Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 78

Sponsored Links

*💖 NIHAAD💖*

*78*

Khalil ya girgiza kai yayi kasa da murya yace “Kar ki ce haka pls Nadeeyah, don’t say that plss, it’s a promise we made na auren juna, do not allow us break that promise plss…” Nadeeyah tace “Plss kada mu ja issue din nan Kjay, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gareni, sannan kuma gareka, let’s close this case forever and ever, in dai ba ja kake son yi da mahaifiyata ba….” Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai, tayi murmushi tace “So what’s up now?” Jinginar da kansa kawai yayi jikin kujera a hankali yace “Ba wani mahaifiyarki Nadeeyah, dama kin riga kin sa a ranki ke baza ki auri me mata ba, kuma kin fada just now, baxa ki aureni ba saboda ina da mata yanzu, i understand u are just using this new issue to cover up” Tace “I agree with what ever u think Kjay, ko da na aureka bazan samu rest of mind ba i know, so i love the way things took a new turn, from henceforth u are the brother i neva had, zan daukeka matsayin babban yayana that will always be there for me” Shiru kawai yayi yana kallonta lokaci daya duk yanayinsa ya canza, tace “Let me get u water and some slice of cake” Daga haka ta mike ta nufi cikin gidan ya bi ta da ido babu ko kiftawa. Bayan la’asar Khalil ya shigo gida bangaren Mami, gaba daya mood dinsa wasn’t good, Parlor ya tadda Mami da Noor xaune suna kallo tare, ya nemi waje ya zauna yana kallon Mami cikin sanyin murya yace “Ina yini” Ta kallesa tace “Lafiya lau” Shiru yayi, bayan wani lokaci a hankali yace “Mami me yasa baki gaya min abinda ke faruwa ba?” Mami tace “Yanxu dai ba ka je ka jiye ma kunnenka ba Khalil” Jin bai ce mata komai ba ta kallesa, taga kallonta yake alamar dai he is speechless, tace “Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ku baki daya, Allah ya bata miji na gari ita kuma” Mikewa kawai yayi ya bar parlon Mami ta bi sa da kallo. Mami na zaune parlon Janar da shigowarsa gidan kenan wajen karfe biyar na yamma, Apple ne da ta yanka masa a gabansa yake ci, ta ci gaba da maganar da take masa a hankali tace “Toh yanzu suna son za su dawo maka da kudaden ne” Ya kalleta da sauri yace “Inyi me da su? No they should keep it, it’s okay ba damuwa, haka Allah ya tsara” Mami ta sauke ajiyar zuciya tace “Toh shikenan, zuwa Anjima zan kira Hajiya Safeenar in gaya mata, kai kuma Allah ya kara girma” Wayarsa dake gefensa ya dauka saboda kiransa da ake ya daga ya kai kunne a takaice yace “Basu wayar kawai in masu magana idan ka iso…” Daga daya bangaren me kiran nasa yace “Amma kana ji na Abubakar, dama ban maka bayani bane, zancen gaskiya bani kadai bane, kuma muna isowa suka fara kora mu babu tantama kila ka gaya masu….” Janar ya katse sa yace “Da kai da waye?” Yace “Da dai ka bugo masu waya kayi masu magana su bari mu shigo sae kaga ni da wanene” Janar yace “Kaga Yaya ni ba kowa nake kawowa gidana ba gaskiya, banda kai sai Abdulrazaq babu wanda yasan inda nake, ban kuma ga dalilin da zaka kawo min wani gidana ba, kai baka ga irin security din wajen bane” Yace “Kwarai na sani Abubakar amma don Allah kayi hakuri dole ce tasa na taho ba ni kadai ba, amma….” Janar ya katse wayar kawai, ya dau wayarsa da sojojin suka san sa da shi ya kira, ya kuma basu umarnin tahowa da Yayan nasa wanda suke uba daya tare da bakon nasa har zuwa cikin gidansa ba sai anyi ta tsayar da su a checking point ba, Mami na kallon Janar tace “Amma baka sanar min za kayi baƙi ba a tanadar masu abu na musamman Janar” Yace “Tun last week yake ta son mu hadu to kinga i am so busy, saboda shi ne ma nayi canceling tafiyata na yau, banda