Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 40

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣

…….Ƙaramar dariya yayi da ɗage gira sama ya ce, “Nima naga alama ƴar ƙanwata babu abinda ta sani sai cin abinci da barci”. Ya ƙare maganar da lakace mata hanci.
Hannunsa ta buge da sake yunƙurin tashi tana faɗin, “ALLAH dai ya shiryaka kai kam”.
Sakin nata yay yana dariya da tashi zaune shima cike da shaƙiyanci.
“Miye na dariyar to”.
“A’a babu komai ƴar ƙararrama, ai ko cikin AA ma a ruwan madara kika sha ni shaida ne.”
“Kaji da shi dai. Fitinanne”.
“Kema zaki zama fitinanniyar”.
“ALLAH ya tasreni wlhy”.
“Sai dai na gaba wannan dai ya faru tunda ga AA a duniya”.
Da sauri ta miƙe cikin ɗage kai tana faɗin, “Oh kama tunamin, yaron nan zai iya tashi ya ce zai sakko wlhy”.
Miƙewar yay shima da cewa, “Yi zamanki ina zuwa, bari na duba shi.” bata Musa masa ba ta koma ta zauna. Sai dai har ya gama haye ɗan steps ɗin hanyar bedroom ɗin nasa tana binsa da kallo, sai da ya shige ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu tana sakin wani ɗan murmushi mai sanyi. Babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da AA kuwa a hannu, sai zillewa yaron yake da ɓata fuska irin na ƙiwa, shi adole bai sanshi ba. Yana ganin Lulu ya wani zabura wajenta yana ɓare baki. Dole ta amshesa dan ya cika mata kunne, yana ganinsa a hannuta sai yay shiru yana kallon Smart da sauke ajiyar zuciya. Zaune Smart ya kai kusa da Lulu cikin damuwa da ɗan murmushi, ya zubama yaron idanu da faɗin, “Kayi fushi da Papa ko Sweet heart? Kayi haƙuri Papa yayi laifi da baizo ya ganka ba tsahon lokaci. Please ka daina min ƙiwa kaji my sweet friend ɗina”. Ya ƙare maganar yana ɗan lakacema yaron hanci. Da sauri AA ya sake lafewa jikin Mamansa ya zata ɗaukar yasa zai sake yi.
Murmushi ya sake saki da girgiza kansa kaɗan. Sai kuma ya dubi Lulu dake saurarensu da kallo kawai. “Yana cin abinci ne?”.
Cikin ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki tana kallon yaron ta ce, “Da ga Kunu sai tea kawai yake sha, sai biscuits haka da ɗan sweets suma wani lokacin ko an bashi bai sha”.
“In dai ya biyo Babansa kam bazai sha ba, dan bana shan zaƙi nikam. Bari na haɗa masa tea ɗin maybe yunwa ce ta tashesa”. Kai kawai ta iya gyaɗa masa. Har ga ALLAH wannan halayyar tashi na saka mata ganin girmansa da kimarsa. A haka idan ka dubesa sai ka ɗaukesa a wani mutum mai jin kai da girman kai, amma sai ka zauna da shi kaga baida damuwa akwai sauƙin kai. Babu jimawa ya dawo da cup ɗin tea, zama yay a gabansu yana fuskantarsu, ya ɗan ɗebi tea ɗin a spoon ya kai bakin AA. A mamakinsu sai sukaga yaron ya ɗan kallesa kamar zai yi kuka sai kuma ya amsa. Dariya suka sanya su duka. Smart ɗin ya ɗan dungure masa kai da faɗin, “Ana son kayana amma ana guduna”. Ita dai Lulu dariya take musu. Tun yana amsa daga cinyarta harya zamo ya rarrafo jikinsa.
“Oh ashe ƙiwar bamai nisa bace Sweetheart”. Smart ɗin ya faɗa yana ɗaukarsa zuwa jikinsa. A haka ya cigaba da bashi tea ɗin suna hira da Lulu duk dai akan yaron ne da yanda yake samun soyayyar ƴan uwanta da nashi. Sosai Smart kejin ɗari a ransa, dan kuwa maganar nan ce dai ta malam bahaushe da kan ce mai ɗa wawa shima ke ɗawainiya da shi….

