Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 89

Sponsored Links

89
Koda su DD suka Isa office din Sir Ashir Shima Kansa ya dauki zafi sbd dd babba Dayake office din suna duba footage na Wanda ya fitar da abincin ranar da abin ya samu DD babu Wanda suka Gani bayan Safnah matarsa,
Basu sake shiga rudu ba Saida same lokaci bayan ta zuba abincin a refuge same me napep dasuka ga Yana bibiyarta bayan tafiyarta Saida ya fito ya Isa sharar ya saka hannunsa ya dauki ledan kayan abincin ya koma napep da ita Yana duba menene yake ciki yabar gurin.

Basu nunawa D Abinda suka Gani dinba bare sanar masa sbd sai sun gama Tara komai tukuna,
Saidai ledan Daya ajiyewa Sir Ashir gabansa tareda report na Asibitin hande ya saka Sir Ashir kallan dd babba Shima kallan DD yayi take aka dauki ledan Dan gudanar da binciken gaggawa akanta.

Report din kan table dake gurin idanuwan DD ya sauka yaga sunan Safnah a sama kafin yayi Wani motsi dd babba ya janye tareda miqewa yace su tafi kafin report din ya fito.

Suna baro office din Sir Ashir Kai tsaye kaantes suka nufa sbd babu Wanda ya zauna ya huta tinda suka dawo suke yawo.

Suna Isa Amnah da gudu tazo ta fada jikin dadynta ya dagata sama Yana sake Jin tsananin so da kaunarta cikin zuciyarsa sbd sai yanzu ne ya tabbatarda yarinyar marainiyace gaba da baya Ashe bayan rashin Uba harda mahaifiyarta ta rasa,Amma ko yayane dai yasan bazata taba maraicin ba bare tasan ma ba sune suka haifetaba.

Gurin Umme suka nufa suka gaisa itama Umme cikeda farin ciki da tsananin son danta ta rungumesa tana hawaye sbd masifun Nan sun fara musu yawa daga anfita wannan Se wannan.

Kofan dakin Bena ya sauke idanuwansa zuciyansa na Wani irin yankawa Dan haka ya miqe yabar sashen ya nufi nasa.

Baiyi mamakin rashin tadda Safnah ba Dan haka Bai Wani damu ba ya wuce bedroom dinsa wanka yafara Yi ya samu Dan qarfin jiki ya fito ya shirya cikin black Balmain Riga da wando yayi sallah
Yana idarwa Nafisat da Amnah suka kawo masa light abinci da Umme ta dafa masa da kanta.

Bazai iya cin komai ba dan babu Abinda yake masa daidai a jiki da Zuciya harma da bakin.

Amnah a gurinsa ta kwana bayan tayita tambayan Ina mummy dinta shi baisan me zai fada mata ba sbd Shima kaman zaiyi hawayen ne kaman yanda itama takeyi,riqe Kansa kawai yakeyi sbd kada taga hawayensa ta daga hankalinta kokuma tasan Wani Abu ya samu mummy din nata.

Har gari ya waye Bai iya rintsawa ba Dan haka zazzabi zazzabi ke Neman shigarsa sbd Bai Saba da qunci da damuwa ba bare wahalan tinani.

Daga shi har Amnah kusan zazzabin suka kwana dashi suka tashi dashi Dan Daman ita matiqar mummy dinta Bata tareda ita kusan kullum zazzabin dare takeyi sbd ta Saba shigewa jikin mummynta tayi bacci cikin tsananin so da kulawan Mummyn.

Hakanan Kansa na ciwo yayi sallar Asuba suna idarwa kusan dukkaninsu a tare suka jima masallacin Saida gari yayi haske kafin suka fito ko ciki Basu qarasa ba Kiran Sir Ashir bello ya shigo wayar dd babban dake hannun Abbakar Kuma shine ya dauka yaji sakon Sir Ashir din Wanda Shima Bai rintsaba ko kadan shi da yaransa kwana sukai Aiki da bincike tareda zuwa gidan DD na highbridge suka duba fingerprints na Safnah dake gidan wanda yazo daidai da Wanda yaje jikin ledan da DD yakai musu hakama same fingerprints ne dake jikin motan da Bena tayi accident da ita kwanakin baya da ake bincike Akai itama a boye da dd babab ya saka.

