Tana gama faÉ—amata haka ta nausa cikin duhuwar dajin kaman an cillata.
Da ƙyar da siɗin goshi suka samu damar barin wajen,bayan wasu a cikinsu sun rasa ransu.
Sati guda akayi ana zaman makoki na rashin Abokan aikinsu da sukayi. Duk da kowa bai kawo komai ba a rashin nasarar,amma su Bombee sun sakawa abinda ya faru ayar tambaya,hakanne yasa suka fara bincike a boye batareda sanin kowa ba.
A zaune take itada khamees a ƙaramin office ɗinta na division din,haidar ne yashigo da kayan aiki a jikinsa,ɗazu yaga ƙiran Bombee bai samu damar zuwa ba sai yanzu.
Gaisawa sukayi da khamees hannu da hannu,sai kuma salute daya mikawa Bombee na wasa.
“Yah captain naga kirnaki inakan aiki,meyake going haka?”
“Uhm inason sanar dakaine cewar,muna buÆ™atar taimakonka na wani abu dayake faruwa gameda barrack”
Labarin mai suka fuskanta a wajen yaƙi ta faɗamasa dukka,shima kansa yayi mamakin hakan,babban abin ayar tambayarma shine yadda a cikin manya babu wanda yace wani abu kan lamarin.
Ajiyar zuciya ya sake tareda cewa.
“Shikenan naji abinda kukace,inshaaallah zanyi iya Æ™oÆ™arina wajen na taimaka,akwai abokiyar aikina danake son na shigo da ita ciki,tana da jajircewa,kuma taÆ™ware wajen binciken irin waÉ—annan abubuwan”
“Uhm bazan hanaka kawota ciki ba,amma baka ganin akwai matsala kuwa musaka wata bare?”
“Kai Bombee kidunga koyon yarda mutane mana”
“Ohk shikenan Allah ya taimakemu,amma koma wani bazai taimaka nikam bazan bar rayuwar mutanena ta tafi a banzaba haka nan”
Su shidane sai wacce suke aiki tare na binciken na ura wato Sameerah,sai kuma kuma Bombee da khamees,Hilyaan da kuma Bilal ÆŠaya abokinsu daya rage.
A cikin sirri suke aikin batareda sanin kowa ba saisu kaÉ—ai,suka fara gudanar da aikin binciken.
A wani bincike da haidar suke gudanarwa da daddarene suka samo wani clue a cikin daji da daddare,domin akwai motoci dake shigowa suna fita,basa yin hakan kuma sai cikin dare,wanda suke da tabbacin cewar yanada nasaba da bindigoginsu,domin bayan yin yaƙin,tun a hanya wata mota tazo ta tafi da makaman dukkansu,kuma sunga shigar motar wajen a Camera.
A dare suka sanar da su Bombee abinda yake faruwa wanda sun tsayar da shawarar da gobe zasu nufi Cikin dajin inda Nau’urarsu ta nuna musu.
Gen Abdu manga ne a zaune yana kurbar lemo a kofi a cikin office É—insa.
Sameerah ce tashigo tareda sara masa,saida yayi mata alamar hannu kafin ta gyara tsayuwarta.
“Mai kika samo wannan lokacin kuma?”
“Sir yanzu kam nasamo wani abun,wanda ina mai tabbatar maka dazamu yi nasarar kaiwa Gen Muhammad Æ™asa da tawagarsa,sannnan kuma ina mai gargadinka da cewar,Captain maryam tagano cewar,makaman dakayi order wannan karon Basuda kyau,idan takai wanann rohoton division,ina mai tabbatarmaka da zata ga bayanmu,ba iya ga babbar kujera ba,harma ga rayuwarka saita shiga haÉ—ari,domin sanadiyyar amfani da makaman yajawo rashin nasarar da Rukunin sojoji tayi a harin daya gabata,yanzu haka sun nufi black room domin gano shaidu akan aikin da muke aiwatarwa.
