Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 5

Sponsored Links

💖💖 *NIHAAD* 💖💖

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

 

~~~~~

 

Tun da Nihad ta kwara masa ruwan bai dago kansa da ya sunkuyar ba, lkci daya kamanninsa suka sauya, sae kuma dai ya daga kai ya kalleta, Tana hararansa tace “To wllh kaji ka sani, ka rasa aikinka a karkashin mu daga wannan moment din, yau ba sai gobe ba xan sa Abbana ya dau wani sabon driver din ya sallameka, baka yi deserving aiki a gidanmu ba…” Mai fruit din na girgiza kai rai bace yace “Amma baki da mutunci, baki da kirki, baki san darajan da Allah yayi ma d’an Adam ba, kuma uwa uba baki da tarbiya wllh…” Tayi masa wani matsiyacin kallo tace “Kai kuma wa ya sako da kai Malam? Kai a wa xaka sako min bakinka cikin lamarina? Ina ruwanka? Ko xaka tilasta ni in san darajan d’an Adam din ne??” Wani tsaki ta ja tana harararsa, Wani mutumi a wajen ya karbe a fusace yace “Xa ki samu dai dai dake a duniya wllh, ke yanxu irin tarbiyar da aka maki a gidanku kenan? Tir kuwa da tarbiyan gidan nan naku, tir da tarbiyan da iyayenki suka maki, idan haka arxikin ke sa mutane a hanyar halaka Allah ya hanamu…” Nan kowa na wajen yayi mata caaa, ko wanne na gasa mata magana son ransa har da masu xaginta, abun da tayi ya basu mamaki sosai ya kuma ta6a su, barin yanda suka ga khalil yayi shiru yaki ce mata komai, har da masu ce mata arxikin ma sai sun nemesa sun rasa, da surutunsu ya isheta ta ja dogon tsaki tace “Duk ku ji da abinda ya dame ku malamai, bani da ikon hukunta driver din gidanmu aka ce maku, ina ruwanku da abinda na masa banda sa ido irin na mutane” Tana fadin haka ta juya, sai ta kara jin ranta ya wani baci, yanxu ya xata yi da xuwa wajensu Husnah, kwata kwata bata son hawa adaidaita, duk k’uran duniya ya kare ma mutum, kuma ma ai ba girmanta bane taje Tahir guest palace a adaidaita Sahu, bata sake bi ta kan mutanen wajen ba ta tsallaka titi abun ta, bin ta da kallo kawai Khalil ke yi, mutanen wajen sai hakuri suke basa, wani dattijo dake tsaye shi ma wajen a kan idonsa aka yi komai ya dafa khalil cike da jimami yace “Kayi hakuri yaro, rayuwa ce, amma bari in baka shawara wannan aiki ba shine xai kai ka aljanna ba balle ka ji shakkun barinsa, ka ajiye masu makullinsu, da dai wannan axababben walakancin gwara ko dako ne kayi ka ci abinci, balle siffarka bai yi kama da ta rago ba, ga ka namiji har namiji, ka nemi wata sana’ar sai Allah ya dubeka, ni ko duk arxikin duniyar nan xa a tattara min amma a hada min da walakanci to wllh na hakura da arxikin gwara inyi ta xama da talauci na, balle irin wannan walakanci da cin fuskar da yarinyar da aƙalla xaka bata shekaru sha uku ko sha hudu tayi maka a kan titi a bainar nasi babu kunya babu tsoron Allah, sannan babu ladama a tattare da ita, aa gaskiya ka sake duba lamarin nan dai, Allah Ubangiji ya saka maka wannan cin xarafi da cin mutuncin da tayi maka” Wani matashi ne da gidansu ke nan bakin titin ya fito da wata jallabiyarsa yana kallon khalil yace “Ga wannan mu shiga wancan shagon sai ka canxa, Allah ya saka maka abinda tayi maka” Mikewa Khalil yayi ya amshi rigar yana kallon mutumin yace “Nagode sosai” shagon da ya gwada masa ya nufa, duk mutanen wajen suka bi sa da kallo cike da tausayi barin ma da suka ga ya ki cewa komai, ya shiga shagon, me shagon ya basa waje ya canxa kayansa, wayarsa dake aljihunsa ya fara cirowa ya dinga jujjuya wayar kafin ya ajiye gently a saman bench, canxa kayan yayi, me shagon ya taho masa da babban leda don ya