Sawun Keke Hausa Novel

Sawun Keke Complete Hausa Novel

Sponsored Links

 

 

[8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 1

           NA
Ayeesha Abdulkareem INDO

Marubuciyar….
DOGON YARO
TAJMAHAAL


IDO HUƊU
WATA HANYA
A JINI ƊAYA
AAMINAT (Bazawara)
da sauransu…

4/8/2023

*Mikiya Writer’s Association*

Bismillahirrahmanirrahim

Garin Kano
Misalin ƙarfe 03:00am….    Dare mahutar bawa,,  a duk lokacin da dare ya tsala sahu kan ɗauke  kowane ɗan Adam  ya killace kansa a makwancinsa domin samawa ruhinsa salama.

a wannan dare  yayin da Asbahi ke shirin ƙaratowa daidai lokacin hadari ya fara gangami, cikin lokaci ƙanƙani ya gama haɗowa    ya fara sakin iska me ƙarfi gami da walƙiya me tsananin haske  ya na wani irin rugugi kamar zai ci babu.
Ya ɗan ɗauki lokaci cikin wannan yanayin kafin ya saki ruwa me ƙarfin gaske.

Sai da aka kira Sallar Asbahi sannan ruwan ya tsagaita ya koma yaf-yaf a hankali a hankali,  ba shi ya tsaya cak ba sai da gari ya fara haske.

mamakon ruwan da aka sha ya haddasa  lullumi gami da wani irin sanyi me matuƙar  daɗi.

  kasancewar safiyar Lahadi ce ya sa titina  har ma da cikin unguwanni  babu yalwar jama’a kowa ya nabba’a a gida, tin daga kan ƴan makaranta har ƴan kasuwa,  tsirarun mutane ne kurum ke yawo  sai  ababen hawa na haya su ma   ba su gama fitowa ba, domin kuwa yadda ƙasa ta sha ruwa  ta jiƙu  ga sanyi na ratsa jikkuna ba kowa ne zai so fitowa a irin wannan lokacin ba.

HOTORO

Hajiya Laure ce zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun Falon, ta harɗe ƙafa   ta na danne-dannen waya  fuskarta ba alamar walwala,  ta haɗe cikin leshi ɗinkin Buba   ta doka ɗaurin ture ka ga tsiya, adon nata ya ƙara fito da asalin suffarta ta Hajiyoyi,    Jiran shigowar Alhaji Salisu kawai ta ke yi don ta sauke masa buhun masifar da ta kwana ta na ƙissimawa  akansa.

Yazeed ne ya shigo falon  ya na tafe  ya na jan ƙafa zagaraf-zagaraf  bai bi ta kanta ba ya saita hanyar bedroom ɗinsa,  cike da takaici ta ce “Ai ko ba za ka gaishe ni ba ya kamata ka faɗa min inda ka je.”     fasa wucewa bedroom ɗin nasa ya yi   ya dawo kusa da ita ya zauna idanunsa ƙasa-ƙasa ya ce   “Why are u doing this to me?? you’re my mother fa  kin fi kowa sanin  ba yaro bane ni Mummy, maganar gaskiya kin fiye kishi da ni”      tsaki ta doka kafin ta ce “Ubanka ne ya lalata ka ba wani ba, na san ba zai wuce daga biye-biyen ƴan mata ka ke ba,     inda zan yi kishi da kai kuma ai ba zan ma haifeka  ba yaro, kawai don ba ka son gaskiya ne.”
Taɓe baki ya ɗan yi cikin ko in kula ya ce “Ina Daddy?”    a masife Hajiya Laure ta ce “Ka ban ajiyarsa ne??  tin jiya ya yi min alƙawarin zai dawo ya same ni amma ya ƙi dawowa.”    “Wani gurin ya je??”    ”To ai in wani gurin ya je ma da ƙauna, ya na sashinsa,  wai wani baƙo zai yi za su tattauna  shine har da ce min kar in sake in zo sashinsa har sai ya dawo ya same ni,  to ka ga da bai iya cika alƙawari ba  ya ƙi dawowa,  sai ka tashi ka je  gurin nasa tinda dama ai shi kaɗai ya haifeka ni  ƴar karere ce,   idan ka je kace masa ya fito ina jiransa.”    Dariya Yazeed ya yi gami da cewa “Gaskiya kina da yawan faɗa Mum,  ki dinga haƙuri mana Daddy fa ya na da aiyuka sosai ki dinga yi masa uzuri,   kuma ba na so in ji ki na cewa ba na martaba ki ɗinnan Please Mum, martaba ki ya zama dole bayan ke ba ni da wata.”   taɓe baki ta yi ta juya masa ƙeya  alamar ba ta gamsu ba.
Tashi ya yi ya wuce sashin Daddy    ya na jiyo Hajiya Laure na mita shi kam sai dariya yake don abin nata dariya yake ba shi.

Ɗan madai-daicin Parlor ne  wanda ya ji kayan Alatu na more rayuwa, an zuba kuɗi wajen tsara shi da ƙawata shi  komai ya ji banda tsiya inji maroƙa.

Banda sanyin AC  gami da ƙamshi ba abinda yake tashi.
a tunanin Yazeed ya na shiga zai tarar da Daddynsa a Falon ya na karatun Jarida kamar yadda ya saba  don haka ya fara cewa “Dad!!!  ka na ina?   ka shirya faɗa da Mum don kuwa ta yi fus……..”  maganar tasa ce ta maƙale a maƙoshinsa,  cikin zazzaro ido ya ke kallon jini da ke kwance malala har ya gangaro  ƙarƙashin Kujera ya fito kasancewar saitin kujerun a tsakiya suke.
cikin tsananin firgici ya zagaya don ganewa idonsa abinda ke zubda irin wannan jinin haka.

Ihu ya kurma gami da yin tsalle ya yi baya  idanunsa kamar za su faɗo ƙasa sabida zaro su da yayi, dandanan   jikinsa ya ɗauki wata irin tsuma,  zuffa ya shiga karyo masa duk da irin sanyin AC da sanyin gari da su ke kaɗawa.

Baya-baya ya   fara yi ya na cewa “No!! wallahi ba dai Daddyna ba,  lallai yau na tabbata Jaki, naje na sha giya ta zo tana nuna min Daddy cikin jini haka? Impossible!  dole ma in dena shaye-shaye!!”  maganar yake cikin fitar haiyaci don kuwa tashin da hankalinsa ya yi ya wuce mizani.

Da gudu ya juya ya koma Parlo ya na ƙwallawa Mummy kira,  gabanta ne ya yanke ya faɗi Rimmmm!!!!!!!  ta yi saurin tashi ta na cewa “Me ya faru??”    Yazeed ya na haki ya ce “Daddyyy!!!  zo mu je ki gani,  na fara haukacewa!!.”   ya ƙarasa maganar ya na jan hannunta,  cikin sauri gami da sassarfa ta bi bayansa su ka koma Falon Alhaji Salisu.

Sai da ya danganata da gawar Alhaji Salisu sannan ya saki hannun nata ya koma baya ya riƙe ƙugu  ya na jiran ta ce masa ai giya ta sa ya fara gane-gane.

ya na kwance cikin jini ko ina a jikinsa  raunin wuƙa ne faca-faca  anyi masa wani mugun kisan gilla  wanda ko Dabba mutum ya ga anyiwa dole hankalinsa ya  tashi bare Mutum ɗan uwansa.

Hilis Share  Mutanena Ƴan  Amana😍🌸🌹

Paid Book ne…..
09079885632

©️INDO
[8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 2

           NA
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer’s Association🦅*

 

Ihu da kururuwa Hajiya Laure ta fara yi, ba ta bi takan Yazeed ba ta fice ta na ihun neman ɗauki.

Yazeed kuwa jin haka ya tabbatar masa ba gane-gane ya fara yi ba da gaske Daddynsa ne aka kashe, jaɓar ya zauna a ƙasa dafa’an murar kwaɗi, gami da fashewa da kuka kamar ƙaramin Yaro ya na cewa “Wallahi ko waye ya kashe min Daddy sai na kashe shi ba zan taɓa ƙyale shi ba.”  abubuwan da ya ke ta faɗa ya na maimaitawa kenan.

Hajiya Laure kuwa ta na fita harabar gidan me gadi ya taso da sauri ya na tambayarta,  cike da masifa ta ce “Maza-maza kira min Ƴan-sanda  wallahi ba zan yarda ba duk wanda ya aikata da me hannu a ciki sai na yi shari’a da shi kuma sai na sa an kashe shi, maza ka kira min su!!.”    ta ƙarasa maganar cikin tsawa,    jiki na tsuma Tala ya ce “Hajiya ai bansan me zan ce musu ba ne”
Kamar za ta cinye shi da masifa ta hayayyaƙo masa ta na cewa “Ka ce musu Alhaji Salisu aka kashe,  su yi sauri su zo tin kafin wanda ya aikata  ya bar garin su kama shi don wallahi  ba zan ƙyale ba ko uban waye shi.”

Jin furucin kisan Alhaji ya ƙara ɗaga hankalin Tala me Gadi, cikin rawar murya ya ce “To Hajiya ku na da lambar Ƴan-sandan??”     tasssss  ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, jikinta ya ɗauki tsuma sai huci take sabida ɓacin rai gami da tashin hankali da su ka yi karo da juna a cikin Zuciyarta.
“In banda kai ɗan iska ne? a kashe  Alhajin shine za ka zauna ka na tambayata lambar Police Dan Ubanka?  kai ba za ka iya zuwa da kanka ka nemo su ba?  Ba akwai mukullin  mashin ɗin da nake aikenka a wajenka ba??”
Ta yi maganar ta na huci  kamar bujimin Sa.

Tala Me Gadi ya na jin haka ya juya ɗakinsa da gudu, ba daɗewa ya ɗakko mukullin ba tare da ya dawo gurin Hajiya Laure ba ya zabari mashin ya fice  kamar ya tintsira  sabida sauri.

Har su ka dawo tare da Ƴan Sanda Hajiya Laure tana harabar gidan ta na zagaye, daga ta kai mari sai ta kai gwauro,  sai surutai ta ke yi   tamkar sabuwar mahaukaciya.

Ta na ganin Ƴan Sandan ta yo kansu ta na cewa “Wai kamar ni  za a kashewa Miji?? Alhaji Salisun za a kashe?? shekararmu kusan Talatin da Aure amma yau ɗaya a kashe min shi?  Inspector  lallai ka kama kowaye ya aikata sannan ka tabbatar an hukunta shi,  wallahi ko me ka ke so zan baka,  kai ko duka dukiyar da Alhaji ya bari ce zan baka ni ban damu da cin gadon dukiyarsa ba kawai Fansar Ruhinsa nake buƙata!!!.”
Inspector Khalil ya jinjina kai   kana ya ce “Mu je ki raka mu inda abin ya faru.”    kafin ya rufe baki ta juya ta na cewa “Ku tawo.”

Bin bayanta su ka yi zuwa Falon Alhaji Salisu, har lokacin Yazeed ya na gurin ya na ɓarza kuka tare da faɗin sai ya ɗau Fansa.
Har Ƴan Sanda su ka gama bincike-bincikensu  su ka yiwa Hajiya Laure da Yazeed da Tala  tambayoyi  ba abinda su ka fuskanta  game da kisan, illa iyaka sun shaida wanda ya yi kisan ba ƙaramin makashi bane don kuwa ba wata alama da  ya bari wadda za ta nuna cewar shi ne.

Gawar Alhaji Salisu Ƴan Sanda su ka ɗauka zuwa Asibiti, wurin ya rage daga Inspector Khalil sai Constable Saleh  sai Hajiya Laure da Tala.
Har zuwa lokacin roƙonsa take kamar ta yi masa sijjada akan ya nemo mata wanda ya kashe mata miji.
Cikin salonsa  na iyayi da kwainane ya ce “Kar ki damu Hajiya ai hakan aikina ne,  yanzu kamata ta yi mu je Asibitin mu gani  don haka ke ki yi gaba ina zuwa, zan tafi da wannan me gadin naku don ba yadda za’ayi a ce bai san anyi wannan kisan ba dole da sa hannunsa.”
Hajiya Laure ta sharce ƙwalla gami da majina  cike da farin cikin jin furcinsa ta ce “Na gode IP  sai kun zo ɗin.”   kai ya gyaɗa mata kana ya  nufi hanyar fita cikin takunsa na ƙasaita da jin kai, Hajiya Laure ta bi bayansa, Constable Saleh kuma ya cukumo Tala me gadi.

Har Inspector Khalil  ya ɗaga ƙafa zai shiga mota  Constable  Saleh   ya dakatar da si da cewa “Sir!!  na yi ƙoƙarin danne abinda ke raina amma na kasa, wallahi da alama ka fara aiki a wannan Office da ƙafar hagu domin da alama SARƘA  ta yi  Rikicinta a wannan gida.”
Fasa shiga motar ya yi cikin rashin fahimtar inda kalamansa su ka dosa ya zuba masa idanu kana ya ce “Me ka ke nufi da haka?  wacece SARƘA??”

“Ba mace ba ne,  Sunansa na gaskiya MUHAMMAD RISLAAN MUHAMMAD  amma   kowa da kalar sunan da yake kiransa sabida ya buwayi duniya,  Sir!  ina ganin a lallaɓa Hajiyar nan    a rufe wannan Case ɗin in ba haka ba kai ma zaman Office ɗinnan sai ya gagareka, na ga irinka da yawa waɗanda su ka zo su ka koma sabida buwayar Yaron nan.”
Murmushin rainin hankali Inspector Khalil ya yi kafin ya ce “Ina ne gidansu??”
Cikin zaro ido Constable Saleh ya ce “Ka yi mini rai ka gafarce ni Yallaɓai kar ka ce za ka kama bawan Allahn nan, wallahi idan ya san ni na gaya maka shi kenan na mutu, Yallaɓai ina da mata da ƴaƴa uku  yanzu ma ta na ɗauke da juna biyu, ka temaka min kar ka yi silar zaman iyalina marayu.”
Inspector Khalil ya dafa kafaɗarsa cikin sigar rarrashi ya ce “Kai fa Jami’i ne akan me za ka ji tsoron wani karankaɗa miyar mutum?  kar ka damu ba zan bari ya san kai ne ka faɗa ba, yanzu bani information nashi, a ina za mu same shi?”
Jiki na rawa Constable Saleh ya ce “Ban sani ba Yallaɓai shi kamar iska ya ke ba shi da tabbas, idan ka ganshi anan a yanzu za ka ganshi a can,  amma ina da lambar Ɗan uwansa malamin wata makarantar Islamiyya  idan ka kira ka tambaya tayuwu  ya na makarantar amma  fa sai sa’a  za a same shi.”

Cike da jin daɗin hakan Inspector Khalil ya ɗan bubbugi kafar Constable Saleh ya na wani irin murmushi me cike da ma’anoni, cikin salonsa na iyayi ya ce “Jami’i me basira,  ba ni lambar.”
Cikin rawar jiki Constable Saleh ya miƙawa Inspector Wayarsa ba tare da ya ce komai ba don kuwa ya hau dokin tsoro da firgici, ya gama sallamawa ya sa a ransa kwanansa ya ƙare.

sai da kiran farko ya katse a na biyu aka ɗaga tare da yin sallama,  Inspector Khalil  ya amsa sannan ya ci gaba da cewa “Ina magana da Sheikh Auwal ne??”    a ɗaya ɓangaren Sheikh Auwal ya ce “Eh ni ne  amma ban gane me maganar ba.”
“Sunana Inspector  Ibrahim Musa Rano wanda aka fi sani da Inspector Khalil,   ina neman Muhammad Rislaan Muhammad ne.”

dimm!!!!  Zuciyar Sheikh Auwal.
“Muhammad Rislaan Muhammad?? What Happened??”   Sheikh Auwal ya faɗa cike da tsoron abinda zai fito daga bakin Inspector.
“I suspect him of murder, so i will arrest him,  i need his informations, ina son sanin inda zan sameshi, ka ba ni haɗin kai Ya Sheikh kar ku wahalar da hukuma.”

wani irin tuƙuƙi zuciyar Sheikh Auwal ta ke yi  gami da tsalle tamkar za ta fasa ƙirjinsa ta fito,  cikin tsantsar ɓacin rai ya ce “Kar ka kuma tambayata bayanan Akhiee domin ba shi da tabbas, yau dai ka yi sa’a ya zo makaranta, ka zo nan ka same shi.”
Farin ciki ne ya lulluɓe Inspector Khalil, ya murmusa sannan ya ce “Godiya nake Sheikh Auwal  sai na zo ɗin.”

Constable Saleh ya ce “Yallaɓai na ga ka na murna?”
“Na samu inda ya ke cikin sauƙi, ka ga dole ne na yi murna, ba ka sani ba ne   dominsa aka turo ni nan aiki ba zan gushe ba har sai na ga bayansa,  yanzu Asibitin ya kamata mu je ko Makarantar?”
“Yallaɓai  na san ana buƙatarka a asibitin nan ko ba za ka yi komai ba ya kamata a ganka, mu je can ɗin in yaso daga baya sai a je makarantar”  Constable Saleh ya yi maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka.

Dariya Inspector Khalil ya yi sannan ya ce “Ka na da tunani me kyau, ya kamata ka zama babban Jami’i.”
Daga haka ya shige mota, Constable Saleh ma shiga ya yi a ransa ya na cewa “Bayan ka gama kashe ni tin yanzu”
Tala me gadi kuwa banda kuka ba abinda ya ke rusawa ya rasa ma ko bakin magana bare ya ce musu shi bai san anyi kisan ba.

Kai tsaye Asibiti su ka nufa don ganin yadda komai ke tafiya a ɓangaren binciken gawa.

Babbar Makaranta ce me ɗauke da sassa da ajujuwa daban-daban, makarantar na ɗauke da ɗumbin ɗalibai masu yawa  manya da ƙanana, mata da maza,  akwai wadatattun malamai  masu koyar  da ƙira’a daban-daban ba wanda ba’a yi a makarantar indai na Islam ne.

a wani babban Aji me ɗauke da mata da maza kowanne gefen zamansu daban,  duk ɗinsu sun duƙufa akan karatunsu,  daddaɗan sautin karatun  Qur’ani ne ke tashi ta ko’ina a ajin gwanin sha’awa.

Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa ta Malami ya zuba tagumi da duk hannayensa,  tunanin ma irin hukuncin da zai yiwa Rislaan ya ke, a duk iya tunaninsa ba hukuncin da zai iya yi masa wanda ya wuce yi masa shegen duka.

Miƙewa ya yi tsaye  ya na rarrabawa ɗaliban nasa idanunsa da su ka yi jajir sabida ɓacin rai, “A dakata!” ya faɗa cikin kamilalliyar muryarsa.

Shiru ajin ya yi kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa, an kai 10 second  cikin yanayin shirun sannan Sheikh Auwal ya ce “Zahra’u Muhammad!”   cikin sanyin jiki ƴar budurwar ta miƙe gami da cewa “Labbaika”    Ganin irin halin mugun ɓacin ran da ɗan uwan nata ke ciki ya ƙara karyar mata da zuciya, zirrrr hawaye su ka fara sharara akan kumatunta.

Sheikh Auwal bai bi ta kan kukan nata ba ya ce “Maza ki hau sama ki kira min Akhiee, sannan ki bi duk ajujuwan makarantar nan ki tattaro min duk Malaman cikinta ina buƙatarsu a yanzu!”
Da kyar ta ɗaga ƙafarta wadda ke faman kakkarwa ta nufi hanyar fita,  ta na fita kukan da take dannewa  ya samu nasarar kufce mata,   shi kenan yau Akhiee ya mutu  abinda zuciyarta ke ƙissima mata kenan don  haka kukan nata ke ƙara ƙarfi.

Duk ajin da ta yi katari da shi sai ta shiga ta kira malamin cikinsa  sannan ta wuce har ta hau sama….

Tsaye yake hannunsa dafe da ƙarfen kariya na bene…

SHARE DOMIN ALLAH

Paid Book ne…….
09079885632

*INDO*
[8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 3

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer’s Association🦅*

 

Matashi ne wanda bai wuce shekara Ashirin da Biyu kacal a duniya ba, Fari ne tas tamkar da an taɓa fatarsa wurin zai yi tabo, Allah ya yi masa baiwar kyawu irin na musamman ɗinnan,  ya na da dogon hanci siriri kamar ya yi magana, sai idanunsa dara-dara fararen cikinsu karr suke sai kwarjini kamar na Namijin Zaki,  bakinsa ɗan madaidaici ne a tsuke tamkar bai taɓa buɗe shi ba ma bare ya yi magana ko cin abinci, fuskarsa a ɗaure tamau kamar wanda aka yiwa Albishir da wuta.

Sanye yake cikin Farar Jallabiya tass wadda ta yi matuƙar karɓarsa kyawunsa ya ƙara fitowa tamkar balarabe.  a memakon aski sai wani tumemen kitso ne ƙwalli ɗaya tal kamar rai akan nasa, zanen hannu biyu ne an ɗauke shi tin daga gabannin goshinsa har sai da ya sauka a bayansa,  ya saƙu ya yi kyau sai ƙyalli da walƙiya yake,   dukkan yatsun hannunsa biyar idan aka haɗa da na ɗaya hannun goma sanye suke da wasu arnakun zobuka wanda su ke wani  irin sheƙi da walƙiya gami da ɗaukar idon me kallonsu, wasu sirara wasu kuma manya.
Gaɓoɓin yatsun kuwa jajir suke da jan lalle sun yi kyau kamar a sace a gudu, ko na wata macen Albarka.

a ɗan nesa da shi ta tsaya  cikin muryar kuka ta ce “Akhiee!  Sheikh Auwal na kiranka”
Ko gezau bai yi ba wai da sunan anyi masa magana,   ta san ba zai ce uffan ba don haka ta ci gaba da tafiya.

Wata ƴar hula wadda ake kira taɓani ka ji hadisi ya zaro a Aljihunsa ya kife kansa kana ya fara takawa saɗaf-saɗaf kamar me tsoron  ƙasa.
Lokacin da ya gama ƙalelejinsa ya je kiran tuni dukkan malaman da aka kira sun halarta  saura shi kaɗai ake jira.

Ba tare da shakka ba ya ratsa tsakaninsu ya wuce   ya dangana da Sheikh Auwal sannan ya durƙusa  ba tare da ya ce cikal ba.
Girman kansa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke fusata kowa da shi,  ganin yadda ya zo ya durƙusa ba tare ya ko kallesu ba  ya ƙara dugunzuma Sheikh Auwal.

“Ba  ka iya gaida manyanka ba?!!”  Sheikh Auwal ya faɗa cikin tsawa.
tamkar dutse  aka yiwa magana haka Akhiee ya yi.
Yasayyadi Jameel  ya dubi Sheikh Auwal  gami da cewa “Alagafarta Malam me ya faru ne?”
“Gashi nan ku tuhume shi, kisan kai ya aikata”
Sheikh Auwal ya faɗa bakinsa har rawa yake sabida tsabar ɓacin rai kamar ya fashe da kuka.

Akhiee kuwa jin wannan furucin ya sa shi saurin ɗago gwarazan idanunsa ya zubawa Sheikh Auwal ba tare da ko ƙiftawa ba,  Murtukekiyar Dorinar bulalarsa  ya zara cikin rufewar ido na ɓacin rai ya shiga zabga masa ta ko ina ya na faɗin ”Dena kallona mara kunya!!!, har sai yaushe na za ka shiryu ka dena abinda ka ke yi??”  ya zuba masa kyawawa aƙalla goma shabiyar a jere sannan ya tsagaita ya na huci tamkar an watsawa garwashi ruwa.

Ko uffan Akhiee bai furta ba haka kuma baiyi ko motsin kirki ba, sai dai ya yi ƙasa da idanunsa saɓanin da da ya yi wa Sheikh Auwal ƙiri-ƙiri da su.
Sheikh Auwal ya na ja baya, Sayyadi Muhsin  ya ƙara ararsa, dukansa yake ba ji ba gani tamkar ba ɗan mutum ba,  sai da daka iyayinsa ya gaji kana ya yi gefe, Shima Yasayyadi Jameel    ya zabareshi.

Duk yawan malaman ba wanda bai dake shi ba sai dai wani ya fi wani yi da yawa.
Duka suka yi masa wanda in wani aka yiwa  ba zai iya miƙewa daga gurin ba sai dai a ɗebe shi, in an ɗebeshin sai Asibiti don sai ya yi jinya.

Ba don sun huce takaicinsu ba dole su ka ƙyale shi don in su ka ci gaba da dukansa ma su za su ci gaba da shan wahala.

Akhiee kam ya na durƙushe a inda yake bai yi yunƙurin guduwa ko ramawa ba haka bai buɗi baki ba bare ya ce su yi haƙuri,   ba za a ce dukan baya shigarsa ba duba da yadda fuskarsa  ta yi wani irin jaa, idanunsa kuwa sun rikiɗe sun canja kala sunyi murtuk, farar Jallabiyar jikinsa ta sirka da jan jini sabida farfasa masa fata da su ka yi.

Mutanen aji kuwa tamkar ba a taɓa halittarsu ba, sun yi tsitt wasu na kuka  wasu hawaye wasu kuwa  da yake sun saba gani  ba su yi kukan ba  sai dai jiki ya mutu liƙis.

Cike da kyara Sheikh Auwal   ya ce “Tashi ka  fice min daga aji ba na son ganinka!!!”
miƙewa ya yi tangargar kamar ba shi aka yiwa wannan mugun lahanin ba, bai ce kanzil ba ya fice daga ajin,  inda ya ke tsaya da ya koma ya tsaya  idanunsa a ƙasa, zuciyarsa na wani irin tuƙuƙi da ruri tamkar za ta tarwatse,   hannu ya sa cikin aljihunsa ya zaro haɗaɗɗiyar Wiwinsa tare da leta,   ya bata wuta  ya fara zuƙar abarsa ya na fesarwa cikin salo da ƙwarewa.

Sheikh Auwal ya ma rasa abin yi don haka ya yi wa ajinsa addu’a  cikin gaggawa ya tashe su.

Husnee wadda take kuka kamar an sanar mata mahaifinta ya mutu  ta miƙe da ƙyar ta na jan ƙafafunta da su ka yi sanyi su ka maƙale ta nufi hanyar fita,    a tsawace Sheikh Auwal ya ce “Keh!!! kukan me kike wa mutane??”
Kasancewar tsoronsa ya gama kafa sansani a zuciyarta ba ta san lokacin da ta tsayar da kukan ba, cikin sauri ta ce “ba komai”
“Dawo ki zauna   dokar makarantar nan ba a fita ana yi mana kuka, ko kuma ki tafi ajin sama a ci gaba da karatu da ke.”
baki na rawa ta ce “Zan je saman”  a cewarta da ta zauna tare da wannan azzalumin gwara ta je ajin saman ta ci gaba da karatu.

Ƙafafunta na karkarwa ta hau sama, ta zo giftawa kenan hayaƙi gami da warin  wiwi  su ka ziyarceta, cakkk ta tsaya ta zuba masa ido cikin tsananin tausayinsa,  ta yi zurfi a tunani  ba ta san lokacin da ta fara cewa “Bawan Allah me yasa ka ke yi musu laifin da za su yi maka irin wannan dukan?? meyesa su na gama yi maka faɗa ka ke ƙara maimaita wani kuskuren? nan fa Islamiyya ce ka ke shaye-shaye a cikinta”   ta yi maganar cikin sigar nasiha da lallami.

idanunsa masu barazanar kauda ganin duk wanda ya kallesu ya zuba mata  har na wani lokaci sannan ya kauda kai ba tare da ya ce kanzil ba.
Rausayar da kai ta yi za ta ci gaba da magana ya yarfa hannunsa gami da yin taku biyu ya matsa gefe.

Tsillll!! ta ji wani abu tamkar kibiya ya soki ƙwayar idonta ɗaya,   ta yi saurin dafe idon tare da yin ƴar ƙaramar ƙara, Akhiee ya sake kallonta ya kauda kai ya ci gaba da busa hayaƙinsa.
Murza idon ta fara yi  sai ta ji zafin ya ɗauke kamar cirar ƙaya sai da wani irin hawaye sharr!!! sharrr!!! da ya fara zuba daga iyakacin ido ɗayan kamar almara.

Ta kuma ɗaga ido za ta kalleshi ta ji an finciketa, wani aji da babu mutane Zara ta ja ta, sai da ta ɗan sarata kana ta ce “Kar ki kuma zuwa kusa da wancan, kin ga ya lahanta miki ido ɗaya idan ki ka ƙara kallonsa zai lahanta ɗayan,  ke kinyi sa’a ma wata ana kiranta  Husaina Isah  wallahi makantata ya yi dulum, sanadin dena zuwanta makarantar nan kenan, amma daga baya ta warke,  ki yiwa kanki arziki kar ki ƙara yi masa magana kar ya cutar da ke a banza.”
Husneee ba ta ɗauki batun Zara da gasken gaske ba a cewarta ta ya daga kallonsa zai makanta mutum?  kuma tayaya ma za a ce shine ya lahanta mata ido bayan ko kusa da ita bai zo ba  hasalima  sai ƙara matsawa can ya yi.
a halin yanzu tausayin Akhiee shine a gabanta don haka ta ce “Ni ba na son ƙarya, haba don kun tsane shi sai ku yi ta yi masa abinda kuka ga dama?  wai shin shi ba shi  da ƴan uwa da iyaye ne da malamai ke yi masa wannan dabban dukan??”
Murmushi me tafe da hawaye Zara ta yi sannan ta ce “Sheikh Auwal, Yasayyadi Jameel, Yasayyadi Usman,  da kuma ni kaina da ki ke tunanin ƙazafi na yi masa, duk  ƴan uwansa ne, ni ƙanwar Akhiee ce  su kuma yayyensa ne, dalilin da ya sa ma muke ce masa Akhiee sunan Babanmu ya ci, amma wasu za ki ji suna kiransa Muhammad Muhammad,  wallahi ina son ɗan uwana ba zan iya yi masa sharri ba da gaske nake shine ya makanta Husaina,  ina gaya miki ne ba don komai ba sai don kar ki kai kanki inda za ki illata, Akhiee haɗari gare shi fiye da zaton masu zato.”

Cikin takaici Husnee ta ce “Amma kun ji jiki wallahi,  ashe ku ne ƴan uwansa amma kuke masa wannan abin?? to ni ba zan taɓa yarda shi ya makantata ko kuma shi ya tsokane min ido ba har sai na gani da idona ko kuma ya faɗa min da bakinsa.”
Rausayar da kai Zara ta yi  ta na shirin yin magana su ka ji jiniyar ƴan sanda, durummm!!! zuciyarsu ta buga a tare,  Husnee ta yo waje cikin sauri, ta na fitowa ta tarar Akhiee…

 

©️INDO
[8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 4

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer’s Association🦅*

Har ya sauka ƙasa,  binsa  ta yi da kallo cikin tsananin tausayinsa, ji take da   da yadda za ta yi ta hana su tafi da shi da ta yi, Zahra ce ta ƙaraso wajen jiki a sanyaye, har ya fice daga makekiyar harabar makaranta idanunsu na kansa,  sun kasa ko da cewa ƙala.

Wajen da ƙoshashshen Dokinsa ke ɗaure ya nufa ba tare da ya bi takan Inspector Khalil ba, ganin haka ya sa Inspector Khalil cewa “Kai dakata min!! Kama ka fa mu ka zo yi amma ka ke shirim guduwa, kar ka wahalar da ni kasa in harbeka.
Kalaman nasa in da dama dariya Akhiee zai yi don kuwa sun fi kama da haka, sai dai dariyar haɗari ce gareshi, ya kalleshi ya kauda kai sannan ya buɗi baki cikin nutsatstsiyar muryarsa ya ce “Ba zan hau muku mota ba, ka barni zan je akan dokina.”
Fakam-fakam Inspector Khalil ya yo kansa a fusace  ya na cewa “Mu za ka rainawa hankali?  ya za mu kama tantirin ɗan ta’adda irinka  amma sabida ka maida mu masu ƙwaƙwalwar yara sai ka ce za ka tafi a doki??”
Cikin sigar lumana ya ƙara cewa “Ba na son ku cutu ne shi yasa ba zan hau motarku ba!”
Inspector Khalil  ya ƙara hayayyaƙowa  kamar zai doki Akhiee, jin suna taƙaddama ya sa Sheikh Auwal matsowa gurin, fuskar sa ba alamun wasa ya ce ”Ba su san hatsabibancinka bane da ka ke tunanin su barka ka tafi kai kaɗai? wuce ka shiga ko ranka ya ɓaci.”

Cikin kurari  Inspector Khalili ya ce “Bar ni da shi Ya Sheikh, sai na nuna masa bambancin ɗan sanda da ɗan ta’adda.”
Duk wannan kurarin da Inspector ya ke yi  damisar takarda ce kawai don a gaskiyance tsoron ma kallon fuskar Akhiee yake a wannan lokacin bare har ya je daf da shi hakan ne ya sa ma ya basar da labarin handcuff.

Akhiee  ba tare da ya ce komai ba ya koma ya shiga motar Ƴan Sandan hankali kwance.
Sheikh Auwal ne ya dubi Inspector Khalil cikin ɓacin ran abinda ɗan uwan nasa ya aikata ya ce “Ba na so ku sake shi har sai kun hukunta shi a bisa laifinsa, kar ku biyewa son Zuciyarsa ku barshi ya dawo ba tare da kun ƙwatowa wanda aka cuta haƙƙinsa.”
Inspector Khalil ya shaƙi iskar da ke kaɗawa ya busar sannan ya ce “Calm down Ya Sheikh! hakan fa aikina ne, don hakan na kama shi.”
Da haka su ka yi sallama, Inspector ya shiga mota  zuciyarsa fari ƙal kamar anyi masa Albishir da Aljannah.

Ƙoƙarin kunna motar direba yake amma ina ta ce ba ta san zance ba  ko motsi ba ta yi da sunan ta na da rai,  abun kamar wasa mota ta ƙi ko da harbawa sau ɗaya har an kwashi lokaci me tsayi ana ta fama, Inspector Khalil sai kai kawo ya ke yi  hankalinsa duk ya tashi ya rasa yadda zaiyi  ga jama’a da su ka taru domin kallo sai dariya su ke masa,  zuwa yanzu ya fahimci cewa Akhiee ne matsalar motar don haka ya lallaɓa kusa da shi, cikin muryar raɗa ya ce “Muhammad  ka sauka to ka hau dokin naka ka ga  motar  ta lalace mu ma tawo daga baya  amma don Allah kar ka gudu kawai tambayoyi zan yi maka  ba wani abu ba.”   cikin zuciyarsa mugun ƙuduri ne akan Akhiee kawai ya faɗi  hakan ne a ganinsa ya lallaɓa shi zai fi zuwa.

cikin ko in kula Akhiee ya ce “Ƙaramin Sufeto, ka je ka canja shiri ka zo ka same ni a Office ɗinka na riga na yi niyar zuwa so zan je ba sai ka yi min ƙarya ba,  kuma ina so ka sani ba a shiga dawa don ƙarya.”

Ya na gama faɗen haka ya dire ya bar Inspector da buɗaɗɗen baki ya na kallonsa.
Bai saurari kowa ba ya haye dokinsa ya zabure shi.
Inspector Khalil  a tunaninsa  Akhiee ya na sauka daga motar za ta dawo daidai  sai ya ga saɓanin haka,  yanzu ya tabbata motar ta riga ta mutu kenan don haka hankalinsa ya  kai ƙololuwar tashi,   abubuwa da dama ya ƙudurce a ransa wanda zai yiwa Akhiee don ya huce baƙin cikin abinda ya yi musu.
Wurin su Sheikh Auwal ya koma ya nemi alfarmar su kai shi Office da motarsu,  ba su yi masa gardama ba  su ka amince masa.

Sai da akuyar cikinsa ta juya da ya yi alaragab da Rislaan zaune kan kujerarsa ya ɗora ƙafa kan teburin gaban kujerar    ya na zuƙar murzazzar wiwinsa,  baki sake ya ke kallonsa  tare da shuɗawa duniyar tunani.

Wayarsa ce ta dawo da shi haiyacinsa  ya yi saurin ɗauka, a ɗaya ɓangare Corporal Halil  ya ce “Sir!  yanzu mu ka kammala da gawar nan mun tafi hanyar maida ita gida”.
“Wane bayanai aka samu akai??”
“To gaskiya dai ba wata hujja illa iyaka dai rauni ne na wuƙa ba wani abu, sai kuma cewar tin daren jiya ne abin ya faru.”
Katse watar ya yi cike da takaici ya soketa kana ya ƙarasa cikin ofishin  ya na takun isa da ƙasaita,  cikin sigar wulaƙanci da ƙasƙantarwa ya ce “Ka zo ka miƙe ƙafa a teburina kamar na tsohonka, office ɗin nan fa ba gidan manyanka bane da za ka zo ka na min shaye-shaye a ciki,  ka na ƙazami da kai ma har ka isa ka zauna kan kujerata?  ka sauka ko kuma na yi maka abinda zaman ma sai ya gagareka.”
Yadda dutse ba ya magana haka Akhiee bai ce komai ba hasalima ko motsi bai yi ba.

Inspector Khalili ya dinga maganganu amma hakan bai sa Akhiee ya yi ko ɗar ba,  gajiya ya yi ya nemi guri ya zauna ya na nazarin ta inda zai ɓullowa lamarin.

“Yanzu ka tsaya mu yi magana, dole kai ne ka kashe  Alhaji Salisu don  kai ne ka gana da shi a daren jiya.
“Don na gana da shi ba shi ya ke nufin ni zan tsara masa ƙaddararsa ba.
“Kar ka yi min zancen banza, kawai ka amsa laifinka ba sai ka wahalar da hukuma ba, ko ka na nufin ka ce ba kai ne baƙonsa na jiyan ba?”
Jan hayaƙinsa ya yi ya busar cikin salo sannan ya ce “Na baƙunce shi jiya, kuma ni na fara yi masa Albishir da mutuwarsa,   amma don ance maka a daren jiya aka yi kar ka yi tunanin irin 12:00am ɗinnan, No daidai lokacin da ruwan sama ya sakko aka shiga gidan  ana tsaka da ruwa kuma  ruhinsa ya bar jikinsa,   na so na ceceshi sai dai kashhh!  bai yi min abinda ya dace ba  shi yasa na bari ya mutu,  Ƙaramin Sufeto  ka ƙara bugu don ba ka buga a daidai ba.”
Zuciyar Inspector Khalil tsalle kawai take yi kamar za ta ɓalle ƙirjinsa ta fito sabida ɓacin rai,
“Wannan gadarar taka da rainin hankali za ta jefaka a matsala, bayan duk wannan ka na nufin in yarda ba kai ka kashe shi ba?  ka faɗa min gaskiya kai ka kashe shi ko??  sai fa ka amsa mini sannan za ka samu hutu daga gareni  in ba haka ba ka shiga uku da ni.
Banza Akhiee ya yi masa ya ci gaba da zuƙe-zuƙensa  sai da ya gama zamansa akan kujerar Inspector Khali kana ya tashi ya na cewa “Haka ake kama mai laifin ba ko handcuff?”
Sai a lokacin ma Inspector ya tuna da hakan,  ya fara cika bakin cewa “Ai so nake na bika ta maslaha  shiyasa nake maka tambayoyi cikin lumana, amma tinda abin naka ya zo da haka dole ne  ai na rufeka, me ka ke ci na baka na zuba?”
Ko kanzil Akhies bai ce masa ba.