zuciyar musulunci ni zan kalli Umaru ma kuwa balle in bar sa ya zo har gidana? Wuyarta dai Allah ya daga mutum nan xai ga wa enda suka yi ta nufansa da sharri sun fi kowa son su kasance da shi, ni fa nan da kike ganina na dawo daga rakiyar mutane wllh” Mami ta girgiza kai cikin kwantar da murya tace “Ka daina kawo abubuwan baya da suka wuce Janar, sannan yan uwanka ne su kuma hannunka baya taɓa rubewa ka cire ka yar, ka dubi girma irin ta zumunci kayi hakuri duk ka yafe masu kai ne a gaba, su kuma a baya, hakurin ka ne ya kai ka har wannan matsayin da su basu samu ko 5% dinsa ba, don haka eraze all this off ur mind” Janar ya mike ya fita daga parlon zuwa parlon baƙi don har sun shigo gidan don a mota yayan nasa yake, Mami ta bi sa da kallo sai kuma ta mike ta bi bayansa, Janar na shiga parlon baƙin yaga Yayan nasa Umaru zaune saman kujera, Alhaji Umaru yace “Ran babban soja ya dade” Kallonta kawai Janar yake da mugun mamaki, ita kuwa ta sunkuyar da kai kamar munafuka, Janar ya kalli yayan nasa rai bace yace “Yaya wacece wannan din ka kawo min gidana? Kuma a kan wani dalili” lokaci daya ta fashe da kuka sosai tace “Don girman Allah yaya kayi hakuri ka yafe min duk abinda nayi maka wllh sharrin shaidan ne, na tuba bazan kara ba yaya, ka dubi girman Allah kayi hakuri, duk inda mahaifiyarmu take bazata ji dadin wannan abinda ka min ba wallahi” Alhaji Umaru yace “Har gidana ta zo ta sameni tana kuka Abubakar akan cewar in rakata ta zo ta baka hakuri domin idan taje ita kadai sojojin koran karya suke mata ga kuma tsallan kwado da za su sa ta tayi ta koma gida kafa duk a kumbure, dalilin da yasa nayi ta kiranka kenan nace maka lallai lallai ina son mu hadu….” Janar yace “Amma baka kyauta min ba Umaru, kuma da nasan da wannan shaidaniyar zaka shigo min gidana wllh bazan bari kai ma ka shigo ba, wannan ai bai dace ba, ina ruwanka da tsakanina da Hassana?” Alhaji Umaru ya marairaice yace “Ni fa gyara zan yi Abubakar, naga dai yarinyar nan uwarku daya kamar yanda muke uba daya da kai, kaga kuwa nima ai er uwata ce kuma baxan ga wata baraka in yi shiru ba” Mami ta shigo parlon da sallama don gaisawa da Alhaji Abubakar, da mamaki ta dinga kallon Hassana warce tayi bakikirin kamar roban wanki, wanda dama baƙin shine ainahin colour dinta amma man shafawa me shegen tsada da Ac da ciye ciyen kayan dadi a gidan Janar yasa ta koma jajir kamar baturiya, Mami ta dai karasa ciki ta zauna ta gaida Alhaji Abubakar sannan ta kalli Aunty Hassana tace “Sannu Hassana ya kwana biyu?” A dakile Aunty Hassana tace “Lafiya lau” Sae kuma ta kalli yayan nata cikin rawan murya tace “Wallahi kwayar abincin da za mu ci babu a gidana Yaya, tun barinmu gidan nan nayi ma Aliyu kira yafi dubu amma wllh yaki dagawa, ban san inda ya tafi yake rayuwarsa baya son mu rabesa ba ya bar mu cikin wannan halin da muke ciki da kannensa, ni ba sisi ba, kuma bani da dalilinsa tunda ba kasuwanci na iya ba, dama dubu dari bakwai ne a account dina bayan bari na gidan nan, na kama mana hayan dubu dari shidda daki daya da parlor da bandaki a can cikin gari, dubu dari din na siya mana kayan abinci, to yanzu ko kwayar shinkafa babu a gidan, tunda muka shigo satin nan a wahale kawai muke wllh yaya, su Sajidah ma babu kudin motar zuwa makaranta” Janar yace “Ina ubansu da zaki kawo min maganar banza?” Tace “Ni dai kayi hakuri duk abinda nayi maka yaya, na maka alkawarin hakan bazai sake faruwa ba, ai mun horu haka kusan wata daya da sati biyu, don Allah kayi hkuri ka yafe min” Janar ya mata tsawa yace “Me kike nufi yanzu?” Daga ita har Umarun sai da suka tsorata a parlon, Umarun yayi karfin hali yace “So take kayi