Saurin ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tareda tashi ya tsayah,dunƙule hannunsa yayi tareda cije baki.
“Wannan yarinyar wai ya zanyi da itane,tun zuwanta wajennan na tsawon shekara guda,babu abinda take sai kawomin cikas,da kuma kawoma gen Muhammad nasara,da farko nayi zaton Æ´ar sace,sai daga baya na gano cewar riÆ™onta kawai yayi.
Yanzu toh ya kike gani,ta wacce hanya zamu bullo musu?”
Dariyar gefen baki tayi kafin tace.
“Karka daku yallabai baza’a samu matsala ba,sun riga sun gama amincewa dani,basuda masaniyar ina tareda kai,inaga kwantan bauna zamuyi musu,mu biyo musu ta bayan gida.
Kaman yanda suka ce zasu black room mu barsu suje ɗin,Akwai Detect camera da zamu saka a jikinmu domin gano inda muke,iyah haidar ne yasan yanda ake kasheta da kuma yanda ake Kunnata,tanada amfani da yawa kana kuma tana da matuƙar hadari.
Idan aka danna danger alarm É—inta,to zata rarwatsa tsokar jikin mutum a area datake,idan aka sakata a wajen zuciya to mutuwa ne direct in aka hareta.
Nida haidar ne kaÉ—ai mukasan yanda ake Hari da ita,zan baka controller a gobe inshaaallah,kafinnan zamu tsara yanda komai zai tafi”
Tafi Gen abdu manga yafarayi irin na alamar jinjinawar nan,HaÆ™iÆ™a ina Alfahari dake,zan haÉ—aki da mutanen dazasu taimaka miki,wannan karon ki tabbatar kinyi nasara,idan har hakan ya tabbata,to zan baki matsayin da kika daÉ—e kina nema”
Kaya suka gama sakawa baƙaƙe wanda zasu saje da aikin dazasu fitan.
Rataya bindigoginsu sukayi,saida suka tabbatar kowa ya shiryah kafin suka fito daga cikin inda suka buyan.
A hankali suke tafiya cikin sanÉ—a,kowa yana kallon inda kowa yake,saboda abinda suka saka a jikinsu,tafiya sukayi mai nisa suna bin na’urar datake nuna musu inda zasu nufa.
Wani waje suka iso a tsakiyar dokar dajin,ba gidane haka normal ba,haka yake square na ƙarfe,kallo kallo suke kafin suka rarrabu kowa ya saita,wasu kuma daga cikinsu suka shiga,saida na wajen suka tabbatar komai normal kafin suka shigo.
Ɗakuna a cikin wajen sukan guda goma,saikuma filin tsakiyar wajen wanda yafi ɗakunan girma,babu koma a cikin wajen sai warin tsatsa da kuma motocin yaƙi guda uku.
Duddubawa suka farayi kowanne daki,abinda suka samu ya basu mamaki matuƙa.
Dukka cikin wajen makaman yaÆ™i ne kala kala,harda wanda ba’a yarda ayi amfani dasu ba.
Hakan bai basu mamaki ba kaman ruwan wasu allurai dasuka samo a wajen.
Kawosu sukayi kan wani babban tebur a tsakiyar wajen sukayi,kowa ya zubawa abubuwan ido baya cewa komai.
“To yanzu waÉ—annan alluran akan wa za’ayi amfani dasu kenan,tabbas gen abdu manga ba baÆ™aramin murum mai hatsari bane,dolene mukai wadannan abubuwan zuwaga headquarter,domin ayi mummunan bincike akai”
“Hakane dama dole mu fitadasu bilal,ta hakane za’a yanke masa hukunci,sannan kuma mu É—au fansar abokanmu da suka mutu a wajen yaÆ™i saboda mummunan aikinsa,irinsune suke sakawa a zagi sojoji kuma a dungayimusu kallon Azzalumai”
Fara tattara kayan sukayi da niyyar tafiya dasu,duk abinda suke Sameerah na tsaye tasaƙala hannunta tana kallonsu,saida suka gama haɗa komai kafin ta sheqe da wata arniyar dariyah tana tafa hannu.