*_NIGERIA_*

A karo na farko tun bayan sakinsa da dawowarsa ƙasar yau sukai zaman meeting na farko da abokan cin mushen nasa. Wato Alh. Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau. Sai yaronsa Malami da aka dakatar daga waje kafin lokacin tasa shigowar yayi, dan akwai abinda ya ke son su fara tattaunawa da ba dole bane sai malamin yaji duk da kuwa a cikin sirrikansa babu abinda bai sani ba. Wani abu ma daya sani su su Alh. Baitan basu sani ba. Sun ƙara jajanta masa abinda ya faru cikin nuna ɓacin rai da tattara laifin gaba ɗaya akan Daddy da ɗan ka-ce-na-ce akan yanda akai suka san inda Lulu take. Shi dai shiru yay kawai yana saurarensu har suka gama bai ce uffan ba. Sai ma ya ɗakko musu batun kayan da yayo order da lokacin da yake ganin zasu iya shigowa Nigeria. Sun ɗan tattauna sosai akan hakan sannan suka dai sake komawa batun Daddy. Duk wani tsare-tsare a kansa sun yisa ne a wannan ranar harda ita Lulu da Smart suna a cikin plans nasu. Hatta da Abba wannan karon shima ya shigo lissafinsu…..

*_UK_*

…..Tunda suka dawo bedroom ɗin domin kwanciya sai tsoro ya shigi Lulu saboda ganin take-taken Smart ɗin a kanta. Sai dai tana ta ƙoƙarin basarwar cike da ƙarfin jali. Alwala tayo zatayi shafa’i da wutri yace ta jirashi. Jitai kamar zatai kuka, ta ɗan kai dubanta kan AA da ya haɗa da tarkacen kwalaben turarensa. Babu jimawa ya fito shima da alamar alwalar yayo. Kayan jikinsa ya canja zuwa jallabiya, cikin umarni ya jasu jam’in salla raka bibbiyu har sau uku, da ga ƙarshe suka rufe da shafa’i da wutrin. Juyowa yay gareta ya ɗaura hannunsa na dama saman kanta ya karanto addu’a. Zuwa yanzu tana da ɗan iliminta na addini gwargwadon iko, dan haka ta fahimci sallar da sukayi, duk da kuwa ita bawai ankawota bane matsayin amarya, sai dai a wancan lokacin ma ai sunyi irin sallar a randa komai ya shiga tsakaninsu. Sai ko ga shi shi da kansa yana faɗa mata cikin tsokana da murmushi ya ke cewa, “Kin san ke yau a amarya kike, dole ai miki tarba irinta amarya”.
Bata iya cewa da shi komai ba, sai dai tuni taji zuciyarta ta fara gudu a cikin ƙirjinta tuno da wahalar da tasha a waccan ranar da sakamakon abinda ya biyo baya na samuwar cikin AA. Sai ma taji ta gagara tashi a wajen. Ganin ya tashi shi ya koma saman gado waje ɗansa hankalinsa a kwance jiki a sanyaye ta jawo handbag ɗinta ta fiddo Alkur’ani itama ta fara karatu. Ta wutsiyar ido Smart ke kallonta yana jin wani irin farin ciki mara misali har tsigar jikinsa na tashi, sai dai baice komai ba dan a ganinsa lokacin cewar baiyi ba. Ya cigaba da yima AA wasa har yaron ya sake ɓingirewa barci. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da kwashe kayan ya gyara masa kwanciya, dan tunda suka shigo Mamansa tai masa wanka da canja masa kayan barci, sai ƙamshi yake mai daɗi. Kwanciyar yay shirin yi shima abinsa bayan ya shiga bayi ya gama uzirinsa ya fito ya canja kayansa zuwa na barci da feshe jikinsa da turarruka ya haye gadon harda yin addu’ar barci. Hakan ya saka Lulu ɗan jin nutsuwa, ganin har ya ja bargo ya rufama kansa ta saki ajiyar zuciya. Mintuna kusan goma sha huɗu baya ta rufe Alkur’anin ta miƙe itama. A tunaninta Smart yayi barci. Toilet ta shiga ta