hakuri ka bata dama na karshe ta dawo nan da yaranta su ci gaba da zama Abubakar, kuma in sha Allahu bazata sake yin abinda tayi ba” Janar ya girgiza kai yace “A area din da nake ma Hassana bata isa ta zauna ba balle cikin gida na, abu daya zan iya yi ma Hassana kuma shine na karshe wallahi kun ji na rantse kuma bazan yi kaffara ba, Sannan bana son ko da wasa ta sake zuwa kusa da inda nake idan kuwa ba haka ba zan sa sojoji su halbe min ita, Nauyin yaranta kuma ba a kaina yake ba ta kwashesu ta mayar gun ubansu da ta rabasa da su tun suna yara, ita kuma albarkacin zumunci zan tura mara miliyan biyar a account dinta taje ta koyi kasuwanci tayi, iyakar abinda zan iya yi ma Hassana kenan, bayan nan kar ta sake making mistake din zuwa kusa da inda nake idan ko ba haka ba bazata ji da dadi ba” Umaru yace “Yo ai hakan ma ta gode, Miliyan biyar a wannan marran, aa wllh ta gode….” Janar ya fice daga parlon, Mami dai na zaune parlon ta kasa cewa komai, Aunty Hassana ta daga kai tayi mata wani kallo ta dauke kai, Mikewa Mami tayi ta fita daga parlon, Umaru yayi kasa da murya tace “Toh yanzu nawa zaki turo min kenan Hassana? Kin ji fa har miliyan biyar, ke ko kin haye wllh” Ta galla masa wani kallo tace “Ehh lallai amma baka da tsoron Allah, kai da nace ka tursasa ka dage kayi min kokari wajen ganin ni da yarana mun dawo gidan da zama, ni ban ma ga amfanin zuwanka ba, ko ni ai zan iya zuwa ya bani miliyan biyar din ba sai ka rakoni ba Umaru” Umaru da ya bude baki yace “Amma ke butulu ce Hassana, haka za ki ce min? Ba don ni ba ke kin isa ki zo kusa da layin nan??” Ko kallonsa bata sake yi ba, Sai ga Janar ya shigo yana kallonta strictly yace “Na tura maki miliyan biyar, yau ya zama rana ta karshe da za ki shigo unguwar nan idan ba haka ba wallahi baza ki ji da dadi hannun sojojina ba” Ta marairaice tace “Toh yaya nagode, Allah ya kara girma” Daga haka ta mike ta dau Handbag dinta ta nufi kofa, Umaru ya bi ta da kallo baki bude har ta fita, Janar yace “Na tura maka 100k ka kara mai a motarka” Yayi shiru da farko, sai kuma yace “Toh, toh, to ba damuwa” Janar yace “Zan shiga ciki, ina expecting wasu baƙin” Mikewa Umaru yayi ya nufi kofa, kana ganin reaction dinsa kasan ya raina 100k din, har ya fice daga parlon babu sai anjima, Janar ya koma part dinsa, Aunty Hassana na barin gidan ta kira wata kawarta da ta hadata da wani sabon malami dake cikin garin Abuja, bayan sun gaisa tace “Sabira na samo kudi yanzun nan, nawa kika ce yace za a bashi last price?” Sabira tace “Ke Allah fa ya sa ya samu lokacinmu, Kinsan yan siyasa kawai yake ma aiki amma zan je har gidansa in lallabasa yayi mana aikin” Aunty Hassana tace “Yanzu dai nawa za a bashi nake tambayarki?” Tace “Wallahi miliyan biyu ma Allah ya sa ya kallemu, shi fa aikinsa kamar yankar wuka yake, karamin kudi da yake amsa idan yayi aiki baya yin kasa da miliyan biyu” Aunty Hassana tace “Toh zan tura maki yanzu, Don Allah ko ma me zai yi yayi kawai aga cewar ba er sa bace a result din nan” Sabira tayi wani dariya tace “Sha kuruminki Hassana, kawai dai ki hado min da miliyan daya da na ara maki kika kai ma wannan munafukin malamin da har yau bakya samunsa a waya” Aunty Hassana ta ɗan yi shiru, yanzu fa idan ta tura 3m kudin saura 2m kenan fa, a ranta tace to meye in dai bukata zata biya, ana gamawa da case din Hanan, sauran miliyan biyun zata ba malamin yayi mata aiki akan Janar, sanda zai ce ta dawo ba sani zai yi ba. Tun da Khalil ya shigo corridor din part din Mami ya ji wani kamshin turaren wuta me birkita hankali na tashi amma ya rasa ta wani direction ne, it’s just past 9 now, yayi ta bin ko ina da kallo, can ya nufi