Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 46

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

46

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

 

Lalla Khadija da Lala Hafsat tare da  wasu mata cousing Sister sa ne suka fara yi masu liƙi, cike da nutsuwa da kuma tarin farin ciki dake bayyane asaman fuskokinsu.

Sarkin Zagi dake can gefe riƙe da Microphone ya matso dashi kusa da bakinsa kana yace.

“Maraba da Lalla Hafsat, Lalla Khadija, Autah Rahma tare da sauran Yayyun ango da ƙannensa”.

Su kuwa cike da farin ciki suka ci-gaba dayi masa liƙi bayan sun gama Lalla Khadija ta ɗan matso kusa dashi tace.

“Kayi sauri ka buɗe fuskar Amayarka ta juya ta fuskanci dukan family”.

Ta ida maganar tare da juyawa suka bar wajen.

 

Shi kuwa Moddibo hankali ya ɗan ƙara matsota, cikin yanayin da shi kansa ya gaza ta tacewa, ya ɗago lallausan tafin hannunsa tare da ware ƴan yatsunsa ya kama kafaɗar ta kana ya juyar da ita  ta fuskanci Al’ummar cikin falon baki ɗaya.

Lokaci ɗaya cikin falon ya kaure da tafi Raf-raf-raf yayin da duk wanda yayi arba da fuskar Khausar suke kallonta cikin tsananin farin ciki da ganin baiwar kyau da Ubangji ya zuba mata suke faɗin.

“Wowwww Masha Allah”. Shine abinda mafiya yawansu suke faɗi.

Lokacin guda kuma wasu zugan matasa wanda sun kai goma sha biyar suka nufo kansa cike da izzah, nutsuwa, ƙasaita suke musu liƙi yayin da sautin busar sarewa da ƙaran algaitu ke tashi da sassayan kiɗan jita…

Moddibo kuwa ahankali ya ɗan juya kwayar idanunsu, ya kalli Khausar, sai kuma ya fesar da wani irin sassayyan numfashi, tare da matse hannun ta dake cikin nasa, cikin wata irin sassautacciyar muryansa yace.

“Toh Mazari Sarkin rawa.

ba kinji Busar sarewa da kiɗaba, kiyi rawa na.

Kiga abinda zanyi miki”.

Cikin narke fuska tace.

“Toh ni nace zanyi rawane”.

Ɗan juyo fuskarsa yayi ya ɗan kalleta tare da hura mata iskar bisa idanunta ganin yadda take jujjuyasu, numfashi mai nauyi ya fesar tare da cewa.

“Uhmm kimayi mana ki gani in ban karya ƙugun naki ba!”.

Kallonsa tayi da shanyayyun idanunta wanda yasa bai san lokacin da ya ƙara rumtse tafin hannunsa da nataba.

Ita kuwa cikin yin mui-mui da da bakinta kana ta tsukesu Pinch lips ɗin ta tana ɗan motsawa ahankali alamar magana take ƙasa-ƙasa sai dai baya jin abinda take faɗa.

Sunkuyawa kanta kaɗan yayi tare da cewa.

“Ni kike turawa baki ko?”.

Ɗan kallonshi zuciya cike da ganin girmansa kimarsa gami da darajar da kuma wani matsayi na musamman da takeji a jikinta wanda yake sakar mata kasala da son ƙamshin jiki nai,

Hararanta ya ɗanyi kana a hankali yace.

“Ci gaba da tura min baki, zanyi mgnin lips en nan, idan na tsinkesu zanga dame zaki kuma yimin rashin kunya kije ƙiyama kuma Allah ya ƙonasu tunda mijinki kikeyiwa tsiwa”.

Wani irin lumshe idanunta tayi sabida yadda taji kalmarsa ta karshe ta ratsa mata jiki da zuciya har yasa tsikar jikinta tashi.

