Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 16

Sponsored Links

 

📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*

_page 16_

 

_NA_

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

*In sha Allah daga gobe zan gama free page, ƴar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 daga wannan page ɗin sai na gobe mun gama free page, ki biya yafi sauƙi tsira ba haƙƙin kowa kanki.*

 

 

 

*GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

 

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

 

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

 

Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

 

 

GARKUWAR MA’AURATA

 

Shiko M Jameel Wani irin tsuma ilahirin jikinsa keyi sakamakon tuni da ayoyin sukayi mishi na jin azabar da Ubangiji ya tanadar wa  da duk wanda ya kashe ran mumini da gangan ba tare da wani haƙiba.

Cikin raunin murya me cike da tsananin tsoron Ubangiji  M jameel ɗin ya kawo fassarar aya na 90 da kuma 91, tsit gaba ɗaya masallacin yayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan M Jameel daya kasa ci gaba, yayinda kukansa yasa da dama cikin mutanen yin kuka.

Middibo kuwa kife tafukan hannunsa yayi kan fuskarsa yana maiyin wani irin sassayan kuka mai masifar sa rawan jiki, gaba ɗaya fuskarsa tayi jazir.

Cikin ƙarfin hali M Jameel ya fara mgn cikin rawan murya  yace.

“A cikin suratul Nisa, Aya ta 92 Allah ma ɗaukakin sarki na cewa, 92:

-:Baya  halasta ga mutum da ya kashe ran mumini, sai dai idan ya kasance kuskure ne.”.

Sai kuma ya tsagaita tare da sayan tafin hannunsa ya share hawyen daketa kwaranyowa da idanunsa, cikin rawan murya yaci gaba da cewa.

“Duk wanda kuma ya kashe! Mumini da kuskure toh, zai ƴanta wuyan Muminin, sannan ya bada Diyya ga iyalan wanda ya kashe”.

Sai kuma ya dire ayar mgnar tare da rushewa da zazzafan kuka mai cike da tashin hankalin da raunata zukata aya ta 93.

Cikin rauni yasa hannu ya karɓi hankicif ɗin da ɗan agajin dake bayansa ya miƙa masa, sharce hawayensa yayi tare da juyowa ya kalli Moddibo da gaba ɗaya jikinsa rawa yake sai sheshsheƙan kuka mai fuzge numfashin da yakeyi, bazai iya hana kansa kuka ba, bare ya samu iko da damar hana aminin nasa.

Cikin sheshsheƙan kuka M Jameel ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Huymmmm, a kuma cikin suratul Nisa ɗin ayata 93, Allah madaukakin sarki nacewa-:

(Duk wanda ya kashe Mumini bisa ganganci, ko Mugunta da zalumci. Toh Sakamakonsa shine wutar Jahannama”.

Sai kuma ya sake sakin wani irin raunataccen kuka mai cike da tsoro kana yaci gaba da cewa.

“Allah madaukakin sarki cewa yayi-:

Duk wanda ya kashe ran mumini zai dawwamane cikin jahannama, kuma Allah yayi fushi dashi, sannan kuma ya tsine masa”.

Kawai sai ya kife kansa bisa Table ɗin dake gabansa, shar-shar haka hawayensa ke kwaranyar babu ƙaƙƙautawa.

Modibbo kuwa cire tafukan hannunsa yayi bisa fuskarsa tare da dafa kafaɗar M Jameel ɗin kawai saka sufashe da kuka a tare, cikin kukan murya na rawa M Jameel ya buɗe baki da nufin zaiyi mgn amman ina ya kasa.

Haka yasa Moddibo rumtse idanunsa kana murya na rawa yace.

“Bayan fushi da tsinuwar ubangiji Allah Mabuwayi da komai baya ɓuyar masa yace.

-:Wa ahdalahun Azaban Azeeymah).

Ma’ana ya tandarwa duk wanda ya kashe ran mumini da ganganci Azaba mai girma!!!!.”

Zuwa lokacin  wasu daga mutanen cikin masallacin kuka sukeyi da sheshsheƙan mafi akasari kuma duk jikinsu yayi sanyi.

Shi kuwa Moddibo cikin rauni da sanyi  yace.

“Duk waɗannan ugubobin sun ta’allaƙane ga wanda ya kashe ran mumini da ganganci, sakamakonshi Jahannama, kuma a cikinta zai tabbata, sannan Allah yayi fushi dashi, kana ya tsine masa, kuma ya ƙara masa da azaba mai girma.

Wannan masifa har ina ɗan adam zai kaishi koda iyayenka ne sukayi fushi da kai taɓewa kakeyi bare Ubangijin talikai, koda iyayenka ne suka tsine maka lalacewa kakeyi bare tsinuwar Allah,  sannan azaba koda ta tururin tea ne tsoronsa muke bare kuma tabbata ta jahannama sannan da tanadin azaba mai girma”.

Kawai sai lips inshi suka fara rawa kar-kar shima ɗin ya kasa ci gaba.

Ganin hakane yasa M Jameel sharce hawayensa tare da cewa.

“Aramma kawo mana dukkan wata Ayar Al,qura’ani da Ubangiji yayi magana akan duk wanda ya kashe ran mumini”.

Cikin tsumar jiki tare da wata raunatacciyar murya mai cike da tsananin tsoron Ubangiji da kuma sanin hukuncin wanda ya saɓa masa Moddibo yayi gyaran murya dai-dai zai fara karanta Ayar manyan Malaman dake wajen suka nuna musu agogon dake liƙe a can bayansu a jikin gini.

