Hausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 33

Sponsored Links

_TABARMAR KASHI_
Book 02 Page 33

Dr raheema na fita ta maida key jikin qofarta,ta koma ta kwanta saman gadonta tana sauke numfashi, idanunta a lumshe bacci ne fal cikinsu. kuma shi take da bugatar vi saboda a jiyan tashin ciwon fadeela bai bari ta samu isashen bacci ba yau din kuma ta tashi da wuri da zummae zasu fita aiki,wannan gaddarar ta fada mata.

Wasu hawave suka sake zarto mata idanunta a lumshe tana bitar abinda ya faru tsakaninta da shi,tun daga sanda ya sanyata cikin jikinsa har zuwa lokacin data wuce bandaki.

Kadan kadan taji ana taba gofar, sau biyu aka murda,sai kuma taji an juya an bar gurin ba tare da anyi knocking ba.

Wayarta dake saman kanta ta jawo tavi kiran nadeeya

“Fadeela ta tashi ne?”

“Eh ta tashi, abbynta ya shigo yanzu suna tare, ashema bakuje office din ba” kai ta gyada

“Eh”

“Amma lafiya?, anty N naji muryarki wani iri?”

“Ba komai kawai inajin kasala ne,please ki kula da fadeela, kada ki bari ta fita gaba daya daga sashen,sannan kada kowa ya bata komai sai abinda kika girka da hannunki, shima kaemi motsa daga kitchen din har sai kin gama,idan ta rage kuma a zubar, kada a ajjiye” Nadeeya ta danyi mamaki, amma kuma tasan sahar din kulawarta ga fadeela ta musamman ce, don haka ta amsa mata da

“To,in sha Allah, sannu Allah ya bada lafiya,ki huta sosai don nasan akwai rashin samun cikakken bacci ma jiva,gwara ma da yaa toufeeq ya hana zuwa aikin yau,kya samu ki huta”

“To nadeeya‚na gode,ki cewa fadde na i missed her ” murmushi nadeeya ta saki, sai itama fadeelan dake kan cinyar toufeeq ta saki murmushin, don duk a kunnensu tayi maganar.

Maganganunta suka sake sakashi zurfin tunani vana da bugatar zauna ya tattauna da ita, amma ya sani a yanzun kamar ya bar mata wani ciwo ne a zuciyarta,ya tabbatar a quilace take dashi, ba lallai bane ta tsaya ta saurareshi. Special care da take bawa fadeelan wani abu ne da bau taba ganin kwatankwacinsa ba,bata da lafiya amma dukka hankalinta da tunaninta yana kanta.

Maida idanunta tayi ta rufe itama ba tare data motsa din ba, tana jin yadda qasusuwanta suke ciwo,cinyoyinta kamar wadda tayi wasan tsere na kwana guda,ko yaya ta motsasu sai tail wannan ciwon,hakanan ta cikin qashinta takeiin zazzabi yana mamaye ilahirin jikin nata,sannu sannu wani gantalallen bacci ya dauketa.

Cikin baccinta ta dinga jin kamar muryar fadeela na gwala mata kira. A hankali ta bude idanunta ta miqe ta zauna saman gadon tana sake jin sautin muryarta daga bakin gofa tana hadawa da knocking. A hankali cikin lallaba jikinta da ya qara tsami ta sauko a gadon, ta isa bakin gofar ta bude.

Fadeela dince, toufeeq yana tsaye daga bayanta,guri daya idanunsu suka hadu,ita ra fara janye nata idon ta taka a hankali cikin takatsantsan tana komawa cikin dakin gami da laluben dankwalinta da ya zame, sassalkan gashinta me santsi wanda ko ribbon bata samu damar saka masa ba tunda tavi wanka ta barshi a haka don ko Draver bata samu ta saka ta busar da shi ba ya tarwatse iskar dake dan kadawa cikin dakin na mata wasa dashi daga hannun hagunta zuwa dama. Idanunsa a kanta har ta zura garamin hijabi wa jikinta yayi qarfin halin dauke idanun nasa ya biyo bayan fadeela.

