Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 71

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

71

Khalil na tsaye balcony a sama yana kallon motocin suka gama shigowa babban compound din, wani soja ya bude ma Mami motarta ta sauko, Nihad ma ta sauko suka nufi entrance din shiga gidan, Mimi da Noor dake zaune main parlor suka yi welcoming dinsu suka wuce Upstairs gaba daya zuwa bangaren Mami, Suna shiga parlor Nihad ta zauna saman kujera, Mami ta sa Bilkisu ta tafi ta hada mata ruwan wanka a bandakinta, Bilkisu na fitowa daga bedroom din Mami ta kalli Nihad tace “Shiga kiyi wanka, sai ki kwanta ki huta, hope u are not hungry?” Nihad ta girgiza mata kai tace “Aa na koshi” sannan ta mike ta shiga bedroom din Mami, Mami ta bi ta da kallo, ko da ta fito wanka taga akwatin kayanta an kawo mata cikin dakin, ta dau doguwar riga mara nauyi ta saka sannan ta kwanta gefen gadon…. Mimi na fito da tsaraban da Mami tayi a Uk a cikin wani babban akwati Khalil ya shigo parlon, duk yawanci kaya ne da ta siya ma Nihad irin English wears, su Mimi ma ta siyo masu abubuwan da tasan sun fi so, Zaunawa Khalil yayi saman kujera yana kallon Mami yace “Barka da isowa Mami” Ita ma ta kallesa tace “Yauwa” Yace “Ya hanya” tace “Alhamdulillah” Bai sake cewa komai ba, Tace “Abbanka yace min ya samar maka aiki ko?” Khalil yace “Ehh haka ne” Mami tace “Toh Allah ya sanya Alkhairi” Yace “Ameen” yana ta zaune parlon yana kallon Mimi dake ta fiddo kaya tana waow, can kawai ya mike ya nufi Bedroom din Mami, yana shiga ciki kuma ya kulle kofar, Nihad ta daga kai ta kallesa don har sannan bata yi bacci ba, ya karasa kusa da ita ya zauna yana kallonta, a hankali yace “How are you feeling dear?” Ta sauke idonta tace “Alhamdulillah” Ya dagota zaune yana kare mata kallo as if wanting to see the pregnancy with his naked eyes yace “Sure?” Ta kallesa dai bata ce komai ba, a nan yaga yanda ta kara ramewa, sae dae kawai tayi haske sosai, yayi kasa da murya a bit worried yace “I want you to go back to ur former Nihad pls, i don’t like the new you…” Murmushi kawai yaga ta yi ta dauke kanta, ya kamo hannunta yace “Plss….” Ta sake kallonsa, yayi kasa da murya yace “Are you not comfortable being with my household? Or do you have any problem staying here?” Ta girgiza masa kai, yace “Then why are u always silent, always moody, and baki son ki saki jikin ki….” ta daga kai ta kallesa tace “I am still recovering, and i am yet to recover fully, but Alhamdulillah i am grateful to God for making me this strong in all situation i found my self…. 1st ban samu proper coach from childhood ba which made me who i am today, and i am still yet to recover from the shock of who i found out my Stepmom was, Bad friends that led me astray, even in relationship i wasn’t lucky, babban damuwata kuma shine Abbana bai ce ya yafe min ba har yanzu, and i have many people to ask for forgiveness from…..” Tana kai wa nan ta daga kai tana kallonsa, Har ransa yaji tausayinta, cikin sanyi yace “Forget ur past and face the future Nihad, and i am assuring you the future is super bright, this is ur new life now, ki manta da komai ki fara sabuwar rayuwarki….” Hawaye yaga ya cika idonta, sai kuma tayi saurin gogewa, shi dai ya tsura mata ido, A hankali tace “And still yet my challenges are not over…” Ya kamo hannunta yace “You think so? Wani challenge ne kike gani a gabanki yanzu” Tace “Time shall