Yanayin yanda suke magana ƙus-ƙus ne da yadda suke kallon juna yasa Ummi dake can wajen zamanta, ta saki amintaccen murmushi cike da jin daɗi, mgnar Jameel ɗinta ya tabbata, domin duk wanda ya kallesu zaiyi zaton hirar soyayya suke.

Yayin da zugan matansa suka cigaba dayi masa liƙi wasu baza su wuce sa’annun saba wasu kuma baza su gaza shi ashekaru ba Zakariyya da Ibraahim dake tsaye suma suka shiga cikinsu suna musu Liƙi…

Sarkin Zagi dake riƙe da Microphone ya gyara masa zana tare da kaiwa bakinsa kana yace.

“Duk wa’anan Cousing Brother’s ɗin Ango ne, Ƴaƴan Baffanunsa,da kuma ƴaƴan Goggonninsa”.

Bayan sun gama Liƙin suka juya suka fita kana suka koma wajen zamansu.

 

Ibraahim kuwa kallon Moddibo yayi kana ya mishi alama da hannu su zauna.

Anutse Moddibo ya gyaɗa masa kai kana cikin nutsuwarsa ya koma ya zauna itama Khausar ta zauna gefensa kasancewar 2sitter ne.

Hakan yasa suka samu kusanci tsananin su bayansu flowes ne masu kyau da ƙamshi sai kuma Hadimai da suma ke tsaye bayansu.

Wani irin yalwataccen murmushi mai cike da Aminci Innayi ke saki tana mai cigaba da kallonsu.

 

Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa mamakine ya kamashi aransa yace.

“Toh dama yaran nan suna soyayya da junansu ne? Koko yaya”.

Sosai yake mamakin yanda suke gudanar da komai tamkar akwai da ɗaɗɗiyar soyayya da shaƙuwa atare dasu.

Haiydar kam hotuna da Video yake ɗaukar su,  kai tsaye yake turawa cikin groups ɗinsu na family.

 

Cikin nutsuwa da ƙasaita kana da yalwataccen farin ciki Abualeey da Didi suka tasu,Yayin da Waziri, Galadima, Sarkin Fada, da sauran manya suka mara musu baya, daga can bayansu kuwa Hadimai ne ke biye dasu.

Suna isa dai-dai mazauni Moddibo da Khausar suka fara yi musu Liƙi cike da girma, sai kuma aka ƙara ssutin Busa sarewa da kuma sautun jitan daya karaɗe baki ɗaya ilahirin wajen…

Didi dake cikin wata shiga na alfarma cikin jin daɗi ta ɗan sunkuya tare da sanya hannunta na dama ta ɗan ɗago Fuskar Khausar ta kalleta.

Ido ta lunshs sabida jin lokaci ɗaya yarinyar ta kwanta mata arai, tana jin masifar ƙaunar yarinyar sake sunkuyawa tayi ta rungumeta,  sai  kuma ta ɗago tare da tallabe fuskan Khausar kana ta sanya laɓɓanta akan goshinta tayi mata kiss.

Fuskarta ɗauke da amintaccen murmushi tace.

“Allah ya miki albarka, Ubangji Allah yasa kin shigo da ƙafar dama, Allah ya baku zaman lafiya mai amfani, mai albarka”.

Lumshe ido Khausar  tayi yayin da take jin nutsuwa da ƙaunar matar na ratsa sassan jikinta…

 

Abualeey kuwa hannunsa na dama dake ɗauke da Zoben azurfa ya ɗaura akan Moddibo tare da faɗin.

“Allah ya maka albarka Ubangji Allah ya albarkanci rayuwarka. Allah ya baka zaman lafiya da matarka!”.

Haka nan Moddibo yake jin wani irin farin ciki ji yake yau kamar ranan Sallah ne, sabida wani irin nishaɗi da yakeji tamkar wanda aka yiwa bushara da Aljanna asaman lips ɗin sa yake amswa da.

“Ameen Ameen”.