Shiru Abbakar yayi bayan kashe wayar Sir Ashir bello din Yana Rasa ta yanda zai isar da bayanin da Neman da Sir Ashir din ke musu.

Dukkaninsu musamman DD da idanuwansa sukafi na iyayen nasa kaifin kwarjini suka zuba masa suna jiran Abinda zai fada shikuwa so yeke iya dd babba zai isarwa sakon.

DD da ransa ya Baci ya hade fuska dakyau tareda kallan Abbakar cikin kamewa da Bata Rai yace

“Banajin akwai sauran Abinda ake boyewa Wanda bansaniba,idanma akwai zan sani ayau din,.ka fada me Sir Ashir bello din yace,Ina sauraronka.”

Shiru Abbakar yayi kafin ya Kalli dd babba Wanda Shima yanzu sakon kawai yake buqatan sani shikuwa dad kaante kallan mamaki duka yake musu sbd baisan binciken me duk suke jiran sakamakonsa har haka cikin daga hankali ba.

Numfashi Abbakar ya sake Yana San kasa kallan DD yace

“Sir Ashir Yana buqatan ganinka acan sbd kace baka buqatan zuwansa Nan koyaushe kawo report sbd kada a ankarar da yan jarida Amma yace Yana buqatan zuwanka sbd sakamakonsa komai ya fita na qwayoyin da aka shayar da DD da Wanda aka shayar da kakarsu Bena harma da sakamakon binciken accident din Bena…..

Wani irin Kallo DD yayiwa dd babba cikin matsanancin mamaki da zuciyarsa dake daukan Wani nauyi da harbawa ba daidaiba sbd Bai taba sanin accident din Bena bana Allah bane akwai zargin da akeyi akan Hakan shine aka boye masa akwai Wanda ke bibiyab matarsa da Wani sharri,
Meyasa zaa boye masa dan kuwa da tini zai fara Bata kariyar da ko Kansa bai sametaba.

Shi Kansa dad kaante mamakin ya shiga sosai Yafara rarraba idanuwa cikin firgicin meyake faruwa da familyn nasu wai.

Dd babba kuwa Kai tsaye Bai iya cewa kowa komaiba ya wuce gaba Abbakar na bayansa ya je ya dauko key din motarsa da sauri.

Shima DD Kai tsaye Naseer ya kira Wanda Shima ranar a cikin Kaantes ya kwana take ya fito cikin qananun guntayen kaya Shima ya tada motar DD din Suma suka rufawa dd babba baya
Dad kaante na kasa tsayawa yayi Dan andena barinsa Baya tinda Shima babba ne a familyn ya dauko key da Kansa Bai tsaya Kiran driver dinsa ba yaja ya mara musu baya.

dd babba ne yafara Isa yau Yana fatan komai yazo karshe sbd zarginsa da hankalinsa Daya kasa kwanciya akan matar DD Dan haka baya cewa komai har suka Isa

Suma DD a cikin motarsa babu me iya magana sai nauyi da tafasan da zuciyarsa keyi akan Abinda zasu tarar na duk Wanda yakeda saka hannu akan accident din Bena,
Bai damu da Wanda ya shayar dashi mugayen drugs dinba shi ayanzu wanda yake son hallaka matarsa yake son Gani.

Suna isowa Kai tsaye suka fito daga shi har Naseer tare suka nufi ciki daidai lokacin da Sir Ashir da idanuwansa sukai Wani luhu luhu sbd rashin bacci da aiki tuquri na azaba dasukai acikin daren.

Miqawa dd babba report din yayi Wanda Kai tsaye DD ne ya fara saka hannu ya karba Dan ganin suna Neman Bata lokaci gurin bayani da boye boye.