tell, may be i will never be happy in life…” Ya girgiza kai yace “Kar kice haka” Ta gyada kai tace “Ohk, but i will love to ask for a favor” a hankali yace “Ina jin ki” Tace “Ina son zan je in ga Mumy…” Ya ɗan yi shiru yana kallonta da mamaki, sai kuma yace “But ai bamu dade da dawowa daga Kano ba, and baki da lafiya yanzu bai kamata kije ko ina and stress ur self out ba” Tace “Ni na samu sauki, plss allow me” Yace “No Nihad, ki bari idan kin kara samun sauki sai in kai ki kiyi 5 days a can….” Ta marairaice masa tace “Nace maka na samu sauki, even if it’s just for 2 days, i just want to see her plss” A hankali yace “Ohk dear, i will talk to Mami” Tace “Thank you” Murmushi kawai yayi mata yana kallonta, a ransa kuwa tunani yake if this is the right time da zai kawo mata zancen Nadeeyah, bai taɓa ganinta speaking so calm with wisdom haka ba, but kawai kuma dai ya fasa cause bai son mood dinta ya canza yanzu ta dalilinsa, yace “Ain’t you hungry?” Ta girgiza masa kai, yace “Ohk” Komawa tayi ta kwanta tace “Ina son zan yi bacci” Daga haka ta rufe ido, yayi shiru yana ta kallonta, can yace “Ohk dear” Gyara mata duvet yayi don dakin akwai sanyi sannan ya mike ya nufi kofa ya fita ya kulle, Bai kalli Mami dake zaune parlon har sannan ba ya nufi kofar fita daga parlon. Bayan Azahar Khalil na saukowa downstairs ya ga Mami zaune main parlor suna kallon wani program da Bilkisu, tun da ta sauko raka Hajiya Safeenah da ta zo yi masu sannu da zuwa ta zauna nan parlon bata koma sama ba, wanda rabonta da zama parlon har ta manta saboda su Aunty Hassana, Khalil ya karaso ya zauna parlorn, Bilkisu ta mike ta bar masu parlon, Mami tace “Abincin ka na can dining din kitchen” Yace “Ohk” Mami bata sake ce masa komai ba ta ci gaba da kallonta, Ganin bai tashi ba bayan wani lokaci ta kallesa tace “Ko kana da magana ne kake ta kallona haka?” Yace “Ai baki gaya min yanda ake ciki ba batun zuwa ganin likita da ku ka yi” Mami tace “To tunda ba kai ka aikeni ba ta yaya zan gaya maka yanda ake ciki” Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace “Alhamdulillah ba wani matsala, sun rubuta mana drugs mun siya a can, sauran measures din kuma duk zan sa ido tunda tana nan” Yayi shiru yana kallonta, can a hankali yace “Amma Mami tace min tana son zuwa wajen Mum dinta, kwana uku kawai zata yi a can” Mami ta kallesa tace “Yaushe ku ka yi hakan da ita?” Yace “U can ask her, nace mata a’a amma da naga ta damu shine nace zan maki magana” Mami tayi shiru kamar me nazari, can tace “Da dai ta bari nan da sati biyu kafin nan ta kara kwari” Yace “Toh ki mata magana Mami, nima haka nace mata” Mami tace “I will talk to her” Mikewa yayi ya wuce kitchen…. Wajajen karfe hudu da wani abu Bilkisu ta shiga bedroom din Mami da abinci iri uku sai farfesun kayan ciki, Nihad dake zaune kan darduma ta bi ta da kallo har ta fita, tana fita Mami ta shigo, Tace “Ki duba abinda zaki iya ci a ciki sai ki diba” Nihad tace “Toh” mikewa tayi ta taho gun abincin ta bude, tuwo da miyar kubewa ta zuba, Mami tace “Eat little at a time don kar kiyi amai kin ji?” Nihad tace “Toh” Daga haka Mami ta fita daga dakin, bata wani ci abincin ba a haka Mami ta dawo ta sameta ta jinginar da kanta da gado ga abincin a gabanta wanda bai fi loma uku tayi ba, Mami ta zauna gefen gado tace “Ko kina son wani abu ne ba tuwon ba?” Nihad ta sunkuyar da kanta tace “Na koshi ne” Mami ta dinga kallonta, ganin