Wanda hakan ke musu nuni da alamar lokaci yayi.

 

Nan-nauyan ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da share ƙwallan da suka zuba masa kana cikin raunin murya yace.

“Lokaci yayi sai dai idan Allah ya kaimu gobe zamu ɗaura daga inda muka tsaya”.

Ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da cewa.

“Ya Allah Ubangiji yabamu zaman lafiya ya Allah karabamu da sharrin ƴan bindiga daɗi Ubangiji ya tsare mu da sharrin kidnappers Ubangiji ya bamu zaman lafiya Allah yajiƙan iyayen mu da duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya.

Wa subhanakallahumma wabi hamdika ash shahadula’ilahu. nastagfirka wanatuubu Ilaik”.

Tunda ya fara addu’ar suke Amsawa da Ameeen har aka shafa.

Mata ne suka fara fita kafin maza.

 

Acan ɓangaren Khausar kuwa, bayan ta koma gida kai tsaye Bedroom ɗinta ta wuce batare data shiga wajen Mommy ba, tana shiga ta kwanta lamo akan gado hawaye na tsiyaya daga kyawawan Idanunta sosai.

Tafseer ɗin da M Jameel Yayi ya riƙa ratsa jikinta har ƙwaƙwalwar kanta Muryar Modibbo kuwa har yanzu yana ratsa kunnuwanta, da haka bacci ya ɗauketa batare data shirya ba.

Washe gari Da safe still haka Khausar ta tashi cikin mutuwar jiki Anutse ta fito daga Bedroom ɗin ta zauna agefen Mommy dake falo.

Lumshe Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Mommy ina kwana”.

Anutse Mommy ta maida kallonta gareta tare da na zartan yanayin ta batare data amsa gaisuwar data mata ba ta jefo mata tambya tare da cewa.

“Meke damunki Khausar na lura tun jiya jikin ki Asanyaye”.

Ɗago Kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye kana cikin sanyi murya tace.

“Wallahi Mommy tun jiya da muka je wajen tafsir ɗin da Malam M Jameel yayi jikina ya mutu hankalina ya tashi gaba ɗaya na rasa mai yasa tsoro ya kamani”.

Miƙewa Mommy tayi tare da matsowa kusa da Khausar ta shafa kanta kana tace.

“Babu komai wannan masiface-masiface ne da Allah ya jarabci Al’umma wannan ƙarnin saidai mu dage da addu’a Allah ya yaye mana ya kuma tsaremu da faɗa wa mummunar ƙaddara Allah ya rufa mana asiri ya karemu da zamewa sanadin mutuwar koda kadagare ne”.

Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.

“Ameen”.

 

Acan gidansu Moddibo kuwa Innayi ce zaune atsakar gida ta zabga tagumin tunda taji tafsirin da M Jameel sukayi jikinta yayi masifar sanyi wani irin tsoron Allah mara misaltuwa tashiga hakan fargaba ya rufeta.

Washe gari.

Da hantsi A hankali Moddibo da M Jameel suka fito, Moddibo na sanye cikin Shigarsa as Usual Jallabiya Sky blue mai yauƙi da santsi kansa ɗaure da farin Hirami  kana takalmamsa farare jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi turaren Oud Khareem na tashi.

Shima M Jameel  sanye yake cikin irin shigar Modibbo jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi kai tsaye sashen Innayi suka nufa,Innayi dake zaune gaban barandar akan kujera ƴar tsugunno ta ɗago kai ta kalli Moddibo da M Jameel kawai sai taji Idanunta na tsats-tsafowa da ruwan hawaye.

Tsayuwa Moddibo ya gyara kana yace.

“Ya dai Innayi”.

Idanu ta zuba masa batare data iya furta komaiba kawai sai hawaye suka shiga kwaranya daga idanunta.

 

Cikin yanayin tashin hankali Moddibo ya tsugunna agefenta na dama yayin da M Jameel ya durƙusa  agefenta na hagu kana suka haɗa baki tare da cewa.

“Innayi ya dai me yasame ki?”.

Kallonsu tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ta sauƙe numfashi kana tace.

“Wa’azinku na jiya ya ratsa jikin mutane wa’azin yasa mutane acikin ɗimuwa wa’azinku na jiya ya tunatar sannan yasa tashin hankali kuma wannan zamanin muna fama da Masifa Allah dai ya yaye mana jiya hankalina atashe yake domin ire-iren abubuwan akeyi!”.

Jinjina kai M Jameel yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.

“Hakane sosai ma Innayi amma mu cigaba da addu’a babu abinda ya gagari Ubangiji ga dama yazo watan Ramadan muyita addu’a Allah ya yaye ya taƙaita ya sauƙaƙa mana”.

Atare Modibbo da Innayi suka amsa da.

“Ameeen”.

Miƙewa M Jameel da Moddibo suka atare kana M Jameel ya Kalli Innayi tare da cewa.

“Toh Innayi zamu tafi Tafseer A masallacin makarantar mu”.

Jinjina kai Innayi tayi kana tace.

“Ubangiji Allah ya tsare ku ya kuma sake ɗaukaku”.

Ameeen suka amsa tare da juyawa zasu fita har sun kai ƙofa Innayi ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.

“Yauwa wai niko ya batun tafiyar mu ne?”.

M Jameel ya juya tare da cewa.

“Komai ya kammala na tafiyar mu Insha Allah ranan sha biyar ga wata zamu tashi misalin sha biyu da rabi na dare jirginmu zai tashi jibi kenan ba in sha Allah, kuma sai munyi tafsir ɗin ranan ma zamu tafi Taraba”.