Tin safe har Azhar ta doso Inspector  Khalil na  famar tambayar Akhiee amma shiru ba amsa, duk wata barazana da zai yi ya yi amma shiru.
Wayarsa ce ta fara ruri  a ƙagauce ya janyota gami da ɗaga kiran ba tare da ya duba me kiran ba.
“Waye ya sa ka kama wannan?  ya ka ke abu  kamar ba ka san abinda ka ke yi ba?  yanzu ka na da  hujjar da za ka nuna wa duniya ta shaida shine ya aikata?”
Cikin girmamawa Inspector Khalil ya ce “Sorry sir, amma alamu ne su ka nuna shi ya aikata don kuwa shine ƙarshen ganawa da Alhaji Salisu.”
a ɗaya ɓangaren ya ce “Wannan rashin lissafi ne irin naka, maza ka sake shi sannan ka ba shi haƙuri, in ba ka yi hakan ba kuma zan cire hannuna daga ciki ko me ya faru kai ka jawa kanka”
“Okay Sir!!!”   bai ƙara magana ba ya katse kiran, Inspector Kalil ya bi wayar da kallo ya na mamakin hakan.

“Yallaɓai me ya faru? waye ya kira?”  Constable Saleh ya jefo masa tambayoyin a jere.
Cike da tsoro gami da shakka ya ce “Abin mamaki kira ne daga CP  da kansa  wai na saki wancan ɗan ta’addar.”
Constable Saleh ya ce ”Yallaɓai dama na gaya maka ko wuni ba lallai ya yi a hannunka ba bare kwana, na gaya maka  dabi da wancan shaiɗan ɗin haɗari ne, nan gaba ma za ka iya ganin takardar kora daga aiki ko ta canjin wurin aiki.”
Cikin ɗaurewar kai Inspector Khalil ya ce “Anya ba shi ka ke yiwa aiki ba Constable? na ga sai faɗa min kausasan kalamai ka ke yi akansa.”  cikin sauri Constable Saleh ya ce “Yallaɓai wallahi ka ji na yi rantsuwa ta muslmi ba na yi masa aiki ban taɓa karɓar kuɗin wani na yi masa aiki ba, Yallaɓai ka tuna da iyalina kar ka sa aikina ya lalace ba ni da hanyar samu sai wannan,  kawai anyi a gaban idona ne ba sau ɗaya ba     ba sau biyu ba shiyasa na shaida kuma na ke baka labari Yallaɓai.”

IP Khalil ya koma ya zauna jaɓar gami da furzar da zazzafar iska, “Ku sake shi!”  ya faɗa kamar zai fashe da kuka don takaici.

ya na bada umarni su ka buɗe Akhiee, ya kakkaɓe jikinsa ya tashi, wurin  Inspector ya nufa ya tsaya akansa sannan ya ce “Kai ƙaramin Sufeto, idan ka ce uwarka Madam ce  to mu haɗu a Coci, ina son ganinta.”
Daga haka ya juya, har ya fice  Idanun IP Khalil na kansa,   dogon tsaki ya zabga  gami da dukan teburibɓn gabansa ya miƙe kamar wanda aka cakawa Allura.

“Ya  Zama dole ma na san da abinda ya ke taƙama Yaron nan, ya zama dole na gane dalilin da ya sa CP ya ce na sake shi”  wannan lissafin IP Khalil ya ke yi cike da ɓacin rai.

Akhiee  kuwa tuni ya ɓata a wurin ya san inda dare ya yi masa.

Baya

Cikin sauri sauri Alhaji Salisu ya shigo Falon,, a kusa da Hajiya Laure ya zauna sannan ya ce “Hajiyata na yi baƙo za mu tattauna da shi, to kar ki shigo part ɗina  har sai na dawo na same ki”
“To sabida me Alhaji?”
“Kar ki tsananta bincike don Allah  kawai ki yi abinda na ce”
“To shikenan Alhajina ka dawo da wuri”
Hajiya  Laure ta faɗa ta na kwarkwasa.

gaba ya yi ya na cewa “In sha Allahu”
Akhiee na zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya Alhaji Salisu ya shigo da sallama, bai amsa ba  har ya ƙaraso ya zauna kan kujerar da ke fuskantar wadda Rislaan ya ke kai……

SHARE FISABILILLAH

Paid book ne…
09079885632

*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 5

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer’s Association🦅*

 

Washe baki ya yi kamar gonar Auduga, cike da farin cikin ganin baƙon nasa ya ce “Na ji daɗi da ka amsa gayyatata don ban zata za ka yarda ka zo cikin sauƙi haka ba,  me za ka sha in kawo maka?”
Ba tare da ya kalle shi ba ya ce “Ba ka da abinda zan sha a gidanka,  je maganarka kai tsaye.”
Gyara zama Alhaji Salisu ya yi kafin ya yi gyaran murya, duk ya rasa ma ta inda zai fara faɗe, sai da ya tattaro duk nutsuwarsa sannan ya fara da cewa “Kai sananne ne  ta fannin kisan kai na san da haka, to ina so  a kashe min wani ne don haka na nemeka, na san kai kaɗai za ka iya kashe shi ba tare da kowa ya sani ba, sunansa Alhaji Habibu mai Kwalli,  ya addaba min a kasuwa wallahi shi ne ya ke hanani arziki da yanzu na fi haka,  ka temaka min ka kashe shi, ko dubunnai nawa  ka ke so zan biyaka indai har zai mutu.”

Tin da ya fara maganar Risslaan ya zuba masa juyayyun idanunsa ko ƙiftawa babu har ya kai ƙarshem maganar,  lumshe ido ya yi sannan ya ce “Ina kashe duk wanda na so amma abinda ya kamata ka sani  ni ba’a  sa ni na yi abinda ban yi niyya ba,  inda na yi niyyar kasheka to fa a yanzu zan kashe ka  amma ban yi niyyar hakan ba,  ni ba matsiyaci bane ka sani   ba ka da arzikin da za ka iya siyan ra’ayina”  ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa “Ka na ta naka haukan ba ka sani ba ma kai ne gawar fari, I mean, you will die today”
Rasss!! zuciyar Alhaji Salisu ta buga  a razane ya ce “will you kill me??”
“It’s not me,  shi wanda ka ke son kashewa shima ya na son kasheka kuma ya rigaka shiryawa a yau za ka mutu, do you understand?”
duk da irin sanyin Ac da ke yawo a falon amma sai da zuffar wahala ta fara keto masa,  kamar Zai yi kuka ya ce “Na fahimta, ashe shima irin tunanin da nake akansa ya ke yi?  Muhammad Muhammad!  ka temaka min ka ceci rayuwata kar ka bari ya kashe ni, wallahi  ba na son mutuwa yanzu ina son ganin jikokina, ɗana guda ɗaya ne kar ka bari a maida shi maraya, don Allah kar ka bari ya kashe ni, na san kai me arziki ne ba zan iya biyanka ba amma nayi maka Alƙawarin ko me ka ce inyi zan yi.”
Akhiee ya kalle shi sama da ƙasa  kana ya ce “Barin irinka ƙalu-bale ne wa duniya, ba zan ceceka ba, amma ka kwantar da hankalinka bayan ka mutu shi ma zai mutu, ka godewa Allah kai ba ni zan kashe ka ba  da sai ka gwammace ba ka zo duniyar ba ma,  ba ni da lokacin zaman saurarenka ni zan wuce, idan ka na da wasiyya ko fatan ƙarshe sai ka gayawa iyalinka amma kai kam ba za a kai gobe da kai ba.”
Jiki na tsuma ya ce “To wai ta ya akai ka san zai kashe ni??”
“Idon Mikiyana na kansa”    daga haka bai ƙara cewa kanzil ba ya miƙe ya nufi hanyar fita.

Zamewa ya yi daga kan kujerar zuwa ƙasa, duk duniyar ta tsaya masa cakk gabaki ɗaya ma ya rasa tunanin me zai yi,  nan ya  zauna ya buga tagumi sai zuffa yake kamar wanda aka sanya a tukunyar dambu,  ya rasa abin yi kuma tinda ya ji Risslaan ya faɗa ya yarda dole ne sai ya mutu don haka ya susuce.

Wannan tashin hankalin ne yasa  ya kasa komawa wajen Hajiya Laure  kuma ya hana ta zuwa bare ma ta san halin da yake ciki.

Duk tsawon daren ya kasa rintsawa sai sukuwa yake a falon shi kaɗai, kansa duk ya gama kwarkwancewa.
a kowane minti jiran shigowar me kashe shi  ya ke  sai dai ya ji shiru har ruwa ya ɓalle,  zama ya ƙara yi ya buga tagumi ya na jiran ya ga abinda Allah zai yi.

Ya na nan zaune ya ji motsin ƙofa  ya yi saurin miƙewa jikinsa na karkarwa idanunsa zuru-zuru   ya na tsaye  suka lalata key ɗin ƙofar su ka shigo,  mutum uku ne fuskarsu duk a lulluɓe hannunsu ɗauke da manyan wuƙaƙe  masu bala’in kaifi,  ya kasa ko da motsa ƙafafunsa da ke karkarwa bare ya gudu har su ka ƙaraso su ka sanya shi a tsakiya.

Ɗaya daga cikinsu ne ya ce “Mu yi abinda za mu yi kar a kama mu.”
Ya na faɗen haka ɗayan ya kafta masa sara a kafaɗa, ɗayan ya ce “Alhaji Habibu me kwalli ne ya aiko mu, kar ka mutu ba ka san laifinka ba.”  bai iya cewa komai ba sai ma durƙushewa da ya yi a gabansu hannunsa dafe da inda su ka sare shi.

Cikin sauri su ka hau kansa da sare-sare da soke soke su na gamawa su ka fice don kar a kama su.

Gaba

daidai lokacin da aka tashi Sallar La’asar Akhiee ya shigo makaranta, sanye yake cikin ƙananun kaya riga da wando  farare tarr!  har ɗaukar ido su ke yi, ya kifa hula P-cap  itama fara takalminsa ma fari tass.
a harabar makarantar  ɗalibai su na ta hudimomin gabansu masu yin alwala na yi masu surutu na yi,  duk wanda ya ankara da shi sai ya yi gefe ya bashi hanya don kuwa hanya ma ba wanda ya ke ƙaunar haɗawa da shi.

Sama ya hau inda ya saba tsayawa   ya coge ya na kallon mutanen da ke sabgoginsu ɗaya bayan ɗaya.
Zahra ce ta yafito Husnee ta na murmushi ta ce “Kin damu da son ganin Akhiee ta kin ganshi ya dawo.”
Kamar anyi mata albishir da kujerar hajji haka ta washe baki ta na cewa “Da gaske??”
Zahra ta ce “Da gaske mana duba sama ki gani.”
Husnee ta sa hankicif ta danne idonta ɗaya da ke zubar hawaye  sannan ta ƙyallara ɗayan ai kuwa ta na ganinsa kafin Zahra ta yi magana ta bar gurin ta nufi sama  da gudu.
Zahrah ta zazzaro  ido ta saki baki ta na kallon Husnee wadda tuni har ta fara hawa steps,  rausayar da kai ta yi ta ce “Allah i tsare ki to.”
Daga haka ta ci gaba da alwalarta.

Husnee na haki  sabida gudun da ta yi ta isa wajen Akhiee  cike da farin cikin ganinsa ta ce “Ya akai ka zo makaranta? ƴan-sandan sun sake ka?”
Kallonta ya yi ya kauda kai a ransa ya na ƙissima irin buyawar yarinyar gabaki ɗaya nema take ta sanya masa  damuwa.
Jin bai ce komai ba ya sa ta matsa kusa da shi ta na cewa “Wai ciwon da aka ji maka ɗazu har ya warke??”
“Ikon Allah, ita kuma wannan kowa ya na guduna sai ƙara cuso kanta take ko ina ruwanta da ciwona??”   aransa yake wannan surutun a zahiri kuwa bai ko motsa ba bare ta san ma ya ji ta.

Kasancewar Husnee akwai rawar kai ba ta damu da shirunsa ba ta ci gaba da zubo masa surutu, ba ta yi shiru ba sai da ta ji idonta ɗayan ya harbu  kamar yadda ta ji ɗayan ya yi da safe nan take duka biyun su ka fara shararar da hawaye,  idanun nata ta zuba masa zuciyarta na tsalle, tunanin kalaman Zahra ta fara yi nan take ta fara yarda  don kuwa abin akwai ban mamaki ba gaira ba sabar idanu su kama zubar ruwa.

Ba ta ƙara cewa uffan ba ta ja dogayen ƙafafunta ta koma ƙasa jiki a sanyaye.
Zahra ce ta kalleta cikin tausayawa ta ce “Ba ki ji ba,  ba ki gani ba za ki  sa ayi miki abinda za ki bar iyayenki da jinya, kinga dai yanzu ɗaya idon ya kamu  sai ki kula don nan gaba za ki iya rasa su”
Goge hawayen ta yi sannan ta ce “Ai yanzu na fara yarda don wallahi ni ban taɓa yin irin wannan ciwon ba;  wai Zara shi ɗin kurma ne?”
Zara ta murmusa sannan ta ce “Ko ɗaya, ya na jinki kuma ya na magana idan kin ji bai yi ba to niyya ce bai yi ba.”
Husnee ta ce “Anya kuwa?  duk abinda na ce ai ya kamata ya ce wani abu ko ba yawa”   Zara ta yi murmushi me sauti gami da rausayar da kai ta ce “Husnee kenan!  ki na da rashin yarda sosai, amma yanayi zai nuna wataran za ki ga ya yi magana.”  Husnee ba ta ce komai ba ta zumɓuri baki don gani take ko me Zara ta faɗa akansa kawai don ba sa ƙaunarsa ne.

Bayan an idar da sallah aka koma karatu, kowa na ƙoƙarin yi amma Husnee ta kasa aikinta ɗaya goge ƙwallarta da ke zuba wata kan wata.

01:00AM
duk wannan daren IP Khalil ya kasa rintsawa sai bincike-bincike da nazarce-nazarce yake yi.
Wayarsa ce ta fara tsuwwa ya janyota tare da duba screen ɗin DCP shine sunan da ke yawo akai,   da sauri ya ɗaga gami da karawa a kunnensa,  DCP Khashim Bello ya ce “IP Ka na saurarena?”  da sauri IP Khalil ya ce “Ina saurare”
“Na ji abinda ya faru tsakaninka da Sarƙa  to ba na so hakan ya dameka, amma ina me gargaɗinka akan iya takunka idan ka bari Wancan CP ɗin ya ganeka shi kenan mun kaɗe, ka samu ka kawo ƙarshen duk tsagerancinsa  kafin ya fi haka, zan turo maka kuɗi ka duba sannan kuma na yo aike  ka kula min da komai.
“Yes sir!!”  daga haka DCP ya katse wayar.

Zazzafar ajiyar Zuciya Inspector Khalil ya sauke sannan ya miƙe ya nufi makwancinsa.

Yau da yake Litinin ce
Husnee Ba ta zo Islamiyya da safe ba sai yamma, tin da ta zo take sa ran ganin Akhiee har ta fitar da rai gashi Zara ta ce mata bai zo da safe ba,  haka kawai duk hankalinta ya tashi sai ta ke ganin kamar wani abin ne ya faru da shi,  sai dai abinda ba ta sani ba  sai ya bushi iska ya ke zuwa makarantar.

Haka aka tashi ta koma gida  ba tare da ta sanya shi a idanunta ba.

Ta na zaune a Parlor ita da Mommy da Khausar su na kallo Yayanta Ahmad ya shigo,  bayan ya zauna ya ce “Wai ke me hawaye ba kuka ba za ki haƙura da kallon ba sai idon ya ƙarasa mutuwa?”
Goge hawayen ta yi ta na murguɗa baki sannan ta ce “Kar ka takura min  ai dai idon nawa ba ciwo yake ba.”  da ɗan mamaki Ahmad ya ce “Ba ciwo yake ba to uban me ya sa shi hawaye?”    “Akh…..”  saurin rufe bakin ta yi ta na zazzare ido, jin irin katoɓarar da take shirin yi, Mommy da Ahmad su ka zuba mata ido  cike da son jin abinda za ta ce “Gyara zama ta yi sannan ta ce “Ƙila tsakuwa ce ta faɗa.”
“Wato ƙila tsakuwa ko?  ki faɗa mana gaskiya idan ma tsokana ki ka yi aka rushe miki shi.”  Mommy ta faɗa ta na tsareta da ido, cikin sauri ta ce “Wallahi ban tsokani kowa ba Mommy, kawai dai ikon Allah ne ” Ahmad ya ce “Ba ta da gaskiya fa, amma ki ƙyaleta idan ta ga uwar bari da tsefaffen gashi ai za ta faɗa.”
Turo baki ta yi ba tare da ta mayar masa da martani ba, aranta kuwa cewa  ta yi “Ba zan faɗa muku ba ku hana ni zuwa makaranta”

ya na tsaye hannunsa ɗaya riƙe da ƙugunsa ɗayan kuma wiwi ce  bango yake kalla ya na nazari  ya na yi   yana zuƙa.

Ɗan Bakwai  ne ya shigo tare da sallama daga  ɗan nesa da shi ya tsaya    ya rissina ya ce “Ubana Ubansu! Wata gyatima ce ta zo nemanka munyi munyi ta faɗi abinda ke tafe da ita ta ƙi  wai sai ta ganka.”

Hannu ya ɗaga ya yi masa alamar ta shigo,  da sauri Ɗan Bakwai ya juya ba daɗewa su ka dawo tare da wata dattijuwar mata,  rissinawa ta yi gami da cewa “Ina kwana!”    shiru   bai ce komai ba jin haka ya sa ta kalli Ɗan Bakwai kamar za ta yi kuka ta ce “Ka roƙa min alfarma ya saurare ni don Allah.”
Ɗan Bakwai ya ce “Ai ya ji ki,  ki je maganarki kai tsaye.”
Gefen hijab ɗinta ta sa  ta goge gumin da ya tsatstsafo a fuskarta sannan tace…..

 

*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 6

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer’s Association🦅*

“Sunana Karimatu sana’ata sayarda Abinci, tafiyayya na yo domin na haɗu da kai,   ɗana ne  bai fi shekaru 17 ba amma sai na ajiye kuɗi ya zo ya ɗauke  ya je su sayi kayan maye shi da oganninsa manya da su amma ba su bashi ko sisi ba sai na sha wahala na nema ya zo ya sace ya kai musu, ya ƙi zuwa Boko ya ƙi Islamiyya aikinsa kenan yawo cikin ƴan shaye-shaye, shi ne sai ka ganshi da sigari ya na sha ba aikin fari ba na baƙi sai wannan, na yi faɗa na yi duka na yi nasiha amma duk ya ƙi ji, shine na samu labarinka,  Ɗannan na yarda da kai ɗari bisa ɗari shi yasa na kawo maka shi ko da zai yi iskancin ma idan ya na ƙarƙashin kulawarka zan fi samun kwanciyar hankali.”
sai a lokacin ya juyo  ya ɗan kalleta cike da kulawa ya ce “Gobe ki zo min da shi.”
murmushi ta yi sabida jin daɗin samun karɓuwa da ta yi, cikin sauri ta ce “Ai ba zai zo ba gardama gareshi.”
Maida kallonsa ya yi kan Ɗan Bakwai gami da cewa “A haɗata da Zabira   ita za ta iya zuwa da shi.”
Ɗan Bakwai ya ce “An gama Uban gayya”
Godiya sosai matar ta yiwa Risslan har ta fice duk da bai ce komai ba ita kuwa ba ta fasa ba.

gaba

Misalin ƙarfe 10:37Pm
Garin Kwanar Ɗan Gora babban Titin shigowa KANO..

Ba wani dare ne ya yi ba amma da yake lokacin damuna ne tuni sahun bil’adam ya ɗauke sai ƙarar iska da ke kaɗawa ba ji ba gani, jefi-jefi motoci sukan wuce su ɗin ma in wata ta wuce wata takan jima ba ta zo ba.

Dirowa ya yi daga kan Dokinsa ya fara haske-haske da dalleliyar Fitilarsa  ya na ƙarewa yanayin wurin kallo, ya ɗan ɗauki lokaci ya na haske-haske sannan ya kashe fitilar, dubensa ya kai ga Dokinsa gami da ɗan shafa shi, cikin daddaɗar muryarsa ya ce “Prince! calm down,  ba daɗewa za mu yi ba yanzu zan gama mu koma.”
Prince dai da yake baya magana bai ce komai ba sai sunkuyar da kai da ya yi.

Daidai lokacin wata ƙaramar mota ƙirar Taxi ta shararo da mugun gudu kamar wadda jiya ta wuce take shirin kamo gobe.

Dalleliyar fitilarsa ya kunna ya haska motar sannan ya kashe ya nufi kan titin, a tsakiya ya coge gami da riƙe ƙugunsa.

a cikin motar kuwa Direban ne ya kalli na kusa da shi gami da cewa “Ka na ganin abinda nake gani kuwa?”  ɗan zaman banza ya ce “Menene?”   “Ba ka ga wata fitila da aka hasko mu ba?  kuma ka ga mutum fa a tsakiyar titi duk irin wannan gudun da nake yi ko ɗar bai yi ba.”
Mutum ɗaya da ke a gidan baya ne ya ce “Kuma ba dai ace ƴan fashi ba, in su ne ma da sauki Oga zai iya da su.”
“Kutumar Uba Sahun Keke ne!!!!!”  Direban ya faɗa  cikin firgici da razani,  wani mugun burki ya ja wanda ya yi daidai da harbe tayar motar da Akhiee ya yi,  tayar ta bada dammm!!!! ta tarwatse, motar ta yi  dara ta yi tsalle ta hantsila sau biyu kana ta tsaya wuri ɗaya ta na juyawa samanta ya koma ƙasa.

cikin ƙasaitaccen takunsa ya gangara gefen titin inda motar ta ke, leƙawa ya yi ta glass ya cewa direban “Ba ni wayarka”
Direba da ke numfashi da kyar da kyar  ya zaro wayar a aljihunsa na gaba, fizgeta Akhiee ya yi kana ya yi baya-baya ya saita wurin man motar da bindigarsa, bai damu da kuka da magiyar da Mutanen ciki ke yi ba ya bata ɗasss,   nan take ta kama da wuta ba ƙaƙƙautawa.

ƴan danne-danne ya yi a wayar ba ɓata lokaci ya cire key ɗinta tamkar ta shi,  kira ya tura gami da kara wayar a kunne, bugu biyu aka ɗauka, JD cikin farin ciki ya ce “Direba Dangin kura, ina fatan kun isa, na kasa rintsawa har sai na ji kyakkyawan Albishir.”
“Ba kyakkyawan Albishir a wannan karon sai dai a tarawa gaba,  na kamaka kuma na mamayeka!!!”  Akhiee ya yi maganar cike da zarra.
Zumbur JD ya miƙe daga kan luntsumemiyar kujerarsa ta alfarma,  a take guguwar tashin hankali da firgici ta tashi a cikin cikinsa,  ido a burbuɗe ya ce “Sahun Keke!!! What do you mean!!???”
“Ohh! Nothing, i mean, your car had an accident,  ka ga yanzu saura kai kenan.
Safa da marwa JD ya fara yi a tamfatsetsen falon nasa, ya kai tsayin minti ɗaya bai iya cewa komai ba sannan ya ce “Wallahi! Tallahi!  ni ne maganin iskancinka,  ni za ka yiwa wannan yankan ƙaunar?  ka jira abinda zai biyo baya, billahillazi  sai  na jefaka a bala’in da za ka gwammace ba ka zo duniya ba.”
“Ina jira idan har kai hafaffen cikin tsohuwarka ne kar ka barni na ƙara kwanan duniya, ina jiran duk abinda za ka yi.
daga haka ya katse wayar gami da jefata  kan motar da take ci da wuta,  juyawa ya yi  ya haye kan dokinsa su ka ɗau hanya.

Kwantsam!!!  JD ya maka wayarsa da ƙasa ya na huci,  yatsansa manuniya yasa ya na nuna ƙirjinsa gami da cewa “Ni???  ni za ka yiwa haka? wallahi ko me ka ke taƙama da shi sai na azabtar da rayuwarka.”
Dukan dafkeken kansa da ke juyawa ya fara yi hannu bibbiyu kamar sabon mahaukaci, sai da ya gaji da zagaye sannan ya jaɓe kan kujera gami da dafe kai ya fashe da wani azababben  kuka  wanda shi kansa ma bai san dalilin yinsa ba.

washegari

Fitowarsa daga ɗakin baccinsa kenan ya tarar da matan gidansu a tsakar gida sun kafa dandalin hirarsa kowacce ta na tofa albarkacin bakinta,  bai kula su ba ya wuce hanyar fita, da gudu Zara ta ƙarasa inda yake ta na cewa “Akhiee Abhi na kiranka.”
Bai yi magana ba ya juyo zuwa cikin gidan, ɗakinsa ya koma ya canja kaya  ya sanya jallabiya da hula sannan ya nufi turakar mahaifin nasu.

Hamza na zaune kusa da  Abhi ya na bashi labari Akhiee ya yi sallama, tsohon  dake zaune kan kujerarsa ta marasa lafiya ya amsa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi, ƙarasawa ya yi ya durƙusa a gabansa gami da cewa “Good Morning Daddy!”  Abhi ya amsa da cewa “Morning Dattijo!  ka manta da ni ne kwana biyu?  dama abinda ya sa na kiraka  na ji a gidan ba zancen da ake yi sai naka, ba kwanciyar hankali a ƴan kwanakin nan  naji sai cari su ke yi ba matan ba mazan, me ka yi ne Dattijo??”
Da sauri ya ɗago kai ya na kallon Mahaifin nasa cike da rashin sanin abin faɗa.
Murmushin gefen baki Hamza ya yi a ransa ya ce “Ai yau taka ta ƙare faɗen gaskiya ya zama dole.”

kamar yadda Risslan ya ce a zo masa da yaron da ke yiwa ummansa sata hakan ce ta faru,  tare su ka shigo da Zabira da Ɗan Bakwai da Salansa sai kuma Mama Karimatu mahaifiyar yaron sai yaron da ke ta famar rarraba idanu kamar an ɗaure zakara ana shirin yankawa.

Akhiee na zaune kan benci ya na aikin shan wiwi su ka shigo da sallama, duk su ka  ja   su ka tsaya su na jiran cewarsa.

Miyagun idanunsa ya zubawa yaron har na ɗan lokaci kafin ya ce “Mama faɗa masa laifinsa.”  da sauri ta ce “To”  sannan ta ƙara maimaita abinda ta faɗa jiya.
Cike da tsageranci yaron ya ce “Ni ba na ɗaukar mata kuɗi, ai idan na yi musu aike ne su ke bani.”
Mama Karimatu ta ce “Wallahi ƙarya yake Muhammad ba sile ɗayan da suke ba shi sai dai shi ya kwashi nawa ya kai musu.”
A fusace yaron ya ce “Ni fa gaskiya ba na sata ni ba ɓarawo bane, akan me za ki ce ina ɗaukar miki kuɗi bayan ban ma san inda ki ke ajiyewa ba?”
Mama Karimatu ta riƙe haɓa  ta na mamakin irin tsaurin ido na ɗan nata.

Cikin takunsa irin na toron giwa ya ƙaraso gabansa ya na binsa da wani irin kallo me sanya nutsuwa ko ba’a so, “Ya sunanka?”   “Rabi’u”  ya faɗa a ƙagauce,  jinjina kai ya yi sannan ya ce “Me yasa mahaifiyarka ta na faɗe ka na faɗe? ka na nufin ƙaryata take maka??”
ƙara haurowa ya yi kamar zai doki Akhiee ya na cewa “Ni ban ce ƙarya take ba, amma ni ban taɓa ɗaukar mata kuɗi ba!!!!”
Akhiee ya  kalli Mama Karima gami da cewa “Mama janye ɗanki don in na saka masa hannu za ki iya rasa shi.”
Da sauri ta riƙo hannunsa ta na cewa “Matso nan”  fizgewa ya yi  ya ce  “Ni rabu  da ni.”
Za ta yi magana Akhiee ya ce “Ƙyale shi” matsawa ta yi gefe  ta zubawa sarautar Allah ido,  Akhiee ya dube shi a tsanake  ya ce “Yanayin tsaurin idonka ya burgeni,  a kayan caji da me kake amfani??”
Ƙasa ya yi da ido ya ce “Sigari kawai nake sha”
miƙa masa Tabar hannunsa ya yi gami da cewa “Na san kana so, to  gwada mana!”  karɓa ya yi ba tare da ya ji ko ɗarr ba  shi a dole ɗan zafin kai.

Ja ɗaya ya yi mata ya wurgar da sauran gami da dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya dafe kai ya na wani azababben tari, nan take idanunsa su ka canja launi su ka ƙara yin ja sosai su ka firfito sabi da azaba.
tari yake ba ƙaƙƙautawa ƙafafunsa ma sun gaza ɗaukarsa har sai da ya durƙushe a ƙasa, Ummansa ce ta matso kusa da shi cikin tausayawa ta na yi masa sannu sai dai ba halin amsawa.

Salansa ya ce “Da ka ce kai shege ne, ai a zafin kan ma aji aji ne dan ubanka.”
Akhiee ne ya durƙusa a gabansa cikin nutsuwa ya ce “Za ka ƙara ne??”  da sauri ya girgiza kai alamar aa,  Akhiee ya dubi Salansa gami da cewa “Ku haɗa shi da Laita.”
ya na faɗen haka Salansa ya kama shi ya fice da shi daga gurin.
Ummansa ta raka su da ido har su ka fice.

“Ki na ba shi kuɗin makaranta?”  girgiza kai ta yi alamar a’a  ya ce “To ki dinga ba shi amma ba da yawa ba, rashin sakarwa yaro hannu yakansa shi fara ɗauke-ɗauke amma idan abin ya yi yawa ya na kawo lalacewa,  In sha Allah zai shiryu, zan sa shi a Islamiyya nan da kwana biyu ko uku.”
Mama Karima ta goge ƙwalla ka na ta ce “To Allah i sa, na gode sosai.”

Kai kawai ya gyaɗa mata alamar ya amsa.

Kwance yake kan  makeken Gado wanda zai iya kai girman wani ɗakin, gadon ya sha shimfiɗa da tafkeken bargo wanda ake kira duniyar kuliya,  ko ina na gadon ado ne ya yi kyau gwanin sha’awa.
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba.
Wani samɓalelen Maciji golden collor ya salallaɓo ya hau kan gadon,   can tsakiya inda Akhiee yake ya nufa  sai da ya hau kansa ya zagaya kana ya sauka gefe ya tsaya ya nannaɗe gami da ɗago kansa sama.

Sanyin Macijin  da ya ji ne ya sa shi   buɗe idanunsa cikin nutsuwa ya zubawa Macijin su kafin ya lumshe ido, a hankali ya ce “My Mother!!!”

SHARE FISABILILLAH

Na kuɗi ne….
09079885632

 

*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 7

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

a hankali Macijin ya fara sauya kamanninsa daga maciji zuwa mutum.
Dattijuwar mace ce fara sol kyakkyawa, fuskarta ɗauke da murmushi ta ke kallonsa cike da kulawa, ɗan shafa kansa ta yi gami da gyaɗa masa kai alamar ta na sane ta tashe shi.
“What Happened my Mother?” ya faɗa yana zuba mata rikitattun idanunsa, cikin nutsuwa ta buɗe kyakkyawan bakinta ta magantu cikin zazzaƙar muryarta me cike da kamala da dattako, “It’s time for prayer!”
Da sauri ya tashi zaune  yana lumshe idanu, cikin sassanyar muryarsa ya ce “Okay Mommah!”
dafa hannunsa ta yi cikin nutsuwa ta ce “Ya na da kyau ka je makaranta yau”
“For what?”
“Calm down, akwai me jiranka ne idan ka je za ka san dalilin.
Gyaɗa kai ya yi sannan ya yunƙura ya miƙe ya nufi toilet wanda aka gina shi da zallar farin dutse, kuma aka yi masa ado da tsirrai da fulawoyi masu furrai kala-kala  gwanin sha’awa.

Sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura Alwala, ya na fitowa ya shirya cikin riga da wando na saƙi farare tass, a samansu ya ɗora doguwar Alkyabba me kyawun ado, itama fara ce an yi mata ado da launin baƙi da ja, ya yi kyau matuƙar kyau wanda zaman misaltashi ma aiki ne.

bayan ya idar da Sallah ya yi addu’a  ya miƙe cikin taku irin na wahainiya ya fito daga makeken ɗakin, a bakin ƙofa ya tsaya  ya na rarraba ido.

Gine-gine ne na  dutse wanda aka yi ɗakuna da kuma madafa sai banɗakuna,  ko ina a ƙawace yake da koren ganye fululu da fulawoyi masu furanni ja yalo pink milk da dai sauransu, idan ka kai dubenka  nesa kuwa tsaunuka ne manya da ƙananu da ƙoramu masu gudana da ruwa fari ƙar  me kyawun kalla,  daddaɗan sanyi  ne ke tashi ta ko’ina gami da  ƙamshin furanni da tsirrai, abin ba a magana.

cikin cool voice nashi ya ce “Mother!”  bata kusa amma ta ji kiran da ya yi mata kuma ta amsa, ba ɓata lokaci ta iso gabansa fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi  “Amma za ka ci abinci kafin ka tafi.
Girgiza kai yayi alamar aa.
Ba ta yi masa musu ba don kuwa ta san ba zai cin ba,   bai kuma cewa kanzil ba ya fara taka korayen tsirrai da ke shimfiɗe a ƙasa tamkar carpet,   da ido ta bi shi har ya ɓacewa ganinta sannan ta ci gaba da aiyukanta.

Ana tsaka da karatu  ya shigo ajin, cikin yanayinsa na jin kai ya isa gaban Sheikh Auwal ya durƙusa ya gaishe shi kamar yadda kowane ɗalibi ke yi wa malaman makarantar.
Sheikh Auwal ya zuba masa idanu shi kansa ya na yi masa bala’in kyau a irin shigar nan kamar mutumin kirki, sai dai kashh! albasa ba ta yo halin ruwa ba,  Ya kasa amsa gaisuwar ya tafi tunani, ganin haka ya sa Risslaan miƙewa zai nemi gurin zama, “Dakata Akhiee! zauna”  Sheikh Auwal ya faɗa cikin sauri.
da yake yau ba ƴan gardamar akansa zaman ya yi dafa’an murar kwaɗi  ya na sauraren ƙalu-balen da Sheikh Auwal ya zo da shi  don a cewarsa ba sa faɗen Alkairi  kuma ba sa neman mutum sai ya yi laifi.

Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce “Me yasa kwana biyu kenan yau ba ka zo makaranta ba??”
“Ba na cikin yanayin zuwan ne”  ya bashi amsa kai tsaye ba tare da shakka ba.
Sheikh Auwal ya jinjina kai sannan ya ce “Akhiee Don Allah ka zamo mutumin kirki ka watsar da harkar banzar nan,  ba a son raina komai yake faruwa ba, ka duba ka ga tinda Allah ya sa ka zo duniya mahaifinmu ya ɗauki so da ƙauna ya ɗora maka, kuma har yake kiranka Malam, ya na da burin ka zamo malami babban mutum tamkar shi, dalilin da yasa ya raɗa maka sunansa kenan, sai gashi an wayi gari ka kasa zama ka sauke Alƙur’ani ko da sau ɗaya, zuwa makaranta ma ba ka yi,  ka ga mahaifiyarmu ta rasu ta na me begenka tare da sa ran za ka zamo bango ga al’uma, don Allah ka canja rayuwa Akhiee!!!”

Maza Gumbar dutse!! ba shakka nasihar Sheikh Auwal ta taɓa masa zuciya musamman da  ya taɓo sashin iyayensa wanda ya fi ƙauna fiye da komai a rayuwarsa.
Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Rislaan ya ce “Mu ga tafin hannunka Ya Sheikh!”  ba musu Sheikh Auwal ya buɗe tafin hannunsa, shima Akhiee buɗe nasa ya yi ya dangana shi da na Sheikh Auwal, cikin tattausar murya ya ce “Iyayenmu ɗaya, jininmu ɗaya, amma ka ga tsagar tafin hannunmu ma kaɗai ta bambanta, to akwai abubuwa da yawa ma waɗanda su ka bambanta, ba mu   muka tsara hakan ba Allah ne ya tsara, tabbas sunanmu ɗaya da Abhi amma ruhinmu daban-daban ne, ka ga dole ƙaddararmu ta bambanta, kowa da kalar ta sa ƙaddarar;  ni wannan ita ce  tawa, ba zan yi muku Alƙawarin zan canja ba domin ba ni da tabbas akan haka, kuma ance jumu’ar da za ta yi kyau tin daga laraba ake ganeta, ni kuma babu alamar rayuwata za ta canja daga haka, ina me bada haƙuri Akhiee!!!”

Tabbas zuciyar maza ta karye, Sheikh Auwal ya kasa cewa komai don kuwa idan ya furta zai iya rushewa da kuka, kalaman Akhiee sun yi mugun tasiri akansa,  tsananin tausayin ɗan uwan nasa ya kama shi.

Akhiee kuwa tashi ya yi ya nemi guri ya yiwa kansa masauki,  ya na zama duk na kusa da shi su ka dare su ka bashi wuri su ka koma can nesa da shi, sai ya kasance shi kaɗai a wurin,  bai damu ba don kuwa in da sabo ya saba kuma shi ma hakan ya fi masa daɗi don a  arashi ma mutum zai iya ɓata masa rai ya illata shi a banza don haka ya fi so su dinga nesanta kansu da shi.

Tinda ya zauna bai ce uffan ba shi bai yi karatun ba bai yi surutu ba.
Hakan ba baƙon abu bane don komai yawan dukan da za’ayi masa ba zai taɓa yin karatun ba don haka Sheikh Auwal bai damu ba bare ma ransa ya ɓaci.
Sai da aka tashi domin yin sallar la’asar  sannan ya tashi ya nufi sama wurinsa na gado  wato inda ya saba tsayawa.

Husnee jikinta har rawa yake don son ta je ta iske shi, ta na shirin fita daga ajin Sheikh Auwal ya kirata, ba don ta so ba ta amsa kiran gami da zuwa ta durƙusa a gabansa,  cikin yanayinsa na dattako ya ce “Me ke faruwa ne naga kamar a kwanaki biyun nan kullum cikin kuka kike?”

maganar ta shi ma dariya ta bata amma sai ta maze ta ɗan murmusa gami da cewa “Ba kuka na ke yi ba Ya Sheikh Idona ne su ke ciwo”
“Kin je asibiti?”  gyaɗa kai ta yi alamar eh kafin ta ɗora da cewa “Na je sun ce ba komai a idon”
Abin ya bawa Sheikh Auwal mamaki, jinjina kai ya yi gami da cewa “To fa! ikon Allah, to Allah i sauwaƙe tashi ki je.”  zumbur  ta miƙe kamar wadda aka sokawa kibiya a mazaunai,  cikin sauri ya dakatar da ita da  cewa “Wani hanzari ba gudu ba.”
Durƙusawa ta yi cike da takaici ta ce “Ina ji Ya Sheikh”
“An kawo min ke makaranta ne don ki yi karatu ki ƙara samun nutsuwa da tarbiya ba wai ki lalace ba, to don haka ki gujewa shiga hurumin Akhiee, shi wani irin mutum ne da ba wanda ke son mu’amala da shi, kinga ƴan uwansa maza ma ƙaurace masa su ke yi bare ke mace, ba zan so wani abu mara daɗi ya faru da ke ba don hakan zai zamo alhakinmu tinda amana aka bamu ke, lallai ki kula.”
Kai kawai ta gyaɗa masa ba don ta gamsu da kalaman nasa ba.

