Billyn Abdul NovelsFurar Danko Complete Hausa NovelZafafa Biyar Novels

Furar Danko 74

Sponsored Links

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣4️⃣

………Haka abubuwa suka cigaba da tafiya a gidan Smart da ɓangaren kwallonsa. Dan matuƙa ya dage da training da kuma kiyaye cin abubuwa tare da miƙama UBANGIJI al’amuransa, harda azumin kwana uku yayi da sadaka. Maganar shaƙuwa ko hirar arziƙi kam tsakaninsa da Lulu babu. Babu mai shiga sabgar wani ta ɓangaren lalama, garama shi wani lokacin yakan ɗan tsokaleta ita kuma tai masifa. Idan lokacin salla yayi kuma ko baya gidan zai tura mata text message akan tayi dan ALLAH, tai ma mahaifiyarta kuma addu’a. Sosai yake karya lagonta da hakan shiyyasa a yanzu kam Alhamdullah da wahala kaga lokacin sallar ma ya shige bata tashi tayi ba, daya turo saƙon ko batai niyya ba zata tashi taje tayi. Idan kuma yana gidan zai mata magana nan ma tayi. Girki ma dai kullum da rigima ake yinsa na safe dana rana idan har yana gidan, idan kuma ya fita na safen kawai akeyi ita dama ba damuwa tai da abincin ba, da dare kuma shi dama ba damuwa yay da cin abinci ba balle yanzu da yake sake ƙoƙarin daidaita jikinsa. Kayan shaye-shaye dai duk da ya toshe ko’ina da samunsu hakan baisa zuciyarsa ta samu nutsuwa ba, a duk motsinta kaffa-kaffa yake yi, ita kuma duk da ta daure kwana biyu a cikar kwana na biyar sai da yanayinta ya canja saboda matuƙa take buƙatar su, ta rage kulashi suyi faɗa, ta zama shiru-shiru, wani lokacin ma yakan shigo gidan ko ɗakinta ya ganta zaune a lungu ta takure kanta cikin damuwa koma tana kuka, sosai take bashi tausayi, dan haka a duk sanda ya ga

Leave a Reply

Back to top button