linke tasa kayan ya sa a ciki, amsa yayi ya masa godiya sannan ya linke ya saka a ledar yana rike da ledar ya fito shagon, mai shagon ya kalli wayarsa da ya bari kan bench, ya d’an bude ido yana sake kallon wayar sannan ya kalli khalil da har ya wuce, da sauri yace “Malam ka bar wayarka” Dawowa Khalil yayi da sauri ya dau wayar, ya zira a aljihun jallabiyar, yana ɗan murmushi yace “Nagode kwarai” daga haka ya fita me shagon ya bi sa da kallo kamar me naxari. Mumy ce tsaye bakin gate ta dalilin kiranta da aka yi ganin Nihad can tsallake ga jama’a a tsattsaye sun taru an sa ta a tsakiya, Mumy na kallon Nihad tace “Lafiya Nihad, me ke faruwa?” Nihad ta rungume hannunta tace “Mumy ko ba wancan driver din bane, wllh bashi da kunya ko kadan” Mumy tace “Me yayi maki?” Nihad tace “Wai fa Sajida ce tace min tana anguwan nan, dama akwai wani textbook da nake son amsa a wajenta, shine nace ya d’an ajiye ni, can gaba ne ba nisa, shine fa yake gaya min maganar banxa, shi wai baxai je ba” Mumy tace “Sai aka yi yaya?” Nihad na yatsina fuska tace “Shikenan, su kuma wa encan bansan me yasa suka taru haka ba” Mumy tace “Ina drivern?” Nihad ta kalli tsallaken titin ta ga ya fito wani shigo da jallabiya, Kafin ta ce komai Mumy tace “Mu je wajen nasa” Da sauri Nihad tace “Aa Mumy kyalesa kawai, ni ai ban biyesa ba, haka yayi min daxu ma a gidan Baffa, aa kawai dai ki bar sa” Mumy tace “Tsallaka mu je nace, bana son surutu” Nihad tayi shiru ganin Mumy ta tsallaka ta bi bayanta, amma gaba daya she isn’t comfortable, Mumy ta nufi driver, yana ganinta yace “Hajiya har kin fito?” Tace “Aa ya sunanka?” Yace “Ibrahim” Tace “Ohk, ya ku ka yi da Nihad?” Gaba daya mutanen wajen kallonsu suke, Nihad dai na tsaye ta ki karasowa ta wani sha kunu, Mumy ta kalleta tace “To karaso mana Nihad” tana tafiya a hankali ta karasa inda suke tsaye da Umma ce baxa ta ji wani shakku ba xata biyo amma Mumy bata da tabbas, Mumy na kallon khalil tace “Ina jin ka” Nihad ta amshe tace “Na fa gaya maki abinda ya faru Mumy, nan nan wajen Sajida xai ajiye ni in amso textbook shine yake min maganar banxa har sa zagina, ni ko biyesa ban yi ba” Mai fruit dake tsaye shi ma ya saki salati yace “Wllh karya take Hajiya, ba haka aka yi ba, ai ina nan a xaune, bokiti guda na ruwa ta dauka ta kwara masa kawai ba laifin tsaye balle na xaune, baki ga ya canxa kaya ba, duk a kan idonmu aka yi komai” Mumy bata bari me fruit ya rufe baki ba ta tsinka ma Nihad mari, Nihad bata gama recover ba ta kuma sauke mata wani, wanda hakan ya ba mutane da yawa dake wajen mamaki, dama ashe ana hukunta ‘ya yan masu kudi, hakan ya kuma mugun burgesu, fuska daure Mumy tace “Wuce ki basa hakuri” Nihad da tunda aka haifeta tana jin ba a ta6a marinta ba ta dinga ganin dishi dishi, ta dafe kuncinta, wani tsawa da Mumy tayi mata sai da ya dada hargitsa ta, Mumy tace “Tafi ki basa hakuri nace kar 6allaki a nan” Bata san sanda ta nufesa ba ta tsaya a gabansa hawaye cike idonta cikin rawan murya tace “Kayi hakuri” Shi dai kallon Mumy yayi yace “Hajiya kiyi hakuri duk bai kai haka ba” Mumy ta bude handbag dinta fuska a murtuke ta fiddo dubu biyu ta jefa mata nan kasa tace “Ki tsayar da Tricycle ki kama hanyar gida yanxun nan, kuma ina nan biyo ki a baya, dama don kiyi displaying bad altitude dinki kika biyo ni kenan, xan yi maganinki” Kuka kawai Nihad take tana jin kamar ta kwanta nan kasa tayi ta birgima ko xata ji sanyi, ko damuwa da mutanen dake kallonta wajen bata yi ba, Mumy na kallon khalil tace “Kayi hakuri don Allah