Ya na bata izinin tafiya ta tashi ba ta zame ko ina  ba sai kusa da Akhiee,  lokacin da ta ƙarasa kusa da shi waya yake, abinda ta tsinkaya ya na cewa “Da wane irin makari kuka kashe shi??”  ba ta ji abinda aka ce masa ba sai kawai ta ga ya kashe kiran, ta saki baki ta na kallonsa kafin ta ce “Dama ka saba kashe mutane? ashe har sawa ka ke yi a kashe??”  gyaɗa kai ya yi alamar eh sannan ya ce “What are you doing hare?”
Mantawa ta yi da zancen da takeyi cike da rawar kai ta ce “Me yasa jiya ba ka zo makaranta ba?”
Kallonta ya yi kafin ya buɗe baki a nutse ya ce “Ke sabuwar zuwa ce?” gyaɗa kai ta yi gami da cewa “Yo eh mana, ranar asabar waccan na fara zuwa, kuma ba taɓa ganinka ba sai wannan lahadin, sai kuma naga ana ta dukanka abin tausayi”  ta ƙarasa maganar ta na marairaicewa.

“Ya sunanki?”
Murguɗe baki ta yi cike da iyayi da feleƙe ta ce “Husna ko Husnee”
“Asma’u! to shekararki nawa?”
Da sauri ta zagayo gabansa suna fuskantar juna  tsabar rawar kai da jin daɗin kulatan da ya yi har ji take kamar ta yi tsalle ta ɗafe shi.
“Shekarata Goma sha bakwai, saura shekara ɗaya na yi candy!”  daga yadda take magana ma kaɗai ya isa nuna irin tsantsar farin cikin da take ciki.

Idanunsa masu matuƙar kaifi gami da kashe jikin wanda ya kallesu ya zuba mata, ƙara sassauata murya ya yi kana ya ce “Shekarunki sha-bakwai amma shine kamar akanki aka fara ƙuruciya aka ƙare?”
“Ahh?!  to me na yi na ƙuruciya?”
“Wai kuka kike don an dokeni, ni da jin zafi ke da yin kuka, duk wannan ba ƙuruciya bace?”
Rausayar da kai ta yi gami da jingina a jikin ƙarfen makari, a sanyaye ta ce “Ni wallahi  tausayinka na ke ji.”

Dafa hannayensa ya yi akan ƙarfen gefe da gefenta ya sanyata a tsakiya  ya na kallon kyakkyawar farar fuskarta,  “Asma’u!!!”  ya kira sunanta cikin wata irin murya me rikita lissafin ɗan adam, hakan ya tilasta mata ɗago idanunta da ke fama da hawaye ta jefa su cikin ƙwayar idanunsa.

Ganin ta maida hankalinta kansa ya bashi damar ci gaba da cewa “Ni ba abin tausayi bane, kar ki ƙara tausaya min, ko ni bana tausayin kaina idan kika ce za ki tausaya min kuma ke za ki zamo abar tausayi,  sannan ki dena yawan kallona, zuciya gareni kamar glass da ta buga shikenan zan iya illata miki rayuwa, wata rana za ki iya rasa ganinki indai ba ki dena ba.”
Kamar macijin da aka zarewa dafi haka ta ke jinta sululu, gashi dai ta na sauraren gargaɗin nasa amma ta kasa dena kallonsa kamar wadda ake ce ta na ɗauke idanunta zai ɓace ta dena ganinsa.

Iskar bakinsa ya hura mata akan idanun nata  ta yi saurin rintse su da ƙarfi ta na jan wani dogon numfashi….

 

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

 

*©️INDO*
[8/13, 7:40 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 8

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta buɗe idanun nata, fayau babu shi a wurin, juye-juye ta fara yi ko za ta hango inda ya yi amma ko  ƙyallinsa ba ta gani ba.
riƙe haɓa ta yi cike da mamaki ta tambayi kanta “Wai har ya ɓace min?”
Wata ƴar budurwa kamarta ce ta ƙaraso inda take ta na fara’a,  Husnee ta bi ta da ido gami da cewa “Ya akai?”  “Don Allah so nake mu zama ƙawaye, ni sunana Asiya  ajinmu ɗaya ma da ke”
Husnee ta murmusa cike da jin  daɗi, dama tinda ta zo ba ta samu ƙawa ba sai Zara ita ce su ke ɗan mutunci su ma anayi ana faɗa.
“Ni kuma sunana Husnee, daga yau mun zama ƙawaye to”
Da sauri Asiya ta ce “na ji daɗi wallahi na gode”
Husnee ta ce “Mu je mu yi Alwala”  da to ta amsa sannan su ka sauka ƙasa.
Sai da ta je yin Alwalar ta lura  hawayen idanunta sun dena zuba cak! kamar ba su yi ba, nan fa ta dinga murna kamar ta hau sama ta faɗo.

zaune yake kan ɗan ƙaramin gado da aka yi shi da jan katako aka sanya masa ƴar katifa daidai da shi, sai shimfiɗar gado ta bargo me taushi.
Salansa da Ɗan Bakwai na tsaye gefensa curko-curko,  Waya ce a hannunsa ya na latsawa cikin kwanciyar hankali, Lambar IP Khalil ya lalubo gami da tura kira.

Inspector Khalil na zaune kusa da matarsa su na kashe love wayarsa ta yi ƙara, ɗan ƙaramin tsaki ta yi gami da cewa “A daren nan ko waye me kiranka?”
Murmusawa  ya yi cike da son koɗa kansa ya ce “Nifa ɗan Sanda ne, ko da yaushe ma ana iya kirana, ba ki saba da hakan bane sabida ban riga na Aureki ba, amma yanzu tinda mun yi aure ai za ki ga abubuwa daban-daban”  murmusawa ta yi kafin ta ce “Gaskiya ne Jarumina, ba ka ɗauka ba to har kiran ya katse,  ko in baku wuri  ne?”
Da sauri ya ce “No zauna abinki”  daidai lokacin wani kiran ya ƙara shigowa, latsa kore ya yi gami da aza wayar kan fala-falan kunnuwansa tubarkallah.

“Ƙaramin Sufeto, Albishir zan yi maka akan mutuwar Abokin wanda case ɗinsa ke hannunka, Alhaji Habibu Mai Kwalli; na kashe shi.”
“What!!!!!!”  IP Khalil ya faɗa cikin kaɗuwa da razani.
“Yaushe? kuma ta ya? me ya yi maka?”
“Idan ka matsanta bincike za ka zamo na gaba a waɗanda za su mutu  don kai ma akwai tamu da kai, amma ba na son kasheka yanzu tamkar na kashe maciji ne ban sare kansa, har sai na kashe ƙashin bayanka sannan zan kasheka!   na faɗa maka ne don ka rubuta a file ɗina  ba wai don ka wahalar da kanka wajen kamani ba;  na samu labarin ka yi Aure,  waccan haɗuwar tamu ba ka zo min da maslaha ba bare in yi maka murna,  Happy marriage to you, a gaida iyali.
Ya na kaiwa nan ya katse kiran gami da miƙawa Salansa ita, Ɗan Bakwai ya miƙo masa wata gami da cewa “Gaba salamun baya salamun, Sahun Giwa me badda na Raƙumi, SAHUN KEKE Ba a Gane Gabanka!!!”
Karɓar wayar ya yi  ya na ƙoƙarin yin wani kiran ɗaya wayar tashi ta fara ƙara.

IP Khalil,
kamar sakatar sakarai haka ya saki baki, duk jikinsa ya yi sanyi kamar an zuƙe masa ruwa,  nazari yake akan shaharar ta’addancin Risslan, ya rasa ma abinda zai yi masa ya kawar da shi, shi dama kowa ya san ba mutumin  kirki bane bare ayi masa wani mugun sharrin,  Zulaihat ba ta lura da halin da ya ke ciki ba don hankalinta na kan kiran da take son yi,  “Nima bari in kira Babana mu gaisa, tinda mu ka yi Aure ba mu gaisa da shi ba .”  IP Khalil dai ba baki sai kunne.

Zaro wayar ya yi daga Aljihunsa  ya zubawa screen ɗin ido har na ɗan lokaci sannan ya ɗauka ba tare da ya ce komai ba,  “Baba!!!” muryar Zulaihat ta doki dodon kunnensa, kasa amsawa ya yi har sai da ta ƙara kiransa sannan ya ce “I’m So sorry my daughter!   me kike yi har yanzu ba ki yi bacci ba? ina mijin naki??”  ya jefeta da tambayoyin a lokaci ɗaya.

zakuɗawa ta yi kana ta ce “Sorry for what my Daddy? kai fa ba ka laifi, ka ganshi nan ya na gaisheka, ko in ba shi ku gaisa?”
Da sauri IP Khalil ya ɗaga mata hannu don kuwa ba zai iya magana ba a yanzu musamman da babban mutum wanda take kira Baba.
Risslan ya ce ”No need, barshi kawai ina amsawa, na san ba kya rabuwa da ƙorafi shiyasa na fara baki haƙuri don na san dole za ki yi”
Ta ce “To shikenan, amma Baba ba ka zo Aurena ba ya kamata ka zo ganin ɗaki, amma tinda duk ba ka zo ba Birthday ɗina ya kusa, amma za ka zo ko??”
“Sai yadda yanayi   ya nuna Daughter,  ta yuwu ma ko na zo ba za ki ganni ba, amma kar ki damu kawai.”
Rausayar da kai ta yi sannan ta ce “To sai da safe”
“Allah i kaimu”
Bai jira cewarta ba ya katse wayar,  ya ajiye gefe,  Kira ya tura da ɗaya wayar ba ɓata lokaci aka ɗauka, kai tsaye ya fara da cewa “Zan shigo garinka gobe da daddare, a janye tsaro.”
IP Hussain ya ce “An gama sir!”
Daga haka ya katse wayar,  kiran CP ne ya shigo Salansa ya ɗaga kana ya miƙo masa “Yallaɓai” shine abinda ya faɗa sannan ya yi shiru don jin abinda CP zai ce “Na san ka sani ba sai na faɗa maka ba, kuma na san za ka aikata, fatan nasara ɗan nasarawa, ni kuma a ta nan zan dafe komai.”
CP ne ke yin maganar cikin hikimar harshe.
Risslan ya ce ”Na lode kuma zan kaɗar, so na gana da IP Hussain ma ta ɓangarensa ba damuwa;   Shu’umin Jami’i Yallaɓai CP Abubakar Ado Gezawa!”
CP ya yi dariya me isarsa kana ya ce “Ja’irin Yaro Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan! sai na ji ka zuwa jibi don gobe na san ba ka da lokacina.”
Risslan ya ce “Ba shakka Bukar, amma ko me zai faru ka ɗauka kawai haɗari aka yi mota ta kama da wuta, banda tsananta bincike”
“Yes sir!”  CP Abubakar Ado ya faɗa cikin sigar Zolaya.
Da haka su ka yi sallama sannan Akhiee ya miƙe ya na cewa “Yau da wuri zan shiga gida, ku dafe ko ina, ku kula da sauran Iyalina,  ina Zare da Aci-bal-bal suke ne??”
Salansa ya ce “Su na can su  na bawa shegiya wuta Ya Babba!  nake liƙa maka Zare ya kwashi harawa, ya kwashi harawa, shiruu!! ka ke ji, magana ma Ɗan iska ba ya iya yi.”
Risslan ya ce “Bari gobe zan ci Ubanshi, shi ga ƙaramin kai ga son ɗaukar kaya”
Ɗan Bakwai ya ce “Inaa! lumbu-lumbu ce, yanzu ka kai masa sara nan za ka gane  iskancin nashi na ƙarya ne, a sauka lafiya me gayya!”  ya ƙarasa maganar tare da rissinawa Risslan, “Hmm!!” kawai ya ce sannan ya fice.

Ƙaton kango ne me ɗauke da part part  da ɗakuna daban-daban  a ciki ma in ba zagayawa za ka yi ba sai ka yi kwana da kwanaki ba ka gamu da wani ba.
ko da ya hau dokinsa ba su dena binsa ba  har sai da ya fice daga tafkeken Kangon.

Washegari
Bayan Sallar Isha’i ya ɗauki hanyar Kwanar ɗan Gora a kan dokinsa.
Bayan ya ƙone motar  ya kama hanyarsa ta komawa gida ba tare da tsoron dare ko shakkar wani abu ya gifta masa ba.

Da sauri ya ɗago kai ya na kallon mahaifin nasa cike da rashin sanin abin faɗa, Murmushin gefen baki Hamza ya yi, a ransa ya ce “Ai Yau taka  ta ƙare faɗen gaskiya ya zama dole.”
cikin son kauda zancen Akhiee ya ce “Abhi! wani abin su ka ce na yi?”
Abhi ya ce “A’a, na ji ne su na ta zancenka ba dare ba rana dole na san akwai abinda ka yi musu.”
Gyara zama ya yi sannan ya ce “Abhi! ka san dai ɗan Adam ba a iya yi masa, kawai fa kwana biyu ne ban je Makaranta ba shine ake ta wannan tashin hankalin.”
Abhi ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ƙara da cewa “Me yasa to ba ka zuwa?  ka san fa kai Malam ne.”
“To ai abubuwan ne da yawa Baba, ka ga ana fita nema haka sannan ka ga yanzu damuna ce ina yawan zuwa gona, shi yasa amma ko jiya… au jiya ban je ba,
amma shekaran-jiya na je,  ka san fa ni manomi ne Abhi”

Abi ya yi murmushi irin nasu na manya gami da cewa “Aff ƙwarai kuwa!  ni ai na sani dama, ai wannan duk ba abin damuwa bane, amma da zarar ka dawo daga gona ka shirya ka je makaranta abinka, ka ji ko Malam?”
“To Abhi in sha  Allah”
Hamza da baƙin ciki ya maƙale masa a zuciya kasa dannewa ya yi ya ce “Wallahi Abhi ƙarya yake yi” wani mugun  kallo Akhiee ya zuba masa, wanda ya sa hantar cikinsa juyawa.
Abhi ya ce “To fa! Dattijo!”  “Na’am Abhina”
ya amsa a ƙagauce,  “Ɗan uwanka ya ce ƙarya ka ke yi,  me ke faruwa bayan haka?”
“Wallayi Abhi ranar nan ne aka samu akasi Yasayyadi Jameel ya doke ni shine fa  na ji zafi raina ya ɓaci, sai na ɗan yi masa rashin kunya,  shine fa wai a dole sai an gaya maka, kai ni naga ta kaina”  ya ƙarasa maganar ya na jimanta al’amarin.
Abhi ya jinjina kai kafin ya ce “A Kul! kar a ƙara yiwa manya rashin kunya, kuma shi malaminka ne ai, Malami kuwa ɗan uwan uba ne ya na da kima da daraja, lallai a kula, zan nemesu in gaya musu kar in ƙara jin ana zancenka.”
“Na gode Abhi, ni yanzu zan fita zan je gona in duba yanayin aikin da aka yi jiya.”
Abhi ya ce “To Allah i tsare, Allah i yi maka Albarka yaron kirki;  kai Malam Hamza maza a je a zo min da Iyayen naku da sauran ƴan uwa.”  Ya ƙarasa maganar ya na duben inda Hamza yake.
“To” Hamza ya ce sannan ya bi bayan Akhiee su ka yi hanyar fita.
Cike da takaici ya ce “Amma kai anyi munafuki wallahi, ka iya ƙarya kamar ɗan duba, ka je ka yi kashe-kashe amma ka ce masa ka je gona.”
cikin ɓacin rai Akhiee ya ce “Ba babban munafuki sama da kai  da ka ke shirin faɗa masa abinda zuciyarsa za ta buga,  su fa iyaye  kalamai masu daɗi ake gaya musu wanda hankalinsu zai kwanta, amma sabida ba ka san darajarsu ba za ka gaya masa abinda zai tashi hankalinsa, kuma na rantse da ubangijin Al’arshi  idan aka samu wani ya gaya masa ainahin zahiriyyata har wani abu ya same shi sai na kashe kowaye  ya faɗa, ba alwashi bane alƙawari ne   kuma zan cika indai an saɓa min.”
Cikin ɓacin rai gami da tsana Hamza ya ce “Banza mara kunya, sai ka kashe ɗin in ran a hannunka yake”
“To ɗan masu da kunya, ni lokacin da aka raba kunyar ban zo duniya ba, idan ka damu da in yi kunyar sai ka ban taka”  Hamza ya ce “Allah i sauwaƙe!”  Akhiee ya ce “Zancen banza, da kunyar ba ta isheka ba kake tallar ta?  ai da ta isheka sai ka ɗeba min taka,  gaso-rogo kawai”
daga haka Bai bawa Hamza damar ƙara yin magana ba ya yi gaba cike da baƙin ciki da takaicin irin ƙyama da ƙiyayyar da ƴan uwan nasa suke nuna masa.

IP Khalil na zaune kan kujerarsa ya kifa kai akan teburi ya na hucewa, kansa duk ya gama ɗaukar zafi, wani mugun ƙunci da damuwa yake ji kamar zai haɗiyi zuciya ya mutu, Risslan ya gama ɗaɗɗaure masa jijiyoyin jikinsa, ya je ya yi kashe wancan ya kashe wancan gashi ya ƙone motar ogansa, sai umarni yake samu daga sama na kawo ƙarshen Risslan, babban tashin hankalinsa bai san menene raunin Risslan ɗin ba bare ya yi masa illa,  a yadda yake a rayuwarsa ba wani abu da ya zamo rauni a gareshi.

Har baccin wahala ya fara ɗaukarsa wayarsa ta tashe,  ya ɗago idanunsa da su ka koma kalar ja ya zubawa wayar, ganin Hajiya Laure ce ya sa shi ɗagawa don ya bata haƙuri ma ta dena takura masa.
a masife ta ce “Kai IP Khalil na gaji da gafara Sa ban ga ƙaho ba,  ina labarin wanda ya kashe mini Miji??”
shiru ya yi mata don kuwa bai san me zai ce mata ba ya ji yau da bala’i ta hauro.
“Tambayarka na ke yi fa??”

Numfasawa ya yi sannan ya ƙoƙarta ya ce “Hajiya mun fi ki son mu ga mun yi aikinmu, amma ba mu da halin hakan,  ki yi haƙuri mu na nan mu na ƙara bincike akan lamarin, wanda mu ka kama kawai zargi ne ba mu da hujjoji ƙwarara, amma da yardar Allah komai zai yi daida….”  “Dakata Ibrahim!!”  Hajiya Laure ta faɗa cikin tsawa,  ɗorawa ta yi da cewa “Na gaji da yaudarar nan da kake yi mini,  yanzu na ɗau haske na fahimci komai,  ai bakinku ɗaya da kai da makasan dama,  to wallahi  da kaina zan ɗauki mataki, yanzu ba na buƙatar temakonka,  don me za ka ce ba ka da hujja bayan ka san wanda ya aikata har ka kama shi sabida bakinku ɗaya sai ka sake shi,  shine fa ya baƙunci mijina a ranar da aka kashe shi, to in ba shi ba waye zai yi kisan?”
IP Khalil zai yi magana ta katse shi da cewa “Kar ka gaya mini komai!!  ba na son ji,  na haƙura da temakonka ka je ka yi Allah na nan kuma kuɗin da na biyaka Allah ya isa,  ni zan bi ta wata hanyar in ɗauki fansar mijina,  wallahi tallahi sai na jefa wannan yaro cikin bala’in da sai ya  kashe kansa,  kai kuma ta Allah ba taka ba munafukin banza”   ta na kaiwa nan ta katse wayar ta na huci.

IP Khalil ji yake tamkar ya yi ta bin layika da kwararo ya na zunduma ihu ko zuciyarsa za ta yi sanyi, nan take wani mugun zazzaɓi da ciwon kai na wahala  da tarin tunane-tunane su ka lulluɓe shi.

Huci Hajiya Laure ke yi kamar bujimin sa ya ga wuƙar yanka shi,  Yazeed da ke zaune gefenta ya ce “Shima munafuki ne ɗan sandan nan ko??”
“Yo eh mana, in ba haka ba ta ya za ka kama mutum ka sake shi bayan ka san shi ya aikata,  wallahi zan ɗauki mataki akansa nan ba da daɗewa ba, je ka fito mini da mota fita zan yi.”
Yazeed ya miƙe ya na cewa “Amma da kin bari kin gama takaba sai ki yi ko me za ki yi.”
“Ubanka!!  na ce ubanka kai da takabar!  kamata ta yi ace ka fi ni damuwa da mutuwar ta shi amma sabida kai butulu ne duk wannan so da ƙaunar da yake nuna maka sai ka ce in bari in gama takaba?  to kai da takabar na ci buhun ubanku, ƴan butar duma kai?”
“Allah i bada haƙuri” ya faɗa cikin sanyi sannan ya fita domin gyara motar da za ta fitan.

 

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

*©️INDO*
[8/14, 8:18 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 9

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

“Asma’u!!!!!!” kira ya ƙwalla mata da ƙarfi cikin tsananin kaɗuwa da tashin hankali, cikin zafin nama ya finciko hannunta da mugun ƙarfi hakan ya sa  ta dawo kansa, garin daidaita tsayuwarsa ya taka ɓawon ayabar da ta jefo masa santsi ya ja shi, gabaki ɗaya su ka yi wata muguwar sufa su ka rikito daga saman benen su ka nufi ƙasa, rimmm!!!!! sai gasu a tsakiyar harabar makaranta.

Ihu ƴan matan da ke kaikawo a wurin su ka sanya gami da tarwatsewa kowacce ta na neman wurin ɓuya.
Hankali tashe Akhiee ya ture Husnee da ke kwance akan ƙirjinsa ya  miƙe  ya na zuba mata idanu don sanin halin da take ciki, hankalinsa ne ya ƙara dungunzuma ganinta a sume ta wani irin ɗashe ta ƙara haske kamar ba jini a jikinta, da sauri ya sanya hannunsa cikin tafin hannunta ya damƙe  jikinsa na wata irin tsuma sabida tsananin ɓacin rai.

“Me ka yi mata??”  muryar Yasayyadi Jameel ce ta dawo da shi cikin makarantar saɓanin da     da duk hankalinsa ya yi nisa,  sai a lokacin ya  lura da mutane sun yi da’ira akansu  kowa ya zubawa sarautar Allah ido.

a fusace Yasayyadi Usman ya ƙaraso wajen ya riƙo ɗayan hannun Akhiee  ya finciko shi,  ba tare da nazari ba ya afka masa wani lafiyayyen mari, “Uban me ka yi mata?? ba tambayarka ake yi ba?? me yasa ba ka jin magana kai?”
ɗago hannu ya yi zai ƙara tsinka masa wani marin Akhiee ya fizge  hannunsa ya doki ƙirjin Yasayyadi Usman da ƙarfi  sai da ya yi taga-taga  zai faɗi su Yasayyadi Jameel su ka daddafe shi.

Idanunsa da suka canja kamanni ya zubawa sauran ɗalibai ƴan kallo kafin ya ce “Kowa ya ɓace daga nan ko na illata masa rayuwa wallahi;  kai kuma kar ka ƙara gigin marina in ba haka ba zan tarwatsa maka farin cikinka, idan ta tashi sai ku tambayeta idan akwai tsiyar da na yi mata.”
Ya na gama faɗen haka ya koma inda Husnee ke kwance ba alamun numfashi a tare da ita.
Ƴan makaranta kuwa tuni sun fice da gudun ceton rai, sai ɗaiɗai da ba su ƙarasa fita ba. rungumarta ya yi a ƙirjinsa ya nufi cikin ajinsu ba tare da ya bi takan kowa ba, ajiyeta kawai ya yi ya fito ya sa kai ko kallon su Sheikh Auwal bai yi ba ya fice daga makarantar, tafiyar kawai yake yi amma bai san inda ma zai dosa ba don kuwa ransa ya gama kaiwa ƙololuwar ɓaci, bai san inda zai nufa ya ji daɗi ba.

Su dai sun tsaya curko-curko kamar dangin Kaji an rasa me yin ko ƙwaƙƙwarar magana.

“Za ka ci Ayaba?”  ta faɗa gami da miƙa masa ragowar wadda take ci.  girgiza kai ya yi alamar a’a, ta ci gaba da cin kayarta hankali kwance, jin bai ce ƙala ba ya sa ta cewa “Akhiee!  yau ba za ka yi mini magana ba ne? ni fa so nake in ga dariyarka, kullum sai dai ka dinga haɗe rai kamar hadarin gabas”
Kyawawan idanunsa ya zuba mata cikin lallami ya ce “Ni fa ki ƙyale a yadda nake don ni ba na dariya.” da sauri ta ce “To sabida me?”  shiru ya yi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma ya ce “Ta na karya min tambaya ne” “Iyye?!!”  ta faɗa gami da sakin baki,  “Ni fa ba na gane wannan yaren naka, ka faɗa min da hausa”  ”Ai ba za ki gane ba sai dai ki wahalar da ni.” turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce  “Don Allah ka yi dariya ko da sau ɗaya ne na san za ka yi kyau” banza ya yi mata kamar ba da shi take ba, jifansa ta yi da ɓawon ayabar da ta cinye gami da cewa “Sai ka riƙe abarka ba a so ma, kuma na yi fushi ba zan ƙara kula ka ba”  daga haka ta juya fayau-fayau da nufin barin gurin   cak!!!!!!  ta tsaya sabida muryarsa da ta karaɗe kunnuwanta.

sun daɗe a tsaitsaye jiki duk a sanyaye  kafin Yasayyadi Jameel ya ce “Mu dai mu na ganin takanmu a rayuwa, wannan yaro ko annoba?”
a sirrince Sheikh Auwal ya goge zazzafar ƙwallar da ta fara gangarowa daga cikin idanunsa, cikin dakiya da mazantaka ya ce “Kar ku damu in Allah ya yarda ba abinda zai faru, ku ci gaba da Addu’a watarana sai labari.”
Yasayyadi Usman  dafe da ƙirjinsa da yake jin kamar maɗaukansa (Ƙashushuwan haƙarƙarinsa) sun kakkarye cike da tsanar Akhiee ya ce “A tunaninku wannan shaiɗanin zai shiryu ne??  ai kuma ya yi nisa ba zai taɓa jin kira ba,  Wai har Abhi ya ce wani kar a ƙara zuwa ana zancensa, ai abin faɗen yake yi ba dole a faɗa ba?”
Malam  Zayd ma ya taya Yasayyadi Usman su ka ci gaba da yi,  takaici  da tashin hankali sun hana Sheikh Auwal yin magana, gashi ya na son shiga ya ga halin da Husnee ta ke ciki sai dai ya na tsoron abinda zai tarar.

Amadu  direban gidan su Husnee ya shigo ya na ƙwalla sallama,  Sheikh Auwal ne ya amsa   ya na ƙoƙarin daidaita nutsuwarsa ya nufi hanyar ƙofa don ganawa da Amadu.
Musabaha su ka yi kana Amadu ya ce “Malam na ga kowane ɗalibi ya fita ne to banga Husnee ba shine na ƙaraso in tambaya ko ta yi laifi ne an tsareta?”
jim!! Sheikh Auwal ya yi kafin ya ce “Ba laifi ta yi  ba kasan yau da gobe sai Allah, larura ce ta sameta.”
Hankali tashe Amadu ya ce “To fa ikon me sama, me ke faruwa Malam?”  “Ai ba wani abin tayar da hankali bane da sauƙi in sha Allah.
Amadu ya ce “To to to, ai ba komai Allah i bata lafiya,  za ta iya fitowa mu koma gida ko?”

a hankali ta buɗe idanunta da su ka yi wani nauyi jingim kamar an ɗora musu dala da gwauron dutse,    tunanin abinda ya faru ne ya fara dawowa mata,  ba za ta iya cewa ga abinda aka yi ba don kuwa tin wannan kira da  Akhiee ya ƙwalla mata ba ta ƙara sanin abinda ke faruwa ba.

Yunƙurawa ta yi ta tashi da ƙyar jikinta duk ya hau ciwo kamar wadda aka yiwa duka da sanda.
Cikin rashin ƙwarin jiki take takawa har ta fito harabar makaranta inda malamai suke tsaye  duk sun rasa abin yi,  ganin ta fito ya sa duk suka tsaya kallonta,  Yasayyadi Usman sam bai so farkawarta ba,,   ya so rigimar ta ƙara girma ta yadda zai huce takaicin ciwon ƙirjin da Akhiee ya sa shi.

Farin ciki ne ya lulluɓe Sheikh Auwal a ransa ya godewa Allah a zahiri kuwa ya cewa Amadu “To ga ta nan ma”  Amadu ya washe baki gami da cewa “Ma sha Allahu ai da sauƙi sosai.”

Husnee dai da ta duba gabas da yamma ta ga saura ita kaɗai a cikin ɗalibai sai ta fashe da kuka, hakan ya ƙara sanya zargi a zukatan su Yasayyadi Usman.
Malam  Zaidu ya ce “Ke Husna me Akhiee ya yi miki?”  girgiza kai ta yi alamar ba komai don kuwa ba za ta iya magana ba, Amadu ne ya ƙaraso wajen ya na cewa “Sannu Husna! Sannu Innata!  Allah i sauwaƙe, mu tafi gida sai a je asibiti ko?”  ba ta kula shi ba ta fice shima ya bi bayanta da sauri, gidan baya ya buɗe mata ta na shiga ta kwanta ta ci gaba da rera kuka.

Cikin sanyin jiki Amadu ya ce “Ki yi haƙuri Innata, kanki ke ciwo ne?  kar dai wannan ɗan daban ne fa ya yi miki wani abun don na lura kamar malaman nan ba wata gaskiya garesu ba.”
Jin surutun da yake ya sa ta danne kukan nata cikin muryarta da ta yi sanyi kamar yadda jikinta ya yi   ta ce “Ba na so ka faɗa a gida cewar wani abu ya sameni, nima kaina ban san abinda ya faru ba kawai  dai na fahimci cewar na suma ne, kuma ƙila ma Aljanu ne, ni yanzu ba abinda yake damuna don Allah kar ka faɗa  za su hana ni zuwa makarantar ni kuma hankalina ba zai iya ɗaukar hakan ba”  cikin tausayawa ya ce “To shikenan ba zan faɗa ba Allah i ƙara lafiya.”
Ba ta ce komai ba sai ma ƙara yin lamo da ta yi ta na tunane-tunane.

baya……..

Hajiya Laure har su ka isa gidan Aminiyarta Hajiya Saudah masifa take zazzagawa kamar zararriya.

A falo ta samu Hajiya Laure ta hakimce  ƴar aikinta na yi mata tausa, jin muryar ƙawarta  ya sa ta fara fara’a ta na cewa “Hajiya Laure manyan ƙasa me ke faruwa ne na ji kina ta ƴan surutai tin daga nesa??  wai ma ina takabar taki?”
“Hmm!! abinda ya fi haka ma ai zan yi, bar ni da batun takabar nan a cikinta nake, amma hankalina ba zai taɓa kwanciya ba indai wanda ya kashe Alhahi Salisu ya na yawo a gari, abinda  ya sa ki ka ganni anan  neman shawararki na zo yi don ke ce kaɗai za ki share min hawayena.”
Hajiya Saudah  ta ce “A’ahh ban gane ba ina kamashi da ƴan sanda su ka yi?”  “Yo ƴan sanda ko ƴan iska?  bayan kawai kuɗina Inspector ɗinnan ya ci ƙarshe ma ashe sun sake shi?  ai cewa na yi na gaji da shigo-shigo ba zurfi gwara na zuba kuɗi a harraƙa min shi lokaci ɗaya.”
shu’umin murmushi Hajiya Saudah ta saki kafin ta ce “Ke Baraka bamu wuri.”
Miƙewa ƴar aikin ta yi ta basu wuri,  Hajiya Saudah ta numfasa kana ta ce “To yanzu ta wace hanya ki ke ganin za mu bi?”  “Ni fa wallahi ta kowace hanya ma zan iya bi,  ni fa shawara na zo nema kawai ni ki bani shawara.
“To ai in hagu ta ƙi sai a koma dama, in da dama sai a dama,  gobe in Allah ya kaimu ki shirya mu je ɗan tsibirin boka Barore,  in gaya miki ba ya tsoron Allah ko kaɗan, kashe mutum a wurinsa ƙaramin aiki ne, Wai baki ga yadda na yi damfareriya da ni ba  na yi ƙiba abina?  ai wurinsa na je neman sa’a kuma na samu, wallahi in gaya miki Alhaji Bara’u yanzu ko ɗan ciki na sai haka,  ita kuwa kishiya tini ma Allah na tuba wa ke zancenta?  tuni na sa ya saketa shegiya dangin mayu, yanzu da ga ni sai Alhajina sai ƴan ƴaƴana kar ki ga yadda yake mini biyayya  kamar ba shine me tsaurin ra’ayin nan ba.”
Hajiya Laure ta tattaɓe baki ta na matse ƙwalla gami da cew “Allah i jiƙan Alhaji Salisu bawan Allah, wallahi ya na yi min iya bakin ƙoƙarinsa ni tin wancan zuwan da mu ka yi gangare  shikenan muke zaman lafiya da shi, amma nima ina mutunta shi kuma ina yi masa biyayya, shine wannan yaron tsinanne ya kashe shi, ba ma dole hankalina ya tashi  ba fisabilillahi fa!!”
Hajiya Saudah ta dafa ƙafaɗarta cikin sigar rarrashi ta ce “Kwantar da hankalinki ƙawata, indai Boka Barore ne sai ya kashe miki ko waye ki ke son ya kashe, ke dai ki shirya gobe mu je, sannan ki tanadi kuɗi kin san ni ba ni da matsala da Alhaji ko bai sani ba na fita ma ba zai ce komai ba,  ai kina ƙoƙari ke ni ai na fi so miji ya zama shine zai nemi Aljannah a ƙarƙashin ƙafata  ba dai ni na nema a ta shi ba, kwantar da hankali bar zubda hawayenki a banza ƙawata.”
Cike da farin ciki Hajiya Laure ta ce “Na gode sosai Hajiya Saudah, wallahi  gobe za ki ji ni  da wuri ma kuwa don ba a bori da sanyin jiki.”
“Yauwa ai gwara dai”  Hajiya Saudah ta faɗa sannan su ka ci gaba da hira.

Tankar Yaƙi
farar budurwa ce  kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa,  ta na da dogon hanci da manyan idanu masu kyawu, da ɗan madaidaicin bakinta me ɗauke da lips coffee collor me duhu.
Sanye take cikin ƙananun kaya baƙaƙe, riga me dogon hannu sai matsatstsen jeans wanda ya kama jikinta sosai, P-cap  ce akanta wadda ko gama rufe murtuka murtukan kitson doka da ke kan nata ba ta yi ba, idanunta sun ji kwalli rabajau tamkar da taɓarya ta saka,  ba ko siririn abu a jikinta  da sunan lulluɓi bare batun mayafi ko hijab.

Cikin nutsuwa take takawa cike da taƙama da izza gami da jin kanta,  tura ƙaramar ƙofar dake maƙale a jikin ƙaton get ɗin kangon ta yi a sannu ta sanya ƙafarta ciki, mabiyanta na shirin bin bayanta ta ɗaga musu hannu su ka dakata.

Ciki ta ƙarasa ta na tafiya ɗagwas-ɗagwas  kamar wadda ake ce ta fito ayi zaɓen sarauniyar kyau ta Duniya.

Laita na kwance kan benci ta yi matashin kai da cinyar Zabira hannunta riƙe da taba ta na zuƙa cikin salo da ƙwarewa,  ita ma Zabira ta-ta na hannunta ta na ja ta na lumshe ido.

Kamar daga sama su ka ga Tankar Yaƙi akansu sai wani binsu take da kallon tara ahu,  Cikin hanzari Laita ta tashi daga kwance ta zauna gami da ɗora ƙafarta ɗaya bisa ɗaya ta na zubawa Tankar Yaƙi mazajen idanunta.

Zabira ce ta miƙe kai tsaye ta tinkari inda Tankar Yaƙi ke tsaye ta karye ƙugu ta cilla ƙafa ɗaya gaba ta coge ta na kallonsu,  “Ke kuma Kazar waye?  rasa hanyar gidanku ki ka yi ne??”  Zabira ta tambayeta gami da tsatstsareta da idanu.

Cikin shan ƙamshi da iyayi Tankar Yaƙi ta ce ”Babanku nake nema, Kazarsa ce ni!”
Zabira ta juya ta kalli Laita kafin su sa dariya su na binta da kallon sokunta,  Laita ta ce “Tambayeta ta rasa tunaninta ne? amma fara tambayarta waye take nufi Babanmu?”
Zabira ta ce “Kin ji abinda ta ce ko??”   Tankar Yaƙi ta ce “Sammin abar hannunki”  ba musu ta miƙa mata tabar, ta karɓa ta ɗoshana a nata bakin ta yi mata wani mugun ja ta busar  kana ta shiga takawa ɗaya bayan ɗaya,  sai da ta yi taku biyar cif sannan ta juyo ta na kallonsu, ba tare da tsoro ko shakka ba ta ce “Ina nufin SAHUN KEKE!!!!”
“Sahun Keke!!!!!”  Laita ta maimaita sunan cikin sigar tambaya.

 

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

*©️INDO*
[8/15, 2:32 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 10

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

Kafin ta ce “Ke dalla kar ki zo mana da raini mana, shi ai ba irinki bane ya na da kamun kai, ko me zai yi da ke ma ki na famar tafiya a karkace?”  Zabira ta ce “Gaggauta fita daga nan kafin mu rabaki wallahi, mara kunyar banza ƙaramar ƴar kwalta!”  wani shu’umin murmushi Tankar Yaƙi ta saki kafin ta ce “Idan ba ku san ni ba shi ya san ni, kuma ba wurinku na zo ba, ku gaya min inda yake tin kafin na shiga nemansa da kaina, koda kuwa ba ya nan zan jira har lokacin da zai dawo.”
Zabira za ta yi magana Laita ta katse ta da cewa “Ƙyaleta,   ita za ta sayowa kanta wahala barta ta jira shi, kuma yadda ta fito haka za ta koma.”
Zabira ta koma ta zauna cike da takaicin Tankar Yaƙi.

Gwaja ne ya tankaɗo ƙeyar Rabi’u su ka shigo tare, Gwaja  ya kalli Laita ya na cewa “Laita ga yaronki nan ya dawo daga makaranta!”  Rabi’u da ke ta famar haɗe rai ya ce “Ni yunwa nake ji”  Wani shegen kallo Laita ta zuba masa kafin ta ce “Zo ka yanka ni ka ci,  ko ni zan nema sannan in sayo maka abincin?  ka bada kuɗi a sayo maka mana”
Kamar zai yi kuka ya ce “To ai kuɗin nawa sun ƙare.”
Harara ta zuba masa gami da cewa “Zo nan!”  ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta, fuska a ɗaure ta ce “Da ina ka ke samun kuɗin?  ba ka ce ba ka sata ba?”
“To ai nawa ne  da su na zo.”  Gwaja ya ce “Ƙarya ka ke yi munafuk…” ɗaga masa hannu ta yi kana ta ce “Je ka duba min kuɗin da  nake ajiyewa a ɗakin kwanansa.”  Bai ce komai ba ya juya ya nufi ɗakin, Rabi’u kuwa ya yi wuƙi-wuƙi da ido duk ya tsorace.