 

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Allah ya nuna mana Ubangiji Allah ya kaimu lokacin lafiya amman kuma kace sai kunyi tafsirin ranar?”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Eh kinga Tara na dare zamu fara, goma zamu tashi, dama kuma kafin mu tafi zamu gama shirin mu duka, tsananin mu Gembulan da taraba kuma tafiyar awa ɗaya da rabine, kinga kenan sha ɗaya da rabi zamu isa, zamu samu awa ɗaya ma acan kafin mu tafi, Abba na kuma su gobe nema zasu tashi”.

Cike da gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da amsawa.

“Allah ya kaimu lfy”.

Ameeen suka amsa a tare kana suka fice mota suka shiga M Jameel ke Driving cikin nutsuwa har suka isa masallacin.

 

Suna shiga suka fars gabatar da tafsirin kamar yanda suka saba ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai suka gabatar da sallah Moddibo yayi limanci bayan sun idar suka cigaba kiran sallar La’asar yasa suka dakata da karatun tare da miƙewa suka gabatar da sallah bayan sun idar suka fito suka shiga mota awannan lokacin ma M Jameel ke Driving har suka iso gida.

Hong M Jameel Yayi Modibbo ne ya fita ya buɗe  musu.

Anutse suka fito tare da furta Bismillahi,

Ahankali Moddibo ya gyara tsayuwarsa tare da fesar da sassayan numfashi.

Ido ya tsirawa bishiyar Ayaba da iska ke kaɗawa  har na tsawon sakonni goma, sai kuma ya maida kallonsa kan Bishiyar mangoro Idanunsa ya lumshe domin Allah ya sani ganin sirrai ya fiye mishi ganin komai daɗi. sannu ahankali ya riƙa tuna lokacin da yarinyar tashigo gidan har tayi nasaran hawa reshen bishiyar mangoro mai girma da tsawo, da kuma sanda ta faɗo akan yatsun ƙafarsa.

Da sauri ya buɗe idanunsa

Tare da jan dogon tsaki mai cike da tsanar lamuran yarinyar. Idanunsa ya juya jin M Jameel na cewa.

“A.J tunanin mai kakeyi haka ka tsiwara Bishiya ido?”.

Sanyayyar Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai sanyi daga bakinsa kana yasa hannu ya shafa kwantaccen Sajen fuskarsa ya maida kallonsa kan M Jameel da har zuwa lokacin shiyake kallo,Ya mutse fuska yayi kana yace.

“Babu komai”.

Daga haka ya wuce gaba Kai M Jameel ya Girgiza tare da bin bayansa suka shiga Babban falon Moddibo da komai ke kimtse sai tashin ƙamshi yake.

 

Zama M Jameel Yayi akan 3sitter tare da faɗin.

“Wash’ Allah!”.

Kallonsa Moddibo yayi amma bai ce komai ba Bedroom ya nufa tare da janye Hiramin kansa kana ya cire jallabiyar dake jikinsa ya buɗe ƙofar toilet da addu’a

Kana yashiga  shawer ya sakarwa kansa  yashiga cuɗe jikinsa ya ɗauki kusan minti ashirin kafin ya fito zama yayi agaban Dressing mirrow ya shafa Mai sama-sama kana ya miƙe ya sanya Jallabiya Maroon colour da farin hirami. Feshe jikin sa da turarukansa masu daɗin ƙamshi yayi. shima M Jameel wanka yayi tare da sauya kan jikinsa zuwa Jallabiya fari kana ya ɗaure kansa da Maroon Hirami Sosai sukayi kyau    atare suka fito zuwa farfajiyar gidan anan suka samu Innayi da Asma’u na aikin abin buɗa baki kallon Innayi dake soya ƙosai yayi sai kuma ya maida kallonsa kan Asma’u dake dama kunun sadaka na masallaci har ta gama ta rufe sai kuma suka bita da ido.

Kallon Asma’u dake kwaɓa fulawa, kuka, da kanwa M Jameel Yayi  yace.

“Yau kuma ɗan wake ake mana ne Asmeey?”.

Kai ta jinjina kana tace.

“Eh dan naji jiya Yaya Moddibo nacewa ɗan wake mukayi ne shiyasa yau nace bari ayi”.

Murmushi Moddibo yayi ya mai binta da wani irin amintaccen  yace.

“Kai kin kyauta mun kuwa, kwana biyu bamuci ba inaga tunda azumi ya kama kamar baku yimana shiba”.

 

Kallonsa Asma’u tare da ce wa.

“A’a munyi amma ranan baka ciba agidan Ummi kuka sha ruwa ranan”.

Jinjina kai yayi  yace.

“Toh yau kam Insha Allah zamu dawo muci ɗanwaken nan”.

Murmushi tayi ta na jefa ɗan waken da cokali tace.

“Allah ya dawo daku lafiya”.

Ameeen suka amsa kana suka mayar da Kallonsu kan Innayi dake musu gashin Zabbi sai tashin ƙamshi yake.

Idanu M Jameel ya lumshe yace.

“Innayi zamu wuce”.

Da murmushi afuskarta ta kallesu  tace.

“Ubangiji Allah ya tsare”.

“Ameen”,Suka amsa sannan suka fice atare kai tsaye masallacin Juma’ar da suke limancin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da tafsirin Alkur’ani acikin Suratul Zariyat yayin da Moddibo ke jan baƙi M Jameel na tafsiri ƙarfe shida dai-dai suka tashi.