Ibrahim, ita kuma xa mu hadu a gida” Daga haka Mumy ta tsallaka ta koma cikin gidan rasuwa. Nihad ta bude jakarta tana kuka sosai ta ciro wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing Abba ya daga ta kara rushewa da kuka me karfi tace “Abbaa” Sai ta xama abar kallo a wajen, Abba yace “Subhanallah what happen Nihad?” Kin cewa komai tayi banda kuka babu abinda take rera masa, Abba ya katse wayar ya kira Mumy, tana dagawa yace “Where is Nihad?” Mumy tace “What about her?” Abba yace “Ta kirani yanxu tana kuka, and she is not responding to my questions” Mumy tace “Ka rabu da ita, ai muna tare, sai anjima” Daga haka Mumy ta katse wayar. Sai bayan magrib Mumy ta dawo gida, Khalil yayi parking ya sauka daga motar, Mumy ma ta sauka, da ladabi ya mika mata makullinta, ta amsa tace “Nagode, kuma kayi hakuri da abinda yarinyar nan tayi maka ka ji” Ya d’an yi murmushi yace “Ba komai Hajiya, nagode” Juyawa tayi ta shiga cikin gidan, shi kuma ya nufa gun mai gadi. Umma na jin shigowar motar Mumy ta shigo main parlor, Tana tsaye tana jiranta har ta shigo, Umma tace “Kin bani mamaki Maryam, yanxu a kan wani shegen driver xaki kama yarinya a titi cikin mutane ki doka sbda rashin sanin ciwon kai?” Bata ba Mumy space din magana ba ta ci gaba rai a bace, “Wallahi kin ban mamaki da gaske, ke a dole sai kin xama me kirki me mutunci a idon duniya? yanxu menene amfanin abinda kika ma Nihad a bakin titi a kan wani matsiyacin talaka ɗan iska can? To wllh in dai ba Ibrahim ne ubansa ba sai ya bar gidan nan yau, aikinsa ya kare a gidan nan, idan yayi ma Nihad ya ci bulus har kuma da tsaraban mari da duka da ya ja mata to wllh babu er da xai ma hakan a gidan nan ya kwana kalau, ba a haifi Ubansa yace xai ma Nihal ko Amina haka ba, don haka yau ba sai gobe ba xai kama gabansa, mu bama hulda da yan iska, sau biyu kenan duk a yau ta kawo min kararsa, ashe d’an iska Habibu ya turo ma Alhaji ba a sani ba, to kuwa xai kama gabansa yanxu yanxun nan, kwanansa daya dubi isa da mulki da yake gwadawa ya yanmu?, nan gaba ai har Alhajin ma cewa xai yi baxai tuka a mota ba” Mumy bata kuma tsayawa ta saurareta ba ta wuce part dinta. Mai gadi na kallon Khalil bayan ya gama shanya kayan da Nihad ta xuba masa ruwa yace “Hakuri kawai xaka yi, amma lallai yarinyar nan shaidaniya ce a siffar mutum…” shi dai khalil bai ce komai ba, mai gadi yace “Ga can abinci da aka kawo mana, na debar maka naka na ajiye” Khalil yace “Aa na koshi, yanxu wanka nake so xan yi” Mai gadi yace “To mu je in raka ka bangarenku” A tare suka nufi boys quarters din bayan mai gadi ya dauko wata er jakar kayan Khalil da ya bari a dakinsa tun xuwansa da safe, suna shiga parlon banda warin kartin maza babu abinda yake, ko ina soo dirty and unkept, ga saminu yayi bake bake kan 3 seater yana kallo ga plate din abinci da ya ajiye saman kujeran, Isiya na one sitter yana shan rake da yake tarawa nan kasa gefensa, Shafi’u kuma na 2 seater ga tasa plate din abincin ya gama ci ya bari saman kujera, Mai gadi ya nufi Saminu yayi kasa da murya yace “Saminu ko xaka ɗan sam masa waje ya dinga kwana a dakinka, ka gansa bashi da matsala wllh…” Ko rufe baki Mai gadi bai yi ba Saminu yayi saurin cewa “Aa nima dakin yayi min kadan” Mai gadi ya kalli Isiya dake jin abinda ya ke cewa, kafin mai gadin yace masa komai yace “Toh wai ba falo kace xai dinga kwana ba” Shafi’u yace “Shi dai na gani, Duka dakunan kaga ai babu waje, wa ke son takura” Khalil ya amshi jakarsa dake hannun mai gadi, mai gadi yace “Ko xa mu je can dakin nawa