Yana budewa yafara bin rubutun ahankali da reports din Yana karantawa.

Shiru yayi tsawon seconds Yana kokarin Dora zancen cikin Kansa a daidai.

Kallan Sir Ashir bello yayi fuskarsa a matiqar hade da yanayin wulaqanta yace

“Waye Safnah din?

Daga Sir Ashir har dd babba da Naseer kallansa suka dago sukai cikeda sanyin jiki da mamaki,
Naseer ya kalla ganin alaman duk sun Santa da idanuwansa ya kafe Naseer Yana jiran amsa

Naseer ya Dan matso gefensa kadan cikin sanyin murya yace

“Second wife Dinka,’yar uncle Dinka Alh basheer bulama, Safnah basheer bulama”

Cikin Wani irin mummunan yanayi yace “kana nufin SSB??

Shiru Naseer yayi sbd bazai iya Basa wannan amsan kai tsayeba Dan kada suyi breaking zuciyarsa bayan tsananin baqin cikin da zai samu Kansa a ciki na Jin matarsa ce tayi wainnan ayyukan.

Kallansu yayi Daya bayan daya kafin ya tsaida kallansa kan dd babba Yana cewa

“Meye ne??
Kunyi shiru ne Kuna tausayin waye ne?
Kuna kunya ko baqin cikin ace matatace tayi wannan aikin??
Like seriously??
Kallan Naseer yayi Kai tsaye yayi wurgi da takardun Yana juyawa yace

“Kira manyan hukumar yan drugs dake Lagos wainda case din nawa yake hannunsu wainda zasu miqata hukumar Zurich dake Neman inda qwayoyin suka fito sune zasu San abinyi da ita Amma kafin Nan muje naji meye hadin wancan mutumin da ita dataje gidansa ta bawa mahaifiyarsa qwayoyin hakama meyasa mahaifiyar tasa babu Abinda take kira sai sunansu su Biyun dole akwai Wani abin da basu saniba hakama idan Safnah ce ta batar da Bena da saka hannunsa tinda yayi niyar guduwa.

Kansa Wani tiriri yakeyi Yana daukan zafin gaske sbd yanzu ne ya tabbatarda Bena na cikin hadarin gaske Jin abubuwan dake faruwa.

Suna ficewa dd babba ya Kalli Sir Ashir ya sauke numfashi cikin nutsuwa yace

“Yanzu da akeda shedu da tabbacin itace zayi wannan ayyukan zaku iya kamota a shigar da case din hannun manyan hukuman yan drugs a fara tambaya da bincikenta yanda ya kamata ta hanyar da kuka Saba ji da irinsu.

Angama” sir Ashir ya fada sbd Daman Jira suke sosai dasu samu ta shiga hannunsu Dan kuwa wainnan qwayoyin ba qaramin zancen bane a gurinsu Dan yanzu akan Hakan shi wata hanyar samun Qarin girmansa tazo musamman manyan hukuman yan drugs da zata shigo ciki basuda Imani ba sani ba sabo Dan kuwa da tin farko hannunsu zancen ya shiga da babu Abinda zaa tsaya yiwa boye boye da tini Safnah anrufe bayaninta na Wani ake.

Dd babba na barin office din Shima Sir Ashir ya Bada umarnin a buga takarda a aika Lagos ta email yau a bugo musu stamp a dawo da ita su fitar ta tabbacin zaman samun qwayoyin dasuka Fi Muni a tareda Safnah din.

DD da Kansa yake tuqin motar Wanda ya saka Naseer yin shiru kawai Yana jiran su Isa Shima.

Koda suka Isa highbridge dokarsu da baa taba takawaba yau duka Saida DD ya takasu Wani mahaukacin horn yake musu jiki na rawa aka Bude masa da matsiyacin gudu ya shige Kai tsaye ya nufi gidansa ko parking daidai baiyiba ya tsayar da motar ya fito.

Naseer ne ya fito Shima da sauri ya rufe motar ya biyo bayansa suka qarasa ciki.