Haka nan yake jin farin cikin addu’ar da Mahaifiyar sa da Mahaifinsa keyi masa…

Liƙi suka cigaba dayi musu suna zuba musu kuɗi kamar ba’asan darajar su ba…

 

Sarkin zaki kuwa hannunsa riƙe da Microphone yace.

“Hattara dai manyan bisa kanku wan’nan sune manyan ƙasar Morocco baki ɗayanta. Jiga-jigan manyan cikin birnin Rarat baki ɗaya manyane bisa kanku ku amsa da Ameen dan addu’a ce ta manyan Ameen.

Baki ɗaya mutanen falon suka amsa da.

“Ameen”.

Saboda sun san cewa addu’a da fatan Al’khairi iyayensa ke masa bayan sun gama suka juya suka tafi…

 

Aunty Ruƙayya da farin ciki ya gama cikata ganin yanda Moddibo da Khausar sukayi bala’in da cewa ga kuma yanda Moddibo ke raɗawa Khausar magana akunne wanda duk mai kallonsu a matsayin zantukan masoyane sukeyi yasa ta kalli Hajiya Bunayya wacce itace akusa da ita kana tace.

“Dan Allah Hajiya kalli Khausar da Moddibo tamkar dan junansu aka halicce su, haƙiƙa sun dace da juna Allah yayi Khausar zaɓi da mafi Al’khairi Ubangiji ya kawar da idanun maƙiya akansu”.

Yaƙe Hajiya Bunayya tayi Amaimakon tace Ameen sai ta sunkuyar da kanta tayi tare da cewa.

“Aikam”.

Wani irin zafi da ƙuna zuciyarta keyi ba zato taji hawayen hassada da ƙyashi na zuba daga idanunta ina ma ace Aminanta ce ke cikin wannan Daular duniya..

 

Daga can cikin falon kuwa Wasu zugan Maza da Mata manya ne suka nufi wajensu Moddibo da Khausar.

Sarkin Zaƙi na ganinsu ya ɗaga sautin muryarsa tare da cewa.

“Hattara dai Ango da Amarya ga Baffanayenku nan da Goggoninku”.

Ahankali Moddibo ya ɗaga kai yana kallonsu cikin wani irin yanayi mara misaltuwa wai yau shine acikin ahalinsa ana gabatar mishi dasu sahu-sahu.

Su kuwa cike da tarin ƙaunarsa suka riƙa yi musu liƙi da kuɗaɗe masu tarin yawa.

 

Aunty Hawwa ce ta kalli Aunty Hajara wacce suke daga ɗaya gefen Hajiya Bunayya kana Aunty Hauwa tace.

“Masha Allah Kinga yanda ake zubar da kuɗi tamkar ba’a cikin tsadar rayuwa”.

Dariya Aunty Hajara ta sanya tare da cewa.

“Aikam acikin wannan ahalin. Basuma san wani abu mai suna talauci ba komai nasu cikin wadata suke”.

Da ƙyar Hajiya Bunayya dake sauraransu ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci daya tokare mata maƙoshi Allah ne kaɗai yasan tashin hankali da ɗimuwar hassada da take ciki…

 

Haka aka riƙa gabatarwa Moddibo da ƴan uwansa

Abokan arziƙi, ƴaƴan Baffaninsa. Da ƴaƴan Goggoninsa sahu-sahu.

Kana bayan an gama aka shiga gabatar masa da Hadimansa wanda zasu riƙa yi masa Hidima.

Bayan an gama wannan.

 

Jakadiya dake tsaye gefenshi riƙe da wasu Ƙore guda uku ahannunta babban na cike da madaran Shanu fari ƙal.

A hankali ta ajiye su agaban timtim da ƙafan Khausar ke kai sai kuma ta ɗauki ƙamarin Ƙwaryan ta ajiye acikin wanda yake ɗauke da ɗanyen madaran Shanu.

 

Kana ta ɗauki ɗayan mai matsakaici, tare da  matsowa gefen Moddibo ta risina tare da cewa.