ka dinga kwana” Khalil yace “Aa kar ka damu, kayi komawar ka bakin gate” Yana fadin haka ya nufi space da aka tanadar domin dinning area a parlon, Kofar da ya gani ya bude ya ga kitchen ne, ya dinga kallon yanda suka mayar da kitchen din kamar na mahaukata duk da ba girki suke ba, tsintsiyar da ya gani wanda bai ga alamar ana amfani da shi ba ya dauka, ya hau share dinning area din, mai gadi ya juya ya fita daga parlon da sauri jin kamar ana horn. Cikin yan mintuna khalil ya gama gyara area din har da mopping, yana gamawa sai ga mai gadi ya kawo masa wani yakunannen zanin gado, amsa yayi ya shimfida a saman tiles din wajen, sannan ya bude window, ya shiga bandakin dake parlon, still yayi yana bin bathroom din da kallo, ko public toilet is far far better and neater than this, fita yayi ya koma gun mai gadi don ya amshi omo. Abba yayi shiru yana sauraron Mumy, Mumy ta ci gaba tace “Kawai ita Hajiya duk wani abu na cin mutunci da cin fuska shine dai dai a wajenta, ai wannan ba rayuwa me kyau bane, har take cewa ka sallamesa, da yayi me? Ruwa fa ta dauka gun me kayan marmari ta watsa masa a jiki, kawai dai ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, haka ta sa Habibu a gaba daga baya ta gaji ta saukar da kanta, mai aikin gidan nan ba dadin Nihad take ji ba, Nihal kuma ba haka take ba, na rasa wannan baƙin hali irin na Nihad ni kam, ni dai ba haka taga nake mu’amala da jama’a ba balle tace, kai kanka ba haka mu’amalar ka da jama’a yake ba, to halin wa ta yo haka, idan ba shiga hakki ba wllh kar ka fara ce ma bawan Allahn nan komai, a kan me xata ce sai ya bata makullin motata ta tafi gantalinta da yamma sbda rashin kunya ma bata yi shakkar cewar motar tawa bace, kuma naga ai ba ita ta basa makullin ba ni na basa, to a kan me xai bata…” Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, ganin ta gama fadin abinda xata fada yace “But that doesn’t warrant u to slap her publicly Maryam, why not ki bari idan kuka dawo gida ki hukunta ta?” Mumy tace “Wato na goyi bayanta kenan Yallabai, ai yanda tayi rashin kirkinta a bainar jama’a gwara nima na hukuntata a cikin jama’ar dai dai kenan, ni fa i am not in support of walakanta d’an Adam Yallabai, kuma babu wani da ya fi wani a wajen Allah sai wanda yafi tsoronsa, idan ma xaka share xancen nan ka je ka huta to gwara ka share” Abba bai kuma cewa komai ba, Mumy tace “Can i excuse my self?” Yace “Alright” ta mike tayi masa sai da safe sannan ta fita, Umma ta fito daga bedroom din Abba don duk ta ji yanda suka yi da Mumy, tana ta6e baki tace “Yau ni naga neman suna kiri kiri gun talakawa, ita a neman sunan ma ta rasa inda xata dinga yi sai wajen talaka? Ai kamata yayi ta dinga kutsa kanta cikin manyan mutane ana yi da ita, ta nan ne neman suna xai mata rana, amma ke kice duk abinda talaka yayi dai dai ne, a dole sai kin burge?” Abba ya mike ya fita daga parlon, compound ya fito, dai dai nan khalil ya fito daga dakin mai gadi ya amshi omo, ganin Abba ya nufesa ya gaida shi da ladabi, Abba ya amsa yana kallonsa yace “Ibrahim, a dinga hakuri da yaran nan don Allah, sannan duk sanda Nihad ta sameka da batun amsan makullin mota kana da number ta ka kirani, idan wanda xaka bata ne sai ince ka bata, don ba wai bata iya driving ba, tana driving to where ever she wants to, just sbda security purpose ne bana barin suyi driving din da kansu, so kar kayi zaton bata iya driving din bane, and u gat respect them all kamar yanda xaka yi respecting dina ka ji” Khalil da kansa ke kasa a hankali yace “Toh in sha