“Anty N,tun dazun nake nemanki sister nadeeya ta hanani shigowa,wai baki da lafiya?” Ta fadi cikin kulawa.

Dan qaramin murmushin da bata shiryawa saki ba shi ta saka, ta saka hannu ta shafi gefen fuskar yarinyar,she was so caring

“am getting better fadee na,so karki damu” Idanunsa a kansu har ya qaraso ya zauna saman sofa bed ta yadda zai iya fuskantarsu. Ledar hannunsa ya ajiye ya fidda magungunan ciki sannan ya dubi fadeela

“Jeki kawomin cup be careful”

“No ta barshi” sahar ta fadi zata miqe, hannu yasa ya maidata, suka hada ido ta kauda kai,sai ya miqe

“‘Karki rufe qofar before na dawo please” ya fadi da sigar lallashi. Bata ce masa komai ba sai sake kau da kanta tayi,ya gaji da saurarenta ya juya yana fita a dakin.

Lokacin da ya dawo fadeela na zaune d’are d’are saman cinyarta tana mata surutu, idanu yadan fidda sannan yasa hannu a nutse ya sauketa daga kan cinyar tata

“Noo my angel,anty N bata da lafiya,kinyi mata nauyi da yawa”

“Ayyah,sorry anty” ta fada tana kallon säahar, kai ta girgiza mata tana shafa kan yarinyar,a yanzu duk wani tunani nata ya tattara kan yadda zata samawa yarinyar lafiya,yanzun shine abinda kadai ya rage mata tayi, tana jin daga wannan ta kammala zamanta cikin gidan.

Tablet din farko va miga mata yana kafeta da idanunsan nan da suke gara mata wani nauyi,sai kuma haushinsa da takeji can qasan zuciyarta

“Take it please” ya fada qasa gasa yana sake watsa masa idanun nasa, hannu tasa ta dauka a tsakiyar tattausan tafin hannunsa sannan ta karbi ruwan da ya zuba a cup. Daya bayan daya ya dinga bata tana sha har ta gama,ta ajjiye cup din sanda fadeela take kallonta

“Ya akayi fadee?”

“Am starving” ta fada qasa qasa daidai sanda yake kwashe magungunan ya dora sanan dressing table, dawowa yayi gabanta ya kama hannuwanta ya rige cikin lallashi

“Fadeela” yayi kiranta

“Yau ba girki, oya ki yiwa zuwaira ko nadeeya magana,su baki wani abun kici,she’s sick kin gani ai ko?” Kai ta jinjina, sai ya fiddo wayarsa yayi kiran nadeeya.

Mintuna kadan ta shigo, suna hada ido da sãahar din taji wani nauyi ya saukar mata,gani takeyi kamar ma kowa zai gane abinda ya faru, kamar an rubuta abunne a gaban goshinta haka takeji a jikinta

“Sannu anty N” kai kawai ta gyada mata tana lumshe ido nadeeyan bata zafafa ta garaso kusa dashi.

Bata ji abinda yace da ita ba,yau an magana dasa
gasanne suka motsa, ita dai taji ta kama fadeela sun fita a dakin. Ta cikin rufaffun idanunta taga hasken dakin ya ragu,a hankali taji an maida qofar an rufe, ta tsammaci tare suka fita saita gyara kwanciyarta cikin duvet. Saidai ko minti daya ba’a rufa ba sassanyan qamshinsa ya mamayeta,kafin ta gara tuna komai ta jishi a cikin duvet din. Wani wawan juyi tayi da nufin tashi, tashin bai samu ba,sai ma kyakkyawan masauki da yayi mata cikin jikinsa, lallausar fatarsa me wani irin gamshi da dumi ta manne a nata jikin,hucin numfashinsa da ya sauka daga wuyanta
zuwa gefen kunnenta ya sanya ta jin wani irin abu na
mata yawo cikin jikinta