“Bismillah zaka wanke ƙafan Amarya da madara da fatan Ubangji Allah ya kareta daga sharrin da yake cikin fadar nan kana Allah ya haɗa ta da Alkhairan dake ciki”.

Juyawa Moddibo yayi tare da kallon Ibraahim da ya dafa kafaɗarsa.

 

Asma’u kuwa Lumshe idanu tayi tana kallon ƙawarta cike da annashuwa kana tana mamakin tarin al’adunsu masu matuƙar kyau da tsari babu wani abu na bidi’a aciki komai bisa tsari suke gudanar wa…

Ibraahim kuwa dake dage da kafaɗarsa cike da so da girmamawa yace.

“Bismillah Yah Aleey  Don Allah kayi mana”.

Lumshe idanu Moddibo yayi tare da ɗaga juya kanshi ya kalli Innayi wacce keji tamkar ta taso tazo ta ɗagashu tasa yayi dukkan abinda ya dace.

Ganin alamun zaƙuwa tare da itane yasashi miƙewa a hankali kana ya dawo gaban Khausar ya zauna akan kujeran da aka ajiye kusa da tum-tim ɗin kujerar da Khausar ke kai kana ya zaune.

Sai kuma ya ɗan kalli Ibarahim dake cewa.

“Ɗa ƙafar dama zaka fara”.

Ɗan hararan Ibraahim yayi kana ya ɗan ronƙofo kaɗan ya sunkuya, a hankali ya sanya hannunsa na dama ya kamo ƙafan Khausar na dama tare da zare mata takalmin, tare da tsirawa fatar kafar lumsassun idanunsa,

Zakariyya ne ya ɗan yi gyaran Muryar da ya sashi,

Ɗan Lumshe ido kana ya buɗesu a hankali, yatsunta sunyi masifar kyau, kana faratun ƙafan ayanke suke fes-fes gwanin ban sha’awa.

 

Aransa yace ikon Allah wannan ita kuma haka tabar ƙafar nata.

Kansa ya ɗago tare da kallon kyakykyawan fuskarta dake fitar da annuri kana ya tsuke fuska ya ɗan harareta tare da cewa.

“Ko Amaryar shamuwa ana sa mata lalle. Amma ke naga alamun Amaren buzuzuma sun fiki ƙyalli”.

Jin abinda yace yasa ta tura baki da ɗan juya ido.

Ƙafanta ya jawo kana yasa cikin ƙwaryan dake gabansa wanda babu nono aciki ɗan matse ƙafar yayi har saida ta ɗanyi ƙara, shi kuwa wani murmushin da shi kaɗaine yasan ma’anarsa yayi.

Jakadiya kuwa nono ta ɗebo aƙaramin ƙwaryan ta miƙa masa.

Ita kuwa Khausar jin yadda yaja ƙafanta yasa ta risino wanda dai-dai lokacin take tura baki..

Karaf sai akan idanunsa ware manyan idanunsa yayi kana ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.

“idanfa kina hararana, ƙwaƙule idanunki zanyi, kafin kije Lahira Ubangji ys ƙona miki su”.

Saurin kallonsa Khausar tayi jin abinda yace girarsa ɗaya ya ɗaga mata tare da cigaba da faɗin.

“Yess ai na lura bakisan daraja da girman miji bako?”…

Uffan batace masa  sai ma lumshe idanunta da tayi tana jin yanda ɗumkn tafin hannunsa ke ratsata…

 

Hannunsa na dama yasa ya tallafi ƙafartata kana ya karɓi ƙwaryar Nonon da hannunsa na hagu ahankali yake zuba Nonon akan ƙafarta…

Yayin da aransa yake tuna tabbas ya taɓa sanin wannan al’adar  amafarkinsa da yake yawanyi…

Cike da nutsu da kuma ƙwarewa yake wanke ƙafafunta daga dai-dai idon sau zuwa kan zara-zaran yatsun ta ya wanke fess.