guess room dake part din don kamar ta nan kamshin ke fitowa ya baza corridor din, bude kofar dakin yayi yana kallon ciki, tana zaune gaban mirror tana shafa kwallacham, ga garwashin turaren wutan a kasa, ta zaro ido tana kallonsa har ya tura kofar ya karaso cikin dakin ya nufota yana kallon gashin kanta da yayi bakikirin sai sheki yake, tayi narai narai da ido tace “Wallahi yanzun nan Mami ta fita kuma yanzu zata dawo, plssss ka fita kar ta shigo” Ya jingina da bayanta yana jin wani fitinannen kamshi na tashi a jikinta hade da na turaren wuta, ga wani laushi na musamman da yaji jikinta ya kara kamar ainahin auduga, kasa magana yayi da farko, can dai ya dake murya can kasa yace “Ina kika shiga duk yau ban ganki ba Baby? I have search everywhere ban ganki ba” yana fadin haka taji chilled lips dinsa a wuyanta, ta marairaice tace “Na shiga uku, don Allah ka bari pls, wllh Mami is coming back now” Ko rufe baki bata yi ba Mami ta bude kofar dakin, da sauri ya saketa ya koma baya, kallo daya Mami tayi masa ta nufi gun garwashin wutan rike da wani kwalban turaren wuta, Nihad dai ta kasa daga kanta ta ci gaba da shafa kwallacham da take yi, Ya kasa kallon Mami shi ma don juya mata baya ma yayi, can dai ya shafa kansa ya nufi kofa kamar munafuki har ya fita daga dakin ya jawo kofar, Mami ta gama sa mata turaren wutan wanda na tsugunno ne, ta sa mata stool din sannan ta gaya mata yanda zata yi, Mami na tsaye for almost 7 minutes kafin tace “Dau kayan baccin naki mu je ki kwanta” da a nan dakin zata kwanta amma jin abinda Mami tace mata ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta bi bayan Mami zuwa ɓangarenta ta kwanta a bedroom dinta, ita kanta wani daban take jin ta, tun da suka fita daxu da safe suka tafi wani tsadadden saloon wanda ya fi inda Mimi ta fara kai ta farkon zuwanta gidan, bayan an gama mata gyaran gashi aka kai ta wajen gyaran jiki duk a katon building din saloon din, ita kanta bayan an gama gyaran jikin sai da jikinta ya bata sha’awa, luwai din kenan don sai wani glowing take ko ina yayi sumul a jikinta, washegari da safe ma zata sake komawa saloon din don ci gaba da gyaran jikin, tun da suka dawo kuwa Mami ta bata abubuwa sun fi a kirga ta sha, shi yasa ko abincin dare ma bata iya ta ci da yawa ba, a haka har bacci ya dauketa, da mafarkai iri iri na mijinta. wajen karfe sha daya sai da khalil ya sake komawa dakin amma ya ga wayam, he felt like dying… Washegari da safe ya shigo bangaren Mami, jiya da damuwa ya kwanta don ko baccin kirki bai iya yayi ba, he just can’t endure it any longer shi dai kawai a basa matarsa su bar gidan nan, Bayan ya gaida Mami yayi shiru ya ma rasa me zai ce mata, Wayar Mami ya fara ring ganin Janar ke kiranta ta mike ta fita daga parlon zuwa ɓangarensa, a hankali ya mike ya nufi Bedroom dinta don tun da ya shigo kamshin Nihad na jiya kawai yake ji a parlon, babu kowa dakin kawai ya juya ya fice daga bangaren rai bace, don kafin ya shigo sai da ya fara shiga guess room nan ma babu kowa ciki, har dakin Mimi ya shiga yaga ba kowa, kawai ya nufi dakin Noor ko amsa gaisuwarta bai yi ba yace “Ina su Mimi?” Tace “Mami ta sa driver ya fita da su not too long” Kasa cewa komai yayi, can ya juya fuu ya bar bakin kofar ya koma dakinsa, makullin mota kawai ya dauka ya bar gidan ko zae samu relieve din walakancin nan da ake masa…. Mami na zaune parlon janar bayan ya sanar mata dalilin da yasa ya kirata har ya bata takardan ta duba, cike da murna tace “Alhamdulillah, what a good news, Naji dadin wannan lamarin wallahi, dama kai ne kawai ka sa kokwanto a zuciyarka tun farko, amma ni har ga Allah naji a raina ba haka bane, to