kamar she is moody kamar ko da yaushe, tace “Kince ma Khalil za ki je wajen Mum dinki ne?” Nihad ta kalleta tace “Ehh” Mami tace “Toh ki bari ko nan da sati daya idan kin huta sai ki je, kinga yau muka dawo daga tafiya” Nihad ta kasa cewa komai, lkci daya hawaye ya kawo idonta tace “Toh” Mami dai bata sake ce mata komai ba ta mike ta fita, Nihad ta hade kanta da gwiwa hawaye na sauka idonta. Mami na fita dakin ta tafi bangaren khalil don har sannan yana gidan bai fita ba, bayan ta shiga dakin tace “Ta shirya gobe ka kai ta sai tayi kwanakin da take so a wajen mamar tata, but za ku tafi da ko Mimi ko Noor” Khalil ya dinga kallonta tace “Sai kayi maku booking flight ko na safe ne gobe” Daga haka ta juya ta fita daga dakin, shi dariya ma ta basa, ya girgiza kai kawai. Washegari da asuba Mami ta shiga dakin Mimi tace “Dear ki shirya kayanki ko kala biyu ne za ku je kano da yayanki, he will be taking his wife home for somedays” Mimi tace “Ohh but am having presentation in school today Mami, amma dai ba komai nasan excuse da zan bada” Mami tace “Aa, je kiyi presentation dinki, you won’t miss that, Noor will go with them” Mimi ta ɓata fuska tace “Mami plss, i know how to cover up, beside Noor da take crams ai bata zuwa ko ina” Mami tace “Ni dai nace kije makaranta kiyi presentation dinki” a hankali Mimi tace “Ohk” Mami ta juya ta fita dakin ta tafi dakin Noor ta tarar tana ciwon mara kamar yanda Mimi ta gaya mata, da taga dai dole babu wanda zai bi su cikinsu ta tafi ta samu Khalil tace “Kar kayi booking flight din ka bari gobe idan Allah ya kai mu, Mimi said she is having presentation today, Noor kuma bata da lafiya” Khalil yace “I have done that since yesterday, flight din karfe sha daya ne, na siya ticket ma” Mami tace “Ticket guda nawa?” Yace “Yanda kika ce a siya” Mami tace “Toh Mimi isn’t going kuma” Yace “Yeahh dama economy class ne, so we will be more comfortable a 3 seat din” Babu yanda Mami ta iya haka ta juya ta fita daga dakin, Nihad was so happy bayan da Mami tace mata ta shirya kayanta kala biyar da duk abinda zata bukata, Karfe goma da rabi Mami ta rakasu har airport din, Ta sauka bayan motar, Nihad ma ta sauka, Mami tace “Toh Allah ya tsare, ya kai ku lafiya…” Nihad tace “Ameen” Mami ta kalli Khalil dake rike da trolly din Nihad tace “Yaushe zaka dawo Malam? Yau ko?” Murmushi yayi yace “Idan na samu flight da zai taho Abuja zan dawo yau din, idan kuma ban samu ba sai gobe” Mami tace “Ohk then” Takardan hannunta ta mika masa, ya amsa yana kallonta don bai san na menene ba, Mami ta kara yi ma Nihad sallama sannan ta koma cikin mota, bai bude takardan ba yana rike da trolly din suka shiga cikin airport din, sai bayan da ya amsar masu ticket suka yi following duk process da ya kamata suna zaune a Departure Lounge sannan ya bude takardan da Mami ta basa, Measures din da likitan US yayi suggesting ne Mami duk ta rubuta a takardan kanta tsaye, bai san sanda yayi dariya ba ya rike kai, Nihad dai sai kallonsa take don bata san me ke basa dariya ba, ya daga kai yana kallonta with smile on his face sai ya mika mata takardan, ta amsa tana duba content din ciki, duk ta karanta comfortably amma tana kai wa na karshe ta ɗan kallesa da gefen ido taga kallonta yake, mayar masa da takardan tayi ta dauke kai, yayi dariya ya linke takardan ya saka a pocket, a haka har suka yi boarding jirgin sannan yayi takeoff zuwa garin