Ita kuwa sai mutsu-mutsi take da yatsun ƙafarta ɗan ji take kamar jakul-ku-kuli yake mata,’.

Yana gama wanke wa sai ga Didi da kanta wani farin ƙyalle mai masifar haske da ƙamshi ta miƙa masa.

Juyawa yayi yaga Mahaifiyarsa tsaye da kanta take bashi.

Didi kuwa kai ta jinjina masa alamar ya karɓa.

Ba musu ya karɓa tare da gogewa Khausar ƙafanta  kana ya mayar cikin takalmin ta, sai kuma ya zaro ƙafara na hagu ya wanke kamar yanda yayiwa na damar.

Wani farin ƙyalle kamar na farko mai azabar ƙamshi Didi ta sake miƙa masa ya goge mata ƙafar kana ya ajiye.

Kallonsa Didi tayi tare da faɗin.

“Toh ka matso da kyau sai ka tallafi ƙwaryar Nonon cinyaka kasa hannunta duka biyu ka wanke”.

Da ɗan sauri ya ɗaga kansa ya kalleta.

Lumshe idanu tayi alamar kayi ɗan Albarka.

Kai ya jinjina hakan yau yake jinsa wani irin farin ciki mara misaltuwa tamkar wanda aka yiwa bushara da gidan aljanna.

Kujeran yaja ya matsa kusa da Khausar sosai yayin da Gwiwoyinta ke gugan Gwiwoyinsa.

Bakajin saurin komai sai busan sarewa da tashin jits, Yayin dasu Ibraahim kuwa suka koma ta bayansa suka tsaya, gudun kada su tsaya agaba su tare wa ƴan baya,

Hotuna yimusu ake yi babu tsayawa tako wacce kusurwa hoto ake musu, yayin da Yayunsa ke zuba musu Liƙi.

 

Ahankali ya kamo lallausan tafukan hannunta ya riƙe acikin nasa kana ya tsunduma su acikin ƙwaryar Nonon da Jakadiya ta ɗaura masa akan cinyarsa wanda aka zuba wasu Jajayen Flowes masu kyau da tsari.

Cikin nutsuwa ya fara wanke hannun, tare da ɗan jan ƴan yatsunta, a hankali, ya ɗan ƙara ware idanunsa lokaci da ya ja ƴar ƙaramar yatsarta ta hannun hagu, gani yadda ta tara faratunta sunyi zaƙo-zaƙo irin dai yanda ƴan matan zamani keyi, sai dai sunyi masifar kyau musamman ma na ƙaramin yatsanta na hagu duk yafi sauran faratun tsawo, matse hannun yayi acikin nasa.

Runtse idanunta tayi cike da raki da shagwaɓa ta furta.

“Wash! Allah”.

Ta faɗa tare da sunkuyo da kanta haɓarta na taɓa goshinsa ahankali ya ɗago kanshi, wanda hakan ya bawa hancinsa damar gogan hancinta.

 

Cikin tsuke fuska ya sanya ƙwayar idanunsa cikin nata tare da faɗin.

“Meye amfanin wannan farcen da kika bari ajikin ki?”.

Cikin sanyi tace.

“Dan yin susa in  ƙaiƙayi ya dameni”.

Sosai ya daure wurin danne yanayin da muryata ta sashi a ciki, a hankali ya ɗan matse yatsar kana a hankali yace.

“Shin bakisan cewa shi farce shine rumfar shaiɗan ajikin ɗan Adam ba?”.

Shiru tayi ba tare da ta cire idonta daga kan sajenshi da takeyiwa kallon kurillaba.

Shi kuwa numfashi ya fesar tare da cewa.

“Ya za’a yi ki tarawa sheɗan Mafaka ajikin ki?No wonder shiyasa kika  cika rawan kai ashe muhalli kikayi ibilis a jikinki”.

Bakinta ta tura tana kallon yanda yake matse mata hannu.