maa sha Allah tunda yanzu zaka kauda zargi a ranka” Janar ya nisa yace “Abokina da ke kaduna will be coming back together with her tomorrow don akwai jirgin sojoji da zai taho nan Abuja” Mami tace “Toh Allah ya kai mu” Bata jima a parlon ba don ta bar wayarta a parlonta kuma za a kawo mata turarrukan wuta da tayi order jiya da daddare, har ranta tayi farin cikin kasancewar Hanan er Janar she is so happy with this good news. Sai kusan azahar su Nihad suka dawo tare da Mimi glowing din yau har ya fi na jiya, gyara ne na gaske aka mata wanda da zaka ji kudin da aka kashe zaka rike baki, bayan sun yi wanka sun ci abinci Mami tace “Kin kira mum dinki yau?” Nihad tace “Ehh mun yi magana da ita” Mami tace “Good, ki hada duk kayanki dake nan, zuwa da yamma za ku koma can gidanku…” Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mimi ce ta hada mata kayan nata duk a akwati biyu, bayan la’asar Mami ta sa ta taje tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da mayafinsa, sannan ta bata sauran magungunan nata da suka rage ta sakata ta shanyesu tas, Ganin normal dankunne ne a kunnenta ta bata na gold ta saka, Suna daki Khalil ya shigo parlon ta dalilin kiransa da Mami tayi almost 2 hours ago, Mami ta fito ta gansa zaune, ya gaisheta can ciki ciki, Mami na lura da yanda ya wani tamke fuska ta ci gaba da harkokin gabanta a parlon, can dai yace “Gani Mami” Mami ta kirawo Nihad, Nihad ta fito parlon ta duka jikin kujera tace “Gani” Mami tace “Fito da kayan naki ku wuce” Khalil ya daga kai ya kalli Mami da sauri yana son sake tabbatar da abinda tace, Nihad dai bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Mami tace “Ko kuma bari in kira Mimi ta kai maki kayan mota” Ta dau wayarta kan kujera tayi dialing number Mimi ta ce ta zo ita da Bilkisu su fitar da kayan Nihad zuwa mota, Mikewa Nihad tayi a hankali ta koma dakin, Khalil ya ɗan kalli Mami sai kuma ya mike ya nufi kofar dakin yana kallon Nihad yace “Ina kayan?” Ta kallesa da sauri, shi yayi abun amma ita ta tayasa jin kunyan, tayi narai narai da ido tana kallonsa kamar zata yi kuka, ko a jikinsa ya karaso ya dau duk akwatin biyun ya fita, Mimi da Bilkisu na shigowa turarrukan wutan da Mami tayi order ma Nihad suka dinga fitarwa zuwa motarsa, turarrukan wuta ne masu shegen tsada, da na tsugunno, kwallacham, Humra, miski, infact duk wani abun kamshi dai da mace zata bukata, Nihad dai na jikin kujera kanta a kasa, Mami tace “Toh Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya Nihad, ki kula da tsaftar jikinki da na gidanki… sannan kuma kiyi hakuri ki zauna lafiya da mijinki kin ji?” Cikin sanyin murya Nihad tace “Nagode Mami, Allah ya kara girma” Mami tayi mata murmushi tace “Ameen” Khalil ya shigo parlon ya shafa kai yana kallon Mami yace “Za mu tafi Mami” Taɓe baki Mami tayi tace “Allah ya tsare” Daga haka ta nufi dakinta tana kallon Nihad tace “Toh tashi ku je, Allah ya kiyaye hanya” Nihad da har hawaye ya cika idonta ta mike a hankali tace “Nagode Mami” Yana gaba tana biye da shi suka fito babban compound din gidan, Mimi na tsaye har suka bar compound din tana daga masu hannu, sai bayan da suka bar anguwan ya kalli Nihad dake share kwallar da yaki tsaya mata, ya gyada kai yace “Na gasken zaki yi anjima, wannan ai ba kuka kike ba” Ta ɗan kallesa cike da shagwaba tace “Toh ina ruwanka da kukana” Er dariya yayi yace “Kin ga kuwa Anjima ai da ruwana da kukanki tunda ni zan sa ki”

 

*Toh a dai yi kokari a sauke hakki, idan baki sauke a nan ba to ban san kuma inda zaki je ki sauke ba, cause my book is not free*

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Leave a Reply

Back to top button