 

Anutse suka fito daga cikin masallacin suka shiga mota akuma dai-dai lokacin wayar M Jameel ya hau ruri cike da nutsuwa ya gyara zamansa tare da ciro wayar daga aljihun sa Sunan Abban sa ke yawo a screen ɗin kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe yayi yace.

“Kaga Abba ke kira”.

Ya ƙara sa maganar tare da Amsa kiran yakai kunnensa tare da cewa.

“Assalamu Alaikum”.

Daga ɓangare Abba yace.

“Wa’alaikum Salam Babana”.

M Jameel Yayi murmushi tare da cewa.

“Na’am Abba na”.

Gyaran murya Abba yayi kana yace.

“Nikam laifin me mukayu mukune da kai da Moddibo da baza kuzo mu samu ladan baku buɗa baki agidan nan ba”.

Murmushi M Jameel Yayi yace.

“Ayyah Abba na laifin me zaku mana mukam a duniyar nan gama A.J ɗin yana jinka”.

Ɗan Matsawa kusa da  M Jameel ɗin Moddibo yayi kana yace.

“Abbah mai zaku mana  A duniya ko kun yi mana abu baza muyi fushi da kuba waye zaiyi fushi da iyayensa?”.

 

Murmushi Abba yayi  yace.

“Toh tun da akayi azumi baku zo kunsha ruwa a gidan nan bafa, abin yana damuna yau fa  kwana goma sha uku  kenan da baku zo kunsha ruwa agidan nan ba fa”.

 

Dariya M Jameel Yayi yace.

“Abba ka dai manta mun zo ranan da akayi azumi biyar agidan muka sha ruwa fa”.

Gyara zaman wayar Abba yayi akunnensa kana yace.

“To ai bana nan ba asha ruwan dani ba yau dai so nake kuzo musha ruwa tare”.

 

Gyara zama Moddibo yayi  yace.

“Abba baza mu bari sai gobe ba?”.

“A’a yau nakeson ganinku kuzo musha ruwa anan”.

Cewar Abba.

Jingina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Toh shikenan Abba zamu zo insha Allah amma bari mu fara zuwa gida”.

Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.

“A’a karfa ku makara kuzo komai ya kammala ku kawai ake jira ga kun lokacin ya ƙarato”.

Atare suka haɗa baki wajen cewa.

“Toh shikenan Abba ga munan zuwa”.

Kallon Moddibo M Jameel dake Driving Yayi kana yace.

“Muje?”.

Moddibo kuwa Idanunsa dake lunshe ya buɗe yace.

“Eh muje mana J”.

Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya juya akalar motar zuwa Unguwar su Abba ba abinda ke tashi acikin motar face ƙira’ar Alkur’ani acikin Suratu Yusuf tare da Sanyayyar ƙamshin tularensu, Wayar Moddibo dake gaban aljihu ne ya hau ruri Anutse yasanya lallausan tafin hannunsa mai zagaye da gashi ya ciro wayar tare da kallon sunan mai Kiran Malam Arɗo amsa kiran yayi tare da kai wa kunnensa.

Daga ɗaya ɓangaren Malam Arɗo yayi gyaran murya kana yace.

“Wai kai baza kazo kasha ruwa agidana ba ko sau ɗaya ne Moddibo?”.

Murmushin gefen baki Moddibo yayi tare da shafa kwantaccen Sajensa kana yace.

“To Malam ka gayyace mune ai baka gayyace mu shan ruwa ba”.

Da sauri Malam Arɗo yace.

“To na gayyace ku xo yanzu”.

Girgiza kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Toh ba yau ba dai sai gobe”.

Da sauri Malam Arɗo ya zare Ido tare da cewa.

“To duk abubuwan da nasa aka dafa muku kuma fa?”.

Murmushin gefen baki Moddibo ya kuma yana imagine fuskarta malam Arɗo kana yace.

“Ka bawa mutanen gida suci ba rabon mu bane

gobe kuma Idan Allah ya kaimu kama na namu kuma ayi da mutanen gida duka”.

Cikin sauri Malam Arɗo yace.

“Wato dai kai ko yaushe sai ka kawo min sabon tsari acikin al’amari na ko”.

Murmushi M Jameel yayi shaƙuwar dake tsakanin Moddibo da malam Arɗo ya wuce zaton mutane.

Moddibo kuwa ɗan Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi kana yace.

“Ai dole dai kam”.

Dariya Malam Arɗo yayi  yace.

“Dama gobe ka tabbatar lokacin shan ruwa yana yi na ganka, ba sai na kira ba ka gaishe da Jamilu kar ku cinye min kati na”.

Ya ida maganar tare da katse kiran.

Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

“Malam Arɗo ko?”.

Murmushi kawai Moddibo yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.

 

Cikin mintunan da baza su gaza biyar ba suka isa ƙofar katafaren gidan Hong M Jameel Yayi mai gadi ya buɗe musu Anutse M Jameel ya cinna hancin motarsa gidan tare da yin parking a inda aka tana da danyi Parking ɗin motoci.

Cike da nutsuwa suka nufi sashen Abban M Jameel, bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga tamfatsetsen Falon nasa daya gaji da tsawuwa yana fitar da sanyayyan ƙamshi.

Tsaye suka hangosa yana gyara ɗaurin agogon hannunsa fuskarsa da damshi da alama Al,wala yayi.

 

Kallonsu yayi tare da sakar musu da murmushi kana yace.