Ba daɗewa Gwaja ya dawo ya sanar mata  ba sa nan,  ta kalli Rabi’u  kamar za ta dake shi ta ce “Fito mini da kuɗina ko na harraƙa ka!”  hawaye ya goge gami da cewa “Allah i baki haƙuri, wallahi idan na ji yunwa  ne ki ka ce  na kawo  kuɗin abinci sai in ɗauka a cikinsu kuma yanzu sun ƙare.”
Gyara zama ta yi kafin ta ce “Ka san Allah sai ka biya ni, in ba haka ba me rabani da kai sai Allah,  kuma ba me baka kuɗin Abinci  sai dai ka nema da kanka,  ai ba ka san darajar nema ba shi  yasa ka ke almabazzaranci da kuɗi har ka ke yin sata.”  fashewa ya yi da kuka ya na bata haƙuri ita kuwa ta ce ba ta san zance ba. sai da ya ga ba za ta tausaya masa ba ya ce “A ina ake neman kuɗi to?”
ta ce “Yanzu ka yi magana, ka ga waɗancan ciyayin?  maza ka je ka dinga fige su ka na haɗa mini su wuri ɗaya,  sai ka yi cikin hannu biyar zan ba ka Naira biyar, adadin yawan da ka tara adadin kuɗinka, idan ba ka yi ba kuma ba ka da Abinci, sai dai ka mutu, kuma da haka za ka biya ni kuɗina  ko na yanke maka hannu”.
Zuwa yanzu ya gane ba ta da imani ko na kobo, don haka ya tashi jiki na rawa ya fara tsigar ciyayi, ya na yi     ya na kuka sabida yunwa da takaici da su ka haɗar masa.

Sai a lokacin Tankar Yaƙi ta magantu da cewa “Ke wallahi anyi mara imani, yanzu wancan ɗan  yaron ne ki ke yiwa irin wannan, nawa ne kuɗin naki ni in biyaki?”   Kallon sheƙeƙe Laita ta yi mata gami da cewa “Da wace kamar??  ke kina ganin ki na da kuɗin da za ki iya biyana ne? ai duk danginku ba me iyawa bare wata ke.”   A fusace Tankar Yaƙi ta ce “Kar ki yi mini rashin kunya fa, wallahi na fi ki dattin ƙwaƙwalwa.”  maida kallonta ta yi kan Rabi’u gami da cewa “Kai zo ka karɓi kuɗi ka ƙyale wannan Ƴar balaja’un”  Laita ta murmusa gami da cewa “Maza zageni lokacinki ne”
Rabi’u kuwa ya zo da gudunsa ya karɓi kuɗin ya na murna, ko gama jin ɗuminsa bai yi ba Laita ta kira shi ta ƙwace su, bai gama tunanin abinda za ta yi ba ya ga ta yaga su gutsi-gutsi ta watsar, ai kuwa ya ƙara fashewa da kuka, tin kafin ta yi magana ya tashi ya ci gaba da aikinsa.

Rai ɓace Tankar Yaƙi ta ce “Ni za ki yagawa kuɗi?  amma ba komai ku ci gaba wallahi indai na Auri Rissy za ku ga wulaƙanci da rashin mutunci duk sai na ƙasƙantar da ku”  Dariya su ka sanya harda tafawa,  daidai lokacin  Salansa ya shigo ya na cewa “A gyara hanya  me gayya ya shigo”  Laita ta na jin haka ta fashe da kuka, ita kuma Zabira ta zuba tagumi ta yi wani kalar tausayi kamar itama za ta fashe da kukan.

Tankar Yaƙi dai sabida mamaki kawai ta saki baki ta na kallon ikon Allah don ta zata ma Aljanu garesu.
Har zai wuce ya ji ba wadda ta tanka masa ga sautin kukan Laita ya na ji don haka ya tsaya  ya na zuba musu idanu,  sai lokacin ya lura da Tamkar Yaƙi da ke tsaye hannayenta riƙe da ƙugunta, “Me yake faruwa ne?”   ya tambayesu Laita ta ƙara sautin kuka, Zabira ce  ta murje ido sannan ta ce “Wannan Matar ce ta zo wai ita Kazarka ce, don mun ce ba ka nan shine ta  zazzage mu, nima don dai ina da  juriya ne da tuni na fara kukan don zagin ƙare dangi ta yi mana”  ta ƙarasa maganar tana tattaɓe baki.

Ransa in ya yi dubu ya ɓaci, maida kallonsa ya yi kan Tankar Yaƙi da ta kasa rufe bakinta,  lallai yau ta shigo inda aka fi ta makirci, tunanin da take yi kenan,  ya katse ta da cewa “Abin naki ya wuce kaina ya koma kan Iyalina kenan?”  da sauri ta ce ”Wallahi ko ɗaya, ni fa ba abinda na yi musu ka tsaya ka saurare ni.”
“Ina ƙyale ki ne kawai sabida ke macece, ki fita kafin  na yi miki illar da ba za ki ƙara taka ƙafarki ba.
Cike da ɓacin rai ta ce “Na ji, zan fita amma sai lokacin da na ga dama tinda ba kai ka kawo ni ba,    nifa wallahi duk abinda za ka yi mini ina sonka ba zan fasa ba sai dai in ba na numfashi,  don ma ina  son naka shine ka ke wani jiwa mutane  kai, duk abinda ka ke taƙama da shi nima ina da shi, kuma ka sa a ranka ba za ka taɓa Aurar wata mace bayan ni ba,  duk wadda ta so ka ma sai na kasheta kuma na kashe banza.
“Ki kasheta mana idan za ki iya, kuma idan ba ki kasheta ba ni zan kashe ki,  fice mini da gani shashasha”  ya yi maganar cikin ɓacin rai da takaici.

Dogon tsaki ta zabga kafin ta ce “Kar ka yi zaton ƙyale ka na yi, zan dawo, ku kuma waɗannan munafukan  ku kuka da randa za ku shigo hannuna.”    ta na kaiwa nan ta fice cikin sauri kamar me shirin tashi sama.

Risslan kuwa bai bi ta kansu ba ya wuce ɓangarensa cike da takaicinsu     da su da suka tsaya yi mata kuka da ita tsagerar.”

Yana barin wurin Laita ta goge hawayen ta na cewa ”Ita ƙaramar ƴar bariki ce, ni sabida tsabar makircina aka raɗa min Laita, kuma wallahi in ba ta yi a sannu  ba  sai mun sa ya kasheta.”
Zabira ta ce “Wa yake ta  ta-ta ma    har me akai aka yi ta? ai bigi sai bigi.”  Gwaja ya ce “Na tsorata da ku mutanen nan”  Laita ta murmusa gami da cewa ”Kaɗan ma ka gani”  hira su ka ci gaba da yi akan ta yadda za su koya wa Tankar Yaƙi hankali, kowa na bada ta shi shawarar.

Hajiya Laure
Kamar yadda ta faɗa tin wuri ta shirya ta nufi gidan Hajiya Saudah daga nan su ka rankaya zuwa wajen boka.

Ƴar bukka ce wadda tin daga waje ma za ka gane ba alkairi ake shukawa a cikinta ba  duba da yadda aka yi mata ado da ƙashushuwa da kawuna ƙwarangwal-ƙwarangwal  na dabbobi iri-iri.

Hajiya Laure ce ta turje ta kasa shiga, a tsorace ta ce “Hajiya Sauda wai ki na ganin abinda nake gani kuwa??  ni fa gaskiya ba kowane boka na yarda da shi ba, ki zo mu koma don ba na son wanda garin na cutar da wani ni sai ya cutar da ni”   Hajiya Saudah ta ce “Ai kin ji inda ki ke bada mata wallahi, to bukkar boka barore ba a shiga a fito ba nasara kuma ki yi tambaya ga waɗanda su ka san shi ki ji,  komai wuyar aiki inda kin kawo shi wajen boka barore kin gama.”
Hajiya Laure za ta yi magana karsanar muryarsa mara daɗin ji ta karaɗe kunnuwansu,  “Shaiɗanun Aljanu sun yi marhabin da zuwanku!!, ku ƙaraso ciki!!!!!!,  ba a zuwa tsibirinmu a koma haka nan dole sai an gana da mu in ba haka ba a hau-kace!! hhhhh”
Hajiya Saudah ta ce ”To kin ji kaɗan daga cikin sharuɗansa gwara ma ki nutsu.”  jan hannunta ta yi kiiii su ka danna kai ciki.
Duhu gami da wata irin guguwa me ƙarfi  su ka gauraye bukkar, kwata-kwata ba  a ganin komai sai ƙarar guguwar wadda iyakacin cikin bukkar ta karaɗe,  Hajiya Sauda da Hajiya Laure su ka haɗe kai su ka ƙanƙame juna.

Guguwar ta kai tsawon minti guda 1 har da ƴan sakanni ta na juyawa sannan ta tsaya cak, wani jan haske ya tsago daga jikin bango sai ga boka Barore tsubul a zaune, sai kuma haske ya dawo daidai.
a tare su ka numfasa musamman Hajiya Laure  da ta yi tunanin abinda su ka zo shukawa ne ya fara tsiro ta kansu, ashe haka salon yake.

“Boka Barore ya bada damar a zaunahhhhh!!” boka barore ya faɗa  ya na dariya.
Zama su ka yi a ɗan nesa da shi cikin rawar baki Hajiya Laure ta ce “Sannu da aik…” kafin ta ƙarasa ya katseta da cewa “Ba a zama nesa da mu, a dawo gabanmu a zauna”  da sauri su ka ƙarasa can gabansa sannan su ka zauna su na fuskantat juna, ƙare musu kallo ya yi kafin ya ƙyaƙace da wata mahaukaciyar dariya da ta sanya su ka tsargu da kansu.

“Kin zo akan batun wani yaro me suna Muhammadu wanda ya kashe miki miji,  wannan Yaro ba zai taɓu ba  sam! hhhhh”  ya ƙara kecewa da dariyar mugunta.
Kallon kallo Hajiya Laure da ƙawarta su ka yi kafin Hajiya Saudah ta ari baki ta ce “Boka Barore, ka na nufin mun zo a banza kenan  ba yadda za ayi mu ci galaba akansa?”
cikin tsawa ya ce “Keh!! wa ya gaya miki ana zuwa tsibirinmu a tafi ba biyan buƙata, dole ne sai mun yi masa illa,   za mu taɓa shi ta hanyar waninsa, wanda in aka taɓa shi zai ji ciwon.”
Hajiya Laure ta ce “To ai  inaga ma  ba shi da mata  bare ƴaƴa.”

“Ya na da ƴaƴa da yawa, ya na da ƴan uwa da yawa,  ya na da mutane da yawa,  nasara ta sameku!!!!  Dole ne sai mun cutar da shi,,,  za mu zami inda ya kamata mu tura ƙullinmu,  ku ajiye kuɗi ku tashi nan da kwana uku ku dawo mini da kyakkyawan labari¡¡¡¡”
jiki na rawa Hajiya Laure ta zaro ta dire masa ta miƙe ta na cewa “To mun gode Boka!”  “Tsaya!!! a fita da tsalle!!!! wannan dokar baƙin Aljanin da zai muku aiki ce”
Da ƙyar su ka iya kai kansu bakin ƙofa da tsallen sabida nauyin jikinsu dukkansu akwai ƙiba ba siririya.

Sai da suka fita su ka yi ta maida numfashi, musamman Hajiya Laure ta fi shan wahala don ta fi Haj Saudah ƙiba.
Haka su ka dawo gida cike da murnar yin nasara da su ka yi.

Wuni da kwana Boka Barore ya yi yana fafata aiki har ya samu nasarar haɗa mugun tsafinsa kuma ya tura.
Akhiee   haka kawai ya tsinci kansa da son zuwa makaranta, ba tare da wani ya sa shi ba ya shirya ya je   sai dai ko aji ya ƙi shiga, har aka tashi Husnee ta zo ta same shi nan a tsaye,   tinda ta fara yi masa surutu bai ce ko kanzil ba har ta gaji ta yi shiru.
Sun ɗauki lokaci a tsaye ba me yin magana sannan Husnee ta katse shirun  da cewa “Za ka ci Ayaba?.”

Akhiee ya na tsaye  a bakin wata ƙorama ya zubawa farin ruwan da ke gudana a cikinta ido, zuciyarsa kawai ƙuna da raɗaɗi take yi, tunanin me tsaurin idon da ke ƙoƙarin turo masa tsafi yake sai dai a iya nazarinsa ya kasa gane kowaye.
Ya na cikin tunanin ya ji gurnanin Zaki a bayansa, juyawa ya yi ya na kallon Zakin wanda shima shi yake kallo,  nan fa su ka shiga yiwa juna  kallon-kallo  kowa na ƙara fusata, Zakin ya yi wani huci gami da gurnani ya girgiza ya yo kan Akhiee da wani mugun gudu.
Tsintsiyar hannunsa  duka biyun ya sa ya kare fuskarsa tare da tsayawa kyam ya miƙa wuya ya saduda don kuwa bai san yadda zai yi ba sai dai abinda Allah ya yi.

Wata muguqar kwasa ya yi masa ya bangaje shi su ka faɗa cikin ruwan tare, ko shurawa Akhiee bai ƙara yi ba tuni ya nutse a cikin ruwan ko alamunsa babu, Zakin ya yi wata girgiza gami da yin sufa ya yi gefe………

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

*An fara Payment🤸🏾‍♀️ ku ƙoƙarta ku mallaki naku*

*©️INDO*
[8/17, 11:44 AM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 11

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

Zakin Ya na direwa a gefe ya zamo mutum, kamanninsa da tsayinsa da komai irin na Akhiee ne sak har kayan jikinsa, dariya ya yi hakan ya ƙara fito da tsantsar kyawunsa, cike da zolaya ya ce “Yau duk ina zafin kan naka?”
Daidai lokacin Akhiee ya yo fitar burgu daga cikin ruwan tare da wurgo masa wata sharɓeɓuyar wuƙa fara tarr  sai ƙyall da ɗaukar ido take, cikin hanzari ya yi gwauron tashi ya dire a gefe har lokacin dariya yake yi wadda take ƙara dugunzuma zuciyar Akhiee,  jikinsa har kakkarwa ya ke yi sabida ɓacin rai,  “Na rantse da Allah   Russlan ka bari na kamaka sai na kakkarya ka, na gaya maka ba na son wasan banzan nan naka ko?  ka barni da abinda yake damuna amma ka zo  ka na ƙara tunzura ni;   za ka sa na yi ɓarnar da ba za ta yiwa kowa daɗi ba wallahi.”
Ya yi maganar ba tare da alamun wasa ba,  jin haka ya sa Russlan ya dakatar da dariyar, cikin sigar rarrashi ya ce “Yi haƙuri mana, ai abin bai yi zafi haka ba,  ni ban san ranka a ɓace yake ba Allah i baka haƙuri jarababbe.”
jin ya kira shi da jarababbe ya sa ya ƙara hassala, ya buɗi baki zai ƙara zaro wata maganar Mother ta iso wajen,  cikin yanayinta na kamala ta ce “Russlan ba ka san cewa ɗan uwanka ya faɗo daga sama ba ne?  jikinsa na ciwo shine za ka ƙara zuwa ka tayar masa da hankali?”  ido Russlan ya zazzaro gami da cewa “Da gaske?  sannu Brother!”  dogon tsaki kawai Akhiee ya doka ba tare da ya ce uffan ba,  Mother ta kama hannunsa ta zaunar da shi gefe,  Towel ta sa   ta na tsane masa gashin kansa wanda ya sauka a gadon bayansa,  fuskarta ɗauke da lafiyayyen murmushi kamar kullum, cikin sassanyar muryarta ta ce “Me yasa za ka faɗo daga sama haka? Domin wannan Yarinyar ne?”  Ƙasa ya yi da ido kafin ya ce “Mother! sabida ni ne hakan ta faru, da ace ban je makaranta ba ma     da Allah ne kaɗai ya san abinda zai faru da ita,  Tsafi ne aka turo, kuma don ni aka turo shi amma ya tafi zai faɗa kanta, shine garin na janyeta na taka ɓawon ayaba sai muka faɗo,  amma mutane gani su ke yi kamar wani abu na yi mata ko kuma ina sane na jawota”  Mother ta jinjina  kai alamar gamsuwa sannan ta ce “Amma me yasa ta suma?”   “Ohh my god!” ya faɗa gami da dafe goshinsa, Mother ta lura tambayar ta-ta ce ba ta yi masa ba don haka ta ce ” Please tell me my son”  “It’s not my fault,  kawai zafin tsafin ne ya taɓa ta shine ta suma,  na rasa gane me hakan yake nufi Uwa!”
murmusawa ta yi kafin ta ce “Da sannu-sannu za ka gane,  ka kula da kanka.”
Russlan da ke zaune ya zuba musu ido sai a lokacin ya ce “To wai ma Uwa!  har akwai wanda ya isa?  na yi mamaki da jin hakan gaskiya.”
Mother ta ce “Ba abin mamaki bane;,   Risslan ka zo mu je ciki ka huta na san ka na buƙatar hakan.”
Bai ce komai ba ya miƙe ta na riƙe da hannunsa su ka wuce cikin tafkeken gidansu.

Husnee
Tinda ta koma gida ba wanda ta saurara ko da Mommy ta tambayeta abinda ya faru da ita sai ta ce ba komai don haka Mommyn ta zuba mata ido.
Toilet ta wuce ta haɗa ruwan zafi  me zafi sosai ta yi wanka sannan ta fito, doguwar riga mara nauyi ta saka  kana ta koma kan gado ta duƙunƙune, jikinta ko ina ciwo yake  amma da ta yi wankan ta ɗan ji sauƙi.
Khausar ce ta shigo ta na cewa “Anti Husnee  wai ba za ki ci abincin ba?”  kamar za ta yi kuka ta ce “Ke dalla na ƙoshi”  Khausar ta ce “Wallahi ba ki da lafiya, dole ma ki ga likita bari Daddy ya dawo.”
Husnee ba ta ce komai ba don maganar ma ba son yi take ba.
Sai da aka yi kiran Sallar magrib sannan ta fito ta ɗaura alwala,  Yaya Muneer ne ya dubeta a tsanake ya ce “Ya jikin naki?”  da sauri ta ɗago ta na kallonsa a ranta ta na tunanin ”Wai ce musu aka yi ba ni  da lafiya?”  a zahiri kuwa cewa ta yi “Da sauƙi”  Yaya Muneer ya ce “Ba ki da lafiyar amma ba za ki faɗa ba sabida Allura ko?”  da sauri ta girgiza kai alamar a’a,  kafin ya yi wata maganar tuni ta gudu ɗaki.

Bayan an idar da sallar isha’i ta na zaune kusa  da Mommy, duk sauran yayyenta dake Parlon  su na hira da raha amma banda ita.
ta yi nisa a duniyar tunani Ahmad ya yi sallama, ko zama bai yi ba ya ce “Ina Me hawaye  ba kukan nan?,  ya jikin?”  ya yi maganar ya na dariya.
Zumɓuro baki ta yi gami da cewa “Ni fa lafiyata ƙalau.”
Yaya Muneeb ya ce “A’a gaskiya dole akwai wani abin da ke damunki,  ke da surutu kuma har a zauna hira ba  ki ce komai ba?”  Ahmad ya ce “Ku ƙyaleta ƴar zafi ce ta isheta, ai an gaya mini abinda ya sameta.”  Daddy ne ya dube shi a nutse ya ce “Zauna Ahmad”   zaman ya yi a kan carpet ya na ƴar dariya ƙasa-ƙasa ya na kallota gami da yi mata gwalo,  ita kuwa hankalinta duk ya tashi, fargabarta ɗaya a faɗi wani abinda zai sa su gane cewa ta gama yin zurfi a cikin shishshigewa Risslan.

Daddy ya ce “Nutsu ka gaya mana abinda ya faru da ita, ba ma son shiririta.”
Ya ce “To Daddy, maganar gaskiya ko me ta ce ƙarya ta ke yi, daga saman makarantarsu ta faɗo, ba ma fa daga ƙafar bene ba daga can sama, in gaya muku gaskiya  gwara ku kaita National Orthopaedic Hospital  ta cancanci ganin likitan ƙashi.”
Ido warwaje Mommy da Khausar su ka furta “Daga sama???”  Ahmad ya ce “Ƙwarai kuwa ga ta nan ku tambayeta.”
Mommy ce ta kama hannunta gami da cewa “Ke tashi in ganki, ai wallahi da gaskiyar Ahmad gaba da Orthopaedic ma sai a kaita.”  Husnee ta miƙe kamar za ta yi kuka ta na cewa “Ni fa ba na jin komai kawai ciwon jiki na ke ji kaɗan.”
Ba wanda ya tanka mata sai ma ido da suka zuba mata, Mommy ta ce “Taka in gani, jeki kusa da Ahmad ki dawo.”  ba dan ta so ba ta taka zuwa inda ya ke don dai kawai ta na son tabbatar musu ƙalau take.

Ganin  ta na tafiya sak! ba alamar ciwo ko buguwa ko ɗingishi    ya sa Ahmad cewa “Kai anya kuwa Daddy yarinyar nan Aljanu ba su shafeta ba?  ka ga ƴar da ta faɗo daga sama? tangaras abinta ko targaɗe babu?  wallahi ni Aliyu cewa ya yi mini da ta faɗo ma suma ta yi sai daga baya ta farko amma kalleta don Allah.”  Daddy ya numfasa kafin ya ce “Kai fa Ahmad akwai ka akwai shiririta, wane irin Aljanu kuma ana zaune ƙalau?”  Ya Muneeb ya ce “Abin dai da alamar tambaya akai, daga kan keke ma idan mutum ya faɗi jiki yake ji bare ta faɗo daga sama amma ta miƙe garau”  Ya Muneer ya ce “To ai ma abin tambayar anan shine, asali me ya gusar mata da hankali har ta faɗo daga sama?  ko tsokanar wata ki ka yi ta ɗebeki ta watso?”  girgiza kai ta yi alamar a’a  Mommy ta ce “Ni dai barkana, tinda ƙalau take ai ta kwana gidan sauƙi,  mu ga hannunki”  ta faɗa ta na miƙa mata nata hannun,  ba musu ta miƙo duka hannayen nata, Mommy ta mammatsata   ta ji dai ba ta yi ko gezau da sunan an taɓa mata inda ke mata ciwo ba, sakinta ta  yi ta na cewa “Ikon Allah,  Allah ya tsareki Husna”  Khausar da ta saki baki ido da hanci ta na bibbinsu da kallo sai lokacin ta ce “Gaskiya ke ƴar baiwa ce Aunty dama ni ce”  Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya ya na cewa “To Bugun la’asar,  ke daɗina da ke muguwar tafki ce,  ta faɗo daga saman ki ce dama ke ce? to idan ke ɗin ce  ki ka faɗo kuma ki kwararraɓe fa?   ita ɗin ma ƙila Aljanu ne su ka shafeta.”
Zuwa yanzu surutan nasu sun fara ɓatawa Daddy rai, a tsawace ya ce “Kar na ƙara jin wani ya ce wai Aljanu gareta!   ku ba ku san kiyayewar Allah ba?   sau nawa ake yin haɗari har wasu su mutu amma a ciki sai ku ga wasu ma abin bai shafesu ba kamar ba sa ciki, amma don ta faɗo daga sama ba ta ji ciwo ba sai ku ce Aljanu ne?  ba ku san cewa Allah na kare bayinsa ba?  ya kuke abu kamar ba musulmi ba?”
Ahmad ya ce “Ayi haƙuri Daddy mun dena.”
Husnee kuwa komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ƙara bi takansu ba.

Washegari ba wanda bai yi mamakin ganin Husnee ta dawo makaranta ba don a zatonsu ko za ta kuma zuwa sai bayan ta yi doguwar jinya, sai kuma su ka ganta katsam, su kansu malaman sun yi mamaki, su Yasayyadi Usman ɗaya bayan ɗaya sai tambayarta su ke yi abinda Akhiee ya yi mata, ita kuwa gaskiyarta take faɗa musu cewar ba ta san abinda ya faru ba dole su ka gaji su ka ƙyaleta.

Yamma ce liƙis…..
Tankar Yaƙi da Abokananta su na zaune a wani fili wanda suke kira Bakin Kwalta, anan su ka saba zaman shaye-shaye da hira. yau ma kamar kullum kowa na  shan abin mayen da ya fi yi masa daɗi amma banda Tankar Yaƙi gabaki ɗaya ta kasa yin komai hankalinta ya tafi akan tunanin Risslan.
Ɗan Kurada ne ya lallaɓo kusa da ita ya zauna, cikin murya  me cike da maye ya ce “Meke faruwa ne Ta gidan Oga?  waye ya taɓa mana ke mu taɓa shi?”  kallonsa ta yi ta kawar da kai sannan ta ce “Tunanin wanda na ke so na ke yi, Wai Ɗan Kurada akwai  wani abun kushewa a jikina??,  shin me yasa Risslan ba ya sona?  me yake so a wurin mace wanda Allah bai ba ni ba?”
Ɗan Kurada ya wulƙita idanunsa da suke wani galmi-galmi kafin ya ce “Ba abinda ba ki da shi ta gidan Oga!!,  amma fa ina ga zaren ne ba kalar yadin ba, kin san Oga na sonki fa amma ke kuma ki na son Abokin gabarsa, anya ki na ganin hakan zai yuwu?”
shiru ta yi ta na ɗan nazari na ɗan lokaci sannan ta ce “Ɗan Karada!!! ni fa gaskiya zan iya rabuwa da Dodo akan Sahun Keke, kuma kai ma ka sani gabar da ke tsakaninsu ce ta sa na san shi ma har na ji na kamu da son shi,  ko fa me za’ayi sai dai ayi amma ni ba zan bar abinda nake so ba, kuma wallahi indai ka ga bai aureni ba to ko shakka babu zai mutu ba aure don duk wadda ya so ko ta so shi sai na rabata da ranta.”
Ɗan Kurada ya yi dariya me isarsa sannan ya ce “Za ki aikata ta gidan Oga!!  ni ina bayanki ki yi yadda ki ke so wallahi mun ɗaure miki abin.”
Murmusawa ta yi a ranta ta ma ƙissima abubuwa iri daban-daban.

Jiki na ɗari-ɗari IP Khalil ya amsa kiran DCP Khashim Bello, don kuwa ya san kwanan zancen, shi kuwa abu  ya fara fin ƙarfinsa, da kyar ya ce “Hello!”  a ɗaya ɓangaren DCP ya ce “Na kasa samun kyakkyawan labari daga gareka,  in ce dai ba ka manta ɓarnar da Muhammad Muhammad ya yi mana  a kwanan nan ba, JD ya fusata  iya matuƙa  kuma ba abinda ba zai yi ba akan wannan dukiya ta shi da aka ƙona,  bayan haka ma yanzu duk harkokinsa sun tsaya sabida takurawar wannan yaro,  ya hana shi shigo da kaya ta kowace hanya sannan shi kuma  ya na shigo da Wiwi ɗinsa ya na sayarwa,  wai duk zaman me ka ke yi hakan ta ke faruwa?”
miƙewa ya yi ya na takawa cikin sigar rarrashi ya ce “Ayi mini uzuri yallaɓai, ba dare ba rana idanuna na kansa  kuma ina nan zan yi maganinsa don Allah a ƙara bawa JD haƙuri kwanan nan zan yi iya ƙoƙarina, zan kama shi a matsayinsa na Dilan Wiwi kuma dole doka za ta yi aiki akansa.”

“Hahahaha!”  DCP ya yi dariya sannan ya ce “Wanda ba ya bin doka ai ba amfanin binsa a dokance,  yanzu ba ta doka za mu bi shi ba, za mu yi masa zagon ƙasa ne ta yadda sai ya ji zaman duniya ma ya ishe shi, JD  ya riga ya fusata kuma ya zuba kuɗi ayi masa aiki akansa, cikin kwanakin nan za mu ji kyakkyawan labari, kwantar da hankali Inspector Ibrahim Musa Rano,  sai ka ji ni”  daga haka ya katse kiran,  murmushin farin ciki ne ya buwaya a fuskar IP Khalil ba ƙaramin daɗin albishir ɗin ya ji ba, ko ba komai shi yanzu zai samu kyakkyawan bacci shi kuwa Risslan lokacin nasa baccin ya ƙare.

Tin ranar da su ka faɗo daga sama Akhiee bai ƙara ziyarta makaranta ba har sai da ya yi kwana tara.
Husnee kullum zuba ido ta ke yi ko za ta ganshi sai dai har rana ta fito ta koma ga ubangijinta ko me kama da shi ba ta gani,  gashi idan ta tambayi Zara sai ta ce itama ta daɗe ba ta sanya shi a idanunta ba.  duk ta shiga damuwa har wani ɗan zazzaɓi take yi, ta yi wata ƴar rama ta yi wuƙi-wuƙi da ita.

Yau  ta sa a ranta indai bai zo ba ita ma ta dena zuwa makarantar sai bayan wani lokaci.
haka nan take zaune cikin aji sukuti, karatun ma ba wani yi take ba,  sai da aka fita sallah ta ɗan ji dama-dama,  tare da Asiya su ka fito daga aji ta na riƙe da hannunta sabida ɗan jiri-jiri da yake ɗibarta sakamakon yawan tunanin da take yi, kamar ance kalli sama ta ɗaga kai ta na kallon inda ta saba ganinsa  ai kuwa  ta yi tozali dashi, ya na sanye cikin manyan kaya shadda ruwan toka me haske da hular Zanna bukar haɗaɗɗiya me ratsin ruwan toka,  kam ta riƙe Asiya yayin da idanunta ke kan Akhiee  mamakin yadda ya yi mugun kyau a cikin irin shigar ya kamata ga tambaya da take yiwa kanta “wai dama ya na sa manyan kaya irin wannan?”  Asiya ce ta ankara da hankalinta ba a jikinta yake ba dalilin magana da take ta yi mata amma ta ji shiru, ɗaga kai ta yi ta kalli inda ta ga ta na kallo itama idanunta su ka yi alaragab da Akhiee  nan take zuciyarta ta bada wani ɗurum!!!!!!!,  cikin dubara ta zame jikinta ta ture Husnee wadda har lokacin kanta a sama yake, ba ta ce mata ƙala ba ta zame ta yi nata wuri.
kamar wadda aka saukarwa ayar zuwa inda yake ba tare da ta sani ba ma ta fara tafiya ta na yi ta na kallonsa kamar ance in ta ɗauke ido zai ɓace.

Sai da ta dangana da shi sannan ta dakata ta na  ƙara ware masa idanunta da su ka yi zuru-zuru ko kwalli babu.
Ya na ankare da  zuwanta amma ko kallonta bai yi ba.

Cikin sassanyar murya me kama da shagwaɓa ta ce “Akhiee! me yasa ba ka zuwa makatanta,  hankalina ya tashi da rashin ganinka gashi ban san halin da kake ciki ba, don Allah ka dena ƙauracewa ganina, idanuna da zuciyata ba sa gajiyawa da kai, don Allah Akhiee ka dinga zuwa makaranta kullum”
White Diamond Watch dake hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba tashin hankali “Asma’u! Please it’s time for prayer, i’m going to the masque”
“Please Akhiee you Listen to me!”  ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka………..

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

 

*©️INDO*
[8/17, 1:12 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 12

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

“Ƴan Daba ne su ka sassari Akhiee jini sai Zuba yake a jikinsa amma ya ƙi yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru akansa, har babban yayanmu ma ya zo amma ya ƙi Amincewa kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ƙarewa”
Ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me imani.
Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje.
Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da’ira wanda yawancinsu yayyensa.
Ya na tsaye ya jingina da bango  sai ƙasa-ƙasa yake da idanunsa da su ka ƙara wani irin haske ƙwayar idon ta ƙara rikiɗa ta yi baƙi siɗik, fuskarsa ma kanta ta yi jawur sabida tsabar zafin rai da kuma azabar da yake ji a jikinsa, ganin yadda jini ya jiƙa shaddar jikinsa me ruwan toka ta koma ja ya sa Husnee fashewa da kukan da sai da ta sa shi ɗagowa ya zuba mata ido,  ba ma shi kaɗai ba duk mutanen wurin idanu su ka zuba mata cike da mamakin tsaurin ido irin nata,  ba su gama firgita ba sai da su ka ji Tassss!!!!! ƙarar marin da ta sheƙa masa ya karaɗe kunnuwansu, cikin shashshekar kuka ta ce “Akhiee me yasa ba ka san ciwon kanka bane!!!?  don me ba za ka je asibiti ba ka na fama da wannan rauni a jikinka?”
Cikin muryar da ke fita ƙyar ya ce “Asma’u!  ki ƙyale ni  ko mutuwa na yi ba su da asara tinda ba ƙaunata su ke yi ba.”  cikin tsananin ɓacin rai ta daki ƙirjinsa cikin tsawa tace “Ƙarya ka ke yi Akhiee!!!  wanda ba ya ƙaunarka ba zai so lafiyarka ba!!, yanzu duk wannan tashin hankalin da su ka shiga ka na nufin ba ƙauna bace??  wallahi tallahi indai ba ka je ba nima sai na ji wa kaina,  idan ka mutu kai ka tafi kenan mu za ka bari da tunaninka!!!!”  ta ƙarasa maganar gami da fashewa da wani sabon azababben kukan,  “Asma’u  ba zan iya ba  ki ƙyale…”  ba ta bashi damar ƙarasa maganar ba ta ƙara kwarfa masa wani shegen mari wanda ya sa ganinsa ya ɗan ɗauke na wucin gadi,  kamar za ta yi hauka ta ce “Kar na ƙara jin zancen banzar nan a bakinka! in ba haka ba zan yi abinda ba zai yi maka daɗi ba wallahi.”  sassautawa ya yi kafin ya ce “Asma’u Calm down cuta fa ba mutuwa ba ce, amma ba na so ki cutu sabida ni, zan so a ce kin rabu da ni kawai”
“In dai ka na so hankalina ya kwanta ka bi ƴan uwanka su kai ka asibiti, in ba haka ba nima….”  katseta ya yi da cewa “Na yarda zan je  amma ki gaggauta tafiya gida.”
Daga haka ya raɓe ta kusa da ita ya wuce,  a kusa da Sheikh Auwal ya tsaya ba tare da ya kalle shi ba ya ce “Mu je”  Sheikh Auwal ya riƙe hannunsa  su ka nufi wajen mota, su Yasayyadi Jameel da IP Khalil wanda aka gaiyato tin ɗazu su ka mara musu baya.

a wurin Husnee  ta zube ta na ƙara sakin kuka me tsuma zuciya.
Zara ce ta dafa kafaɗar ta na ƙwalla ta ce “Na gode Husnee kin temakemu ba don ke ba na san ko me zai same shi ba zai taɓa yarda ya je ba,  ki tashi ki tafi gida ki dena kuka anan kin ga mutane su na kallonki.”

Husnee ba ta iya cewa komai ba sabida kukan da take yi,  sai da Zara ta yi da gaske sannan ta yarda ta shiga mota Amadu ya ja su ka nufi hanyar gida.

har su ka isa ba ta dena kukan ba ta na shiga gidan ta wuce ɗaki ta faɗa gado ta ci gaba da abinta,  Mommy da hankalinta  ya gama tashi ta yi mata tambayar duniya amma ta yi banza, jikinta ya yi sanyi  tuni ta fara tunanin ko dai da gaske Aljanu ne su ka shafeta.
Tunanin Amadu Direba ne ya faɗo mata don haka ta yanke shawarar tambayarsa,  ya na zaune ya yi jugum akan ɗan bencin me gadi ta iso wajen cikin sanyin jiki,  gaisheta ya yi ta amsa ba yabo ba fallasa  kana ta ce “Na ga Husnee ta shigo gida ta na ta kuka, na yi tambayar duniya ta ƙi yi mini magana.”  Amadu shima kamar zai fashe da kukan ya ce “Wallahi Hajiya tashin hankali ta gani wanda dole ta yi kuka,  ko ke Hajiya in ki ka gani ƙila sai kin yi hawaye don mata kuna da rauni sosai.”  hankalin Mommy ne ya ƙara tashi, ta zaro idanu gami da cewa “Me ya faru ni Salamatu!”
Amadu ya ce “Hajiya Yaron masu makarantarsu ne  ƴan daba su ka sassare shi, kar ki ga yadda su ka yi masa jina-jina amma sabida zafin rai da gardama yaron nan  sai ya ƙi a kaishi Asibiti,  da kin ganshi kin san ya galabaita amma wallahi sabida taurin kai irin na ɗan daba sai ya ƙi,  in ki ka ga jinin da ya zubar za ki koka masa Hajiya.”
Mommy ta ce “Ikon Allah,  Allahu Akhbar Allah i bashi lafiya, kowa dai da irin ƙaddararsa shi kuma irin ta shi kenan!  Allah ya bi masa haƙƙinsa in cutarsa su ka yi.”
Amadu ya ce “Amin Hajiya”  jiki ba ƙwari ta koma cikin gidan,  wajen Husnee ta koma ta zauna gefenta ta fara rarrashinta gami da kwantar mata da hankali.

Ba su suka dawo gida ba sai ƙarfe 11:00 na dare, a hakan ma gado asibitin su ka so ba shi amma ya tubure ya ce indai su ka kwantar da shi duk sai ya ƙarasa sauran marasa lafiyan da suke tare  jin haka ya sa su ka tarkata shi su ka dawo da shi gida.
Sheikh Auwal da Zara ne su ka gyara masa Ɗakinsa su ka yi masa kyakkyawar  shimfiɗa  gami da ajiye masa abubuwan ciye-ciye na marmari kala daban-daban sakamakon jinin da ya zubar.
Sauran mazan kuwa duk sun watse sai matayensu da matan Abhi da kuma sauran ƴan uwan nasa su ke ta leƙo shi, wasu su ce Allahi i sauwaƙe wasu su yar masa da magana su yi gaba.
Shi dai ko kanzil bai furtawa kowa ba hasalima ba ya ɗora hankalinsa akansu don in  ransa ya ɓaci duk zai iya yi masa illa.

Da zazzaɓi Husnee ta kwana, amma hakan bai hana ta shiryawa don zuwa makaranta ba kasancewar ranar lahadi ce ba za ta je boko ba don haka ta shirya tin sassafe.
Ta na fitowa Mommy ta ce “A’ah Husnee lafiyarki ƙalau kuwa?  da zazzaɓi ki ka kwana fa har da surutai marasa kan gado amma yanzu kin ɗauki uban hijabi kin zurma kin ce za ki je makaranta, kya bari ai jikinki ya yi ƙwari.”
“Ni na ji sauƙi Mommy, ba zan iya zama a gida ba hakan shine  zai ƙara mini zazzaɓin ma, don Allah ki barni in tafi Mommy.

Mommy  ta rausayar da kai kamar marigayin zakara  gami da cewa “Allah i tsare  sai ki kula sosai,  ni ban taɓa ganin makarantar da ki ke so da ƙauna ki ka nacewa zuwanta irin wannan ba, Allah ne  masanin abinda ke ɓoye a cikin hakan”
Husnee dai ba ta ce ƙala ba  tuni ta wuce hanyar fita.