Allah Alhaji” Abba yace “Sun baka daki a can boys quarters din ko? Don nasan akwai empty room da Habibu ya bari” Khalil yace “Ehh an bani” Abba na kallon omon hannunsa yace “Wanki xaka yi da omo?” Yace “Eh xan wanke bandaki ne” Abba yace “Ohk good, wannan ai yayi kadan, no problem xa a kawo maka daga cikin gida yanxu” Yace “To nagode Alhaji” daga haka Abba ya juya ya koma cikin gida, khalil ya koma can boys quarters din. Abba na komawa part dinsa ya kalli Umma yace “Ki ba ko Sudais ne blanket with some detergents ya kai boys quarters” Umma tace “A kai ma wa a can?” Abba yace “Driver” Umma tace “Aa da dai kaje gun uwar dakinsa ta bada a kai masa, ni kam bani da old blanket, kaji Alhaji da wani xance, shine yace ka basa blanket din?” mikewa Abba yayi ya fita, ya tafi bangaren Mumy, tana daki ya sameta yace “Maryam blanket xaki ba Sudais with some detergents ya kai ma driver din can” Mumy tace “Sudais ai yayi bacci yallabai” Abba yace “To bani” Wani blanket dinta ta dauko, sannan ta dau pack din omo da sabulu with toothpaste ta hada ta ba Abba, Abba ya amsa ya fita dakin, a stairs ya hadu da Nihal xata dakinsu, tace “Abba where are u going with the blanket” Yace “Boys quarters xa a kai ma drivern can” Nihal tace “Ohk, bari in kai Abba” Abba yace “Good” Amsa tayi daga hannunsa don dama da Hijab a jikinta ta juya ta koma downstairs ta nufi kofar fita main parlor, boys quarters din ta nufa, tayi Knocking duk da kofar a bude take, isiya ne ya karaso ganinta ya gaisheta da ladabi xai amshi blanket din yace “Wanki ne Hajiya?” Tace “Aa, ina sabon driver yake?” Jin haka Khalil dake bandaki xai fara wankewa ya fito ya nufi kofar, kallonta ya dinga yi don da farko ya xata Nihad ce, amma sai yaga ba itan bace don wannan fuskarta bai rabo da murmushi, ya amshi abinda take mika masa, yace “Nagode sosai” Juyawa tayi ta sauka chalet din, ya koma cikin parlon yana kallonsu Isiya yace “Ku yi kokari ku bar barin kofar nan a bude sbda sauro” Da ido duk suka bi sa, lkci daya suka kya6e baki, ya ajiye blanket din ganin omo, sabulun wanki da na wanka sannan ga Toothpaste ya kwashe su gaba daya ya wuce bandakin, ya bata fiye da minti talatin yana wankin bandakin don sae da omon yayi rabi, lkci daya bandakin ya dawo hayyacinsa, wanka yyi ya fito, ya kulle bandakin da makulli sannan ya cire makullin ya koma dinning area, ya shimfida babban bargon wanda laushinsa ba a cewa komai, ya bude window dake wajen sannan ya kwanta ya rufe ido, bayan minti sha biyar yaji ana magana, ya bude ido ya ga Saminu tsaye a kansa, shiru yayi yana kallonsa, Saminu yace “Makullin bandaki da ka kulle xaka bada” Khalil yace “Ohk, dama kuna amfani da bandakin kenan?” Saminu yace “Yo me xai hana” Khalil yace “Ohk, shine ku ka bar shi yanda na samesa?” Bai jira Saminu yace komai ba, yace “Amma dai kamar babu bandaki a dakunan naku iya wannan kadai ne ko?” Saminu yace “Akwai mana, amma wannan din muke shiga gaba daya ai” Khalil ya ciro makullin da ya ajiye a aljihun gaban rigarsa ya mayar aljihun wando sannan ya gyara kwanciyarsa ya rufe ido, xuwa yanxu daga Isiya har Shafi’u na tsaye parlon suna kallonsa gaba daya, Saminu yace “Toh wai kai gayen nan me kake nufi tukunna ma dai” Mikewa Khalil yayi ya tsaya sai ga Saminu ɗan tsut a gabansa, Khalil na kallonsa da kyau ya tsaya dab da shi yace “Baxan bada ba nake nufi” Shafi’u ya koma ya xauna haka ma Isiya suna kikkifta ido, sui sui Saminu ya bar dinning area din shi ma yana gwaggwale ido.

 

07087865788✍🏻

Leave a Reply

Back to top button