“Ku shiga kuyi al,wala kunga muna shan ruwa sai mutafi masallaci”.

Kai suka gyaɗa sannan M Jameel ya nufi toilet dake Falon kana ya kalli Moddibo da faɗin.

“A.J kashi ga toilet ɗin ciki kayi al,wala”.

Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

“A’a kashiga na ciki ni zan shiga wannan”.

Kallon Moddibo Abba yayi kana yace.

“Wato shi yashiga ɗaki na kai ba zaka shiga ba ko? To ai kaima ɗana ne kashiga babu komai Moddibo”.

Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

“Toh shikenan Abba”.

Sannan ya wuce Bedroom ɗin Abba ahankali ya saki murmushi ganin komai na Bedroom din tsaf-tsaf akimtse Aransa yace ashe de J gadon tsafta yayi awajen Abba shima komai nashi tsaf-tsaf ajiyar zuciya ya sauƙe tare da shiga toilet ɗin nan ma komai atsaftace Al’wala ya ɗaura kana ya fito atsaye ya samu M Jameel da Abba Kallonsu Abba yayi kana yace.

“Ku ƙaraso mu isa dining”.

Kai suka gyaɗa tare da nufar dindin ɗin da aka ƙawata da kayan ciye-ciye na alfarma wani irin kwando ne na kayan marmari ne kama daga, Inabi, Abarba, Ayaba, Kankana, Lemo, Ruman, Tuffa, Mangoro.

Sai kuma wasu Warmers masu kyau dake ɗauke da pride rice da yaji kayan lambu,sai daga ɗaya gefen kuma wasu jug ne masu kyau ɗaya kindirmo ne mai sanyi adame ɗayan kuma kunun shinkafa  ne sai Flaks dake ɗauke da ruwan tea da kuma kofina daga gefensa kuma gongomin madara ne dana Bounvita sai kulan ƙosai sosai dining din ya ƙawatu.

Anutse suka zauna akan kujeran Abba ya zauna daga ɓarin kudu Moddibo ya zauna daga ɓarin yamma yana fuskantar gabar M Jameel kuwa daga ɓarin gabas ya zauna yana fuskantar yamma.

Anutse Moddibo ya ɗauki dabino guda bakwai ahannunsu idan yaci sai ya sanya ƙwallon ahannunsu na hagu bayan yaci sai ya ɗauki inabi yaci M Jameel kuwa dabino uku yaci tare da apple haka ma Abba.

Sai.kuma suka sha kankana da inabi kana suka ɗan ɗaura da ayaba.

Kallon su Abba yayi cike da so da ƙaunarsu kana yace.

“Toh kuci abinci”.

Girgiza masa kai sukayi kana atare suka ce.

“A’a Abba sai mun dawo daga masallaci”.

Kai ya gyaɗa musu kana suka miƙe atare suka tafi masallaci suka idar da sallah bayan sun dawo M Jameek ya ɗebi Pride rice Kaɗan da tsokokin kaza. Modibbo kuwa kindirmon da aka dama ya ɗiba a Cup Abba kuwa chicken peper da pride rice shima ya ɗebi yana ci.

Fara cinsu babu daɗewa aka turo ƙofar aka shigo Idanun Hajiya Karima bai sauƙa ko ina ba sai kan Moddibo dake  riƙe da kofin kindirmon kana da plate ɗin da Abba ya sa mishi pepper chicken and vegetables da fork a samansu.

 

Cike da tsanarsa ta watsa masa wani wulaƙantaccen kallo kana tace.

“Toh acire tsatsan haƙori anan, kaska raɓi mai jini wato ko zuwa shi kaɗai ya samu ya keɓe da mahaifinsa ba za’a bari ya samu damar hakan ba ko?

Oh ni Kareeme tunda nake a duniya ni dai ban taɓa ganin mutum mai shegen nacin tsiya irin kaba, sam baka da godiyar Allah ba zaka tsaya amatsayin ka ba shin kai wani irin Jarabebben mutum ne Aliyu?!”.

Cikin wani irin fushi da ɓacin rai Abba ya mike ahasale ya dubeta kana yace.

“Hajiya Karima mai kikeyi haka ne?

Wai meyasa ne ke baki da hankali ne? kinsan abinda kike faɗa kuwa!”.

 

Fuska ta ɓata kana tace.

“Toh Alhaji gaskiyane ya barka kaida ɗan ka kuhuta mana kuyi shawara acikin sirri”.

Afusace Abba ya katseta tare da faɗin.

“Me kike nufi shiɗin ba Uwa da Ubane suka haifeshi ba shima ɗana ne”.

Sheƙeƙe Hajiya Karima ke Kallonsa kafin cike da Isgilanci ta kallesa kana tace.

“Yaushe  ka haifesa bamu da labari?,yaushe ka auri uwarsa har ka haifesa bamu sani ba?”.

Cikin tsananin fushi Abba yace.

“Kifita anan ki fita Karima bana son ganinki tun da ke kince baki da ɗa’a baki iya Mu’amala da mutane  arayuwarki ta duniya ba, bana son haka, Bana son haka kar ki sake yin haka na yi miki kashedi na ƙarshe wannan shine last warning Hajiya Karima!, Kada ki sake yimin haka.

Domin kuwa koda Mahaukaci Jameel ya ɗauko ya kawo wannan gidan wallahi yafi min ke daraja, saboda nasan koda mahaukacine Jameel zai nuna masa cewa ni mahaifinsa ne kuma na tabbata zai mutunta ni”.