“Captain maryam,da kuma captain haidar kuda mutanenku haÆ™iÆ™a kunyi Æ™oÆ™ari sosai,da tun lokacin da kuka fuskanci akwai wata matsala kukayi shuru,da baku kawo kanku mahallakarku ba,amma yanzu kam aikin gama ya riga yagama kun haÆ™a raminku da kanku.
Kuskurenku É—aya shine bari da kukayi na san shirinku.
Saitata da bindiga bilal yayi zai harbeta,da sauri Bombee tayi saurin riƙeshi ganin abinda take riƙe dashi.
“Yana harbina zan dannan abinnan,duk wanda nice na saka musu na’ura ba haidar ba to zata tarwatse a cikii Æ™irjinsu tareda Zuciyarsu”
“Me kina nufin a wajen zuciya kikayi injecting É—in na’urar Sameerah,amma kinsa ba’a saka waje mafi hatsari,shiyasa dana cemiki wajen Æ™irjina naga ciwo kikace cokata kikayi baki sani ba?”
Da murmushi ta daga masa kai alamar eh.
Juyawa yayi ya kalli inda Bombee take,fuskarsa dauke da nadamar abinda ya faru,domin gani yake duk laifinsa ne Sameerah tasan shirin su,da kuma abinda zasu aikata.
“Karki damu maryam,har yanzu muna da damar yin nasara,karku damu ku banasaka muku a wajen da zatayi muku illah ba,sannan nariga na danna tawa na’urar,nasan division É—ina sun karbi sakon,kuyi saurin barin wajennan yanzunna kafin lokaci ya Æ™ure”
Jijjiga kai Bombee tayi hawaye na ziraro mata,ba abinda taki jini irin ganin haidar É—in a haÉ—ari.
“Hhhhhh kunfah riga kunzo hannu,babu wanda zai tsira daga cikinku,bari kuga na fara da wasu”
“Tana gama faÉ—in hakan ta danan jar danjar datake hannunta,tass kakejin a Æ™ara a Æ™irjin mutane biyu,da bilal da kuma Haidar”
Wata irin gigitacciyar ƙara Bombee tayi tareda ƙiran sunan sa kaman maƙogaronta zai fice.
A
Da gudu ta nufi inda ya tsaya akan gwiwoyinsa dafe da ƙirjinsa,kallonta yayi da idanuwan da suka rasa rayuwa a cikinsu,
“Bombee Æ™awata,naso maidaki matata saidai hakan bazai taba yiyuwa ba,da alama banine mijinki ba Bombee,koma waye zai kasance mijinki kice masa yayi sa’a, Bombee kiyafemin abinda nayi miki daga haÉ—uwata dake,sannan ki nema min gafarar iyayena ma,ina sonki sosai”
Daga haka yafara faÉ—an kalmomin da batajin abinda yake faÉ—a har yayi shuru.
Jijjiga kai tafarayi tareda cewa,
“Bazaka mutu ba Haidar ina alÆ™awarin da kamin na ganin ranar dazan dau fansa,indan naÆ™i aurenka ne ka tafi,zan aureka Haidar kada ka barmu banida tamkar ka a wannan wajen,bazan juri rashinka ba,karkamin haka na roÆ™eÆ™a haidar,nima inasonka a har cikin raina”
Tana tsugunne a wajen taji khamees yana kiran sunanta.
“Maryam maza ki bar wajennan akwai haÉ—ari”
Kafin ya rufebaki taji alamar samu mutane suna shigowa,saitata Sameerah tayi da bindiga zata harbeta,tun kafin ta harbetan ita ta fasa mata hannun da take É—auke da bindigar,kafin ta karamata taji khamees ya fizgeta sun bar wajen.
