ππ²π©π’π§π
π« ππππΌπ πΏπΌππ’π…..!!π«
π©ππππ π¨ππ πππ πππ€π»
πͺππππππ 7οΈβ£0
…….Zaune take a falo dafe da kanta dake matuΖar sara mata saboda Ιacin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta Ιauke da tunanin sake kiran Daddy Ιin kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya Ιagawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya Ζwace mata. Ζaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, βMy Daughter yau babu gaisuwa ne?β.