Ta yi sa’a ba ta yi karo da wani  ba har su ka fice daga gidan ita da Amadu direba.
“Innata ya jikin naki  na ji Khausar ta ce ba ki da lafiya”  ya faɗa cikin tausayawa  “Na ji sauƙi Malam Amadu, don Allah ka kaini gidan su Akhiee idan ka sani.
Durumm!! Bom ɗin zuciyarsa ya tashi sabida jin abinda ta faɗa, cikin sauri ya ce “A’a Innata ki shafa min lafiya in kai ki makaranta don nan aka sa ni in dinga kai ki.”
“Malam Amadu kai ma ka shafa mini lafiya ka kaini in ganshi ko hankalina zai kwanta,  zazzaɓin da na ke yi kawai tunanin halin da yake ciki ne ya kawo hakan,  kwana na yi ina mafarkai kala-kala akansa, har mafarki nayi ni ce me jinyarsa  ina kusa da shi ina yi masa komai, sai da na farka na ga mafarki ne sai na ji haushi don na so ace da gaske ne.   Amadu  ya jinjina kai cike da tausayinta, zuwa yanzu ya lura  gabaki ɗaya hankalinta ya koma kan Akhiee, me kuwa za a yi mata wanda ya wuce a tausaya mata, ta na da ƙuruciyarta da hankalinta amma za ta lalata ta hanyar wannan babban tantirin,  abin da yake tunani a zuciyarsa kenan, a zahiri kuwa bai ce mata uffan ba.

***************************

White diamond watch da ke hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba  tashin hankali, “Asma’u Please! It’s time for prayer, i’m going to the masque”
“Please Akhiee you listen to me!” ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka……..

Fararen idanunsa masu tamkar nono ya zuba mata  har na ɗan lokaci sannan ya ce “Kukan naki zan saurara kenan??”   girgiza kai ta yi ta na ƙoƙarin goge hawayen cikin sauri, dandanan ta tsayar da kukan ta goge ƙwallar  kamar ba ita ke kukan ba sai dai da an kalleta za a gane ta yi,  ido ta zuba masa sai kuma ta rasa abin ce masa,  sai da ya ce “Go ahead!” sannan ta yi zumbur ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da tattaro dukkan nutsuwarta, cikin sanyin jiki ta ce “Akhiee ban san abinda ya faru ba ranar nan, na ji su Yasayyadi Usman sai tambayoyi su ke yi mini,  na ga mutanen makarantar nan sai wani irin kallo su ke yi mini, gashi kai kuma ka ƙi zuwa bare na ji daɗi,  ina ƙoƙarin zuwa makaranta kullum sabida in ganka, amma kai ba ka son ganina.”
Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe a hankali ya ce “Za ki faɗi ne shine na yi ƙoƙarin tsayar da ke sai kuma na taka ɓawon ayabarki  mu ka faɗa ƙasa duka,  saɓanin  fahimta ne sun yi zaton wani abu ne ya faru bayan haka,  Asma’u ke ƴa macece kuma me daraja,  ki na da hankali,  tarayya da ni duk zai tarwatsa miki wannan, duniya za ta kalleki a matsayin mara kamun kai, iyayenki ma kansu ba za su so ki dinga kusantar inda nake ba, bayan haka ni kaina ba na so domin kasancewar ki a kusa da ni haɗari ne, every time  wani abu zai iya faruwa da ke, takan iya bayuwa har ki rasa ranki ko kuma ki samu nakasar da ba za ki iya morar kanki ba ma,  don Allah ki fita daga rayuwata.”
shiru ta yi ta na tunani kamar ta ɗauki abinda ya ce, jim kaɗan kuma sai ta murmusa sannan ta ce “Indai akan haka ne Akhiee ba ni da matsala,  kowa ya zageni ko ya faɗi mummunar kalma a kaina, Allah shine me hukunci akan kowa kuma ya san me gaskiya ba zai hukuntani akan abinda ban aikata ba don mutane sun faɗa,  zan yi farin ciki idan na zamo abokiyarka, ka yarda da ni Akhiee  ban damu da rasa rai ba, don Allah ka barni na yi farin ciki.”
Girgiza kai ya yi  cikin murya me kama da ta raɗa ya ce “Asma’u ki fahimce ni don Allah.
….”  ba don ya gama faɗen abinda zai faɗa ba ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannun, ƙara matsowa ta yi kusa da shi ta na zuba masa zaratan idanunta  fuskarta ɗauke da murmushi me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, cikin muryarta me zaƙi da daɗin saurara ta ce “Akhiee yau ɗaya ina son ganin dariyarka  ina so na ga ka na yin abu kamar kowane mutum .”
Rausayar da kai ya yi kafin ya ce “Ni ba mutum ba ne  kamar kowa,  kar ki sa ni dariya please”  tattaɓe fuska ta yi a shagwaɓe ta ce “Ni fa ban yarda da hakan ba, ni dai yau ko ka yi dariya ko kuma in dinga kuka ba zan yi shiru ba kuma.”
“Akan wannan sai ki yi kuka?  ko za ki jarraba in gani?”  ya faɗa ya na kasheta da kaifafan idanunsa.

Dire-dire ta fara yi tana gungunin kuka ta na ce “Ni wallahi ka bar tsokanata da gaske nake ba da wasa ba, in ba haka ba wallahi za ka ga abinda zan yi sai na kwana ina kuka  kuma ko abinci ba zan ci ba.”
“Hmm!!”  kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba,  ai kuwa ta taƙarƙare ta rushe da kuka har da dafe kai kamar an sanar mata iyayenta sun mutu.

har ga Allah ma tsorata shi ta so yi don kuwa har hankalinsa ya gusa ya tafi wani tunanin,  ganin yadda take ɓarzar kuka akan shiririta ya ƙara bashi damar gane lallai ba hankali ta cika ba, bai san ma lokacin da dariyar ta kufce masa ba,   ya na dariyar ya ce “Na ce ƙuruciya na damunki amma kin ƙi yarda.”
Tsam!!!! kukan nata ya tsaya tamkar ba ta taɓa yinsa ba sai hawaye yare-yare akan fuskarta, idanunta kuwa su na kan kyakkyawar fuskarsa wadda ainahin kyawunta ya ƙara baiyana fiye da ko yaushe,  wani irin haske gami da kyawu tsananin kyawu ta ga ya ƙara yi kamar ɗan aljanu.   dariyar ta fara yi   a take farin ciki ya lulleɓeta ta ko ina, cikin wata kasalalliyar murya ta ce “Akhiee!  ashe zan iya sa ka dariya?  hakan na nufin ina da muhimmanci a rayuwarka?  amma a hakan ka ke tunanin zan iya juya maka baya?”

Kallon kallo su ka shiga yiwa juna kowa da abinda yake tunani, shi sai yanzu ma ya tuna wai ashe dariya ta sa shi  yau kenan ba lafiya gareshi, ya cika da zullumin ta inda iftila’i zai afko masa amma bai nuna mata alama ba.
hankicif ya zare cikin Aljihunsa ya miƙa mata cikin tattausar muryarsa ya ce “Goge hawayen fuskarki,  na san yau kin yi farin ciki, zan so ki ɗore da haka amma na san ba lallai ne ba, Asma’u in da hali ki tafi gida yanzu don Allah ba don ni ba.”
Ba don komai yake son ta tafi ɗin ba sabida ko ma me zai sameshi kar ya same shi ta na nan, don ya san sai ta tayar da hankalinta shi kuwa zai so farin cikin da take yi na yin dariyarsa ya ɗore har wani dogon zango.
Karɓar  hankicif ɗin ta yi ta  goge fuskarta sannan ta miƙo masa ta na cewa “Ba zan tafi ba har sai an tashi,  idan ba ka son ganina ne ba komi ba za ka ƙara ganina ba sai gobe, ka yarda?”  gyaɗa kai yayi alamar “eh”  a zuciyarsa ya yanke shawarar fita ya bar mata makarantar.

Zara ce ta iso wurin ta na cewa “Sai kin daku a wurin Yasayyadi Muhsin, ba ki da labarin har an idar da sallah ko?”   ido warwaje ta ce “Na shiga tara ni Asma’u! shi kenan na kaɗe wallahi ba na so a taɓa lafiyata.”  jan hannunta Zara ta yi murya ƙasa-ƙasa ta ce “Ai kuwa sai kin daku don kinsan haushinki su ke ji dama sabida ki na kula Akhiee”  tsaki ta doka kafin ta ce “Ni wannan tijara Allah i kawo mini ƙarshenta, kawai don Allah ya jarabci mutum sai a ɗauki karen tsana a ɗora masa, ba kusan cewa tsangwamar mutum na sa shi ya faɗa wani mugun halin ba?  ƙila ma baƙar masifar ƴan gidanku ce ta sa shi ya zama haka don kun cika jaraba.”
sam Zara ba ta ji daɗin furucin Husnee akan ƴan gidansu ba amma ba yadda za ta yi don su su ka jawowa kansu,  ita ma kanta abin ya na ci mata rai irin ƙiayya ta zahiri  da suke nuna masa, ko dan wasu daga ciki ba Uwa ɗaya suke ba?..

Su na sauka shima ya sauka ya bar makarantar, kasancewar yau ba a kan dokinsa ya ke ba a ƙafa ya ke tafiya cikin nutsuwa  ya na yi ya na nazarta duk wani motsi da yake jin ya gilma.

Mursali  ya na ganin fitarsa daga makaranta ya tambayi malamin cikin ajin cewar zai je famfo ya sha ruwa, cikin sa’a ba tare da dogon bincike ba ya barshi ya fita duk da cewar ba a daɗe da komawa karatu ba.
Ya na fita daga makarantar  ya bi sahun Akhiee har ya gane  hanyar da zai bi sannan ya tsaya, wayarsa ya zaro keypad  ƴar kamfanin Airtel  ya turawa  Ɗan Kurada  kira, ya na ɗagawa ya ce “Ya ne  Idon Mikiyar Oga!”  “Sai da kai Ɗan Kurada Gatarin saran nama ba!  Sahun Keke ya fito daga makaranta yanzu, kuma ya yi hanyar Lungun Shege, ina fatan kun gama shirinku”
“Hhhh!! Wihuhu!!!! ina yinka yaron nan, wallahi kai ɗan iska ne, Allah i kamaka  Ɗan Mursali!!!  yau Sahun Keke dole ne mu gane gaban sa da uwassa!!! wihuhu!!! Dodon Lunguwa uban ƴan sarari me nasara ɗan nasarawa!!!”  Ɗan Kurada ne ke maganar cike da tsananin farin ciki.
Ya na katse wayar ya dubi  sauran  riƙaƙƙun ƴan daban da suke tare ya ce “Ku shirya mu shiga Lungun Shege Sahun Keke ya tawo.”
Dukkansu ba wanda bai yi murna ba kuma su ka sa a ransu sai sun yi nasara akansa ko dan su ƙara samun shiga a wajen ogan nasu.

Ba zato ba tsammani ya na cikin tafiya su ka yi masa da’ira sun kai su goma sha biyar kowa sai muzurai yake yi a dole jan wuya.
Ɗaya bayan ɗaya ya ƙare musu kallo kafin ya ci gaba da tafiyarsa.

Ɗan Kurada  ya ce ”Kai ƙaramin Tsako duk ka tattaro ƴan yangu-yangun naka ku taru duk sai mun ga bayanku,  Mun ƙara samun horo daga Oganmu kuma yanzu za’a fara wasan dolen doliya sai mun tureka mun gaje karagarka mun gaje duk wani iskanci naka,  ka yi sake ɗan zaki ya girma, da  ka ke nasara akan Dodon Ɓoye amma yanzu shine zai binneka!!” cikin kurari da cika baki Ɗan Kurada ke maganar, Akhiee dai bai ce musu komai ba, Ɗan Kurada ya ce  “”Yara ku hau min kansa.”
Mutum biyar ne su ka nufe shi.
wani  ɗan buda ne a hannunsa, mutum biyu wuƙa kamu uku me azababben kaifi, ɗaya kuma dogon ƙarfe ne wanda aka yi masa wasu kibiyu cako-cako a jiki, ɗayan kuma Wuƙa ce me zarto samɓaleliya.

Wata ƴar ƙaramar wuƙa wadda ba ta wuci tsayin ɗan yatsan tsakiya ba Akhiee ya zare  gami da yin cikinsu.

ta ko ina hari su ke kawo masa ya na kaucewa cikin zafim nama,   duk idanunsu ya rufe kowa alla alla ya ke yi a ce shine zakara,  ba su ankara ba Akhiee ya zame ya tsugunna da ƴar wuƙarsa, ba su ankare ba sai jini su ka ji ya fara tsiyaya daga ƙafafunsu ga azaba na ratsa su tin daga sama har ƙasa, kowa ya saki makamin hannunsa ya riƙe wurin ya na ihu.

mugun yanka ya yi musu wanda indai ajalin mutum ya yi zai iya mutuwa nan take don kuwa kan jijiyar agara ne.
Ganin haka ya sa hankalin Ɗan Kurada ya  tashi nan fa suka afka masa su duka.
faɗa ne ya kaca me a tsakaninsu  wasu ya yayyanke su wasu kuma in ya kai harin sai su kauce.

Ɗan Kurada ne ya shammace shi ta baya ya kafta masa sara da wata ƙatuwar wuƙa me kama da Adda sabida faɗi da tsayinta, dandanan wurin ya dare jini ya fara zuba kamar an yanka bujimin sa

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*
[8/19, 11:04 AM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 13

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

A take wani irin duhu ya rufe masa idanu ganinsa ya fara ɗaukewa, hakan ne ya basu damar ci gaba da yankarsa; yanka uku su ka yi masa ƙwarara ya zube a wurin jini na   shatata. su na ganin haka su ka ara a ta kare su ka bar wajen cike da farin ciki da murnar sun yi nasara.

a sannu-sannu  duhun da ya mamaye ganinsa ya fara washewa har ya buɗe idanunsa tangaras, cikin ƙarfin hali da tsaurin zuciya irin na shi ya miƙe ya na takawa a hankali a hankali ya nufi makaranta,  kafin ya kai ga zuwa tuni waɗan da su ka ganshi a hanya sun je sun kwanzamawa su Sheikh Auwal nan fa duk hankalinsu ya tashi su ka bar cikin makaranta su ka fito wurinsa.

Cikin tausayawa Sheikh Auwal ya ce “Akhiee maza  mu je a kai ka Asibiti don ka na guƙatar temakon likita.”   Kamar ba shi da kunne haka ya yi don kuwa ko alamar ya ji ma bai yi ba,  Yasayyadi Usman ne ya dubi Sheikh Auwal cike da takaicin baƙar gaddama ta Akhiee ya ce “Ka ga irinta ko?  ya na ji fa ba wai ba ya ji ba amma sabida ɗan iska ne ya yi banza,  ka je ka mutu ma mana ina ruwan wani?”
Yasayyadi Muhsin ya ce “Ai shi dama hadari ɗaya ba ya yi masa ruwa,  Kai Akhiee ka zo tin da girma da arziki a kai ka Asibitin  nan don wallahi jini na zuba a jikinka  sosai.”
Cike da zafin rai gami da zafin ciwo ya ce ”Ku ƙyaleni abina, ba ruwanku da ni tinda ba a jikinku ciwon yake ba kuma in na mutu ba ku da asara, duk ku watse ku ba ni wuri.”
Yasayyadi Jameel ya tausasa murya cikin sigar rarrashi ya ce “Yanzu ba lokacin wannan ba ne, duk  ƙara ɓata lokacin da ka ke yi ƙara cutuwa ka ke yi, don Allah ka bar labarin yasayyadi Usman ka ƙyale surutansa ka zo mu je.”  wani dogon tsaki ya doka ba tare da ya ƙara ce musu ko kanzil ba,  sai lumshe idanu yake ya na cije gefen leɓensa.

Sheikh Auwal da Yasayyadi  da sauran wasu daga cikin malaman har ma da maƙota sun taru akansa sai rarrashi su ke yi su na haɗa shi da Allah da Annabi amma ya yi kafus,  ya ce murje shi fa allambur ba wanda ya isa ya kai shi wani Asibiti.
Haka su ka yi ta fama da shi har Tashin hankali  ma ya sa sun manta  sun baro ɗalibai a ciki gashi har lokacin tashi ma ya wuce ana ta turnuƙu da shi.  shi kuwa har lokacin girarsa ɗaya ba ta karayaba.

Magriba ce ke shirin rufawa amma a yau MADARASATU NOORUL ISLAM   ba alamun za a sallami ɗalibanta.
Tin su na karatun da aka koyar da su cikin ƙwarin guiwa har su ka gaji wasu su ka fara yin shiru, ƙananu kuwa tuni wasu sun fara kuka sabida tsoro don sun yi tunanin anan za’a bar su su kwana.

Husnee ce ta shafa cikinta da ke kukan yunwa kafin ta ce “Asiya wai lafiya kuwa?  ace har yanzu ba malamin da mu ka gani bare ya sallamemu?”  Zara ce ta leƙo tsakaninsu gami da cewa “Bari na je na duba ni dai wallahi na gaji a zo a sallamemu haba!”  Husnee ta yi dariya ta na cewa “Yauwa ƙanwar masu abin jeki don Allah.”
Harara ta maka mata kana ta fice.   Ba ta wani daɗe ba ta dawo hankali a matuƙar tashe, ganin haka ya sa zuciyar Husnee ta fara dukan sittin saba’in tamanin casa’in ɗari da hamsin!
“Ƴan Daba ne su ka sassari Akhiee, jini sai zuba ya ke yi a jikinsa amma ya ƙi yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru a kansa, har  babban Yayanmu ma ya zo  amma ya ƙi Amincewa, kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ƙarewa”
Ta ƙarasa maganar gami fashewa da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me imani.
Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje.
Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da’ira wanda yawanci Yayyensa ne……….

Gaba

Da tambaya su ka isa ƙofar gidan   jikinta sanyi  salam haka ta fito daga mota ta na ƙarewa tafkeken get ɗin gidan kallo,  yadda gidan yake tamfatsetse idan na shiga  ina zan fara tinkara?  tambayar da zuciyarta ta ke yi mata kenan.

Kamar Amadu ya sani ya ce “Innata shiga za ki yi da Bismillah ki na addu’ar Allah i haɗa ki da wanda ki ka sani kawai.”
Jinjina kai ta yi gami da sauke ajiyar Zuciya sannan ta nufi get ɗin gabanta na ƙara faɗuwa.

Sallama ta yi a  haraba  ta na rarraba ido don ganin ta inda za’a ɓullo.
Ji ta yi an amsa sallamar daga can gefenta ta yi saurin kai dubenta wurin, Hamza da Adamu ne zaune kan wata makekiyar tabarma sun tasa kofuna da fulas ɗin shayi gaba da alama karin kumallo su ke yi ko kuma za su yi.
Danne fargabarta ta yi ta ɗan dubesu gami da cewa “Ina kwana!”  duk idanunsu na kanta  Hamza ya yi zaram ya amsa ya na fara’a.
Cikin kame-kame ta ce ”Um!..in..ina ne… zan ga Akhiee?”
Idanunsu ne su ka ƙara girma  su ka yi kallon kallo cikin madarar mamaki, Adamu ne ya yi saurin shiga zancen da cewa “Waye kuma Akhiee ?  daga ina ki ke meye haɗinki da shi??”
baki na rawa ta ce “Muhammad Risslan fa ni…ni..a…”  kasa ƙarasa maganar ta yi sabida kuka da ke shirin  kufce mata.

Hamza ya karkaɗe mazaunar rigarsa ya miƙe ya na cewa “Abin ya ƙara girma kenan, bari dai in matso in ji yadda ake ciki.”
“Ƴar ajinmu ce  ita, kuma ta zo duba lafiyarsa ne,  Husnee sannu da zuwa mu je in raka ki wurinsa.”
Zara da ta iso yanzu ta basu amsar tambayarsu, kana ta ja hannun Husnee su ka kutsa kai ciki.
Riƙe haɓa Hamza ya yu ya na cewa “Iyye?  neman mata ma ya fara yi kenan?  to Allah i sauwaƙe lallai Abhi ya haifi bala’i.”  Adamu ya taɓe baki ya na cewa “Ƙaddararre ni wallahi na so ma sun kashe shi kawai mu huta aikin banza, kullum sai ya yi mana baƙin tambari ya gada mana abin magana sannan ya ke jin daɗi, ya gama gurɓata kima da mutuncin Ahalinmu.”  Hamza ya ce “Ni ma da hakan ta faru ai sai na fi kowa murna wallahi, yanzu ga dai wannan yarinya har yarinya amma ya lalatata.”
Adamu ya ce “Umm! to ya za mu yi haka za mu suba ido har sai ya mutu sannan mu huta, ɗan wahala kawai.”
Masifa su ka ci gaba da zazzagawa kowa na tofa albarkacin bakinsa wanda yawanci ba alkairi su ke faɗe akan Akhiee ba.

Sai da su ka ƙara shiga ciki Husnee ta ƙara tabbatar da girman gidan, sashi kala daban-daban ga ɗakuna rututu haka mutane yara manya maza mata duk gasu nan  a hakan ma wasu sun tafi makaranta, matan gidan da ƙananun yara sun fi yawa sai samari su  na ta shirin  fita kasuwa.
Ita dai kamar ɓarauniya haka ta ke tafiya saɗaf-saɗaf sai fiƙi-fiƙi  ta ke yi da idanu kamar an tarfa munafuka.

Duk wanda ya lura da su sai ya tambayi wacece da uwar safiyar nan ta zo musu gida musamman matan gidan, sai Zara ta yi zaram ta ce Ƴar ajinsu ce sai kuwa su taɓe baki.
Da haka su ka isa  can ƙarshen gidan. inda   ba mutane  wuri ne a ɗan kewaye wanda za a iya kiransa gida   ɗan ƙarami me ɗaki ɗaya sai banɗaki da wani ɗan ƙaramin ɗaki wanda bai kai a kira shi ɗaki ba sai ɗan tsakar gida ba wani babba ba,  wurin shiru sai iskar safiya da ke kaɗawa a hankali a hankali don kuwa wurin ya yi nesa da cikin jama’a sosai kwata- kwata bai alaƙanci wani sashi na  mutan  gidan ba.
Husnee dai da bata iya gani ta yi shiru sai da ta kalli Zara ta ce “Ni ban taɓa ganin ƙi da tsangwama ba sai a gidanku, wato ɗakin nasa ma shine a can bayan gari  inda ba mutane, wajen kwanan ma sai an  nuna bambanci ko?”  Zara ta ce “Ai ba laifina ba ne Husnee nima tinda na yi wayo a nan na ga ya na kwana tin kafin ya girma shima, ban sani ba ko shi ya zaɓi hakan ko su su ka zaɓa masa, amma ba me shigowa ma sai in baya nan ko kuma dai wani babban abu ya kawo mutum.”
Daidai lokacin Zara ta kutsa kai cikin ɗakin nasa  tare da sallama, Husnee kuwa dakatawa ta yi domin a bata izini sannan ta shiga.

Turus Zara ta yi ganin Wata kyakkyawar budurwa wadda ba ta wuce shekaru daidai na da na Husnee ba zaune ku sa da shi idanunta sun yi jajir sun yi ɓulu-ɓulu  da zarar me hankali ya kalla ko ba a faɗa ba ya san kuka ta ci har ta godewa  Allah, har yanzu ma akwai sauran hawayen akan  dogayen gargasar idanunta.
Akhiee kuwa ya na zaune bisa ƙaramin gadonsa wanda aka shimfiɗe shi da kyakkyawan bargo duniyar kuliya.
abin ya bala’in bawa Zara mamaki don kuwa kaf shirin ɗakin da su ka yi ita da Sheikh Auwal an canja shi ciki kuwa har da wasu abubuwan irin su bedsheet pillows da sauransu.
Idanu ya zubawa Zara alamar tambaya,  ta yi ƙasa da kai zuciyarta sam ba daɗi ta ce “”Husnee ce ta zo dubaka shine na rakota.”

Juyawa ya yi ya zubawa ƴar budurwar ido a na yi mata wani shegen  kallo me cike da alamomi daban-daban.
Zirrrrrr!!!  hawayen su ka ƙara biyo kan kumatunta.
Tsaki ya yi kafin ya buɗi baki a hankali ya ce “Ta shigo kawai.”
Zara ta juya gami da cewa “Ki shigo Husnee”  ba za ta iya komawa ba don haka ta ce “Ni kam  bari in je wajen su Umma”  gami sa yin gaba.
Husnee ta ce “To”  gami da turmutsa kai ɗakin tare da Sallama.
a inda yake zaune a nan yake bai ko motsa ba,  Husnee kam ba ta ga abinda Zara ta gani ba don haka ta ƙarasa gefen  gadon nasa ta zauna  ta na murmushi me tafe da ƙwalla.
Ido ta zuba masa har na lokaci yayin da nasa idanun su ke a ƙasa ko ɗagowa ya kalleta bai yi ba.

Cikin  rawar murya ta ce “Akhiee!  ba ka son ganina ko? ya jikin naka?  ka yi haƙuri don Allah wallahi ba a son raina na ɗaga maka hannu ba jiya, hankalina ne ya tashi na rasa yadda zan yi don gani   nake tamkar za ka rasa ranka.”
“Wannan bai ɓata mini rai ba a kan rashin jin maganata Asma’u, me ya kawo ki har gidanmu? shin bance ki fita daga rayuwata ba ne?   kin ga abinda ya faru da ni  jiya  cikin ƴan mintuna ki sani idan ki na bibiyata watarana ke  za’ayiwa abinda aka yi mini don za  a ɗauka ne kamar ke wata ce a wurina.”  Hijab ta sa ta na goge ƙwalla cikin shashshekar kuka ta ce “Ina so in yi abinda ka ke so amma na kasa, Akhiee tausayinka da son kasancewa tare da kai ba zai barni na yi abinda ka ke so ba,  ka barni kawai idan an kashe ni  ka ga dole zan dena bibiyarka”
“Ke mahaukaciya ce wai Asma’u? meye haɗina da ke da har ki ke tunanin a kashe ki a kaina?  me yasa ba za ki yi ƙoƙarin gyara rayuwarki ba  sai ki yi ƙoƙarin lalatata??”

“To Akhiee kai me yasa ko na rana ɗaya ba za ka kwatanta zamowa mutumin ƙwarai ba?  ba ni da wata alaƙa da kai amma  akwai ƴan’uwantaka ta muslimci Akhiee ko dai kai ba muslmi ba ne?  me yasa za a dinga haɗa ka da Allah akan abu amma ka rufe idonka?  Akhiee!!  indai ba ka zamo mutumin kirki ba to fa  ba na jin akwai ranar da hankalinka zai kwanta,  da ba ka shiga harkar banzar nan ba da babu wani ɗan ta’adda da zai cutar da kai, amma ka  shiga harkarsu, ƴan gidanku duk malamai ne kai ɗaya ne ka zamo daban,  ba ka jin nauyin  yin kisa, ka ɗauki jini tamkar ruwa kwata-kwata zubarsa ba ta tsorata ka, ka yanki wancan ka kashe wancan Akhiee meye  ribar wannan rayuwar?  ka tarawa kanka maƙiya da masu son ganin bayanka,  ƙarshenta fa  haka za su yi maka kisan wulaƙanci  mu da mu ka damu da kai kuma ka bar mu da shan wahalar rashinka; Akhiee!!!   Ka yi min haƙuri amma ba zan iya fita daga rayuwarka ba ina son zamowa Abokiyarka, don Allah ka yarda da ni”  ta kai ƙarshen maganar ta na wani irin kuka me tsuma zucuyar me saurarensa.

Rintse idanunsa ya yi da ƙarfi gami da haɗe kansa da guiwa, zuwa yanzu ji yake kamar ya kasheta ya huta don kuwa ya tabbatar indai ba za ta fita daga rayuwarsa ba za ta sha baƙar wahala ta ko’ina.
Sai bayan wani lokaci zuciyarsa ta  ɗan lafa sannan ya ɗago idanunsa ya zuba mata  “Asma’u Babana kawai na yarda da yiwa ƙarya, Babana kaɗai na ke iya saurara kuma na ke iya amfani da kalaminsa,  sai dai ko shi bai taɓa sa ni dariya na yi ta ba sai ke Asma’u, ban sanki ba bansan wacece ke ba  nan san daga ina ki ke ba, lokaci ɗaya kin shigo rayuwata  kuma ki na son haifar min da matsaltsalu a cikinta,  iya abinda ki ka samu a baya ki yi haƙuri da shi amma daga yanzu ki daure ki ɗauke kanki daga gareni,  rayuwata rayuwata ce ba na jin za ta taɓa canjawa, ki tashi ki tafi.”
“Amma Akhiee ai…..”  dakatar da ita ya yi da cewa “Ba na son jin komai daga bakinki, na riga na gama maganata ki tashi ki fice mini da gani, ba na son ƙara ganin fuskarki haka ba na son ko da ƙara jin sunanki, da so samu ne  ki yi mini tazarar da har abada ko labarinki ba zan ƙara ji ba, ki fita tin kafin raina ya ɓaci na yi miki abinda hankali ba zai ɗauka ba.”

miƙewa ta yi ta na tafiya da baya da baya idanunta da ke famar zubda ruwa su na kansa,  wani irin abu ne ke turnuƙo mata tin daga ƙahon zuciyarta har maƙogoro hakan ya sa ba za ta iya cewa komai ba, yadda take shashshekar kuka kuwa ka ce duk ƴan gidan su ne su ka yi haɗari su ka mutu.
Sai da ta fice daga ɗakin kana ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali a hankali.

a haka ta dinga ratsa shafukan gidan daban-daban   ba tare da damuwa akan kallon da su ke binta da shi ba har ta fito waje inda Amadu ke  ta safa da marwa cike da zullumin abinda zai faru da ita a ciki, ganin ta na wannan mugun kuka ya ƙara ɗaga hankalinsa ya shiga yi mata tambayoyi sai dai ko uffan ta ƙi ce masa.

a ɗakin Akhiee kuwa Husnee na fita  Razia ta bayyana a gabansa ita ma ta kafa aradun nata kukan,  cikin shashsheka ta ce “Risslan  ina raye  kuma ina tare da kai  amma  ba ka taɓa yi mini abinda ka yiwa wannan yarinyar ba, ka faɗa cikin wannan halin ne fa dominta ka yi abubuwan da ba wanda ya taɓa saka ka yi su  sai ita,  ta ya-ya hankalina zai iya ɗauka?   billahillazi huwar rahmanu Sai na kasheta indai ba ta gaggauta  fita daga rayuwarka ba!!!, in ban kasheta ba kuma zan yi mata illar da duk duniya sai ta Zame mata tamkar wuta, da ita da danginta sai sun gwammace mutuwa ta yi akan irin izayar da zan yi mata.”

Jikinsa kawai karkarwa ya ke yi  jijiyoyinsa jikinsa sun wani irin mimmiƙe sun firfito, kansa na wani irin juyi da gwamutsi tamkar karon Babbar mota da ƴar uwarta, Zuciyarsa  wani irin tuƙuƙi ta ke yi wanda ya ke jin tamkar  ba za ta ƙara minti ɗaya ba  za ta yi bindiga ta tarwatse.
Leɓensa na ƙasa ya kame ya cije gami da dafe kansa da dukkan hannayensa.
ganin irin  wahalar da ya faɗa bai  sa Razia ta saurata masa ba,  ta ci gaba da surutai cikin fitar hayyaci da tsananin ɓacin rai,  baƙin kishi ya sa duk ta zamo tamkar mahaukaciya,  ta daɗe ta na faɗar duk maganar da ta zo bakinta sannan ta gaji ta yi shiru ta ci gaba da zabga kuka.
sai a lokacin Akhiee ya samu damar tofa tashi  “Asma’u ba ta da laifi kuma muddin wani abu ya sameta sai na jefa ki a  masifar da har ƙiyama ta tsaya ba za ki fita daga cikinta ba wallahi!!!!  tashi ki bar min wuri kuma za ki je ki haɗu da Father.”
rikiɗaɗɗun idanunta ta zuba masa cike da tsananin mamakin furucinsa.
Cikin tsawa ya ce “Ki tashi na ce!!!  ko kuma ni in baki wuri!!!”
Ya na rufe baki ta ɓace ɓat!!  kamar ba ta taɓa wanzu a wurin ba.
Zafi, ƙuna, raɗaɗi, ciwo, azaba, uƙuba,  ba abinda zuciyarsa da kansa ba sa yi  ya rasa ma abinda zai yi ya samu sassauci.

Zabira da Laita Da sauran iyalin Akhiee su na zaune sun yi jungum-jungum kowa na tunanin halin da yake ciki, Rabi’u kuwa kuka yake ta ɓarzawa  tin jiya da ya ga halin da Uban gidan nasa ke ciki tsoro da tashin hankali su ka hana shi sakatt,  a kyauta Laita ta ba shi abinci amma ya ƙi ci sabida ya gama firgicewa, da kuka ya yi bacci da shi ya tashi, har kawo  yanzu ma ya kasa denawa, su kuwa sai ƙara tsorata shi su ke yi, a take ya ji harkar daba ma gabaki ɗaya ta fice masa daga rai, nan take ya sa a ransa zai yi karatu tuƙuru kamar yadda mahaifiyarsa ta ke so  zai watsar da dukkan wata shiririta.

Zabira ce ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce “Wai yanzu zuba ido za mu yi kenan ba za mu ɗau fansa ba??”   Gwaja ya ce “To in ba da umarnin Sarƙa ba wa zai yi hakan?  sai mun je mun tambayeshi mun ji me zai ce”  Laita ta ce “Ya kamata a gaggauta tambayarsa; anjima kaɗan ku shirya mu shiga gidan nasu.”  Salansa ya ce “Hakan ma za ayi, amma ya zama dole mu ɗaukar masa fansa  ko ba ya so  sai mun yi bai sani ba.”
Ɗan Bakwai ya ce “Asalin gaskiya kenan nima haka zan ce”   tattaunawa su ka fara yi kowa na faɗen abinda ya kamata su yi.

Tankar Yaƙi……….

(To sai gobe😒😒 su balolo har an baza kunnuwa a ji Tankar Yaƙi a wane Hali take😒🌝)

SHARE FISABILILLAH

 

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*
[8/19, 7:24 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 14

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

Kamar daga sama aka jefota haka ta faɗa  ɗan madaidaicin Kangon da su Ɗan Kurada ke zaune su na ƙidaya kuɗin da Dodon Lungu ya basu na aikinsu, sai murna su ke yi kamar an yi musu Albishir da Aljanna.

Ba wanda ya ankara sai ganinta su ka yi akansu, fuskar nan ta-ta ba annuri, cikin tsananin ɓacin tai ta ce “Wai har da kai za’a ci amanata a karɓi kuɗi a kashe wanda na ke so,  to wallahi duk sai kun gane kurenku!”  Ɗan Kurada ya yi saurin miƙewa ya na tausa kuɗinsa cikin wata ƴar lalita, cike da son kare kansa ya ce “Wallahi kin san dai ba yin kaina ba ne, Dodo ne ya samu kuma kinga aikinsa mu ke yi ba zai lamunce mu ƙi yi  don ki na son Sahun Keke ba, wannan kuɗin ma da ki ka gani ba nawa bane na waɗannan ne”  ya faɗa ya na nuna abokan aikin nasa wanda su ke zazzare ido kamar na mazarin tsire a kasuwa,  sun tsorata da ganinta don dukansu ba wanda bai san halinta ba,  ana cewa mace akwai tausayi amma ita ta fi wani namijin rashin imani.

Ƙwafa ta yi kafin ta ce “Ɗan Kurada ka je don kanka  kai ba zan taɓa ka ba amma tabbas sai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.”  Jin haka ya  sa sauran miƙe su na neman wajen tsira,  a hankali ta taka ta doshi inda suke, baya-baya su ka fara yi su na bata haƙuri gami da bata yadda aka yi amma ko saurarensu ta ƙi yi,  sai da su ka ƙure da bango sannan su ka dakata.
Cikin dakakkiyar muryarta  ta ce “Da ku da suwaye ku ka aikata??’ Asabubu ya ce “Wallahi Ɗan Kurada ne babbanmu, sai wannan sai sauran yaran Oga, ni ba abinda na yi masa wallahi.”  ya ƙarasa maganar ya na yi mata nuni da na kusa da shi.

Wata lafiyayyar wuƙa ta zare a ƙugunta  ta na zuba musu idanunta masu ban tsoro, sai da ta goge wuƙar sannan ta ce “Ya zama dole ku ɗanɗana!!”  ta yi maganar tare da ketawa Asabubu wuƙar akan cikinsa, ihu ya zunduma sabida azabar da ta ratsa shi har cikin ƙoƙon ransa,  cike da rashin tausayi da imani ta ƙara kafta masa sara a kafaɗarsa hakan ya sa dole ya zube a wajen.
Takawa ta yi da gudu ta bi ɗayan da tuni ya tsela a ta kare ya na neman ceto,  kafin ya kai ga fita ta cimmasa, ta na danƙo shi ta shata masa yanka a hannunsa kan jijiyar gaɓar hannun ai kuwa jini ya ce salama alekum,  riƙe hannun ya yi ya na wulwula shi cike da azaba,  ba ta saurara masa ba  ta burma masa wuƙar a ciki ta zareta gami da sa ƙafa ta harbatsa shi can gefe.

Ɗan Kurada da jikinsa ke ta tsuma ta kalla ta na huci  kamar wadda aka danne za’a yanka,  “Wallahi Tallahi indai ka ƙara taɓa Sahun Keke sai na raba kanka da gangar jikinka,  ka je ka gayawa Dodo na ɗauki mataki akan yaransa, duk hukuncin da zai yi mini ina jira, don Uwar babassa ko me zai yi ya yi, kuma daga yau na bar aiki a ƙarƙashinsa, nima ƴar kaina ce kuma ina da tawa dabar,  ku iya takunku tin kafin na hallaka ku.”
Ɗan Kurada ya jinjina kai alamar ya fahimta, da kyar ya harhaɗo magana ya ce “Amma bai kamata ki bar ƙarƙashin Dodon Lungu ba, na san ma don kin yi haka ba zai ce komai ba.”   “Idan ma ya faɗa ba ni da asara  ka je ka gaya masa saƙona.”  ta na gama faɗen haka ta fice fuuuuu kamar iska.

Husnee
Ko da Amadu ya kai ta makarantar cewa ta yi ba za ta shiga ba gwara ya kaita wani wurin idan  lokacin tashi ya yi sai su koma gida.
Cikin sanyin jiki ya ce “Innata ni yanzu ina zan kai ki don Allah?”
“Mu je bakin titi kawai ka ajiye motar zan zauna a ciki”  Amadu kamar ya fashe da kuka ya ce “Hakan fa bai da amfani ki yi haƙuri mu koma gidan dai tinda ba kya son makarantar.”
“Ba na son gardama don Allah kawai ka yi mini abinda na ke so.”  rausayar da kai ya yi sannan ya kunna motar gami da fara tafiya.

Sai da ta kimanta lokacin tashi sannan su ka nufi gida,  Mommy na harabar gidan ta na duba shuke-shuke  su ka shigo,  baki a sake ta tsaya kallon Husnee wadda ta yi jemai-jemai da ka kalla za ka gane a bala’in wahale take.
“Ikon Allah kwanan nan dai duk in ki ka fita ba kya dawowa ƙalau, me yake faruwa ne??”
Numfashi ta ja ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar zuciya,  cikin muryar da ke ƙara nuna tsantsar damuwar da take ciki ta ce “Ba zan ƙara zuwa makarantar nan ba har sai bayan wani lokaci.”
“Oo ni ƴasu, to dalilin me?”   “Mommy Ba ni da lafiya  kuma shine su ka doke ni, don Allah Mommy kar ki matsa mini akan hakan ki barni duk ranar da na yi niyya zan koma.”  Mommy ta rausayar da kai kamar kazar da ke jin yunwa, a sanyaye ta ce “Shi kenan, Allah i ba ki lafiya, dama ke ki ka zaɓi makarantar ai ba ni na zaɓa miki ba, ranar da ki ka ga dama kya je, kuma idan yayyenki su ka tambayeki dalilin rashin zuwanki sai ki san abin gaya musu.”
Gyaɗa kai kawai ta yi alamar ta yarda da hakan, ba ta ƙara cewa kanzil ba ta wuce ciki,  tinda ta zauna ta doka tagumi ba abinda take tunani sai irin tsatstsauran matakin da Akhiee ya ɗauka akanta,  a yanzu ba ta da zaɓin da ya wuce ta ƙaurace masa na wani lokaci, kuma ta dinga addu’ar Allah i yaye mata duk abinda ta ke ji akansa, tunane-tunanen da ta ke yi kenan gabaki ɗaya hankalinta ya tafi akai.