Cikin fushi ya sauƙe ajiyar zuciya tare da furzar da Iska kana ya cigaba da cewa.

“Na tabbata ko  Mahaukaci Jameel ya kawo gidan nan zai mutuntani, kuma zai ɗauke ni da daraja fiye da yanda ke ki ɗaukeni ban isa da keba, misali ga yadda idan na baki umarni kike fatali dashi, ba zakiyi amfani dashi ba.

Dan haka ko kin san Jameel ya fimin komai.

Jameel da kike gani shine Komai nawa a Duniya akan farin cikin Jameel ina iya yin komai dan haka tun wurima ki kiyayeni!

Kifita idona in rufe Hajiya Karima!!.

Ki kiyayeni kada inci miki mutunci!!!”.

Ya ida mgnar tare da buga jikin kujerar dining ɗin kana yaci gaba da cewa.

“Na tabbata kare idan Jameel zai kawo gidan nan sai yamin biyayya fiye da yanda ke kike min biyayya. Kare dai nasan idan Jameel zai kawo min gidan nan bazai tsaya yamin irin haushin da kike min ba!”.

Sai kuma ya watsa mata Kallon mai cike da fushi  kana yace.

“Kare idan Jameel zai kawo gidan nan kare mai ɗa’a da biyayya zai kawo min ba karen da zai kunya ta min baƙi na ba amma ke kullum baki da hankali. idan Jameel ɗan kine da kika haifa acikin ki zaki yi masa haka ne?”.

Kasa cewa komai Hajiya Karima tayi sai huci da take tamkar zakanya.

 

M Jameel kuwa ƙasa yayi da kansa cike da jin daɗi karo na farko kenan da mahaifinsa ya burgesa a kanta daya buɗewa Hajiya Karima wuta akan abinda ta keyiwa Moddibo domin kullum idan ta wulaƙanta Moddibo sai sunbar gidan kafin yake mata faɗa akan ta daina, amma yau yaji daɗin faɗan da Abba yayi mata agaban Idon Moddibo saboda Moddibo zaiji daɗi sannan zai san cewa yana da daraja da kuma kima awajensu.

Moddibo kuwa kansa ya sunkuyar ƙasa da cike kunya sam baiji daɗin  ɓatawan mata da Miji adalilinsa ba, yayi dana sanin zuwa gidan, yasan cewa duk lokacin da yazo gidan sai yayi sanadin da za’a samu hatsaniya, sannan ya riga daya sani tun yana yaro matar nan bata sonshi bata ƙaunar ganinsa da Jameel sai dai ya fahimci ba wai shi ta tsana ba tana fakewa da guzma ne ta harbi karsana.

Cikin sanyi murya ya ɗago kansa tare da furzar da iska mai zafi kana yace.

“Abba kayi haƙuri dan Allah dan darajar Annabi”.

Juyawa Abba yayi ya kallesa kana ya ɗaga masa hannu da faɗin.

“Yi shiru ba maganar ka Aliyu barni da ita haka take yimin, ba kai kaɗai ba, duk baƙon da Jameel zai kawo gidan nan sai taci masa zarafi, duk mutumin da zata gansa da Jameel saita nuna min ba mutumin kirki bane!”.

Sai kuma ya juyo Afusace tare da kallonta har zuwa lokacin tana tsaye cike da ɓacin rai ya tsira mata idanu kana yace.

“Mai Jameel ya tsare miki?, Jameel tun tasowar yana ƙarami biyayya yake miki bai taba Musa Miki ba duk da kinzo kin samu yana da shekara goma sha huɗu na tabbata baki yiwa Jameel wahala ba amma yana karramaki sannan yana mutuntaki kamar yanda yake mutunta mahaifiyarsa”.

Zazzafan iska ya furzar  kana still muryarsa cike da ɓacin rai yace.

“Amma ke kullum baki da buri daya wuce kici masa zarafi, Idan kin zauna ki riƙa faɗa mun magana kinyi zaton cewa bana son Jameel ne?.

Shin inada wani ɗa aduniya daya wuce Jameel ne?”.

 

Cikin tsananin fushi da ɓacin rai Hajiya Karima ta nuna kanta kana tace.

“Ni ka ciwa zarafi akan yaro ɗan maƙota dan yana abokin ɗan ka, sannan dan na faɗa maka gaskiya, kai baka ga yadda yake liƙewa ɗan nakaba duk ya hana sa tattalin arziki sannan ya hanasa ya tara abin kansa”.

Cikin wata fusatacciyar tsawa daya amsa ilahirin falon yace.

“Ki fice min anan Karima bana son ganinki”.

Afusace ta juya kamar zata tashi sama tana wani irin huci tare da jin tsanar Moddibo da M Jameel fiye da komai arayuwarta!.

 

Anutse Abba ya juya ya kalli Moddibo kana cikin sanyi murya yace.

“Dan Allah Aliyu kayi haƙuri kada ka damu da abinda tayi maka, sannan bance ka ɗauki wannan amatsayin wani mataki da zai hana ka zuwa gidan nan ba, aduk sanda kaga dama zaka zo”.

Murmushi yayi kana yace.

“Babu komai Abba ai ita mahaifiya ce agurin mu dan tayi mana haka ba zai zama wani aibu ba”.

Jinjina kai Abba yayi tare da cewa Ubangiji Allah ya al’barkaci rayuwarku”.

Atare suka amsa da.

“Ameen”.

Juyawa M Jameel yayi tare da kallon Moddibo Cikin sanyin murya mai cike da so da shaƙuwa ya numfasa kana yace.