Ƙoƙarin kwacewa take tana kallon wajenda gawar haidar take,
“Khamees kabari na É—akko shi tukunna,sannann nayi daga daga da tsokar waccar tsinanniyar,sannan ne zan bika mubar wajennan”
“Kai Maryam ki fahimata mana,muna cikin yanayi mafi muni,dolene mubar wajennan,shikansa haidar idan yana raye zaiso ki bar wajennan”
Yayi maganar yana share guntun hawayen dayake zubo masa.
“Inji uban waye ya mutu,bazan bar wa…….”
Ɗan duka yakai mata a wajen ƙasan kunnenta,nan da nan kuwa tayi shuru ta suma,kinkimar ta yayi yanufi fita da ita daga wajen.
Muryar Sameerah yaji wacce take ihun hannunta tana shunensu.
Shida Hilyaan ne kadai idonsu biyu,sai Bombee wacce yasaka a kafaÉ—a,gudu suke falfalawa a cikin daji har saida suka gaji suka tsayah.
A bangaren Sameerah kuwa sojojine suka shigo wajen,domin saƙon Haidar ya isa garesu,iya Sameerah ce kawai a wajen tana riƙe da hannunta,tana ganinsu tasaka kuka tareda cewa.
“Yallabai ka taimakeni,captain maryam ce ta kasheshi tareda É—aya Sojan,nima dan bata sameni bane wajen makasa da ta kasheni,inbaka yarda dani ba ka duba bullet É—in da shaidar dukka natane,a Æ™irjinsu dukka ta harbesu”
“What ina take,sannan mai kuke a wajennna”
“Uhm in labene jiya sai naji suna zasu jawoshi wajennan su kasheshi,to dana biyosu saina ga sun harbeshi,shi wancan yana cikinsu,amma sai yace bazai yi shuru ba,shine shima suka kasheshi,danayi kokarin cetansa nima ta harbeni,tana shirin kashenine haidar yace ai yatura saÆ™o division É—inmu,shine sukaji tsoro suka gudu”
“Itada waye a tareda ita?”
“Uhn…….uhhh itada Mataimakinta ne captain Khamees”
Sameerah tana gama basu labarin ƙaryar ta suma,gawar haidar da bilal suka ɗauka inda a daren aka baza neman su Bombee a cikin garin abuja da kewaye.
Labari yana isa kunnen gen Muhammad yafaÉ—i jininsa ya hau,da farko bai gaskata abinda Bombee ta aikata ba,saida shaidu suka fito,kuma ta rashin bayyanar Bombee yasa yafara yadda hakanne,saidai duk yadda yayi tunanin menene dalilinta na hakan yakasa ganowa.
A kwana basufi uki ba labarin abinda Bombee tayi ya karafde cikin barrack da kewaye,kowa banda tsinuwa babu abinda yake yimata.
“Lokacin da Bombee ta farfaÉ—o a cikin kogon da suka buyah,taji labarin abinda yake faruwa,wanda Hilyaan ta jiyo musu,tunda ita babu wanda ya zargeta,zuciyarta ba Æ™aramin tafarfasa tayi ba.
Yanzu kenan da wanne ido zata kalli iyayen haidar,bayan suna mata kallon wacce ta kashe musu É—ansu.
“Khamees inada wajen dazamu je,dolene mu bar garinnan kafin komai ya lafah,dolene na dawo na É—auki fansa,ke Hilyaan ki koma bakin aikinki kawai”
“Ahah cap……anty maryam,na ajiye Aikin soja harsai ranar da sunanki ya wanke zan kasance taredake idan harkika bani damar hakan”
Shuru Bombee tayi batada abin cewa,dan gaba É—aya duniyar tayi mata zafi a lokacin,haka zata Æ™are rayuwarta kenan ana yi mata sharrin kisa,anya kuwa zata iya sake yarda da wani ma????……
***DAWOWA LABARI***
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________