“Karki wahalar da kanki, don ba zaki iya qwacewa
ba, dukkanmu bacci mukeji ni da ke, so mu rage baccin koda na one hour ne you will feel better idan muka tashi, and baccinki it will be more comfortable idan tare mukayi,karki wani yunqurin yin komai, just relax please”ya garasa fadin please din yana cooling voice dinsa sosai cikin yanayi na salon shagwaba. Ido kawai ta rufe tana jin yadda bugun zuciyoyinsu ke sauri ita
dashi,hawaye ya cika idanunta tana jin zafi cikin ranta. Ya yaudareta,ya karya alqawarin dake tsakaninsu,yayi
abinda ransa yakeso, dama jikinta ne yake bashi
sha’awa?,hakan kuma bai isheshi ba yanzu ya dawo ya tilasta mata yin bacci dashi. Ta tabbatar yadda ya fada ne, no way da zata iya qwatar kanta, amma kuma bakinta tana ganin zai iya qwatarta

“Bamuyi aure da kai don mu dinga wannan abun ba, ka karya yarjejeniya kaci amana” garamin murmushi ya subuce masa,a yanzun son tsiwar nan tata yakeyi,ya fuskanci da tayi masa shuru gwara tayi masa tsiwar,yana enjoying sosai,sai yasa hannunsa ya birkitota,ya sanya tafin hannunsa ya tallafe kansa bayan ya dogare gwiwar hannunsa saman gadon, qwayar idanunsa ya narka cikin tata yana mata wani mayataccen kallo

“You are saying na karya alqawari, naci amana,i break the rules,dama munyi alqawari da ke? yaushe mukayi yarjejeniya?, uhmmm madam suna ina? ‚nunamin su” Baki ta saki tana kallonsa tsakanin idanunsa guda biyu,wata qwallar ta sake cika mata idanu. Sai yanzu ta tuna basuyi a rubuce ba,yace baya bugata ta rige kayanta to rami yayi mata a sannan?, ko dama ya shirya faruwar hakanne? yanzu bata da wata huija kenan koda bavan ta gama aikinta akan fadeela ta nemi takardar sakinta?.

“Kinzo kulawa da fadeela amma baki yarda ki kula da daddynta ba ko dan gangani?” Ya fada yana langabe mata kai, wanda shi kansa baisan lokacin da hakan take faruwa ba. Ta karanci abubuwa na neman saba saiti, gaba daya kamar ba da MT JARMA take magana bama, sai taji kanta bazai iya dauka ba

“I need space please ka sakeni ka fitarmin daga daki” wata wawiyar rungumar yayi mata yana saka kanshi tsakanin boobs dinta da har yanzu yakeji basu isheshi ba

“Ki huta hakanan please magani kika sha” yadda yaketa morewa albarkatun girjinta yana masifar gona mata rai,cikin rawar muryar dake nuna kowanne lokaci kuka zai iya qwace mata tace

“baka da bugatar bazawara in all ways,so me zakayi da ilkin da ba’a san darajarsa ba?” Bai gara barinta tace komai ba sai tsintar bakinta tayi cikin nasa ya hade bakunansu gam,ya hanata sake cewa komai, sai wani zazzafan mouth to mouth kiss da yake sauke mata wanda cikin mintuna yaso sake birkitashi, da qyar ya zare bakinsa yana jin dumin hawayenta suna taba fuskarsa

“Idan kinason zaman lafiya kiyi baccinki kawai” ya fada yana aza mata nauyin girjinsa idanunta kawai taja ta rufe gam, bata sake cewa komai ba, saidai tuni ta yanke hukuncin abinda zata aikata. Ba jimawa bacci yazo yayi gaba da ita, ya gyara mata kwanciya cikin jikinsa yakai lips dinsa yayi kissing goshinta,kamar zai cinyeta da idanunsa wani irin murmushi na fita akan fuskarsa

“Rigimammiya ta” ya fada softly yana jin zuciyarsa kamar wadda aka canzawa muhalli.

Afwan,yau na baku shi a rarrabe kuma page d’ai
d’ai,ayimin uzuri na wuni a asibiti ne. Amma gobe komai zai zama normal in sha Allah, Na gode da kasancewa tare dani.
[27/09, 8:42 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Leave a Reply

Back to top button