“Dan Allah A.J kayi haƙuri”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Laa babu Komai J. Yanzu dai tashi muje mu bata haƙuri”.

 

Da sauri Abba ya kalli Moddibo kana yace.

“Baza ku bata haƙuri ba ku zauna kuci abinci”.

Kai suka gyaɗa sannan suka zauna baki ɗayansu, basu wani ci abincin kirki ba, domin ko kowa da irin damuwar dake ransa, bayan sun kammala suka miƙe tare da yiwa Abba Sallama haƙuri Abba ya sake bawa Moddibo.

Murmushi Moddibo yayi kansa aƙasa yace.

“Ayyah Abba Allah babu komai”.

Sannan suka juya har sun kai ƙofa Abba ya ɗan ɗaga sautin muryansa tare da cewa.

“Yau kam ba zamu kwana anan bane?”.

Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

“A’a Abba idan mun kwana anan Innayi ita kaɗai zamu bari acan”.

Jinjina kai Abba yayi kana yace.

“Eh kam ya kamata gida babu namiji ba gida bane kuje”.

Godiya suka masa kana suka fice.

Suna cikin mota aka kira Isha’i kai tsaye masallacin da suke limancin suka nufa kamar ko yaushe Moddibo ne yaja Sallar bayan sun idar sukayi Asham kana suka wuce gida.

 

Suna shiga gida kai tsaye sashen Innayi suka nufa zaune suka sameta riƙe da carbi ahannun Asma’u kuma tana riƙe da Alkur’ani mai girma tana karatu.

Batare da sun ƙarasa shiga ba Moddibo yace.

“Innayi Barka da shan ruwa”.

Anutse ta kallesa kana tace.

“Yawwa yau ina kuka tsaya ne baku dawo da wuri ba, nace Asma’u ta kira min ku inji kuma ashe wayar ba kati”.

Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

“Ayya Innayi Abba ne ya kiramu wai muje mu sha ruwa acan shiyasa kika jimu shiru”.

Kai ta jinjina tare da kallon Moddibo tace.

“Fatan duk suna lafiya?”.

Kai Moddibo ya gyaɗa mata  kana ya sake labulen tare da faɗin.

“Innayi akawo mana abinci”.

Ya ida mgnar tare da zama akan shimfiɗar dake barandar Asma’u Innayi ta ƙalla kana tace.

“Ɗauki abincin ki kai musu”.

Kai Asma’u ta gyaɗa sannan ta ɗauki lemun tsani ta yanka ta matsa kaɗan akai  kana tayi slinzing ɗin ƙwoyi kana ta zuba musu wadataccen man gyaɗa da kuma dakekken yajin barkono sai Cucumber da Cabbage ta Kai musu.

Sosai suka Moddibo da M Jameel suka ci ɗan waken tare da 5alive, bayan sun kammala kai tsaye ɗakinsu suka wuce tare da watsa ruwa, kana suka sake shiryawa tare da feshe jikinsu da turaraku masu daɗin ƙamshi.

Cikin nutsuwa suka fito aharabar gidan suka samu Innayi da Asma’u sun fito buɗe bayan motor sukayi suka shiga sannan Moddibo ya shiga mazaunin Driver yayin da M Jameel yashiga gefen mai zaman banza, kai tsaye masallacin suka nufa har suka isa ƙira’a na tashi amotar suna parking Innayi da Asma’u suka shiga sashen mata suka ma suka ƙara sa sashen su.

 

Yau ma kamar kullum gaba ɗaya cikin masallacin da harabar sa cike yake da ɗumbin jama’a cikin tsantsar nutsuwar daya zame musu jiki suka nufi wajen zamansu cikin sanyi mai cike da kamala da kuma kamun kai Moddibo ya ajiye System ɗin sa kana ya zauna tare da ɗan jingina bayansa da  jikin kujeran ya lumshe Idanunsa tare da motsa laɓɓansa alamar tasbihi Shikuwa M Jameel zaman microphone da aka dasa masa  ya gyara tare da buɗe System ɗin sa Lokaci ɗaya cikin masallacin ya gauraye da  ƙamshin sanyayyan turaren su yayin da hasken Fararen glob ɗin ya haskaka hasken farin fuskarsu na fitar da sheƙin annuri yayin da baƙin sajensu ya kwanta luf-luf komai nasu kusan ɗaya yake tamkar tagwaye.

 

Cikin nutsuwa M Jameel ya lumshe Idanunsa tare da gyara zaman Microphone kana Yayi gyaran murya cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da kamala yayi gyaran murya kana yace.

_“Innalhamdulillah Nahmaduhu Wanastainuhu wanastaghfiru wa’nazubillahi billahi min shuriri anfusna wamin sayyi ati a’amalina manyah dillahu fala hadiyala waman yudil fala mudillalah Wa’ash hadu Allah ilahalillahu wahdahu lasharika Wa’ash hadu anna Muhammadu Abduhu warasulu Ya Ayyuhal lazina amanut taƙullaha haƙƙu tuƙatihi wala tamu tunna illah wa’antum muslimun Ya ayyuhan nasu taƙu rabbakummalazi halaƙakum min nafsi wahida wahalaƙa minha zaujuha wabassa min huma rijalan kasiran wa Nisa’a wattaƙullahal lazi tasa aluna bihi wal arhama innalaha kana bikum raƙiba, Amma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”_.

 

A tare jama’ar dake cikin masallacin suka amsa da.

“Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

A hankali M Jameel ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa kana a hankali yace.

“A yau muna sha huɗu ga watan Ramadan a cigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma da muke acikin masallacin mai Martaba sarki Bashiru acikin Suratu An-Nisa’i ayau zamu tashi akan aya ta Cassa’in da huɗu wala Allah kuma bazai wuce da biyar zamu tsaya ba, sai kuma shekara mai zuwa idan Allah ya bamu aron rai da lfyar”.

Sai kuma ya sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.

“Tun daga kan aya na cassa’in da biyu muka shiga babi akan kashe ran mumini, da kuma hakkin ran Muminai,  ayau Insha Allah zamu cigaba, amman kafin nan zamuyi duba i zuwa kan dukkan ayoyin Alkur’ani dake mgna kan ran muminai”.

A hankali ya buɗe kwayar idanunsa, sabida jin yadda masallacin ya cika da kabbara.

Gyara system ɗinshi yayi kana yace.

“Insha Allah ayau Aramma zai zaƙulo mana Ayoyin da Ubangiji yayi magana akan hakkin kashe ran mumini, domin tunatar wa da kuma jan hankali da kuma fito da darajar ran ɗan Adam Dan kiyaye lalacewar zamani da kuma tunatar da hakkin ran musulmi amatsayin ba komai ba”.

Cikin yanayin kamala ya juya tare da maida kallonsa kan Modibbo  da idanunsa ke lumshe ajiyar zuciya sauƙe  kana yace.

“Aramma bamu ayoyin da Ubangiji yayi magana akan kashe ran mumini”.

Anutse Moddibo ya gyara zamansa tare da ɗan ture system ɗin sa gefe kana yayi gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryarsa ya fara kamar haka.

Surah Al-ma’idah Aya 32

مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعًا

Ya ƙare jan karshen ayar da fesar numfashinsa da ya riƙe domin fidda cikekken haƙin ko wanne harafi,

Yayin da Al’ummar Annabi dake cike a masallacin kuwa, sukayi sit suna masu samun cikekkiyar nitsuwa ta mu’ijizan jin karatun Alqur’ani mai girma kenan.

M Jameel kuwa cike da raunin murya ya fara fassara ayar Allah madaukakin sarki nacewa-:

“Sakamakon haka ne muka wajabta akan ‘ya’yan Isara’ila cewa, duk wanda ya kashe wata Rai ba tare da ita Rai ɗin ta kashe wata ba, ko kuma yayi ɓarna a kan ƙasa (ta’addanci, Fashi da makami etc) toh kamar ya kashe mutane ne gaba ɗaya na Duniya kuma ubangiji zai hukunta shi dai-dai da laifinsa”.

Shiru masallacin yayi baki ɗaya, kowa jiki nai a mace, yayinda manyan dottaɓai dake ciki kuwa, suka zuba M Jameel da Modibbo ido suna nazartan yadda akayi akalar tasirin ya sauya daga kan Suratu An-Nisa’i ya koma kan duk ayar da ke mgn kan kisan kai.

Shi kuwa M Jameel juyowa yayi ya kalli Modibbo tare  cewa.

Aramma koma cikin suratul Al-ma’idah akwai ayar da Allah ke mgn kan rayuka”.

Cike da ƙwarewa da cikekkiyar hadda mai ɗauke da kaifin basira, Modibbo ya lumshe idanunsa da yakeji suna cika da rauni cike da zaƙin murya ƙira’a mai sa nitsuwa ya kawo ayar

Surah Al-ma’idah Aya 33 إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ.

Cike da nitsuwa ya dire ƙarshen ayar,

M Jameel kuwa gyara zamansa yayi tare da fara fashin baƙin.

“Allah madaukakin sarki nacewa-:

Lallai sakamakon waɗanda suke yaƙar Allah da Manzo nai, kuma suke yaɗa ɓarna a doron ƙasa (ta’addanci, Fashi, ƙwamushe Garkuwa Da mutane etc), shine a kashe su, ko a giciye su”.

Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa wanda tuni suke sheƙin ruwan hawaye, murya cike da rauni yaci gaba da cewa.

“Ko a yanke Hannayen su da Ƙafafuwan su a saɓani (hannun hagu da ƙafar dama, ko kuma Hannun dama da ƙafar Hagu), ko kuma a kore su daga Garin.”.

Zuwa yanzu shar-shar hawayensa ke kwaranya yayinda tuni muryarsa ke rawa, haka yasa da yawa mutanen suke zubda hawaye.

Haka dai Modibbo ya rinƙa zaƙulo dukkan ayoyin Alkur’ani dake mgna kan ran mumini, M Jameel na fassarawa, yayinda gaba ɗaya zuƙata  jama’ar masallacin ya cika da rauni.

Kasan cewar gobe ne, Modibbo da M Jameel ɗin zasu wuce ƙasa mai tsarki, damin yin Umrah Ramadan, yasa dole a ranar aka rufe tafsir ɗin. Bayan jero Addu’o’in wa al’ummar musulmi dama kasa baki ɗaya.

 

Washe gari ranar 15 ga watan Ramadan misalin ƙarfe tara na dara dai jirgi su Modibbo ya tashi daga cikin Taraba zuwa ƙasa mai tsarki…!

 

 

 

Daga yauwa ɗin nan Laraba mun gama free page, in kina son ci gaban littafin SAKAYYAH to ki biya ki karanta cikin aminci. Littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Ki biya ki karanta ba haƙƙin kowa a kanki.

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button