Hajiya Laure da Hajiya Saudah ne zaune a gaban Boka Barore  sai tsitstsilla  idanu su ke yi sabida tsoro da fargabar abinda zai fito daga bakinsa.
shi kuwa Dariya kawai ya ke  tilliƙawa kamar an yi masa wahayinta, ya kai aƙalla minti biyar ya na yi sannan ya ci mur kamar ba shi ba, kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya fara magana ya na yi ya na zare musu munanan idanunsa,  “A kwana uku na ce ku dawo, shine ku ka ƙi dawowa sai yanzu da ku ka yi niyya, to aikinku ya tarwatse,  wadda mu ka turawa aikin a lokacin ta na tare da shi kuma ya temaketa   ya hana aikin shiga jikinta,  kuma ba ku dawo lokacin da mu ka ce ba kun tarwatsa komai, Shaiɗanun Aljanu sun Fusataaa!!!!”  ya kai ƙarshen maganar tare da wani ƙaraji da gurnani tamkar mahaukacin zaki.

Kallon Kallo  Hajiya Saudah da Hajiya Laure su ka yi cikin tsoro da shakku kafin Hajiya Laure ta ce “Ranka ya daɗe Boka Barore me zamani, wallahi rashin lafiya ce ta kama ni ba zato ba tsammani kawai sai na tashi da cuta har ba na iya ko tashi zaune sai an temaka mini, amma yanzu na ji sauƙi shine fa na yi maza na garzayo, abin dai ya na raina amma tsautsayi ne ayi haƙuri manyan mutane”  ta ƙare maganar cikin sigar rarrashi.
“Hahahahahahaha!  Ta baya ta wuce,  za ayi aiki me wahala kuma za mu ƙara tura shi ne kan wannan yarinya,  amma muddin ku na so aikinku ya yi kyau sai kun cike sharuɗana”  Hajiya Saudah ta ce “Meye sharaɗin?  ai tinda da akwai mafita komai me sauƙi ne Boka”   ”Ina buƙatar yarinya ƴar shekara ƙasa da ashirin, za ku kawota gobe  bayan ta yi kwana uku za ku zo ku ɗauketa, muna buƙatarta!!!!.”
Hajiya Laure cikinta ya bada wani ƙulululu!!  ita duk irin wannan manyan asirce-asircen ba iya yinsu ta yi ba, abinda ta fi ganewa  ƴar mallakar miji  da ɗan abinda ba a rasa ba shima mallakar ba irin ta muguntar nan ba.
Ganin ta ruɗe ya sa  Hajiya Saudah ta ce “Za mu kawo Boka, indai za mu yi nasara dole ne za mu nemo mu kawo.”
Boka ya yi dariya me isarsa sannan ya ce su zube kuɗi ya sallamesu.

Suna fitowa Hajiya Laure ta ce “Haba Hajiya Saudah, yanzu ina zan bi in samo yarinyar mutane in kawowa boka?  haba a dinga tunawa fa a duniyar muslimci muke ba ta kafirai ba.”
Hajiya Saudah ta yi wani Shu’umin murmushi kafin ta ce “Hmm!! kin ɗauki duniya da wasa Ƙawata, ki na son ɗaukar fansar mijinki, amma ki na tsayawa sanya, samun budurwa ba wani abu ba ne ba fa,  kuma ba wai kasheta zai yi ba  kawai ina tunanin zai ɗan ci amarci da ita ne” ta ƙarasa maganar ta na dariya,  ita ko a ƙasan silifas ɗinta.
Hajiya  Laure dai har yanzu abin bai yi mata ba, cikin sanyin jiki ta ce “To yanzu wa zan samu in kawo masa a goben nan?”
“Ba ki na da Ƴar aiki ba?  ƙila ma ba ɗaya ba to a cikinsu za ki zaɓa ki darje kawai ki ce ta zo ta raka ki, indai boka ne da ya gama abinda zai yi ya rufe bakin shegiya shi kenan.”
Hajiya Laure dai ba ta iya cewa komai ba sai tunane-tunane, wannan Damar Hajiya Saudah ta samu ta zizzigata ta kwantar mata da hankali har ta ji ta yi na’am da hakan.

Washegari kamar yadda su ka shirya tin wuri Hajiya Laure ta ci ado ta gaiyaci Ma’u ƴar aikinta rakiya,  su na zuwa su ka direwa boka ita su ka yi nasu wuri.
anan fa Ma’u ta ga tashin hankali, tin ta na kuka da hawaye har su ka gaji su ka dena zubowa.

Bayan kwana uku.

a cikin ƴar bukkar Boka Barore su na zaune gabansa  sai fara’a su ke yi da alamu dai duniyar ta buɗe musu, Ma’u kuwa ta na gefe ta haɗe kai da guiwa tsirit da ita.
Hajiya Laure ta ce “Boka ɗana ya takura mini akan hakan, ban san ya  zan yi masa ba.”  Barore ya yi dariya sannan ya ce “Za mu rufe masa baki, ba zai ƙara hanaki yin abinda ki ke so ba”  ta ji daɗin hakan ta yi masa godiya kana su ka miƙe,  yau ma kwana uku ya basu su dawo.
Ma’u dai da kyar da kyar take iya tafiya, duk ta zama kamar sokuwa ba um ba um-um, su Hajiya Laure ma ƙyamarta su ke ji da sun kalleta sai su tsartar da yawu su yatsine fuska, da haka har su ka dawo gida.

Hajiya Laure ta yi Sa’a  da su ka shigo gidan duk ba kowa a kusa don haka ta yi sauri ta balbale Ma’u da masifa akan  ta je ta yi wanka ta dawo daidai,  cikin yanayinta me kama da sokunta ta aiwatar da abinda Hajiya Laure ta ce.
Ba laifi ta ɗan dawo hayyacinta sai dai tana nan sukuti da ita.

Husnee na kwance kan gado ta na malelekuwa kamar yadda ta saba don kwanan nan aikinta kenan, Mommy ce ta ƙwala mata kira, ta amsa cikin muryarta da ta gama dashewa, Mommy ta ce “Zaman ɗaki da kwanciyar nan naki ya isheni ya ishi kakata INDO  ba dole cuta ta ƙi warkewa ba ki na famar kwanciyar kamar ɗan malele? anyi allura ansha maganin amma abu ya ci tira, fito ni ki tayani girki ko kya ji ƙwarin jikinki.”
Da kyar ta iya amsawa da “to”  sannan ta yunƙura ta tashi ta na bibango sabida wani ɗan jiri-jiri da ke ɗibarta.

Ta na fitowa daga ɗakin daidai lokacin ƙullin asirin Boka Barore ya nufota gadan-gadan, ƙiris ya rage ya faɗa mata Razia ta faɗo kanta da ƙarfin gaske hakan ya sa ta ƙwalla ihu gami da faɗuwa gefe ragab, a take ta sassanƙare kamar gawar sababi.  tsafin Boka Barore kuwa ya faɗi ƙasa ya ƙone ƙurmus tuni ya bi iska ya san inda dare ya yi masa.

Hankali a matuƙar tashe Mommy ta yo kanta ta na kiran sunanta, ta na taɓata ta ji ta sandare komai na jikinta ya dena aiki sai zuciyarta ce kawai ke bugawa, Addu’o’i ta fara jerowa ta na tofa mata nan fa hankalinta ya ƙara ƙololuwa wajen tashi ganin Husnee ta fara kanannaɗewa  ta na wani irin lanƙwashewa kamar jikin tsutsa gareta, ma’ana dai tamkar ba ƙashi a jikinta.

Mommy ta fashe da kuka  ta na ƙara karanto addu’o’i gami da janyota jikinta ta rungume ta na ƙoƙarin  hanata lanƙwashewar sai dai kash abin ya ci tira.
Ta ɗebi kusan minti shidda cikin wannan halin sannan kuma jikin nata ya dawo daidai ya wani saki lakaf kamar gawar da ta samu ziyarta lahira yanzu.

wani azababben kuka ta saki ta na cewa “Mommy zan mutu kaina zai fashe  wayyo Allah na”  jin haka ya sa Mommy ta ƙara rungumota ta na cewa “Ki yi haƙuri Husna ai cuta ba mutuwa ba ce, ki yi ta addu’a za ki samu lafiya in sha Allahu.”    inaa kukanta kawai ta ke yi ba ji ba gani don ko fahimtar inda Mommyn ta dosa ba ta yi ba bare ma ta yi addu’ar, su na  nan zaune Mommy na Kuka Husnee na yi har wani lokacin kafin ta saki kai ta kama ciki  ta na kukan cikinta na ciwo,  ita dai Mommy ta ga tashin hankali, Ayatul Kursiyyu gami da Suratul Baƙarah da sauransu take  karantowa in ta saki wancan sai ta kama waccan gabaki ɗaya ta burkice.
Ta na cikin haka ta ji wani hucin zafi ya bugeta itama ta zame ta kwanta a wajen a sume.

Russlan ne ya yi dirar mikiya a wajen ko ƙasa bai sauka ba ya fizge Razia daga jikin Husnee su ka yi sama, nan take Husnee ta ji kamar cirar ƙaya sai dai ko yatsanta ta kasa motsawa ji take kamar an daddatsa ta da adda, idanunta ma kansu sun yi mata nauyin da ko buɗe su ta kasa yi, Mommy kuwa itama ta na kwance a sumenta  ba me tashin wani tsakaninsu.

Su na cikin wannan halin Muneeb ya shigo fakam-fakam tare da sallama bai bari an amsa ba ya ci gaba da cewa “Mommy  kin ganni  da wuri yau fita zan yi.”   da yake hanyar banɗakin tsakar gida ya nufa sam bai lura da su ba sai da  ya leƙa banɗakin ya fito da nufin ajiye wayoyi da tarkacen jikinsa kafin ya shiga wankan, nan fa idanunsa su ka yi alaragab da su a sheme.
cikin hanzari ya yi kansu ya na tambayar lafiya.

Ya na taɓa Mommy ya ji ta a sume zuciyarsa  ta bada rimm!! idanunsa ya kai kan Husnee da take zubda ƙwallar wahala ita ma ƴar siriri take bin gefen idanunta, hankali tashe ya ce “Ke Husnee lafiya??”  ba za ta iya magana ba  don haka bai samu amsa ba.
Ruwa ya lalubo ya  yayyafawa Mommy ai kuwa ta ja wani gwauron numfashi ta sauke ajiyar Zuciya sai kuma ta ci gaba da kuka ta na cewa “Ina Husna, kar dai sun ɗauke mini ita”  cike da mamaki da tsoro Muneeb ya ce “Me ya faru Mommy?? su waye za su  ɗauketa??”  ba tare da ta dena kukan ba ta ce “Yauwa gwara da ka dawo, ashe da gaske Aljanu sun hau Husnee kar ka ga irin wahalar da su ka bata”  ta yi maganar ta na ƙoƙarin tashi zaune, temaka mata ya yi ta Zauna, ganin Husnee kwance a kusa da ita ya sa farin ciki ya kamata,  goge hawayen ta fara yi ta na cewa “Kalleta nan kar ka ga yadda su ka dinga cukurkuɗa ta kamar ba mutum ba.”
sunanta ya kira ya na shafa gefen fuskarta cikin tausayawa, a hankali ta buɗe ido ta na kallonsa sai kuma ta ɓare baki ta kama kuka ta na cewa “Jikina ciwo ya ke yi   ji nake kamar zan mutu!”  ya ce ”Sannu kin ji, Allah i sauwaƙe ki dena cewa za ki mutu ai  mutuwa sai lokacinta ya yi.”  Mommy ta ce “Ɗauketa ka mayar da ita ɗaki, laifina ne ni nace ta fito.”  ta faɗa ta na goge hawaye.
Rungumarta  ya yi ya kaita ɗaki ya kwantar ya na  ƙara jaddada mata sannu.

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*
[8/21, 11:31 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 15

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

A ɓangaren su Russlan kuwa ya na yin sama da Razia bai zame ko ina ba sai gaban Uban Dawa,  ya na zaune kan haɗaɗɗiyar kujerarsa ta zinare  ya na jiran dawowarsu.
Russlan ya durƙusa a gabansa gami da cewa “Ga ta nan Father”  cikin ɓacin rai Father ya ce “Razia!  waye ya Ƴantaki daga ɗaurin da aka yi miki har ki ka fita?”  Cikin shashshekar kuka ta ce “Risslan fa……”  dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, shiru ta yi  ta na ci gaba da ɓarza kuka kamar za ra mutu don yinsa.
ba tare da damuwa da hakan ba ya ce “Maza a ƙara ɗaureta  ba na buƙatar ƙara ganinta.”  Russlan ya ce “To” kana ya damƙeta ya mayar da ita keɓantaccen  ɗakin da aka ɗaureta a wancan lokacin,  ta na kuka ta na komai amma haka ya yi mata banza ya aiwatar da umarnin da aka ba shi don kuwa shi ma ta gama kaishi maƙurar ɓacin rai.

Akhiee abin duniya duk ya ishe shi,  koda Russlan ya ba shi labarin abinda ya faru  ya kasa ma bambance tsakanin Husnee da Razia waccece ta fi hauka,  a gefe guda kuwa ya ji daɗin zuwan Razia kan Husnee don kuwa ta zo a kan lokaci tinda har ta yi silar  faɗuwar tsafin da aka turo mata ƙasa.

Bayan kwana uku

Hajiya Laure da Hajiya Saudah an koma wajen boka ana ta murna don duk a tunaninsu haƙar su ta cimma ruwa,  sai dai kashh yau ma kamar waccan ranar sai da ya tilliƙi dariya ya ƙoshi sannan ya fara da cewa “Aikin ku ya tarwatse!! hhhhhh!!!” Hajiya Laure ta zaburo ta na kallonsa sabida jin abinda ya faɗa, ganin ya na ɓaɓɓaka mata dariyar mugunta ya sa ta jefa masa harara ta bayan ido a ranta ta na cewa “Azzalumin banza”  shan kunu ya yi kana ya ce “Wata shaiɗaniyar Aljana ce ta zo ta ce-ceta,  hhhhhhh Barore ba ya taɓa karaya ba ya taɓa sarewa, dole ne sai mun cimma abinda mu ka sa gaba, hhhhh, ku ajiye kuɗi ku tashi, zan ta buga aiki har sai na yi nasara, da kaina zan kira ku indai buƙatarku ta taso, a duk lokacin da ku ka yi mafarkina to ku tawo ina nemanku!!!”  su ka amsa kana su ka zube kuɗi su ka tashi.

Kamar yadda Hajiya Laure ta saba mita kullum yau ma ta yi akan ta gaji da ajiye masa kuɗi kuma ba nasara, Hajiya Saudah ta  lallaɓata ta kwantar mata da hankali.

Ana kwana ana tashi gashi yau duk da faruwa abubuwan baya watanni biyu kenan.

Risslan ya samu lafiya tangaras har tabbai ma sun fara ɓacewa don shi jikinsa ba ya ajiye tabo da zarar ciwo ya warke tabo ma zai warke tamkar bai taɓa jin ciwo ba,  tini har ya fara baɗaɗin zuwa duk inda ya so kuma ya koma ruwa harkarsa ta da  sai ma abinda ya ci gaba.

Razia dai ta na can a ɗaure an ma manta da ita don in ba  masu kula da ita ba   ba wanda ya san ma inda take.

Husnee ma da sauƙi ta samu lafiya, ba yawan zazzaɓi da ciwon jiki irin na da sai dai har yau ba ta koma makaranta ba, sai kuma tunane-tunane ba dare ba rana kwata-kwata ba ta walwala kamar dai ba ita ba.

Tankar Yaƙi da me gidanta kuwa har yau suna tare
da yake ya san hannunsa sam bai nuna mata ta yi kuskure ba akan abinda ta yiwa yaransa har ɗaya a ciki ya mutu, sai ma haƙurƙurtar da ita da yake yi ya na kwantar mata da hankali,  a gefe guda kuwa abinda ya  ke nuna mata a zahiri ba shine a zuciyarsa ba,  ya riga da ya ƙudurce ɗaukar fansa akan Risslan kuma ba zai iya fasawa ba, burin da ya ke son  cimmawa shine kashe Risslan ɗin ita kuma ya mallaketa.

a ɓangaren Iyalin Risslan kuwa   sun ci gaba da gudanar da lamuransu cikin kwanciyar hankali, su na aiwatar da duk abinda ya umarcesu kuma su na barin wanda ba ya so,  shigo da Wiwi da sayar da ita kuwa ba kama hannun yaro ba abinda ya ragu sai ma ci gaba, ga ɓarna kamar ƴaƴan ɓeraye.
Rabi’u  tuni ya koma wajen Ummansa ya na tayata aiyuka kuma ya na zuwa makaranta ya bar iskancin da yake yi da.

Su Hajiya Laure dai har yau ba a amsa kiran Boka ba,  kuma gashi dai Risslan ya na ta yawatawa abinsa, da alamu har yau ba wannan nasara da su ke ta fata.

JD ne zaune kan hakimar kujerarsa ta alfarma ya  babbaje ƙafafu ya  turo uban tumbi gaba ya na waya da DCP Khashim,  wani irin shauki ne ke ɗibarsa har wani slow yake yi a maganar don ba ya so ta ƙare “Na gama tsara komai, a gobe Kano za ta yi baƙo, kuma a cikin satin nan al’amura za su fara gudana, kai dai ka zuba idanu za ka ga yadda zan ɗauki fansata ta hanyar da sai an gwammace fito na fito aka yi da ni.”
DCP ya murmusa  cike da jin daɗi ya ce “Wannan ai kyakkyawan Albishir ne JD  ni kaina ina buƙatar hakan don na gaji da ji da ganin labarinsa,  idan mu ka kawo ƙarshensha hukuma za ta zauna lafiya ba ciwon kai, haka kuma za mu dinga harƙallolinmu  cikin kwanciyar hankali.”
JD ya yi dariya irin ta ƴan duniya kafin ya ce “To kai DCP Banda abinka idan wannan ya na raye a duniya ai hawan jinina ba zai sauka ba, kwantar da hankalinka kawai ni na dafe kan.”
Tattaunawa su ka ci gaba da yi sannan su ka yi sallama kowannensu ya na ta farin cikin sun samo mafita.

Daren yau kwana ta yi ta na mafarkin Akhiee da kuma Makaranta don haka duk ta tashi hankalinta akan sai ta je ko za ta ganshi, Mommy dai ba ta hanata ba.
cikin riga da siket na atamfa tsadaddiya ta shirya sannan ta zura hijab ɗinta light blue ta futo.
Shi kansa Amadu ya yi mamakin jin cewar za ta je makaranta amma ko kaɗan bai nuna mata ba don ya lura ta zama Sarƙa me rikicin gangan, yanzu ya na yin magana za ta iya ɓare masa baki daga haka sai zazzaɓi da ciwon kai su hau.

Risslan  ya na tsaye  Hannunsa ɗaya riƙe da Wiwi ɗayan kuma ya riƙe kwankwaso, cikin salonsa me matuƙar burgewa da jan hankali ya ke zuƙarta ya na busarwa ba tare da wata damuwa ba.

Acibalbal da Zare su ka shigo Tafkeken ɗakin tare, bakinsu ɗauke da sallama, ba su jira ya amsa ba su ka ci gaba da zabgo masa kirarinsa kamar yadda su ka saba.
a hankali ya fara takawa ya juyo ya na fuskantarsu kafin ya matsa gefen gadonsa ya sa hannu ya ɗebi wasu haɗaɗɗun IV  wato Katin Ɗaurin Aure.

Cikin ƙasaitaccen takunsa irin na namijin Zaki ya isa gaban Zare ya na Zuba masa rikitattun idanunsa.
Ganin irin kallo me tafe da saƙonni da ya ke aika masa ya sa zuciyarsa ta fara tsalle tin kafin ya ce abinda zai furta.

Miƙa masa IV ɗin ya yi gami da cewa “Duba wannan”  ya yi maganar cikin sassanyar muryarsa me daɗi kamar busar sarewa.
Idanu a waje Zare ya karɓa ya shiga dubawa cike da fargaba da tashin hankali.
Kafin ya gama karantawa zuffa tuni ta fara yanko masa ta ko ina,   Bai yu ƙasa a guiwa ba ya zame ya dire guiwoyinsa a ƙasa, kamar zai yi kuka ya ce “Sarƙa Wallahi tallahi ba laifina ba ne  ba ni na sa su buga ba,  ga Acibalbal nan nasan zai shaideni, Allah ɗaya kenan ba ni na sa su ba.”
Akhiee ya ja wiwi ta tsarga masa kana ya furzo da hayaƙinta ta baki da kuma hanci, a ƙasaice yace “Ba kai ne da Alhakin buga IV ba ai, ni ne  don kuwa ka na ƙarƙashin kulawata,  soyayya  ka fara   ni kuma ba na buƙatar shiririta shi yasa na buga Iv a wannan Jumu’ar na ke so a ɗaura auren”
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un!!!”  shine abinda Zare ya shiga maimaitawa cikin kaɗuwa da tashin hankali.

Shiru wurin ya ɗauka kafin Zare ya samu ƙwarin guiwar cewa “A yafe min Ya Babba, Wallahi Tallahi ban tashi yin aure ba yanzu,  ni da ko kaina ba na iya riƙewa ta ya zan iya riƙon iyali?  a bari sai nan gaba ba yanzu ba don Allah”   tassss!!!!!  Risslan ya kwasa masa wani azababben mari wanda ya sa taurarin azaba su ka shiga gilma masa na wucin gadi.

Sai da ya juya musu baya kana ya ce “Ba na son yaudara kuma ba na son shiririta, ka san ba aurenta za ka yi ba ina ruwanka da ita?  meye haɗinka da soyayya??   Ba na so ko na lokaci ɗaya ku bari Mata su shigo rayuwarku, Mace ba komai ba ce face Rauni,  itace Lagon kowane Namiji, Mace haɗari ce ga Mutane irinmu  zamanmu babu su ya fi mana Alkairi akan tarayya da su,  daga yau sai yau kar wanda ya ƙara saurarar duk wata Mace, duk wanda ya yi hakan kuma zan sallameshi sannan zan zare hannuna daga huruminsa bayan na aurar da shi na yi masa duk abinda yake buƙata.”
Jiki na tsuma Zare ya ce “An gama Sarƙa me rikicin gangan!!, Ba za a kuma ba,    ba ni ba mace daga yau,  umarninka shine abin dubawata Oga, Na tuba  ba zan kuma ba.”
Jinjina kai ya yi kafin ya ce “A ƙonasu,  a kawo mini Prince!”  haɗa baki su ka yi wajen amsawa kana su ka bar fadar ta shi.

Su na kawo Dokin ya hau ya fice kai tsaye ya nufi makaranta.

Husnee na tsaye wajen famfo ita kaɗai tamkar Aljana ta yi zugum ta na tunaninsa kawai ta ganshi kamar an jefo shi daga sama,  murza idanunta ta yi ta ƙara zaro su      wai ko  gane-gane ta fara yi,  cikin sauri ta kora sunansa “Akhiee!!!”  cakk!!  ya tsaya shi bai yi gaba ba shi bai yi baya.

Yanzu ta tabbatar shine ba gizo idanunta ke yi mata ba, saɗaf-saɗaf ta ƙarasa kusa da shi cikin sanɗa, har lokacin ya  na tsaye sai dai ko kallon inda take bai ba,  a gabansa ta tsaya ta na fuskantarsa idanunta na kanshi ta na binsa da kallon yaushe gamo,  murmushin  farin ciki tuni ya gama mamaye fuskarta,  cikin sanyin murya ta ce  “Akhiee ciwonka duk sun warke, na ji daɗi.”
Sai a lokacin ya kalleta sai kuma ya ɗauke kai,  a miskilance ya ce “Na zata ba zan ƙara ganinki ba?  me yasa ba za ki girmama maganata ba? shin ba na ce kar ki ƙara bari na ga fuskarki ba?”
Murmushi me tafe da hawaye ta yi gami da cewa “Hmm!!! Risslan kenan,  ka yi tunanin don ka yi mini wannan kurarin zan iya rabuwa da kai kenan?  abin da kamar wuya in iya ɓamɓare kaina daga gareka, ba yin kaina bane haka kawai na wayi gari cikin mugun hali  dominka,  da alama Ruhina ya na buƙayar kasancewa tare da naka domin samun salama; Akhiee ko da Mutuwa zan yi ina so in mutu dominka ko kuma in ce ma tare da kai, ba zan iya bin umarninka ba domin na riga na yi nisa ba zan ji kira ba.”
“Idan kuwa haka ne ki na cikin wahala, kuma ki sani ba za ki yi tsawon rai ba indai har ba ki nisance ni ba, na fi samun kwanciyar hankali da ba na  ganinki,  ina so Ki ƙara ɗaukar hutu kamar yadda ki ka yi a wannan lokacin.” ya yi maganar cikin ɓacin rai,
Ya na kaiwa nan ya raɓa kusa da ita ya na ƙoƙarin wucewa ya barta.

“Akhee!!!!”   rinannun idanunsa ya ɗaga ya zuba mata alamar ya amsa,  rintse idanunta ta yi zuciyarta na dukan sha-lugude  kamar ana shirin yin yaƙin duniya  na uku a cikinta, cike da jarumta ta ce “Akhee! Ina sonka”    “What!!!! are you serious???”   ya furta gami da ƙara tsareta da tsibbabbun idanunsa.
a hankali ta buɗe idanunta da su ka canja launi sabida tsananin fargabar da take ciki, murya na rawa ta ce ”Yes, I’m Serious,  I Love  You Akhiee!!   ba zan ƙi gaya maka ba ko da hakan zai sa ka kashe ni”    cikin tsananin zafin rai Akhiee ya yi taku uku zuwa gabanta, idanunsa masu bala’in kwarjini ya ƙara warewa akanta fuskar nan a murtuke kamar hadarin ya haɗo yake rugugi ya na shirin  zubda ruwa,  “Kin fara hauka kenan Asma’u??  ko kuma dama ke mahaukaciyar ce ban sani ba????”  cikin hargowa ya watso mata tambayoyin.     cike da ƙarfin hali irin  nata ta jefa idanunta cikin nasa tana cije gefen leɓenta,  cikin tsananin rurin azabar da zuciyarta ke yi ta ce “Yes!! ni mahaukaciya ce amma akanka na hau kace,  idan ba ka fahimta ba zan maimaita ina son…..!!”    tassss!!!!!!   ya wanke ta da wani fitinannen mari kafin ta ƙarasa furta kalmar da take son furtawa,  cikin hanzari ta dafe kumatunta gami da sunkuyar da kai ta runtse ido kanta ya na wani irin juyi kamar an buga mata baƙin ƙarfe,     a hankali muryarsa mai cike da barazana ta yi nasarar dawo da ita duniyar mutane saɓanin wadda ta faɗa  “Shin mahaifiyarki a  ruwan koko ta haɗiyi cikinki ta haifeki a lokcin??  ko ki na tsammanin iyayenki ba sa ƙaunarki?? ashe ke mahaukaciya ce ba ki san ciwon kanki ba??  ni a rayuwata babu mace domin mace ta riga ta mutu, saɓaninta kuma kowace macen Duniya rauni ce!!    ina me umartarki ki fita hurumina”  murmushin ƙarfin hali ta yi wanda ya yi daidai da zubowar zafafan  hawayen da suka cika kwarmin idanunta, sassauta murya ta yi sannan ta fara cewa “Akhiee!!!!!!  kenan sonka kuskure ne da har ka fara tunanin ba haifata aka yi ba?? shin wane laifi mace ta yi maka da kake yi mata wannan kallon? wadda ta mutu ta yaudareka ne??”   shiru ya yi na kusan 5  second sannan ya girgiza kai gami da cewa “No!!,  She’s my mother, and my confidence!!  Tin daga kanta aka gama mace..”   za ta yi magana ya katseta da cewa “Relax Asma’u, Listen  to me!      a gidanmu har guba ana zuba min a abinci sabida in mutu  don ba a son alaƙa da ni, meyesa ke za ki kawo kanki ga hallaka??  za ki mutu indai ki ka shigo rayuwata, kuma ba zan iya baki farin ciki ba, ni ba ni da shaukin So ko na wani abu    ni ba namiji ne kamar kowanne ba  ɗaukar rai kawai na sani bayan shi bansan komai ba, ba na so iyayenki su rasa ki shiyasa ba zan yarda ki shigo rayuwata ba, idan kika matsa kuma,  madadin na bari wasu su kashe ki da hannuna zan kashe ki, kafin ayi da kai ka yi da kanka!!”      murmusawa ta yi gami da gyara tsayuwarta. hallau cikin tausasawa  ta ce “I’m very happy  that it was you who will kill me. I’m listened to you, it’s good to listen to me!”
Wani mugun tsaki ya doka cikin matuƙar ɓacin rai ya ce “I Don’t have time for that!!”     ya na faɗen haka ko kallonta bai ƙara yi ba  ya juya ya nufi get ɗin  tafkekiyar makarantar,  cikin ɗaga murya Asma’u ta ce “Why Akhiee??”     ko gezau bai yi  ba  bare ta san ya jita  ya ci gaba da tafiyarsa.

har ya fice idanunta da ke faman zubar da hawaye tamkar an kwance dam  na kansa.
“Me ki ke yi a nan??” muryar Sheikh Auwal ce ta karaɗe  kunnuwanta,   sai da nunfashinta ya ɗauke na wucin gadi  sabi da tsananin tsoro da razani.
Rai a ɓaca ya ce “Ba magana na ke yi miki ba??”
Sai da kyar ta iya girgiza kai gami da magantuwa cikin muryar kuka, “Ba komai Ya Sheikh”   “Don me za ki ce ba komai bayan gashi na ga ki na kuka??  wai ba na taɓa gargaɗinki akan shiga hurumin Akhiee ba?  lokacin da ki ka zo makarantar nan me hankali da ke amma yanzi ya lalata ki kin zamo mara jin magana,  to tinda ba ki ji faɗan da na yi miki ba zan samu iyayenki sai in sanar musu halin da ki ke ciki, ba za mu lamunce wannan  lalata a cikin Islamiyya ba”  sake fashewa ta yi da kuka ta na cewa “Don Allah Don Annabi Ya Sheikh ka jiƙaina  kar ka gayawa iyayena,  wallahi ina son makarantar nan ina so na yi karatu sosai nima na zama malama idan ka faɗa musu cireni za su yi don Allah ka temaka mini”    Tabbas kalamanta sun ratsa zuciyarsa nan take tausayinta ya kama shi, shiru ya yi ya na ƴan nazare-nazare kafin ya ce ”Na haƙura amma ki sani indai ba ki fita shirginsa ba  da kaina zan koreki ba sai na memi shawarar iyayenki ba, kuma idan na koreki ba dawowa kin ji ko?”  da sauri ta gyaɗa kai ta na sauke ɓoyayyar ajiyar Zuciya har cikin ranta ta ji daɗi.
Ci gaba ya yi da cewa “Ki na so ki zamo Malama amma ki ka mayar da hankalinki akan  wanda ko fatiha ba lallai in ya iya ba?  ki san da cewa Akhiee  tin ya na yaro bai taɓa furta kalma ko guɗa ɗaya daga cikin Alƙur’ani ko Hadith ba;   duk zuwan da yake yi makaranta ba ya taɓa yin karatu komai yawan dukan da za mu yi masa, gashi yanzu har mun gaji kafin mu dake shi ma ana daɗewa sabida ya riga ya kangare ba ya jin dukan don ko kuka  bai taɓa yi mana ba,    ina fa gaya miki ne ba don ki yi koyi da shi ba sai don ki gane shi ba aboki na ƙwarai bane,  ki barshi ya yi rayuwarsa kema ki je ki yi taki.”  gyaɗa kai ta yi jiki a sanyaye ta ce “To zan kiyaye in sha Allah”   a zuciyarta kuwa abinda ta faɗa a zahiri ba shi bane don kuwa ba ta jin duk wanman zai sa ta iya  ƙauracewa Akhiee.

Yau ta na shirin fitowa zuwa makaranta  Zaheer ya yi sallama a gidansu,  tin da ta gaishe shi take son silalewa ta gudu amma Mommy ta hanata a cewarta don ita ya zo bai kamata ta tafi ta barshi ba, dole ta zauna ba don ta so ba sai zumɓure zumɓure ta ke yi  a zuciyarta kuwa ta sauke masa zagi yafi Cikin carbi dubu,  sai yanzu ma ta ke jin gabaki ɗaya ta tsane shi, a hakan kuma har an riga an  ba shi ita,  tunani ta ke ma da ta yarda ta Aureshi gwara ma ta gudu ta bar gidan kowa ya rasata.

Akhiee ne durƙushe a gaban Abhi  bayan sun gaisa  Abhi ya  ce ”Kai na ke ta nema Dattijo, Saudi Arabia  nake son a kaini amma tare da kai na ke son mu tafi.” zaro ido  ya yi gami da cewa “What? Abhi ni zan je Makkah yanzu? impossible Abhi a dai ƙara dubawa don Allah”  cikin matuƙar mamaki Abhie ya ce “What Happened Muhammad?  na ga ka sauya lokaci ɗaya,  ka tuna fa sau ɗaya ka taɓa zuwa Makkah   ya na da kyau ka ƙara zuwa,  a wannan karon ni dai ina son tafiya tare da kai.”
Gyara zama ya yi   ya koma  dafa’an murar kwaɗi kafin ya fara da cewa “Abhi………………….

(Sai Gobe😒)

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*
[8/22, 3:44 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 16

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

“Abhi Don Allah ka yi haƙuri  ku tafi tare da wani, yanzu ina yanayin da ba zan iya zuwa ko’ina ba, ga ka Kaka ta kusa ina buƙatat duk noman da na yi ayi aikinsa a gabana,  ga Hamza ko Adamu ko Jaafar  sai su rakaka, ni na yarda zam yi komai kawai sai ky tafi, ayi mimi afwa Abhi.”
Abhi ya jinjina kai ba don ransa ya so ba sai don jin an ambaci Gona,   “Lallai ya na da kyau ka zauna a gida sannan ya na da kyau ka ƙara ziyartar Makkah,  amma a wannan lokacin ka yi zamanka kawai  sai mu tafi tare da Jaafar.”
Ya na jin haka ya yi zaram ya ce “Yauwa Abhina ai na san akwai fahimta a tsakaninmu, ni yanzu bari in tafi zan je Gezawa ne.”
Abhi ya yi murmushi irin nasu na manya cike da ƙaunar ɗan nasa ya ce “Allah i tsare mini kai Dattijo, lallai a gaishe mini da Mutanen Gezawa.”  “Za su ji”  ya na gama faɗen haka ya miƙe bai ƙara yin magaa ba ya fice cikin sauri don kar Abhi ya ƙara taso wata maganar.

Ma’u na harabar gidan Hajiya Laure maƙale a jikin bango sai ɓarza  kuka take yi me cin rai da cin Zuciya, gabaki ɗaya ta rasa inda za ta  tsoma rayuwarta ta ji sanyin, tin lokacin da su Hajiya Laure su ka lalata mata rayuwa  duk ta rasa farin cikinta, gashi dai ta na son gayawa wani abinda ke damunta da ma abinda su ka yi mata amma ta kasa,  a duk lokacin da ta yi yunƙurin hakan sai ta ji kanta ya hau juyi ya fara wani bala’in ciwo  hakan ya sa dole ta haƙura.

da wannan sassafiyar Yazeed ya dawo daga gantalinsa don jiya bai kwana a gida ba.
Har ya wuce da nufin shiga ciki ya fasa  don jin sautin kuka da ya yi, saɗaf-saɗaf ya yo baya cikin sanɗa don har cikin ransa ya yi tunanin Aljanu ne domin kuwa sassafiya ce sosai.
Juye-juye ya fara yi don ganewa indonsa me kukan,  can gefe da shi kaɗan ya hangota ta rufe ido sai kukanta ta ke yi ba ji ba gani.
Ganin Ma’u ce ya sa hankalinsa ya kwanta tsoro ya gushe, idanu ya zuba mata har na ɗan lokaci kafin y  matsa kusa da ita, cikin muryarsa da maye bai gama sakinta ba har yanzu ya ce “Me kike yiwa kuka anan da sassafe kamar Aljana?”   zumbur ta matsa gefe ta na zaro masa idanu domin kuwa har ga Allah tsoronsu ta ke ji daga shi har Mominsa,  tuni ta fara kiciniyar tsayar da kukan don kar ta ɓata masa rai har tarihi ya ƙara maimaita kansa don ta san shima tamkar bunsuru haka yake don neman mata.
Ga mamakinta sai ta ji ya karya murya  ilai ya na ƙara cewa “Me aka yi miki?  ko kin gaji da aikin ne?”
Girgiza kai ta yi alamar a’a gami da cewa “Ba komai.”    Jinjina kai ya yi kafin ya ce “Hmm!  to maganar gaskiya kin iya ƙarya,   dama ina lure da ke  kin daɗe ba kya walwala kamar da,  kuma kina yawan kuka  daga ganin idanunki ma ai amsan kin yi,  yanzu ma Allah ne kaɗai ya san adadin lokacin da lika ɗauka ki na kukan.”
Ƙasa ta yi da kai ba tare da ta ce komai ba  don kuwa ba ta da bakin magana, ba ƙarya ya yi ba gaskiya ya faɗa sai dai ba za ta iya gaya masa abinda ke damunta ba.

sun ɗan ɗebi lokaci a tsaitsaye kamar Dangin soja kowa da abinda yake tunani a ransa,    shi kuwa Yazeed sai zubawa kyakkyawar fuskarta ido ya ke yi,  shi tuni ɓa ya manta akan me suke magana ya tafi wani tunanin.
Ta na shirin zamewa ta koma ciki ya dakatar da ita da cewa “Kin yi baƙi da yawa ya kamata ki fara Bleaching.”  ido ta zaro masa kamar za su faɗo ƙasa cike da mamakin jim furucinsa.
Wani sassanyan murmushi ya sakar mata wanda shi kansa bai san lokacim da ga kufce masa ba, cikin wata  kasalalliyar murya ya ƙara da cewa “Ki na kyau sosai musamman ƙwayar idanunku, shi yasa  na ke son kallonki a koda yaushe, hakan ne ya ba ni damar gane ki na cikin damuwa tin ba yau ba,  amma kinsan wani abu? sam ba na son ganin mace Baƙa na fi son Fara shi yasa ma na ce ki fara Bleaching sabida za ki fi kyau.”