Kano, garinsu Aunty Maryam din danladi nasidi….. Karfe daya saura Nihad suka iso kofar gidansu, bata wani jira Khalil ya gama gaya mata cewar sai da yamma zai dawo gidan ba cause she is too eager kawai ta gyada masa kai ta shige cikin gidan, Bayan sun gaisa da Aminu da ya mike da sauri yana jiran ganin Khalil, ita dai ta nufi entrance din shiga gidan, tayi mamakin ganin motar Abbanta a gida on a Tuesday, ta dai karasa cikin parlor, wanda ta tadda babu kowa ciki, ta tafi side din Mumy, nan ma bata ga Mumy ba ta shiga har bedroom dinta, kannenta dai tasan suna makaranta, Khalil bai bari ta shiga da trolly dinta ba yace zai kawo mata anjima idan ya dawo, ta cire doguwar rigar jikinta don zafi taji take ji, duk da suna samun wuta sosai a anguwansu amma akan dauke wani lokacin, ita kuwa ta saba electricity 24/7 a gidan Janar, tana kwance kan gadon Mumy bayan ta bude curtains din sai ga Mumy ta shigo dakin, tsaye tayi tana kallonta da mamaki, Nihad ta mike zaune tana murmushi kafin tace komai Mumy tace “Lafiya??” A hankali Nihad tace “Ina missing dinki ne shine Maminsa tace ya kawoni in gaisheki” Mumy ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta karasa cikin dakin, Nihad dai sai kallonta take ganin her eyes are swollen, and gaba daya a sanyaye take, Mumy ta zauna gefen gadon amma bata ce komai ba, Nihad taji gabanta na faduwa tace “Mumy are you okay?” Nan da nan hawaye ya fara sauka idon Mumy kamar jira take, Hankalin Nihad ya tashi sosai, ta dawo kusa da ita tace “Mumy me ya faru?? Ki gaya min meke faruwa?” Mumy na girgiza kai tace “Nothing dear, a kawo maki abinci?” Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ba tace “Mumy don Allah ki gaya min, is everything alright” Mumy na share idonta tace “Tafi ki duba Abbanki kiyi masa ya jiki sai ki dawo, he is sick” Sosai gaban Nihad ya fadi wanda har sai da taji wani jiri, tace “Mumy what’s wrong with him?” Mumy tace “He is getting better now, ki je ki dubasa a dakinsa” Nihad ta mike jiki ba kwari ta dau rigarta ta saka ta nufi kofa ta fita daga bangaren Mumy ta tafi na Abba, ba kowa a parlon nasa ta karasa kofar bedroom dinsa har sannan gabanta bai daina faduwa ba, tayi sallama bakin kofar aka amsa mata ta shiga ciki, Farooq ne zaune gefen Abban nasa, sai Hamid dake daya side din da Alhaji Abubakar sai wani kawun Abba, tun da ta shigo duk suke kallonta a dakin, ita dai idonta na kan Abba dake kwance saman gado, ta durkusa gaban gadon gabanta na bugawa, can kuma ta tashi ta koma can kusa da shi muryarta na rawa tace “Abba what’s wrong with u?” Ya gyada mata kai kawai, muryarsa ko fitowa baya yi sosai yace “I will be fine Nihad, how are you?” Bata san sanda ta fashe da kuka ta hade kanta da gadon ba, Alhaji Abubakar yace “Taso ki dawo nan Mamata” Ta tashi ta koma inda yake tana kallonsa hawaye na sauka idonta, cikin kwantar da murya yace “Yaushe kika zo?” Muryarta na rawa tace “Yanzu” Yace “Ina me gidan naki?” Tace “Yace zai shigo anjima” Yace “Toh maa sha Allah, he is recovering in sha Allah, ki je ki huta” Ta kalli Abba da ya rufe idonsa, a hankali Farooq dake kallonta yace “Ki je ki huta” Ta tashi kawai ta nufi kofa ta fita daga dakin ta koma bangaren Mumy tana kuka sosai, Mumy bata hanata kukan ba, tayi me isarta sannan ta kalli Mumy da kyar tace “Mumy me ya samu Abbana?” A hankali Mumy tace “Yana samun sauki in sha Allah” Nihad tace “Toh amma menene ya samesa?” Mumy tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can tace “He had stroke, but he is recovering now” Nihad ta zaro ido a tsorace tace “Stroke?” Mumy tace “Baki ga ya fara magana ba, ai baya magana sai few hours ago ya fara, kuma da sauki sosai jikin yanzu, in 2 days time za a fita India da shi” Kuka kawai Nihad take ta ma rasa me zata ce ma Mumy, Mumy ta goge nata hawayen tace “Ai ba kuka za kiyi ba, addu’a za kiyi masa, he will be fine in sha Allah” Tuni Nihad taji ta fara jin jiri ga sara mata da kanta ke yi amma duk da haka bata fasa kukan da take ba, Mumy tace “Ke meye haka? Idan baza kiyi masa addu’a ba meye amfanin kukan?” Mikewa Mumy tayi ta fita daga dakin, Nihad ta dafa gado ta koma ta kwanta da kyar don ji tayi kamar zazzabi zai rufeta, Mumy na fita kitchen ta tafi ta zubo abinci kadan a plate, miyan ma ba da yawa ta sa ba, ta hada just milo a cup sannan ta dawo bangarenta, tana shiga dakinta taga Nihad ta lullube har kanta da bargo kuma bata fasa shesshekan kukan da take ba, Mumy ta tafi gaban madubinta ta dau makullin da ta ajiye bayan wani kwalban turare sannan ta fita ta bude dakin Nihal dake bangarenta ta shiga da tray din shinkafar da cup din milo, sannan ta kulle kofar, tana zaune at the very far end of the room kamar ko da yaushe, Mumy ta ajiye tray din hannunta ta zauna gefen gadon tace “Ta so ki ci abinci Nihal” Nihal ta daga idonta da yayi ja kamar garwashi tana kallon Mumy, Mumy tace “In kuma baza ki ci shinkafar ba ki shanye ruwan milo din yanzu ki bani cup” Mikewa Nihal tayi tana tafiya a hankali kamar iska zai hurata ta fadi, ta taho ta durkusa gaban tray din abincin ta dau cup din milon, Mumy tace “Ba lokaci daya zaki shanye ba, ki dinga bin sa bit by bit” Kamar yanda Mumy tace mata haka ta dinga shan shayin wanda take jinsa kamar magani a baki, she don’t want to say no to Mumy ne shi yasa har ta daure take sha, amma ko sip uku bata yi ba taji ya dawo mata, da sauri ta shige bandaki, Mumy ta mike ta bi bayanta, bayan tayi aman ta fito Mumy ta sa ta kara shan kadan sannan ta hada mata ruwan wanka a bandaki tayi wanka, sai da Mumy ta ɓata almost 35 minutes a dakin, bayan taga Nihal ta kwanta sannan ta dau tray din ta fita ta sa ma kofar makulli ta tafi kitchen, Mumy ta zuba ma Nihad abinci ta kai mata daki, kwance ta sameta har sannan kanta a rufe da duvet, Mumy ta cire tana kallonta, Nihad ta bude ido da kyar Mumy tace “Sauko ki ci abinci” Nihad ta girgiza mata kai tace “Na koshi” Mumy tace “Ban son iskanci ga abinci na kawo maki kice min kin koshi, ki sauko ki ci abinci Hajiya” Nihad ta mike zaune da kyar ta sauko da kafafuwanta daga saman gadon, kallo daya tayi ma shinkafa da miyan dake dauke manyan nama, ta toshe hancinta da sauri, lokaci daya taji amai ya taho mata, Mumy dai sai kallonta take da mamaki ganin reaction dinta, Nihad ta sauka daga kan gadon da sauri ta tafi bandaki ta fara kwarara amai, Mumy ta bi bayanta ta kamata tace “Are you okay?” Sai da ta amayar da ɗan shayin da Mami ta lallabata ta sha a Abuja kafin ta samu nutsuwa, lokaci daya tayi laushi, Mumy ta taimaka mata ta wanke bakinta ta fito da ita daga bandakin, Nihad ta kwanta gefen gado tana jin zazzabi sosai, Mumy ta sauke idonta daga kallonta ta ja duvet ta rufe mata jiki tace “Sannu”

Related Articles

 

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

 

Ur evidence via 07087865788

Leave a Reply

Back to top button