Shi kuwa Moddibo cikin sanyin murya ya cigaba da cewa.

“Shiyada duk rashin ji da neman mgn duk kece a gaba ashe-ashe muhalli kika tarawa sheɗan agangar jikinki. Toh kiji da kyau, ko kiyanke faratun nan ko kuwa idan na tashi da kaina zan haɗa da ƴan yatsunki in yanke kana na wurgawa karnuka su cinye”.

 

Cikin yanayin tsoronsa da sanyin murya tace.

“Dan Allah ka sake min hannuna zafi fa yake min”.

Sake matsawo kusa da ita yayi tare da faɗin.

“Bazan sake ba”. Da sauri tace.

“Afwan”.

Cikin kasala yace.

“Sai kinyi al’ƙawarin zaki yanke farcen”.

Da sauri ta gyaɗa masa kai cikin narke fuska tace.

“Nayi al’ƙawari zan yanke amma zan bar ɗaya”.

Fuska ya ɗaure tare da faɗin.

“Ban yarda ba duka zaki yanke”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Na yarda zan yanke toh ka sake min hannu”.

Wani irin murmushi mutanen dake wajen sukayi yayinda wasu ke binsu da kallon sha’awa.

 

Asma’u kuwa hannu ta miƙawa Dije dake gefenta suka tafa cikin yanayin farin ciki Dije tace.

“Asmeey kinga wata Madarar soyayya kamar a Indi’a muke, lallai na yarda cewa Ustazan nan sunfi kowa iya soyayya”.

Kai Asma’u ta jinjina tana mai binsu da kallon sha’awa yayin da aranta take musu addu’ar samun dawwa-Mam-miyar farin ciki tace.

“Ai kam ko tattabaru bazasu gwadawa su Khausy zama da junaba, kinaga wani irin mayataccen kallon da Yah Modibbo keyi mata, ko me yake gaya mata?”.

Da sauri Aseeya tace.

“Sai Allah gashi dai tun ɗazu suketa wani ƙus-ƙus ji Khausar yadda take lumshe ido”.

Dariya sukayi dukansu

 

Zakariyya kuwa cikin sarawa salon Modibbo ya ɗan sunkuyo daf da kunne Moddibo kana yace.

“Dan Allah ka riƙa tunawa, cikin mutane da kuke.

Na lura gaba ɗaya ka zauce ƙa kauce hanya baki ɗaya, ka wani gigice daga ganin yarinya kana ƙoƙarin taɓarewa acikin tsakiyar taron al’umma duk kuma wani narkewa”.

Khausar kam kanta na ƙasa Zakariyya kuwa cike da sheƙiyanci ya cigaba da cewa.

“A cikin Family fa kake ba cikin falonku kuke ba”.

Shi kuwa Modibbo Numfashi ya sauƙe mai nauyi A ransa yace.

ohhh ni Aliyu na lura Zakariyya magana ne abakinsa shida. Dr Jameel sai dai Allah ya shirye su.

 

Hannunsa na dama yasa ya damƙe nata da ƙarfi, sai ya zama na kamar sunayin musabaha ne.

Sai kuma yayi shiru tare da rintse idanunsa da sanya haƙoransa  ya cije gefen lips ɗinsa na ƙasa kana ya sunkuyar da kansa ƙasa, wani irin abu yake ji tun daga tsakiyan maɗigan ƙwaƙwalwar kansa, har zuwa tsakiyar tafin ƙafarsa, lokaci ɗaya yaji gangar jikinsa ya fara tsuma baki ɗaya jikinsa ya fara tsuma amma ta ciki yanda babu wanda zai fahimta sai shi…

 

Ibraahim ne ya tsugunna kansa tare da faɗin.

“Bismillah Yah Aleey, Continue”.

Jin muryan Ibraahim yasa ya fesar da sanyayyan numfashi sai alokacin ya fara dawowa hayyacinsa.