Zuwa yanzu Zuciyar Ma’u ta koma tamkar ganga sabida yadda take bugawa da ƙarfi kuma akai akai,  Cikin rawar baki ta ce “Ka yi haƙuri ba zan iya ba,  ni gwara na zauna a yadda Allah ya bar ni, Rayuwata ma sam ba ta da amfani, ni yanzu jiran mutuwa kawai nake yi za ta fi mini sauƙi akan rayuwa.”  Ta ƙarasa maganar gami da fashewa da wani sabon kukan.
“Oh! Ashsha ai ban san abin ya yi zafin haka ba, Mutuwa ki ke son yi Ma’u?  to mutu mana?  ni zan kawo miki guba ma ki sha  ala raka tali gona,  da wata baƙar fuskarki”  ya faɗa ya na gyatsine fuska,  daga haka ya wuce ciki ya barta nan,  da harara ta raka shi  har ya ɓacewa ganinta kafin ta zame a wajen ta na cewa “Allah ya isar mini abin da ku ka yi mini, ai idan kun fi ƙarfina ba ku fi ƙarfin Allah ba.”
Nan ta zame ta kwanta ta na ci gaba da kuka kaɗan-kaɗan har bacci ya yi nasarar sunkutarta.

Yau ta kasance Ranar Asabar  hakan ya sa Husnee ta shirya tsaf domin zuwa Islamiyya da safe.
ta na jefa ƙafarta a harabar makadanta ta hangi Akhiee a sunkuye ya na gyara takalminsa,  ba ta san lokacin da murmushi ya zuɓuce mata ba, har cikin rai ta yi matuƙar farin cikin ganinsa, da sauri ta ƙarasa kusa da shi cikin taku wanda ba zai ji motsin tawowarta ba,  har lokacin ya na sunkuye don haka ta dunƙule hannunta tamau ta ɗaga za ta ɗirka masa dundu ta gudu don ta tsokane shi,  sai dai kash!!! ta na kai hannun kansa ta ji ya maƙale   a take wata azaba ta ratsata wadda ta ji tamkar hannun ya karye.
Ƙara ta sako gami fa ƙwalla masa kira,  ya ɗago ya na kallonta cike da mamaki.

Har lokacin hannun nata azaba yake yi sai ƴar ƙaramar ƙara take saki idanunta tuni sun kawo ruwa,  a taƙaocr ya ce “Ya akai?”  kamar za ta yi  kuka ta ce “Tsokamarka zan yi na zo dukanka kawai na ji kamar hannuna ya karye, sai zafi yake yi mini tamkar ƙashushuwana sun rugurguje.”
Lokacin da ya  ta kai ƙarshen maganar ƙiris ya hana ba ta fashe da kuka ba amma sai ta maze  ta cuje bakinta da ƙarfi.

Hannun nata ya zubawa ido kafin ya ce “Ba ki nemi izimin dukana ba, ta baya ki ka zo shi yasa?”  baki ta saki  ta na kallonsa  cike da mamakin abinda ya faɗa  “Me kake nufi da hakan?”   ɗan matsowa ya yi kusa da ita kana ya ce “Allah ne ya yi ba za ki ci zalina ba, nan gaba sai ki kula kar ki jawowa kanki babbar jinya.”
Daga haka ya ratse zai ci gaba da tafiya ta yi saurin shan gabansa   ta na murmushi ta ce  “Akhiee jiya Yayana ya zo daga Kaduna,  in ce ya zo ku gaisa?”  zuba mata idanu ya yi yana ƙara yaba girman wautarta  ta wurga shi Duniyar  tunani sai da ya ji ta ƙara cewa “Ka yarda?”  sannan ya ja numfashi ya sauke,  a taƙaice ya ce “A matsayinsa na wa?  meye alaƙata da shi da zai zo  mu gaisa?  ni ba na buƙatar hakan ya sha zamansa, ke ɗin ma ba na fatan ƙara ganinki.”
Turo baki ta yi zuciyarta sam ba daɗi,  ba ta ƙara ce masa kanzil ba ta wuce cikin aji cike da tausayin kanta.

Jikin bango ya koma ya maƙale sannan ya zaro Wiwi ɗinsa ya bata wuta, sai da ya yi ja uku sannan ya ciro wata ƴar Keypad  ya yi latse-latse a cikinta  sannan ya kara a kunne.
Shiru na kusan sakanni bakwai kafin ya buɗe baki  ya ce “Yau Dodon Lungu zai shigo Fagge sabida bikin Abokinsa,  a wannan wasan  da za su yi nake so  ku ɗanɗana masa kuɗarsa,  Yaransa Uku kawai na ke so a kashe bayan su kar a ƙara mini,  sannan ina so duk su ji a jikinsu musamman shi ɗin da yake jin ya kai.”
a ɗaya ɓangaren  Wuta ya ce “An gama Ya me Jama’a,  jiya wasu ƴan- sanda su ka kawo mana hari yankin nan wai sai sun kama Wiwi nace ai Ogana ya fi Ƙarfin wannan.”
Risslan ya ce “Yanzu ba wannan ba  ina so ku aiwatar da abinda na ce kuma cikin salo yadda zai ƙayatar da ni.”
Wuta ya ce “Kamat an gama da yardar Rabbi.”
bai ƙara cewa komai ba ya katse wayar gami da soketa a Aljihu.

ya na ƙoƙarin shiga Aji wata wayar ta shi  ta fara ƙara,  zarota ya yi ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa tare da yin shiru.
a Ɗaya ɓangaren cikin Muryar kuka ta ce “Zakiyya da  Farhana ba a gansu ba Muhammad tin jiya mu ke nemansu amma har yanzu shiru,   wai sai yaushe ne wannan abin zai zo ƙarshe? na san an ɗebe su ne domin a ci galaba akanka  wai me yasa ba za ka watsar da harkar nan ba Muhammad?”

Shiru ne ya ratsa tsakani  na ɗan lokaci kafin ya ce “Me yasa  ba ku gaya mini da wuri ba?”
“A tunaninmu abin bai kai haka ba, ashe har ya wuce nan,   mun ƙi gaya maka ne don kar hankalinka ya tashi  amma yanzu ya zama dole ka sani domin kai ne Babansu.”
“Relax Rahma!  in sha Allah za a gansu, ki dena kuka Please”    numfashu ta ja  ta na ƙoƙarin tsayar da kukan, cikin sanyin murya ta ce “Shi kenan, amma ina so ka sani da ni da su duk   da kai mu ka dogara,  sai anjima”  daga haka ta katse wayar.

Bin wayar hannunsa ya yi da kallo cikin tashin hankali da mamaki sai dai a kan fuskarsa sam babu wata damuwa.
A gefe guda kuwa tunanin wanda ya yi masa wannan ɗanyen aikin yake yi.

Tsugunne ba ta ƙare ba, an sayar da Biri an sayi Mage, don haka bai ga ta zama a makaranta ba.
CP  ya turawa kira, har ta katse bai ɗauka ba sai da ya ƙara kira sannan ya ɗauka.

“Yallaɓai akwai damuwa fa!”    Rass ƙirjin CP ya buga da sauri ya ce “What Happen Risslan?”
“An sace mini yara guda biyu, kuma Mata,  hankalina ya tashi domin kuwa an samu wanda ya iya gane Lagona, za su yi mini illa ta ɓangaren iyalina,  amma ba komai ina so ka tayani binciken waye ya ɗaukesu da kuma wanda ya sa a aikata, sannan ina buƙatar in gansu.”
CP  ya jinjina kai kafin ya ce “Gaskiya  kuwa in haka ne an samu matsala, amma su da aka rasa in sa Allah za su dawo,  ba za su iya yin galaba akanka ta kowace hanya ba,  ya kuma zama dole ka ruɓanya tsaro ka sa taka-tsan-tsan  akan duk waɗanda su ka shafeka, domin da alama kowaye ya aikata hakan ba ƙaramin shege bane don ba wanda ya san ka na da iyali bayan wanda ake ganinku tare,  lallai ka kula nima zan yi iya ƙoƙarina daga nan.”
“Okay”  kawai ya ce ba tare da ya ƙara magana ba ya katse wayar.

Yasayyadi Usman Jaafar Adamu Hamza, su na zaune suna tattaunawa akan batun Abhi da Akhiee.
Adamu ne ya taɓule baki kafin ya ce “Wallahi ina jin haushin wannan son kai na Abhi, ban san me yasa ba ya fi son lalataccen Yaron nan.”
“Aikin banza kai ma ba ka ji ance lalataccen Ɗa ya fi shiga rai ba?”  Hamza ne ya yi maganar cike da tsanar Akhiee.
Jaafar ya ce “Ni ba wannan ne tashin hankalina ba,  wai Makkah na fa ya ke son zuwa amma Abhi duk yawan ƴan gidan nan da yayyen Akhiee ɗin waɗanda  da can su suke kai shi Makkahn amma wai yanzu Akhiee ya nema, shi kuma sabida munafurci har da wai shi zai yi komai.”
“Ai ba zai yuwu ba, ba za  mu  bari akai Mahaifinmu Makkah da kuɗin Haram ba ya zama dole mu nemi  Yaya Sani  da Yaya Bello mu sanar musu  tsiyar da ake shirin tufkawa, ko Sheikh Auwal ma ba za mu bari ya sani ba in sun ji sai su sanar da shi.”
Adamu ya ce “To banda abinku ai Sheikh Auwal ɗin ne ya ke ɗaure masa,  wallahi shi ya ke goyon bayansa shi yasa ma ba ya jin maganar mutane, munafukan banza.”
Yasayyadi Usman ya ce “Ina sane da su ai, kar ku damu mu ma lokacinmu zai yi ai.”
Jafaar ya tafka tsaki kafin ya ce “Ni fa da ni na ke so a je Makkan nan idan an tashi, ato! ”
Adamu ya ce “Yo dama kai Abhi ɗin ya ce ai bayan Akhiee sai ku yi ta tafiya Allah i tsare.”
A gadarance Jaafar ya amsa da “Amin”   surutu su ka ci gaba da yi akan Akhiee kowa na tofa tashi.

A ɓangaren Akhiee komai ƙara cin tira yake yi, don kuwa gashi har wuni ya na neman ƙarewa la’asar ta yi ba a ji ko da labarin su Zakiyya ba.
ɓacin rai da takaici sun yi masa caa!  ya ma rasa me zai yi gabaki ɗaya.

Sai la’asar ɗin ya shigo makaranta shima ba don ya so ba sai don ya rasa inda zai je ya ji daɗi.
Bai bi takan kowa ba ya wuce inda ya saba tsayawa.
Idanunsa a ƙasa ya na tunanin ta inda zai ɓullowa lamarin wanda ya ke bibiyarsa kamar daga sama ya ji Muryar Husnee a kusa da shi……

“Ai na zata ba za ka zo ba”    kallonta ya yi kafin ya doka tsaki cikin ɓacin rai ya ce “Wai ke kunnen ƙashi gareki ne??”
Jingina ta yi a jikin makari ta na murmushi, cikin sanyin jiki ta ce “Kunnena  irin na kowa ne,  ka yi haƙuri Akhiee na ma yi ƙoƙari da na jure rashinka na ƴan lokutan da su ka wuce a baya,  ni fa da gaske da kai nake so na yi rayuwata,    kuma idan ka shiga tsakanina da kai to tabbas abinda ba ka so na zama zan zama,     ba za a kuma ganina a makarantar nan ba, kwanan gidan iyayena ma zai gagareni, nima zan lalace na dawo irinka,   bai zama lallai ka yarda ba amma za ka gani a aikace.”
“To wai ke me kike so na yi miki?  na gaya miki  shiga  rayuwata  ba burgewa ba ce,  ban yi miki wani abu na ƙuntatawa ba duk da irinn takurawar fa kike yi mini, na kasa ɗaukar mataki akanki,  har yau kuma ki na samun damata, to me ya rage miki? ni na ce miki ban san menene so ba.
“To Akhiee tinda ni na so hakan ai ban damu da sai na burge wasu ba indai na burge kaina, dan dai ka na ganin kamar da wasa na ke yi maka ne, amma har cikin raina ni ina ƙaunarka, ban damu da halinka ko wani abu ba iya abinda na sani shi ne ina sonka!”

Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci sanna Akhiew ya katse shirun da cewa “Kin shirya Rayuwa da ni?”
Lumshe ido ta yi ta na murmushi cikin ƙwarin guiwa ta ce “I’m ready”
“Okay good, i want you to vote for me”
Idanu ta zuba masa cikin sauri ta ce “Ban fahimci inda maganarka ta dosa ba.”
gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce “Ina nufin ki zaɓeni  ki bar kowa, in kin yi hakan shine zan san ki na tare da ni duk rintsi duk wuya, nima zan fi jin daɗin kasancewa a tsaginki”  ya yi maganar ya na zuba mata kaifafan idanunsa, sai da ta sunkuyar kai sabi da kallon da yake binta da shi, ta ɗan numfasa sannan  ta ce “I already voted for you,  tin tuni kai na zaɓa shi yasa ma na gaya maka iya gaskiyata”
Cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa ya ce “Kin tabbata?”
kai ta gyaɗa gami da cewa “Eh”

Bai ce uffan ba ya kama tsintsiyar hannunta ya shiga janta,  da kallo ta bishi a ranta ta na tambayar kanta  ina zai kaita?   kuma gashi ta kasa cijewa ta dena binsa.
Haka ya ratsa jama’a da ita ba tare da damuwa da kallon da ake yi musu ba,  sai da su ka dangana  da wajen da Amadu ya ajiye mota sannan ya tsaya,   daidai lokacin Zara ta ƙaraso da gudu-gudu hankali tashe ta ce “Ina za ki je Husnee??”   “Nima ban sani ba tambayi Akhiee”  ta faɗa  ta na kallonsa.
“Ki koma makaranta kar ranki ya ɓaci”  ya faɗa  ya na zuba mata wani shegen kallo wanda ya sa ta yi saurin juyawa.

Amadu tuni ya fito daga cikin Motar  cike da mamaki ya ce “Lafiya dai?”   Akhiee ya ce “Ki shiga mota  Ni zan tafi akan Dokina, amma kar ku bari na ɓace muku  duk inda na yi nan za ku yi.”
Amadu ya ɗan yi gyaran murys cike da tsoro ya ce “To Malam ina za mu je haka?”
Rikitattun idanunsa ya watsawa Amadu gami da cewa ”Kar ka bari  ka yi mini ba daidai ba.”  daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Dokinsa.

Husnee dai sai rarraba ido ta ke yi   duk ta rasa ma tunaninta gabaki ɗaya.
Amadu ne ya katse mata tunani da cewa “Innata ki na ganin mu bi shi ko kuwa?”  buɗe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba hakan ya sa shima ya shiga   ya bata wuta ya shiga bin bayan Akhiee.
Bakin wani masallaci ya tsaya  wanda Almajirai ke ta karatu a ciki da wajensa.
wajen Motar ya dawo  ya ɗan leƙa gami da cewa ”Ki jirani anan Asma’u!  kai kuma ka zo mu shiga ciki”  gyaɗa kai ta yi gami da sa hannu ta buga tagumi ta na  tunanin abinda ke shirin faruwa  sai dai duk iya nazarinta ta kasa fahimtar komai.

A cikin Masallaci kuwa gaban Babban Malamin Makarantar Allon su ka durƙusa daga shi har Amadu.
Malam Kabiru da fara’a akan fuskarsa ya ce “A’hh!  yau ɗan namy ne a gabana haka?”
Akhiee ya ce “Ni ne Baba Kabiru, wata  alfarma na zo ayi mini.”  Malam Kabiru ya jinjina kai cikin dattako da manyance ya ce “To ina saurara  Allah i sa abinda bai fi ƙarfina ba ne,   duk ya wajen manyan ina Baban naku ya na lafiya?  kwana da yawa ban zo mun gana ba”
Akhiee ya gyara zama sannan ya ce “Yana lafiya,  Aure nake so a ɗaura mini a yanzu-yanzu, Baba Kabiru  kai Aminin Mahaifina ne, hakan ne ya sa ba ni da wurin zuwa ayi mini haka in ba wurinka ba”
Kamar saukar aradu haka Malam Kabiru ya ji maganar Akhiee ta faɗo masa, tsananin mamaki da kaɗuwa su ka lulluɓe shi lokaci ɗaya, sai dai abin manya sam bai nuna alama ba, cikin nutsuwa da kuma tattausar murya ya ce “Muhammad! Aure fa ba abin wasa ba ne, idan har da gaskr ka ke yi mini  me yasa ba ka sanarwa Mahaifinka da ƴan-uwansa ba?  me yasa kuma sai yanzu-yanzu kake so a ɗaura?”
Sam ba ya son yawan tambaya don kuwa ransa ɓaci yake yi, amma da yake Malam Kabiru tamkar uba yakw a wurinsa sai ya danne.

Kai tsaye ya ce “Ba buƙatar kowa ya sani har sai bayan anyi,  ka manta da batun gaya musu kawai.”
“A’a fa,  ko ba ka so Malam Muhammad ya sani ai ya kamata ko yayyenka ka sanarwa,  Muhammad Aure fa ba a yi masa gaggawa, idan aka jira lokacinsa ya yi sai a yi shi cikin kwanciyar hankali,  kafin Ɗaura Aure ana buƙatar Dangin Ɗiya domin a gana a san juna kuma a nemi yardarsu.”

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*
[8/24, 9:23 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 17

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

“Wannan shine Wakilinta”  ya faɗa ya na nuna Amadu, kafin ya ɗora da cewa “Ni kuma kai za ka yi mini komai;  Ba na so na aikata ba daidai ba shi yasa na ke bin komai a maslaha.”

(Ohh! ni Indo su Amadu an zama Wakili🤣)

Zaro ido Amadu ya yi cikin matuƙar razani da firgici ya ce “Iye? wallahi Malam Allah ɗaya ba zan iya ba, a je a nemo wani dai don Allah.”  wani shegen kallo Akhiee ya aika masa wanda ya sa shi saurin haɗiye surutun nasa.
Malam Kabiru ya san halin Akhiee sarai, zai iya tuɓe rigar kunya ya zuba masa rashin mutunci duk da cewar Abokin babansa ne don haka ya jinjina kai kana ya ce “Shi kenan, na san zan iya yi maka komai amma  ina son sanin dalilin da ya sa kake so ayi hakan.”
“Ina so ta dawo ƙarƙashin kulawata ne  sabida za’a iya cutar mini da ita idan na tsaya ɓata lokaci,  Yanzu abin da za’ayi ka tattaro dattawan Abokanka ɗinnan ku yi komai tare.”
Malam Kabir ya ce “To Sadaki fa?”
“Yanzu za a kawo”  ya faɗa a taƙaice.

Malam Kabir dai a gefe cike yake da fargabar ɗaura auren don  kar wani abun ya je ya zo, a gefe guda kuma ya na shakkar iya shegen Akhiee,  don haka ba shi da zaɓin da ya wuce ya ɗaura Auren kawai a huta.
Ɗaya daga cikin Ɗalibansa ya tasa  ya ce ya je ya gayyato masa Dattawan da ke zaune a wajen Masallaci.

Ba tare da wata daɗewa ba suka shigo Tare da su Salansa.
Kusa da Akhiee ya zauna sannan ya miƙo masa kuɗin, Akhiee ya ce “Ka lissafa?”   “Eh Dubu Tamanin ne kamar yadda ka ce”  bai ce komai ba ya miƙawa Malam Kabiru gami da cewa “Ga shi nan idan da ciko su yi bayani zan basu ko nawa suke buƙata.”
Malam Musa ne ya dubi Malam Kabir cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya ce “Me za a yi ne Malam?”

Dalla- dalla Malam Kabir ya yi musu bayanin duk abinda ya faru da kuma wanda zai faru anan gaba,  ba su yi musu ba su ka gyara zama domin ɗaura Aure.
Malam Kabir ya miƙawa Amadu da ya gama rikicewa kuɗin gami da cewa “To gashi, idan an yiwa iyayenta bayani idan suna buƙatar wani abin sai a sanar”  Amadu ya karɓa hannunsa na rawar mazari, ko uffan ma ya kasa cewa.

Tare da sauran Ɗaliban Malam Kabiru manyansu da yaransu aka ɗaura Auren.  Bayan an gama su Gwaja su ka kawo Alewa da Biskit da Dabino aka rarraba, sannan kowa ya san inda dare ya yi masa.

Akhiee ma sallama ya yiwa Malam Kabiru sannan ya fito, su Salansa na biye da shi ciki kuwa har da Amadu da jikinsa duk ya gama mutuwa.
Ta na ganin sun fito ta fito daga cikin motar ta tsaya ta na binsa da kallo.
Tinda su Gwaja su ka faɗa mata abinda aka yi ta fara kuka  ta cika da tsoro da fargabar abinda za ta tarar a gidansu.
Har ya ƙaraso inda take shi take kallo har  ya zo gaf da ita,  idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali ya zuba mata ya na jin kukan nata har  cikin ransa, wani farin hankicif ya zaro a Aljihunsa ya fara goge mata ƙwallar ya na hura mata iskar bakinsa a hankali, hakan ya sa ta fara fizgar numfashi ta na sauke ajiyar Zuciya,  cikin wata tattausar murya wadda duk wanda ya jita zai so ya ƙara saurarenta ya ce “I’m so sorry Asma’u,  ba ni da zaɓin da ya wuce haka, Allah ya riga ya  ƙaddara ke ce abokiyar rayuwata,   kuma abubuwa da yawa  na cutarwa su na bibiyar rayuwarki  shi yasa na yanke wannan hukuncin, da zarar na kai ki gidanmu babu wani abu da zai ƙara barazana wa rayuwarki sai dai in kin fito daga cikinsa.”
ɗan jinkirtawa ya yi  kafin ya ci gaba da cewa “Ki dena kuka, ko da duk Duniya za ta juya miki baya ni ina tare da ke, tinda ki na so na a ganina ba abin tashin hankali ba ne hakan, kuma ba na yi ne dan na ɓata miki ba sai dan ba na son na ga kin cutu, ki na da muhimmanci a rayuwata kuma ke ta musamman ce a wurina;  Yanzu ki bi Amadu ya kai ki gida kafin na zo Ɗaukarki.”
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa zuciyarta cike da tunane-tunane,  ganin ta kasa ko motsawa ya sa shi kamo hannunta ya buɗe mata motar gami da cewa “Shiga mana”  shigar ta yi har lokacin ba ta ce ko uffan ba,  wata tamfatsetsiyar waya ya zaro cikin Aljihunsa ya miƙa mata gami da cewa “Ga wannan a koda yaushe idan ki na nemana za ki  sameni,  lambobin ciki duk nawa ne.”
Karɓa ta yi gami da gyaɗa kai ba tare da ta yi magana ba,  ido ya zuba mata  a ransa ya na jin kamar  ya tafi da ita tin a yanzu sai dai   ya na so  iyayenta su fara sani ya ga iya gudun ruwansu, don ya san mawuyaci ne su amince da shi.
Cikin sigar zolaya  Salansa ya ce “Me House ko za ka bi ta ne?”
rufe motar  ya yi gami da yin baya,  Su Salansa kuwa sai dariya suke a ciki-ciki don kar ya ji su.
Amadu ne ya matso kusa da shi kamar zai fashe da kuka ya ce “To Yallaɓai ni dai wannan ƴa a matsayin amana take a wurina da zarar na rabota da gidan iyayenta, sai gashi yanzu kai kuma ka mallaketa ta hanyata ba ta hanyar iyayenta ba, nima na shiga matsala ban san wane kallo za su yiwa hakan ba,  ina fatan ba don cutarwa ka yiwa wannan baiwar Allah haka ba.”
Dafa kafaɗarsa ya yi kafin ya fara magana cikin salonsa na izza “Ita ɗin matata ce kuma mallakina,  Ka kula mini da ita sosai,   ba ka cikin matsala don kuwa ina da kafaɗun da zan iya ɗaukar komai akanta, inda zan iya cutar da Asma’u da na daɗe da rabata da rayuwarta ko kuma wani abu mafi muhimmanci nata,  ku je kawai a gaishe mini da mutan gidan”.
Amadu ya jinjina kai, yanzu ya samu ƙwarin guiwar da zai iya komawa gidan  saɓanin da da  ya cika da tsoro.

Sai da motarsu ta bar layin sannan Akhiee da tawagarsa su ka ɗaga.
Kai tsaye  Makwantarsu su ka koma inda suke yiwa laƙabi da suna Masarautar Sarƙa.
Har cikin Fadarsa su ka raka shi a memakon su bashi wuri kuma sai su ka zauna su ka mamaye shi, kowa cikinsa cike taff da tambayoyin da yake son yi masa, ciki kuwa har da su Laita da duk sauran yaransa.

Zabira ce ta fara buɗe musu fagen tambayar da cewa “Wai dama ka na soyayya Abba?”
Da sauri Ɗan Bakwai ya ce “Yauwa!! abinda nake son ji kenan nima, daɗina da ke kanki ya na kawo wuta ta gidana”
Nan fa kowa ya fara tarkato tashi tambayar ya na jefowa, shi kuwa Akhiee sai  shan wiwi ɗinsa yake yi    ya ƙi cewa komai.
Sai da su ka gama su ka fara yin slow sannan ya ɗan yi gyaran murya  duk  su ka nutsu,    “Ni ba na soyayya hasalima ban san ya akeyinta ba,  abinda nake so ku sani shine   Asma’u ita kaɗai gareni,  idan a cikinku ne aka illata wani to ina da wani, amma  ita duk Duniya  ba ni da tamkarta, kuma ba ni da wadda za ta zamo kamarta,  duk tsawon rayuwarku da ni bayan Iyalina akwai wata mace da kuka taɓa ganin ina saurara?”   amsawa su ka yi da “A’a”    ya ci gaba da cewa ”Nima kaina na yi mamakin ta yadda aka yi na fara saurararta har ta yi nasarar sa ni abubuwa da dama a  cikin waɗanda ba na yinsu,  haka kawai nake jinta tamkar Ruhina idan aka cutar da ita tabbas an yi mini babbar cuta, hakan ne ya sa nake so ta dawo ƙarƙashin kulawata  hankalina zai fi kwanciya,  ga bayani nan na yi muku wanda bai fahimta ba kuma ba zai taɓa fahimta ba don haka ku tashi ku ban wuri ba na buƙatarku a yanzu.”

miƙewa su ka yi su na ta murna su ka rankaya su ka yi waje,  can gefe su ka haɗa majalisa su ka fara tattaunawa, Gwaja ya ce “Ai na godewa Allah tinda yanzu ya samu mata mu ma ƙila zai barmu mu dinga kula mata har mu yi Aure”
“Mewtchh!!!”  Salansa ya doka tsaki kafin ya ci gaba da cewa “Kai ta Aure ma ka ke yi,  idan shi ya iya kula da ita kai yadda kake kai a sama ɗinnan ba abinda za ka iya yi mata, ƙarshe ka sa ya kasheka a banza”  ɗan sassauta murya yayi kafin ya ce “Wai kun san me?  ya ce bai san so ba ko? to wallahi sonta yake yi.”
Laita ta yi dariya kafin ta ce ”Bar ɗan iska ya na son kayarsa mana.”   su ka ƙara kwashewa da dariya,  hira su ka ci gaba da yi cikin farin ciki domin kuwa su daɗi abin ya yi musu.

A Ɓangaren Husnee kuwa kamar ɓarauniya haka ta shiga gida da sanɗa, ta yi muzu-muzu da ita  kamar jiƙaƙƙiyar kaza.
Mommy da Yaya Muddassir su na zaune su na hirar yaushe gamo ta shigo Falon cikin takunta me kama da na masu koyo.
Yaya Muddassir ya bita da kallo kafin ya ce “Lafiya kuwa Ƙanwata?”  kusa da shi ta zauna kafin ta yi magana cikin muryarta da ta dishe, “Lafiya lau”
Mommy ta ce “Lafiyar Kura ba?   in gaya maka gaskiya sai an haɗa da addu’a don kuwa Aljanu ne su ka shafeta, ka ga yadda tafita ɗazu lafiyar Allah ko?  to ka ga yanzu yadda ta dawo, to haka  take kan da lafiya jikin ba daɗi, kwanaki haka su ka dinga lallanƙwasa  kamar tsutsa, ni dai naga abin al’ajabi,  na ce ma zan kaita Islamic Center ko Allah zai sa a samu sauƙi”
Muddassir ya bi Husnee da kallo, shi dai a rayuwarsa Allah ya ɗiga masa so da ƙaunar ƙanwar ta shi fiye duk sauran ƙannensa, tausayinta ya gama kama shi, cikin sanyin jiki ya ce “Sannu kin ji ƙanwata?,  meke miki ciwo yanzu.”
“Ba komai” ta faɗa ta na turo baki gaba.
Ya ce “Kin tabbata?,  to idan ki na buƙatar wani abin sai ki gaya mini kin ji?  ko mu je ki sha Ice Cream?”  rasss ta ji gabanta ya faɗi,  “Ba ka san cewa ni yanzu matar Aure ba ce Yaya”  abinda ta faɗa a zuciyar kenan a sarari kuwa ta yi saurin girgiza masa kai.
Ya ce “Shi kenan yanzu ki samu ki ci abinci ki huta  in anjika zan baki labarin Kaduna, kin ce ma za ki bini ko?”  girgiza kai ta yi alamar “a’a”  gami da cewa “Na fasa”  ya yi dariya a ransa ya ce “Nima ba za ni da ke ba” a sarari kuwa ya ce “To shi kenan.”
Tashi ta yi ta koma ɗakinsu  ba ta nemi abincin ba ta baje anan bacci  me cike da mafarkai masu daɗi da marasa daɗi ya yi  tafiyar ruwa da ita.

Hajiya Laure na zaune  ta na waya ita da Hajiya Saudah,  ƙorafi take yi akan Boka ya ƙi kiransu har yanzu, Hajiya Saudah ta ce “Ke fa kin fiye gaggawa Ƙawata, ki jira mana ai komai ya na da lokacinsa   indai Boka Barore ne za ki sha mamaki, ai ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin faɗa ne.”
Hajiya Laure ta sauke wani gwaurin nishi gami da murmushi, cikin jin daɗi ta ce “Allah i nuna mini wannan ranar Ƙawata, na haƙura  ai ni da na ji shiru har na yanke shawarar za mu canja wuri.”
Hajiya  Saudah ta ce “Ina!! ai ba wannan maganar, ke wai ba ki ga yadda nake ba a gidana?  Boka Barore fa ba wasa ba ne in gaya miki gaskiya.”
Hajiya Laure za ta yi magana ta ankara da Yazeed akanta, fasa maganar ta yi daga ƙarshe ma sai ta katse wayar, ta bishi da kallon rashin gaskiya ta wani ci mur,  a masife ta ce “Kai kuma mara Zuciya ƙalau kake kallona? mara kishin nasa?”
Zama ya yi kafin ya ce “Ni indai irin kishin nan naki na bin bokaye ne ba ni da shi,   In  da ƴan daba ki ka haɗa ma da tuni sun yi miki abinda kike so amma sai wani ƙarar min da dukiya ki ke yi akan bin bokaye,  ai Ɗan Daba da ɗan Daba ake haɗa shi.”
Ta yi tsaki kafin ta ce “Kai dallah rufe mini baki shashasha,  kai ai soko ne na asali, yaron da ya gagari hukuma shine ka ke tunanin wasu Ƴan daba za su iya da shi?  shima fa ɗan daban ne kuma ya na da ƴan daban,  ni na fi son abinda zan yi masa illa lokaci guda.”
“Allah ya bada sa’a”  ya faɗa ya na taɓe baki.
“Amin” ta amsa a gadarance gami da miƙewa ta bashi wuri, a cewarta ya katse mata magana.

Kashingiɗa ya yi a kan kujera ya na lumshe ido, sanyin AC na ratsa shi, Kwatsam! tunanin Ma’u ya faɗo masa, musamman yanayinta  a da   ta na da fara’a ga ladabi da biyayya ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba “To wai meye ya sameta da ta dena walwala?”  tambayar da ya yi wa  zuciyarsa kenan sai dai ba shi da amsarta,   ya daɗe  ya na tunaninta kafin ya yanke hukuncin zuwa ya tambayeta ko za ta faɗa masa damuwarta.
miƙewa ya yi ya fice daga sashin Mommy ya nufi ɗan sashin da aka ware domin ƴan aiki.
Da Iya ya fara kaciɓuss ta yi saurin buɗa masa hanya gami da gaishe  shi, bai amsa ba ya ce “Ni fa ba na so ki dinga gaishe ni tsofai-tsofau da ke”
Ta ce “To Ɗannan   ai ni baiwarku ce,  Hajiya ta yi mana umarnin mu dinga gaishe da kowa.”
Ɗan tsaki ya yi kafin ya ce ”Ni ba na so, yanzu dai ina wannan baƙar yarinyar Ma’u?”
Iya ta ce ”Aff! Ta na kicin ita da Talatu  bari in kira maka ita.”
Da sauri ya ce “No ba buƙatar hakan zan je can in sameta.”
Iya ta amsa da “To”  a  ranta  ta na mamakin neman nata da yake yi.
Ta na cikin yankan Albasa kamar ance juyo ta na kallon hanyar shigowa idanunta su ka yi katari da shi, Gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, da sauri ta sunkuyar da kanta ta na jin wata irin tsanarsa da shi da mahaifiyarsa,  shi kuwa kallonta kawai yake yi kamar tsohon maye.
Sai da Talatu ta gaishe shi sannan ya  farga ashe ba su kaɗai ne a wurin ba.

Haɗe fuska ya yi cike da manyance da nuna isa ya ce “Maza ki bar nan”  Talatu ta ce “To”  jiki na tsuma ta ajiye abinda take yi   ta raɓa ta kusa da shi ta wuce.

Ma’u kuwa jin abinda ya cewa Talatu ya ƙara firgita ta jikinta ya ɗau karkarwa, tunanin abinda Mommynsa  ta yi mata ne ya fara dawo mata, musamman irin tashin hankaki da azabar da ta fuskanta a wajen Boka.
Ta lula duniyar tunani hakan ya sa ba ta san ya zo kusa da ita ba sai jin muryarsa ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta tamkar an kauɗa mata baƙin ƙarfe a ka, zaburar da ta yi ta sa wuƙar hannunta ta kufce ta shigi ɗan yatsanta, da sauri ta watsar gami da damƙe yatsan ta saki ƴar ƙara.
Zazzaro idanunsa ya yi a kanta yana sa cewa “Lafiya??”  ganin ta riƙe ɗan yatsa ya sa shi saurin riƙo hannun nata ya na cewa “Mu gani?”    ƙoƙarin fizgewa ta fara yi ta na yi masa magiya akan ya saketa.
kamar zai fashe da kuka  ya ce “Sannu! Ki dinga bi a hankali, kin ga kin  yanke kanki  ko tunanin me kike yi oho.”  ya na sakar mata hannun ta yi sauri matsawa gefe ta na fashewa da kuka.
Cike da takaicin kukan nata ya ce “Ai ka ji!!!!  dama na zo tambayarki akan matsalarki ne amma yanzu kin ƙara ƙirƙiro wata matsalar.”
Cikin kuka ta ce “Ba abinda yake damuna don  Allah ka dena nemana”
“Dole in nemeki mana tinda kin barni cikin tunaninki?  ki faɗa mini  damuwarki ki ka sani ko zan iya yi miki maganinta?”
“Ba abinda yake damuna  fa!’  ta yi maganar ta na shashshekar kuka,
ɗan tsaki ya yi kafin ya ce “Ke na ga abin kukan ma ba ya yi miki kaɗan, ranar da ba kya kukan sai ki gaya mini abinda aka yi miki”  ya faɗa tare da juyawa ya nufi hanyar fita Zuciyarsa sam ba daɗi.

Husnee misalin 02:40 juyi kawai take yi akan katifa  yayin da bacci ya ƙauracewa idanunta, ba abinda take tunani sai Akhiee da kuma abinda zai iya faruwa idan iyayenta su ka san  gaskiya,  ta yi nisa a tunanin ta ji motsin wayar da ya bata  wadda ta zo ta turata a ƙarƙashin filonta  don gani take idan ta ajiye a wani wurin kamar za a iya dubawa a ganta.
Da sauri ta tashi ta zauna ta na dube-dube, babu alamar kowa a kusa Khausar ma sai baccinta take lakadan, zaro wayar ta yi daidai lokacin da wani sabon kiran ya kuma shigowa, Lamba ce sabuwa ma’ana ba save, gabanta ya yanke ya faɗi dandanan jikinta ya ɗau karkarwa ta shiga firgici da razani gami da kokonto akan me kiran nata da tsohon daren nan,  shawarwari take yi akan ta ɗauka ko a’a   wata zuciyar ta  na gargaɗinta wata kuma na tunzurata akan ta ɗauka ɗin,  zuciyarta na  dakan sha-lugude  ta taɓa kore gami da ɗora wayar akan kunnenta…………..

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

*©️INDO*
[8/26, 4:38 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 18

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

 

“Kin Ƙi yin Bacci ko??”  muryarsa ce ta doki dodon kunnenta, ta zazzaro ido a ɗan razane kafin ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya  ba tare da ta yi magana ba,
Jin ta yi shiru ya sa shi ƙarawa da cewa “Me yasa to?”   kamar za ta fashe da kuka ta fara magana cikin muryar shagwaɓa, “Tsoro na ke ji Akhiee!!”  ɗan jim ya yi kafin ya ce “Haka ne? ko in zo mu tafi gidanmu?”
Ƙara firfito da zara-zaran idanunta ta yi  “Tsakar dare ne fa yanzu!! kai  ka na ina ba ka tafi gida ba??!”  ta yi maganar cikin firgici.
Cikin wata kasalalliyar murya ya ce “Asma’u ni dare ba ya hanani yawo hasalima ban fiye bacci da daddare ba da rana nake yi,  ina kusa da ke   in ki na so na zo mu tafi zan zo  idan kuma ba kya so to ki yi baccinki cikin kwanciyar hankali.”
Ajiyar Zuciya ta sauke gami da sassauta murya  a sanyaye ta ce “Ka na kusa da ni Akhiee to ta ya kenan?”
Ɗauke wayar ya yi daga kan kunnensa kafin ya furzar da wata zazzafar iska,   ya so ya yi ɓaram-ɓatama kuwa,  kiran sunansa da ta yi ne ya dawo da shi hayyacinsa, cikin nutsuwa ya ce “Ina nufin ki sa hakan a ranki kawai,  Sai da safe yanzu zan shiga gida.”   da sauri ta ce “Akhiee!!”  cikin wata irin shagwaɓa ta yi maganar kamar wata ƴar shekara biyu na kiran Ummanta,  rasss zuciyarsa ta buga ya lumshe idanunsa da su ka fara canja launi kafin ya mayar mata da martani ta hanyar kiran nata sunan “Asma’uhh!!”  murmushi ta saki kafin ta ce “Da gaske ne ka na kusa da ni? kuma ka na tare da ni Akhiee? ”
“Kin san ba zan faɗa miki ƙarya ba don hankalinki ya kwanta, ki yi baccinki ina tare da ke, kuma za ki yi mafarkina.”  gyaɗa kai ta yi ta na murmushi  cike da farin ciki da shaukin sonsa ta ce “Allah i tsare min kai Akhiee.”
kai kawai ya gyaɗa ba tare da ya yi magana ba ya kashe wayar.
Sumar kansa ya cafka gami da   sauke nannauyar ajiyar Zuciya me tafe da wata Zazzafar iska.