Hanyar kitchen suka nufa Kai tsaye tareda nufar store din da sauri Naseer yayi gaba ya Ciro key din inda ya ajiyesa ya Bude kofar tareda turawa ta Bude gabaki Daya.

Ababa dake zaune gabaki Daya karfinsa ya qare kaf babu sauran kuzari a jikinsa ko kadan sbd azabar kwana zaune dayayi Yana kirgan kudin da lisassafinsa gabaki Daya ya kunce,

Idanuwansa gabaki Daya sunyi luhu luhu sun fito sunyi jajir zagayen idanuwansa su Yi baqi sosai sbd azabar rashin rashin rintsasu da yayi ko kadan be rintsasu ba kudine yaketa Daman kirgawa ya kasa hada ko miliyan Ashirin tin dare har safiyar,
Idanuwansa Basu taba haduwa da azaba irin ta yau din ba,
Fankokin sunqi mutuwa sai daga kudin sukeyi koya hada ya aje,
Yayi yayi ya kasa kashesu,
Ya kasa hakura sbd taurin zuciya da naci da kwadayi da Neman mafitan dayakeyi.
Babu iskan ventilation a dakin Wanda ya sake azabar dashi da numfashinsa sbd tsananin qamshin kudin Daya cika dakin babu inda window yake yasaka ko iskan fankar bayaji zufan jikinsa kusan ya qare Dan kuwa tin Daren yake tsiyayan zufa me yawa har safiya,
Ruwan jikinsu sun qare daqyar yake iya daga hannunsa Yana cigaba da taba kudin Amma lissafin tini ya kunce masa babu Abinda yake so kawai a budesa ya fita iskan Allah ya dakesa ko baa basa ko sisi ba abarsa ya tafi sbd qamshin kudin kashesa zaiyi ya masa yawa aciki ya zamar masa cuta.

Kallansa sukai a wulaqance suna kallan idanuwansa da basa Gani sosai sbd kumburi da Jan dasukai,

Shi Kansa dagowa yayi ya kallesu dishi dishi yake ganinsu ko magana baiya iya Yi sbd azaban nauyin da Kansa yayi da azabar ciwo.

DD ne ya matso gabansa ya tsaya sai dayayi shiru ya hadiye tafasa da zafin da zuciyarsa keyi ya Bude baki Kai tsaye ya jefa masa tambayar waye ya Akai yasan Safnah bulama hartaje gidansa ta durawa mahaifiyarsa qwayoyi.

A yanda yake cikin matsananciyar azaba da wahala Yana Jin tambayar ya dago ya sake Bude idanuwansa dasukai masa zanen na Panda ya Kalli DD dakyar ya Bude baki yace

“Safnah ce ta Kori Bena da Annensu,
Safnah ce ta biya kudin gaske me yawa suka bawa hande bana Nan hande ta Basu Anne da Annen sukai amfani suka Kori Bena ta tafi sun shiga duniya.”

Naseer ne ya shigo dakin tareda cakumo Ababan ya fito dashi daga dakin ya jehosa harabar gidan inda zai samu iska ya Dan dawo daidai yayi bayani da kyau.

Sake maimaita Abinda ya fada yayi DD ya Kalli Naseer yace sakashi booth muje inda zeyi magana.

Ababa na Jin Hakan ya zare idanuwansa na Panda Yana cewa

“Safnah ce da haj Nuratu sukai komai yanada duka shedu da komai da zai bayar”

Naseer be sauraresa ba ya shaqosa wannan Karan idonsa biyu ya Bude Booth ya Jefasa ciki Ababa na Neman siqewa suka rufe Booth din suka shiga motar.

Kai tsaye office din Sir Ashir Suka nufa suna Isa aka Bude both Wani marar Imani cikin yaran Sir Ashir bello din ya saka hannu Daya ya Ciro Ababan Wanda tini yafara Neman somewa a Booth din sbd azabar zafi da rashin numfashi.
##MAMUH#

Leave a Reply

Back to top button