Ahankali ya buɗe Idanunsa da suka kaɗa sukayi Jawur ya kalli Khausar yana mai jan wani dogon numfashi da ɗan ƙarfi ya sauƙe numfashin kana ya ɗago idanu ya kalleta.

Da sauri ta fito da idanunta waje ganin yanda ƙwayar idanunsa suka sauya launi baki ɗaya.

Khausar kuwa ahankali tace.

“Ayyah kasake min hannu na zafi”.

Numfashi ya fesar tare da sakin hannu kana ya kamo yatsunta.

Didi dake tsaye ta dauki wani ƙyalle me kyau kamar farko ta miƙa masa karɓa yayi kana ya goge mata tafin hannun zuwan ƴan saffa-saffa yatsunta.

 

Rahma kuwa kaskon turaren wuta dake fitar da wani Masifeffen ƙamshi ta miƙa masa.

Ƙamshin da ya fara gigita masa tunaninsa lokaci ɗaya ya fara jin wani irin yanayi yana game masa gangar jikinsa da ruhinsa baki ɗaya.

Kaskon turaren wutan ya ɗaura akansa kasancewar gindin Kaskon nada faɗi sai ya kamo hannayenta ya kife akai.

Ahankali hayaƙin turaren wutan ke ratsa yatsunta yana buga fuskanta.

 

Mai busa Algaita ne ya cigaba da busawa dare da haɗawa da kirari.

Sarkin Zaƙi kuwa hura Microphone yayi tare da cewa.

“Idan akwai ƙanin Amarya ko ƙanwar amarya ta fito, ta amshi kaskon bisa al’adarmu”.

Cikin sauri Haiydar dake ta faman Video ya miƙe ya fita kana ya zare Kaskon turaren wutan kasancewar haka Al’adarsu take.

Shi kuwa Haiydar sunkuyowa kan Khausar yaui tare da faɗin.

“Kai Addah Khausi kunyi kyau.

Kinga yanda kika zama kamar wata acikin taurari baki ɗaya ke kike haska wajen nan”.

Kallonsa tayi cikin yanayi gajiya, sai kuma ta ɗan hararesa kana tace.

“Dole mana kace haka tunda ni kaɗai ce ƴar Uwarka”.

Murmushi yayi kana cikin gaskiya da gaskiya yace.

“Wallahi ba haka bane Addah Khausy kinyi masifar kyau fa”.

Ya ida maganar tare da miƙawa Jakadiya Kaskon.

Jakadiya kuwa da ido ta yiwa Moddibo alamar ya tashi ya koma kan kujera.

Kai ya gyaɗa tare da komawa mazauninsa.

Haka ma Didi da yayunsa suka koma wajen zamansu…

Sarkin Zaƙi kuwa cike da rakaɗi yace.

 

“Alhamdulillah da wannan al’adar tamu mu kazo ƙarshen wannan taro na yau, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu bisa dai da lafiya, za’a fitar da Aleeyu Youseep Muhammad Mouley atsakiyar fada, domin gabatar dashi atsakiyan Fada a matsayinsa na sarki mai jiran gado”.

Daga nan aka tashi  kasancewar ƙofofine da dama cikin falon,  yasa lokaci ɗaya duk aka fita cikin nutsuwa batare da wani cunkuso ba duk da kuwa yawan mutanen.

 

Acan ɓangaren Innayi kuwa cikin sauri ta nufi wajensu Moddibo tare da riƙe hannun Khausar ta juya.

Moddibo kuwa baki ɗaya Cousing Brother’s ɗin sa ne suka riƙa bashi hannu suna rungumesa cike da ƙaunarsa tare da gabatar mishi da sunayensu da dangatakar su.

Shima cikin yalwataccen farin ciki yake rungunarsu.

Kafaɗarsa Zakariyya ya dafa tare da faɗin.

 

 

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N 09097853276, in tura miki ki karanta abinki salamun Salam.

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button