ƙara gyara jikinta kamar yanda aka koyar da ita salo-salo a wannan fanin duk da ita batayi da manufa ba, dan bata ma fatan a kai ga hakan saboda tsoro yake ji sosai. Ta jima tana kallon kanta a mirror kafin tai ƙundunbalar fitowa. Ta ƙasan ido Smart da yay likimo yake kallonta, gaba ɗaya tsigar jikinsa ta shiga tashi dan rigar barcin da ke jikinta ba wata ta kirki bace, sai dai a gareta ita bawai tasa da wata manufa bane dan dama can tana sakawar a ita kaɗanta. Gadon ta nufa zuciyarta dai na kai-kawo, dan haka data ɗan kai zaune a bakin gadon ta tsurama Smart ɗin ido. Ganin bai ko motsa ba ta sake yarda yayi barci, sai kuma ta dubi a inda ya kwantar da AA, da ga gefensa sai dai ya kakkaresa da filos ta yanda ko juyi yay bazai faɗi ba, shi kuma ya kasance kamar a tsakkiyar gadon ya bar mata ɗayan gefen nashi. Sai da ta ɗan hararesa duk bata san yana kallonta ba sannan ta tura baki tana kaiwa kwance a hankali, tasan idan tace zata ɗakko AA ta maido tsakkiyasu Smart ɗin zai iya farkawa, koma yaron ya farka shi ya sanya mata daru duk da dai yanzu ya bar kukan dare, dan haka ta haƙura akan zuwa da safe dole a nema mafita, tunda dai taga ba ɗaki ɗaya bane a gidan ita zata koma wani ɗakin ta bar masa ɗakinsa, tun ma ɗazun da ace tasan nashi ne bazata yarda ta sauka anan ɗin ba. A hankali ta ɗan ɗaga bargon kaɗan ta yafama jikinta tana wani rumtse ido da cije lips, harda waigawa ta dubi Smart sai taga yana a yanda yake dai ko. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sake saki da lumshe ido ita a dole tasha da ƙyar.
Dariya Smart ke dannewa da ƙyar, sai da ya tabbatar ta gama dabarun nata sannan ya mirgino jikinta a hankali ya rungume ta tsam. A firgice ta juyo jikinta har yana rawa. Sai ya sakar mata murmushi da kashe mata ido ɗaya.
Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Dama idonka biyu?”.
“A’a yanzu na farka” ya bata amsa cikin gimtse dariya.
Kallonsa take cikin rashin yarda da cewar yanzu ya farka wai. Zatayi magana ya ɗora yatsansa saman lips ɗinta da faɗin, “Shiiii!!!”.
Dole ta haɗiye maganar idanunta na kawo ruwan ƙwalla. Juyota yayi da ƙyau suna fuskantar juna, murya ƙasa-ƙasa yake magana yana busa mata iska a fuska. “Amarya mai tsoro da fa ƙyar take sha a hannun ango. Karki zama raguwa mana Nooru Nisa”.
Fuska ta ɗan ƙwaɓe kamar zata sakar masa kuka. Sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Aliyu kaga dai ALLAH ni har yanzu wajen da akai min aikin nan bawai ya gama warkewa bane, sannan ma banda wani isashen lafiyar jik…..”
“Irin wannan sharhi haka Madam. Ni nace zanyi wani abu ne?”. Ya faɗa cikin katseta da kai yatsarsa saman lips ɗinta yana zagayawa. Sai kuma duk taji kunya ta lulluɓeta, irin wannan kama kai har ina. Shima murmushi yayi dan ya fahimci ya rufe bakin maganar, abin faɗar sun maƙale. Idanunta ta maida ta rufe a hankali tana haɗiyar zuciya, daga haka ta fara ƙirƙiroma kanta barcin dole. Jin numfashinsu ya sake kusanta da juna ya sata buɗe ido da sauri, sai dai kafin tayi wani yunƙuri lassafin ya canja, dan Smart ya rantse yau fa a angonsa yake, ya barta ne kawai ta gama kame-kamen nata……….✍️

Hummm🚴🚴🚴🚴

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button