Ji ya yi an dafa kafaɗarsa  ya yi saurin cewa “Russlan!!”    Russlan ya zauna a gefensa kan katafaren gado irin na sarakuna da yake zaune a gefensa.
Cikin sanyin jiki Russlan ya ce “Ko shakka ba na yi ka na son matarka Risslan,   ya zama dole ka dinga iya bakinka kar ka faɗa mata abinda dole ne sai ka kasheta da hannunka.”  jinjina kai ya yi kafin ya yi magana “Ban san me yasa Asma’u take da tasiri a kaina ba,  na kasa samun nutsuwa sai tunaninta na ke yi, ji nake tamkar na je na kwana a kusa da ita domin na bata dukkan kulawata.”
Russlan ya ce “Na gane hakan ai duba da yadda ka ke zagewa ka na gaya mata gami da nuna mata iyakar abinda ke ɓoye a Zuciyarka wanda ba kowane me wannan  Darajar ba,  amma fa ina ji maka tsoron Uban Dawa kar ya hukuntaka akan aurenta ba tare da sanin iyayenta ba.”
Shiru ya   yi na ɗan lokaci kafin ya ce “Asma’u!  itace mahaɗin rayuwata ko da so ko babu da ita zan rayu,  ko da Father zai yi fushi   zan jure duk hukuncin da zai yi mini,  abu ɗaya kawai na yarda da shi kuma na sa a Zuciyata, ko da ta sanadin Asma’u za a yi mini izayar da ban taɓa fuskanta ba duk tsawon rayuwata   ba zan Saketa ba   ina tare da ita kamar yadda na yi mata alƙawari  har sai in itace ta so rabuwa da ni wannan zan iya amincewa; Bayan haka kuma sama da ƙasa, Duniyar Mutane da ta Aljanu har ma da sauran Duniyoyi babu wanda ya isa  ya sa ni sakinta  duk azabarsa,  Allah ne ya halicceta kuma ya jefota cikin rayuwata  kuma ina komai  ne da ikonsa  shine kaɗai zai rabani da Asma’u ta kowace hanya, ko a raye ko muce  Russlan  kai ma ka riƙe hakan.”

Zuwa yanzu Russlan tsananin tausayun ɗan uwan nasa ya gama kama shi,  ya san a zaman tare dole wataran za ta gane gaskiyar waye shi, kuma hukuncin wanda ya yi hakan kisa ne,  bayan haka  akwai ƙalubale da yawa a gabansu wanda shi Risslan ba ya hangosu sabida idanunsa sun rufe,   “Risslan  na yarda da kai kuma na san za ka aikata  amma ka sani akwai sauran rina a kaba.”
“Na san da hakan Russlan,  ka koma gida kawai   nima zan wuce gidanmu    Gadon nan ka sa Dogarai su kwashe shi kar safiya ta yi Bil’adam su dinga karo da shi.”
Russlan ya ce “Okay sai ka fito goben,  Mu haɗu a Daji in an isa.”
a hankali Risslan ya ce “Ka san fa ni ba kamar kai ba ne,  musamman ina cikin wannan yanayin   da akwai mutane da yawa waɗanda su ke buƙatar kulawata.”
Russlan ya ce “Okay shi kenan see you later.”

Risslan bai ƙara magana ba ya ɓace ɓatt!  sai gashi a kusa da Dokinsa.
Prince na ganinsa ya fara haniniya ya na ɗaga ƙafafu sama ya na direwa,  Risslan ya shafa shi cike da ƙaunarsa hakan ya sa ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar ba shi ya gama dara ba yanzu,  wata kyakkyawar sufa Akhiee ya yi ya dire akan Prince  tare da Komawa asalin Suffarsa ta Ɗan’adam   wanda kowa zai iya ganinsa saɓanin Da  da ya koma Suffar mutanen ɓoye.

Hanyar komawa Hotoro yankinsu ya ɗauka  ya na tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da  wata fargaba ba.
Cijewa Prince ya yi gami da ɗangale ƙafafunsa  ya na wata irin haniniya hakan ya tabbatarwa Akhiee wani abin ya gani.
Bai gama nazarta yanayin ba ya ga Alburushi  ya nufo kansa gadan-gadan  sunkuyawa ya yi   ya wuce sannan ya ɗago, kafin ka ƙifta ido ka buɗe  wasu murtuka-murtukan mazaje sun bayyano ta kowace kusurwa ta filin, sanye suke cikin baƙaƙen kaya  kowanne fuskarsa a rufe, su na ɗauke da wasu lafiyayyun bindigu  wanda suka rufe bakunansu ta yadda ba za su yi ƙara sosai Ba.

Harbi suka fara ba shi ta ko’ina ba ƙaƙƙautawa idanu a lulluɓe neman makasarsa su ke yi.
Abin da ya yi bala’in basu mamaki gami da dugunzuma hankulansu,   kasancewar ƙwararrun maharba ne ba sa saɓa saiti bayan Alburushin farko ba wanda su ka harba masa ya faɗi duk sun same shi  sai dai   da zarar Alburushin ya sauka a jikinsa zai gangare ya faɗi ƙasa  ba tare da ya ratsa shi ba,  duk da suna  ganin hakan  kuma sun razana amma  ba su fasa ba don kuwa ganu suke yi kamar za su iya cimma nasara in suka ƙoƙarta.

Wani wawan juyi ya yi gami da buɗa hannayensa  ya yi wani wurwuro kamar fanka  sannan ya diro ƙasa hannunsa  riƙe da manyan bindigu guda biyu.
Turus su ka tsaya kallonsa ido a warwaje, sun kai maƙurar tsoro da firgici  ganin bindigu sun bayyana a hannunsa bayan ba shi da su ba shi da dalilinsu.

Cikin rashin imani da tausayi Na Akhiee ya fara sakar musu harbi   a matuƙar fusace,  ganin haka ya sa su ka ci gaba da harbinsa  su ka fara artabu tsakaninsu, sai dai   shi harbi ɗaya yake yi musu su baje  don dai su na da yawa.
ba ɓata lokaci duk ya ƙarar da su saura mutum ɗaya wanda Alburushi ba ya shigarsa don kuwa shi ma babban shege ne.

Akhiee ya yi wani ƙwaƙƙwaran taku gami da watsar da bindigun a gefe  dandanan su ka ɓace ɓatt!!   sai kuma wata lafiyayyar farar wuƙa ta bayyana a hannunsa, duk da dare ne  hakan bau hana ƙyallinta da haskenta fitowa ba, kan Maharbin ya nufa gadan-gadan  hakan ya sa ya arta da gudu domin ceton ransa, jefa masa wuƙar ya yi cikin sa’a kuwa ta ratsa ƙashin bayansa,  ya saki ihu gami da zamewa ya kife a rubda ciki, Akhiee ya ƙarasa gabansa ya durƙusa kafin ya ce “Duk wanda ya ga wannan Sirrin nawa  mutuwa  ce makomarsa  ba za ka iya tsere mini ba,   amma kafin ka mutu ina son sanin wanda ya aiko ku.”  cikin ƙarfih hali   Mutumin  ya kama dariya  ya na cewa “Wani Jarumi ne, kuma ya riga  ya sa ka a tarko ta kowace fuska, ya yi mummunan shiri na  kawo ƙarshen hatsabibancinka,  kuma ina me tabbatar maka ruhina ba zai tafi a banza  sai ya ɗaukar mini fansa,  Gobe za ka samu gawar Ƴaƴanka  mun ci moriyarsu don haka za mu dawo maka da su,  ka shiga matsala Sarƙa, duk hatsabibancinka sai wannan Shu’umin ya ga bayanka  shi ba kanwar lasa  bane zazzafa ne,  kuma jama’arsa daga kowane State na Nigeria har ma da Ƙasashen ƙetare sun shigo Nigeria sun yi maka ƙawanya,  in ka isa ka tsira hhh!!!”.
Ya ƙarasa maganar ya na ƙara ƙyalƙalewa da dariyar mugunta a wahalce.

A fusace Akhiee  ya zare wuƙar da ke maƙale a bayan Mutumin ya suka masa ita a wuya, ko shurawa bai ƙara yi ba tuni ya mutu idanunsa a bubbuɗe.
Akhiee ya miƙe jikinsa na wata irin tsuma sabida ɓacin rai, tuni wani irin duhu ya mamaye  idanunsa kansa ya fara wata irin yamutsawa.
Bai bi ta kan Dogarawan Aljanun da suka kewashi ba ya haye kan Prince  ya ci gaba da tafiya.
Aljanun su ka koma kan mutumin  da ya kashe daga ƙarshe   shi ma su ka ɗauke gawar ta shi   sauran kuwa  tuni sun kwashe su   sun kai su bakin wani Daji sun zubar.
Ba su gushe daga wurin ba sai da su ka gyara shi tsaf ba alamun jini ba alamar Alburushi ba ma me cewa wani abu ya faru a wurin.

ya na isa bakin get ɗin gidan ya dire daga kan Prince  ya dafa ƙofar nan-take ta buɗe ba tare da hayaniya  ba,  ya shiga gidan tare da Prince sannan ya ƙara dafa ƙofar ya rufe,  sakatu harda Pad lock ɗin da ake sawa get ɗin duk su ka koma su ka  rufe kamar   dama ƙofar tinda aka rufeta ba wanda ya ƙara taɓata.

Kawai sakin Prince  ya yi    ya tafi makwancinsa da kansa shi ma   ya nufi na shi makwancin,  ta bayan gidan ya bi  inda ya fi kusa da ɗakinsa ba sai ya ratsa sassan gidan ba,  ita ma ƙofar bayan kulleta ake yi amma ya na ɗora hannunsa akanta    ta buɗe ya shige sannan ya rufeta,  kwata-kwata a wannan daren bai yi bacci  ba tunane -tunane sun yi masa katutu.

Husnee ta na gama  waya da Akhiee ta ji wani irin sanyi na ratsa dukkan sassan jikinta har cikin Zuciya da Ƙoƙon ranta, nan take farin ciki ya ziyarce   ta fara manta dukkan Damuwarta, ba ta daɗe cikin wannan yanayin ba Bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita.
Cikin Baccin kamar yadda Akhiee ya faɗa mafarkansa ta dinga yi,   har abinda ya faru tsakaninsa da waɗanda su ka farmake shi sai da ta gani, wani ɓangaren  kuma soyayya su ka zuba a mafarkin kamar ba  za a mutu ba,  haka ta dinga yinsu kala-kala har Allah ya wayi gari.
Jiki a muce ta tashi yau hakan ya sa ba ta yi yunƙurin fita makaranta ba, sai da yamma ta shirya tsaf sannan ta fito,  Amadu da me Gadi su na zaune su na hira ta fito ɗogal-ɗogal wai ita makaranta za ta je.
Baki a sake Amadu ke kallonta har ta ƙaraso inda suke,  cikin siririyar muryarta ta ce “Malam Amadu Makaranta zan je fa”
jinjina kai ya yi gami da cewa “Tirƙashi!!!! ai kuwa ban amince ki fita ba har sai kin tambayi mijinki.”
Kamar za ta yi kuka ta ce “Makaranta fa zan je”.  “Ko nan da ƙofar gida za ki je indai ni zan kai ki sai kin tambayi Mijinki bare makaranta, sai in ke kaɗai za ki fita  to wannan alhakin bai shafe ni ba ko a wurin Allah ba ni da  laifi,  ai ya baki waya,  ki kira shi ki tambaye shi.”
Magiya ta shiga yiwa Amadu amma ya ce shifa bai ji ya gani ba, dole ta ɗauko wayar ta tura masa kira don kuwa ta na son fitar.
Ta kira ya kai sau goma su na gaya mata waya yake yi…………

**************************

A nashi ɓangaren kuwa  wayar ta na maƙale a kunnensa  ya zubawa wuri ɗaya idanunsa wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ya na cikin matsanancin hali, duba da yadda suka rikice su ka koma tamkar ba na ɗan-adam ba,  a memakon su yi ja  sai ma farin  ya ƙara wani irin haske wanda har ya wuce na muhammadiyya, baƙar ƙwayar kuwa ta ƙara yin baƙi siɗik  sai ƙyalli take yi tamkar  baƙin ɗan Maciji  har wani irin abu take yi tamkar tiriri, ƴar ƙaramar ƙwayar ciki kuwa ta koma Golden collor  me duhu hakan ya ƙarawa idanun nasa wani irin haske da kwarjini    har ma da abubuwan Al’ajabi,  fuskarsa kuwa ta yi jajir tamkar irin jariran da ake haifarsu kamar   ana latsa fatarsu jini zai yi tsartuwa,  duk da jan da fuskarsa ta yi hakan bai hana inda Alburushin  jiya ya sauka a duk jikinsa nuna kansa ba,  duk inda Alburushin ya sauka a jikinsa ya yi wani irin jajir  har a fuskarsa ya yi tabbai;    cikakken bil’adam kuma me lafiya ba zai iya haɗa ido da shi a wannan lokacin ba.

a ɗaya gefen kuwa Surayya ce ke yi masa kuka akan irin cin zarafin da aka yiwa Ƴan Uwanta Zakiyya da Farhana,  ya kasa ce mata komai don kuwa ba za ta iya fahimta ba sai dai su yi cacar baki don haka ya yi mata banza har ta gama ta katse kiran.
Kafin Kiran Husnee ya shigo kiran Firdous  ya shigo, ya na ɗauka ya kara a kunnensa ta fashe da kuka wanda ya sa tsigar jikinsa ta mimmiƙe a lokaci guda,  Cikin shashshekar kuka ta ce “Daddy!! na gaji da zama a ƙasar nan ina ganin tashin hankali iri-iri,   ka na kallon abinda aka yiwa ƴan uwana, an yi musu fyaɗe ba sau ɗaya ba ba sau Biyu ba,  sannan an Kashe Zakiyya  an ƙwaƙule mata idanu!!  Farhana ma bayan keta mata haddi an yi mata izaya kala daban-daban  yanzu ta faɗa godon suma ba tabbacin ma za ta rayu,   kuma sun ce abin bai ƙare ba yanzu ma su ka fara,  Nan gaba Allah ne kaɗai ya san abinda  Za su yi Baba!!!!  ni dai ka fitar da ni ƙasar waje in ƙarasa karatuna a can   ba zan iya zaman nan ba!!!!!!”  ta ƙarasa maganar cikin kuka me natuƙar rikita tunanin me saurarensa.
Da ƙyar ya iya ɗaga harshensa ya magantu “Ki Zaɓi ƙasar da ki ke son zuwa  ki tafi tare da Raihana, ki kula da ita sosai, in kin zaɓa ki yi magana zan shirya miki komai.”
Daga haka bai bata damar sake yin magana ba ya katse wayar, wani kiran ne ya ƙara shigowa  ba tare da ya duba kowaye ba ya kara a kunnensa gami da yin shiru.

Cikin rawar murya ta magantu “Akhiee ina son zuwa makaranta n…”   kafin ta  ƙarasa faɗe ya katse ta da cewa “Ban yarda ki fita ko’ina ba indai ba tare da ni ba,   idan kuma kin ƙi ji har ki ka yi mini asarar ranki   ki sani sai na ɗauki Fansa akan Danginki!!!!!.”  daga haka ya katse wayar, daidai lokacin wani sabon kiran ya shigo, bai yi ƙasa a guiwa ba ya ɗauka, Zulaihat ce, itama kuka  take yi wurjajan,  cikin jin zafi da ciwon abinda ya faru ta ce “Baba don Allah ko waye ya aikata hakan ga su Zakiyya kar ka barshi da rai shima ki yi masa abinda ya yi musu don Allah Daddy!!.”
Lumshe ido ya yi kafin ya ce “I Promise you Zulaihat!”  Ya na faɗen haka ya katse wayar domin amsa wani kiran da yake shigowa a ɗaya wayar ta shi.

“Mukhtar!!”  shine  abinda  ya faɗa cikin wata irin murya me ƙunshe da yanayi kala-kala, Mukhtar ya ɗan yi gyara murya sabida dashewar da ta yi, kamar zautacce haka ya fara magana “Daddy! yanzu shi kenan ba zan ƙara ganin Zakiyya ba?  me ta yi musu da za su yi mata wannan ɗanyen aikin? Ji nake kamar zanyi hauka wallahi don Allah Daddy ka dakatar da wannan abin tin kafin ya yi nisa”     ya ƙarasa maganar gami da sakin wani marayan kuka………

SHARE FISABILILLAH

*©️INDO*

_______________________________
DATA SERVICE

*GARAƁASA Kar ku bari ayi ba ku💃🏼*

            MTN
500 MB  150
1GB  280
2GB   550
3GB  840
4GB 1,100
5GB 1,380

  AIRTEL
500  MB  160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB  1,450

           GLO
500MB  170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

   9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
………………………………..
WhatsApp Number or Call:  09079885632
_______________________

[8/27, 11:19 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 19

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*M.W.A🦅*

Cikin tausasawa ya ce “Kwantar da hankali Mukhtar!  Lokacinta ne ya yi  ba yadda za mu yi dole sai mun rasata ko ba ta wannan hanyar ba,  bai kamata ka yi kuka ba;  kamata ta yi ka rarrashi ƙannenka,  kai fa Namiji ne,   ba na son ƙara ganin hawayenka,  ka bar komai a hannuna kuma ka manta da abinda ya faru  ina so komai ya wuce.”
Mukhtar ya ja numfashi ya sauke kafin ya ce “Amma ba yadda za mu yi haka za su dinga   yi mana?”    “Ta ya kake tunanin wani ƙaramin abu zai dawwama a Duniya??   lokaci juyawa ya ke yi, Ka kula da ƙannenka    a shirya jana’izar Zakiyya kafin na iso.”
Daga haka ya katse wayar   ya yi wurgi da ita ta faɗi can gefe,  safa da marwa ya shiga yi a wajen ya kai mari ya kai gwauro,  duk iya nazarinsa ya kasa gane kowaye   yake yi masa wannan zagon ƙasan, kuma ya na buƙatar sani tin kafin tafiyar ta yi nisa.

Ya daɗe cikin yanayin tunane-tunane  kafin ya shirya  domin zuwa wajen Jana’izar Zakiyya.

Husnee jiki a saɓule ta sauke wayar daga kan kunnenta ta na kallon Amadu kallon da ya ke nuni da cewar bai barta ba,   Ya kalli Ahajiji Me Gadi ya ce “Ahaf!!!   Allah na tuba  Shu’umin Mutum irin wannan Yaron ne zai bar matarsa ta dinga yawo a gari?  ai shi yasa na yi azancin cewa ta Tambayi Mijinta.”
Alhajiji ya ce “A’ah iko sai Allah,  to ni na kasa gane me kuke nufi ai, ba ku ga tin ɗazu na ke kallonku ɗaya -bayan-ɗaya ba  Ni ai a  sanina Husnee ba ta da Miji.”
Amadu ya ce “Na shafa maka lafiya to yanzu Matar Aure ce,  ga shi dai a gabanka ai ta tambayi mijin nata fita ya hanata”

“Matar Aure???  Mijinta kuma??  ita Husnee ɗin???”  Mommy   da ta iso wurin ba tare da sun sani ba ta jefo musu tambayoyin a jere.
Rassss Gaban Husnee ya yanke ya faɗi har ƙasa,  jikinta ya fara karkarwa  ta zazzaro fararen idanunta akan Mommy wadda ta ke kallonsu ita da Amadu Ɗaya-bayan-ɗaya  kallo me cike da tuhuma gami da mamaki da ɓacin rai.

Amadu ya ji tamkar Motar Gingimari ta hau kansa lokacin da ya ji tambayar Mommy.  Lokaci guda duk su ka shiga firgici da tashin hankali.
a ladabce Alhajiji ya ce “Hajjaju Makkatu ikon Allah barka da fitowa.”
Mommy ta ce “Ba ka ji tambayar da na yi ba ne?  shine ka ke kawo mini taka idea?”
Ya rissina gami da cewa “Ayi haƙuri,  wallahi Hajiya nima yanzu na ke tambayarsu yaushe ne ta yi aure ban sani ba, Allah i sanya Alkairi.”
Cikin tsawa Mommy ta ce “Husna!!!  Dan Ubanki ba kya jina ne????  yaushe ki ka zama Matar wani????”    zamewa ta yi ta durƙushe a wajen gami da fashewa da wani marayan kuka wanda sautinsa ma ya ba ya fita sosai,  ta na so ta magantu amma ta kasa.
Jiki na tsuma Amadu ya ce “Ina zuwa Hajiya”    cikin Mota ya nufa ya ɗauko kuɗin Sadakinta wanda ke nannaɗe a cikin  hankicif,  ya dawo gaban Mommy ya durƙusa jiki na ɓari ya ce “Hajiya Allah ya baku haƙuri,  Ga wannan”  cikin mugun mamaki ta sa hannu ta karɓa ta na ƙarewa hankicif ɗin kallo,  Amadu ya ci gaba da magana murya na rawa “Hajiya waɗannan kuɗi su ne Sadakin Husnee, Jiya Wanda take so ya aureta,  Hajiya ba laifina ba ne,   Tilasta mini ya yi akan cewar ni zan karɓi Aurenta,  mun ɗaura Auren a Masallacin wani Malami,  Malam Kabiru”   iya abinda aka yi a gabansa ya kwashe ya gaya mata.

Kallon Husnee ta ke yi cikin tsananin mamaki da al’ajabi, ta na yi ta na jinjina kuɗin hannunta.  Cikin murya me  nuna tsantsar ɓacin rai ta ce “Husnee?  har kin yi girman da za ki iya bin wani ɗan iska ya aureki?   Ashe duk burin Mahaifinki na ki yi karatu me zurfi   ba ya cikin tunaninki?”

Girgiza kai ta ke yi ta na wani irin kuka wanda  ke fitowa tin daga ƙasan Zuciyarta,  murya a dishe ta ce “Ƙaddara ce Mommy don Allah kar ki zargeni sam ba laifina ba ne, nima ban zata abinda zai yi kenan ba.”
Amadu ya ce “Gaskiya ne haka ne Hajiya ita ma ba ta zata ba, sama taka ya aikata hakan”
“To wai shin waye shi ?  Su waye iyayensa a ƙasar nan da har zai aure mini ƴa ba tare da Sahalewata ba??”
Amadu ya ce “Ranar wanka ba a ɓoyon cibi Hajiya,  Sunansa Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan,  Ɗa ne ga  babban Malamin  nan na duk Hotoro da kewaye, kuma shi ɗin  Babban Tantiri ne na kaf Nigeria,  wasu na kiransa SARƘA  wasu na kiransa SAHUN KEKE,    kowa ma da irin sunan da yake gaya masa,  ko kwanakin baya an kamw shi da laifin kisa amma  sai aka sako shi domin ya fi gaban nan,  wannan shi ne kaɗai abinda zan iya faɗe a kansa.”

Duhu-duhu Mommy ta fara gani nan take jiri ya fara ɗibarta ta tafi luuuu!!! za ta faɗi Husnee ta yi kanta da gudu da nufin tareta, kafin ta ƙarasa Muddassir ya rigata, ya rungumota a jikinsa ya na tambayar lafiya.

Hawaye ne su ka shiga tsiyaya akan kumatunta, da kyar ta ce “Husnee ce!!!   mu na zaune a gida ashe ta je ta Auri wani bayan mun yi wa Zaheer Alƙawarin aurenta,  wai yanzu har ta yi girman da za ta iya zuwa ta Auri wani Namiji  ba tare da sanin iyayenta ba?? har yaushe ta fara zuwa makarantar da ya hure mata kunne haka?”
Muddassir  ya zubawa Husnee ido ya na binta da kallon tuhuma,  a masife ya ce “Ashe ba ki da hankali?   me ya sa za ki aikata haka?    akwai wanda ya fiye miki iyayenki ne duk son da ki ke yi masa?   Kwantar da hankalinki Mommy kowaye sai  ya saketa ni zan je in yi magana da shi,  mu ba za a yi haka da mu ba,  ba ma son tantiranci.”

Mommy ta ce “Shi ɗin Tantirin gaske ne kuwa, kuma Shaiɗani wai Sunansa Sahun Keke”    dimm!!!!!!!  Zuciyar Muddassir ta yi wata muguwar bugawa wadda  ta sa numfashinsa ɗaukewa na wucin gadi.
“SAHUN KEKE!!!!!!”  Ya maimaita kalmar cikin kaɗuwa gami da tashin hankali da firgici.
idanunsa na kan Husnee wadda take wani irin galabaitaccen kuka,  a hankali ya ce “Mommy  shiga ciki ina zuwa.”
Mommy ta ja jikinta da kyar da kyar ta shige cikin gida ta na kuka  ta na faɗin “Ai ko waye shi, Allah i sa Iblis ne sabida hatsabibancinsa sai mun yi shari’a da shi  sai ya saketa, ba za ta taɓa zama da ɗan Ta’adda ba.”

A kiɗime Muddassir ya matsa kusa da ita ya durƙusa a gabanta su na fuskantar juna,  cike da son tabbatar da abinda kunnensa ya jiye masa ya ce “Da gaske ne Kin zama Matar Sahun Keke???”
cikin shashshekar kuka ta ce “Amma ba laifina ba ne don Allah ku yi haƙuri   kar ku yi fushi da ni!!”  jinjina kai ya yi cikin wani irin yanayi   na tashin hankali da ya riske shi,  “Husnee  ki na nufin Sahun Keke ya na sonki ne ko kuma ya yi hakan ne kawai don wata manufar?  ke ma ki na son shi ne?  a ina ki ka haɗu da shi??”
A jere  ya zubo mata tambayoyin  cikin kiɗima.
ba tare da ta dena kukan ba ta ce “Ba don wata manufa ya yi ba,  sabida ina son shi ne ya sa shi yin hakan,  don Allah Yaya kar ku rabani da shi ni ina son shi a haka  duk da irin halayensa.”
Muddassir tamkar zai fashe da kuka ya ce “Duk faɗin Duniya Husnee ki rasa wanda za ki so sai wanda bai ɗauki ran Mutum a bakin komai ba??  anya kuwa kin yi tunani?  yanzu ƴaƴan da za ki haifa ya sunansu??  ki temaka mana ki temakawa kanki   ki  rabu  da shi.”
kai tsaye ta ce “Ba zan iya ba Yaya!!!  ba yin kaina ba ne Allah ne ya jarrabeni da son shi,  so me tsanani wanda na ke jin tamkar shine bugun Zuciyata Yaya!!!”
Miƙewa ya yi   ya na bubbugar kansa da ya gama hautsinewa gami da juyewa,  yarfa hannunsa ya yi  ya na cewa “Kaih!!! Impossible  ta ya-ya zan bari ya auri ƙanwata??”  No ba zai yuwu ba!”  ya yi maganar tamkar wanda ya fara zaucewa,  kamar an tsikare shi ya  zabga da gudu zuwa cikin gidan.

Husnee ta miƙe ta na ɗingisa ƙafa da ƙyar fa ƙyar ta bi bayansa.
Ya na shiga ya Zauna kusa da Mommy  ya na cewa “Mommy ta ya-ya kenan?  Ta ya Auren Husnee zai halatta ga wannan Ɗan ta’addan, ya zama dole mu ɗauki mataki!!”  Mommy ta sa ɗan hankicif ɗinta ta fyace hanci sannan ta ce “Ai na kira kowa da kowa na sanar musu abinda ya faru, kwantar da hankalinka dole ne a raba Auren nan indai da gaske ne an ɗaura shi.”

Da sauri Muddassir ya ce “Yess ta yuwu ma ba a ɗaura ba, ba ri in je in tambayo wanda ya ɗaura ɗin  ko Ƙarya su ka yi mana.”
Bai jira ta ce komai ba ya fice da gudu kamar ƙaramin yaro,  Amadu ya tambaya  bayanan wanda ya ɗaura Auren Amadu ya gaya masa komai, nan ya zabare shi da sunan ya raka shi wajen Malam Kabiru.

Husnee na tsugunne gaban Mommy ta na kuka ta na neman yafiyarta amma sam ta ƙi ko da kallonta,  Wayar Mommyn ce ta fara ruri Ta ɗauka gami da sa hands free yadda Husnee za ta ji ko me za a ce,  Daddy ne ko sallama bai yi ba ya fara surfa faɗa ta inda yake shiga ba ta nan   yake fita ba,  da Mommy ta gaji sai ta ce masa ga Husnee ɗin ta miƙa mata wayar ta tashi ta bar musu Parlorn.
Ba Irin kuka da magiyar da Husnee ba ta yiwa Daddy ba amma ya kanne idanunsa,  bai katse wayar ba sai da ya tabbatar mata gobe za su shuɓigar da ƙara Kotu dolen doliya sai an raba Auren,  a cewarsa ba zai  kai ƴarsa inda za a dinga ciyar da ita da Haram ba.

Ko da Muddassir ya jewa Malam  Kabiru da tambayar sai da ya haɗa masa da Shaidu waɗanda a gabansu aka ɗaura Auren sannan su ka haɗu su ka yi masa bayani,  nan fa ya ƙara burkicewa ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa, shi ba abin ya dinga kurma ihu ba ko ya samu sauƙi.

Ma’u na kicin tare da Iya da Talatu  su na girke-girke   Yazeed ya shigo kamar an jefo shi. da sauri Iya ta ce “Lafiya kuwa Yallaɓai?!
ya ɗan sosa ƙeya kafin ya ce “Don Allah ku ɗan ba ni wuri mana.”
Iya ta komaɗe baki  Zuciyarta cike da saƙe-saƙe,  kafin Iya ta miƙe Talatu da Ma’u sun miƙe,  Iya ta ce “Ke ƴar nan kamani in miƙe mana.”  Ma’u ta temaka mata  ta tashi sannan su ka nufi hanyar fita, jikin Ma’u na rawa  sai gaggawa take yi don ta yi   ta fita kar ya ce mata wani abun.

Caraf ta ji ya damƙo hannunta, a firgice ta juyo ta na zazzaro masa ido, ya marairaice kamar zai yi mata kuka “To Ma’u kika tafi  ki ka bar ni   da wa zan yi magana? dominki fa na zo.”
da kyar ta fizge hannunta daga riƙon da ya yi mata cike da baƙin ciki ta ce “Ni ban ga abinda za ka yi mini ba Yallaɓai,   indai Abinci ka ke so ka nemi Iya mana sai dai in zalumci ne ya kawoka”.  wani irin sakin baki ya yi galala  ya na kallonta kafin ya ce “na yi miki kama da Azzalumai Ma’u??    to in ma haka ki ka gani  ni ba haka ce a Zuciyata ba, ki je ki shirya ki raka ni.”  “Ni ba zan je ba!!”  ta faɗa a masife kamar za ta hau kansa da dukan.
wani lallausan  murmushi ya saki Gami da cewa “Dama kin iya faɗa?  sai naga kin yi kyau a cikinsa;    ke sai fa kin je ko kuma in ɗauke ki  da kaina in zuba ki a Mota,    wata cikal-kal da ke har wani hargowa ki ke yiwa mutane?   to ki gaggauta shiryawa in ba haka ba zan ɗaukeki ko babu gyale.”
Ba ta ce masa komai ba ta fice daga Kicin ɗin ta na kuka  ta nufi ɗakinsu.

Iya da Talatu na zaune sun ci gaba da hirar da su ke yi ta shigo ta na kuka, Iya ta riƙe haɓa  gami da cewa “Oo!  Duniya,  me ya yi miki ki ke kuka haka?? ni fa ina ji miki tsoron yaron nan, me ki ka ci masa me yake ta zawarcenki??”
Cikin shashshekar kuka ta ce “Ba abinda na yi masa  haka  kawai  yake mini haka, wai yanzu ma in shirya in raka shi, ni dai ba zan je ba ko me zai yi mini.”
Talatu ta yi karaf ta shiga zancen da cewa ”Ke wallahi ki bi shi  ki ga inda zai kai ki,  ai dai ba zai sayar da ke ba ko.”  cikin takaici iya ta zabga tsaki gami da kaiwa Talati duka ta na cewa “Ja’irar gora, to in bai sayar da ita ba ai zai rabata da darajarta, ki na gani in uwar ba ta nan yadda yake yo safarar Mata ya na kawowa gidan.”  Talatu ta ce “Eh kuma fa haka ne…”
Ma’u kuwa ƙara fashewa ta yi da kuka  jikinta sai tsuma ya ke yi gabaki ɗaya ta ƙara firgicewa.

Sun ɗauki lokaci a nan Talatu da Iya su na maida yadda aka yi Ma’u kuwa ta na razga kuka…….
Kamar daga sama su ka jiyo muryarsa ya na ƙwalla mata kira, ta ƙara sautin kukanta  cike da tsoro da firgici.
Iya ta rausayar da kai  kamar marigayin zakara  kafin ta ce “To Allah i tsare  sai ki tashi ki je, amma ki dinga Addu’a.”  Talatu ta na jin haka ta tashi ta ɗakko koɗaɗɗen Hijab ɗinta ta fara ƙaƙaba mata, ta na turewa ta na komai amma sai da ta sa mata shi    sannan ta ɗakko mata takalmi  ta ajiye mata ta na cewa “Gwara ki bi shi ta maslaha kar ki yi masa abunda zai cuceki a banza,  sai ki dinga Addu’ar.”

Sai da kyar da  siɗin goshi  suka lallaɓata ta fito wujiga-wujiga da ita  sai  murza kuka take yi kamar an yi mata wahayinsa.
Shi dai  ba abinda ya ke iya yi banda kallonta, har cikin ransa ba ya jin daɗin kukanta amma ita ta kasa ganewa.
A wani rafkeken Super Market  ya yi Parking, ido ya ƙara zuba mata   kamar zai cinyeta, kanta ya na ƙasa har lokacin ba ta dena kuka ba.

Cikin wata karyayyar murya ya ce “Ma’u me yasa ba za ki saki jiki da ni ba?     ba zan iya cutar da ke ba Ma’u hasalima  burina a koda yaushe in ga ki na farin ciki, kuma ina so farin cikinki ya ɗore har Abada, ki temaka ki gaya min damuwarki  domin ina so in zamo miki Bango.”    Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, ai kuwa ta  ƙara fashewa da wani sabon kukan filll, cikin shashsheka ta ce ”Ba zan iya ba!!”
“Yau na ji ikon Allah, kuka na ƙara sa ki? to Allah i ba ki haƙuri na dena,  ki kwantar da hankalinki,   Nasan ki na tunanin wasu halaye nawa  ke ba ki yi kama da irin waɗannan matan ba, ke mace ce wadda ya kamata a yi kishinta,  ki zo mu je to, sayayyar kaya zan yi miki  sai ki zaɓi abinda ki ke so.”  “Ni ba zan je ba”  ta ba shi amsa cikin kuka.

Bai matsa  mata ba ya wuce shi kaɗai, bayan wani lokaci ya dawo ɗauke da tirƙa-tirƙan ledoji guda biyu  wanda aka shaƙesu da kaya,  bayan ya zuba a Motar  ya shiga mazauninsa sannan ya ja ta.
Har su ka dawo gida Ya na zuba mata surutu ita kuwa ba ta da aiki sai kuka, muryar ta shi ma duk ta gaji da ji;    ji take kamar ta kashe shi ta huta.

Talatu jiki na rawa ta fara zaro kayan ta na dubawa  sai murna  ta ke yi kamar ita aka bawa.
Dogayen Ruguna ne wanda yawancinsu Abaya ce, sai  riga har ƙasa me wando, sai kayan ciki su pant, da su turaruka, da Alewoyi da chocolate kala-kala .
Iya da Talatu sai yabawa su ke yi yayin da Ma’u ta ke jin Zuciyarta na wata irin ƙuna, lokaci guda zazzaɓi ya rufeta    bayan ta gama masifa da cewa ba za ta yi amfani da komai a ciki ba  ta haye yamutsatstsiyar shimfiɗarsu ta kwanta, ba abin da ke ɗaga mata hankali idan ta tuna sama da surutan da ya dinga yi mata a hanya kamar mahaukacin da ya ƙwato da ga gidan Masu rangwamen hankali.  Sai da su ka gama gani sannan su ka mayar su ka ajiye mata, ita kuwa ko wajenda kayan suke ba ta ƙara kalla ba.

Washe-gari Ranar litinin kenan,  Ranar jirginsu Abhi da Jaafar    ya ɗaga zuwa Saudi Arabia, hakan ya mugun yiwa Akhiee daɗi  ya san duk rigimar da za a yi za ta ƙare kafin Abhi ya dawo.

Gidan Su Husnee
Komai ya yamutae lokaci guda ta zamo tamkar Mujiya a cikinsu  kowa ya ƙi saurararta  hatta Khausar in ta kulata sai Mommy ta doka mata tsawa, Faɗa kuwa ba irin wanda ba ta sha ba Muneeb har da kai duka.
Cikin kwana ɗaya ta wani zuge  ta zube ta yi zuru-zuru  ta dawo tamkar tsumungiya, ga wani ciwon kai da ya sakota gaba ko abinci ta kasa ci,  Ta rasa inda za ta sa kanta ta ji daɗi.
Wata Zuciyar ce ta bata shawarar kiransa ta sanar masa abinda ke faruwa don haka ta ɗakko wayar  ta lalubo lamba ta tura kira.

Ya na tsaye  a  kan wani tsauni hannayensa harɗe a bayansa, sai ƙarewa ko’ina kallo ya ke yi    Zuciyarsa cike maƙil da tunane-tunane,  jin motsin wayar ta shi   ya dawo da shi hayyacinsa  ya ɗauka ba tare da ya ce komai ba.

Cikin Dasashshiyar muryarta ta ce “Akhiee!!”  “Asma’u  ki na lafiya? waye ya taɓa ki?”  goge ƙwalla ta yi kafin ta ce “Ba  wanda ya taɓa ni  kawai ina cikin tashin hankali ne, iyayena da ƴan uwana duk fushi su ke yi da ni, na fahimtar da su na basu haƙuri amma duk hakan bai yi tasiri ba,  kuma sun ce sai sun rabamu.”
ƴar ƙaramar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce “Asma’u Calm dow……..” kafin ya ƙarasa faɗen abinda ke Zuciyarsa ya ji anyi masa wata muguwar runguma ta baya  wadda ta sa Numfashin da Zuciyarsa su ka dena aiki na wucin gadi, ya rintse idanunsa da ƙarfi  gami da cije gefen leɓensa.
Ya na jin Husnee  na kiran sunansa gami  da tambayar lafiyarsa amma ba zai iya ce mata uffan ba a wannan yanayin.
a hankali sautin kukanta ya fara karaɗe kunnuwansa  hakan ya sa tsigar jikinsa su ka hau tashi.  katse wayar ya yi gami da sakinta ta faɗi ƙasa, cikin wata irin rikitacciyar murya ya ce “Raziahh!!!!!”
Cikin shashshekar kuka ta ce “Kai fa Mijina ne Risslan me ya sa za ka haɗa ni kishi da wata?  ka san kai kaɗai nake so kuma  ina kishinka  shine za ka je ka auri wata? me yasa ni ba za ka so ni ba?”
Cikin wata irin murya me matuƙar gusar da hankalin duk wanda ya ji ta take maganar,     a sannu ya zagayo da ita gabansa su na fuskantar juna  ya jefa idanunsa wanda su ka canja launi cikin nata, kamar wanda aka tilastawa yin magana ya ce “Amma duk da ke matata ce wajibi ne na nemawa kaina Abokiyar rayuwa, kin sani dai  ba jinsinmu ɗaya ba,  babu ɗorarren aure tsakanin Mutum da Aljan, ko ba ma haka ba Asma’u ta cancanci hakan, ki yi haƙuri”
Sake ƙanƙame shi ta yi  ta na cusa kanta cikin ƙirjinsa gami da sake wani sabon salon kukan, cikin wata shu’umar murya ta ce “Nima zan zamo Bil-adam domin na rayu da kai,  idan babu kai a rayuwata  zan sha wahala, Don Allah ka dena guduna Mijina ka amince mini mu rayu tare, ina azabtuwa da banzatar da ni da ka ke yi;  ka sa Uban Dawa ya ɗaure ni kawai sabida ina kasancewa tare da kai, idan laifi na yi maka ka hukuntani ta wata hanyar amma ba ta wannan ba Don Allah!!!!!!”
Ta ƙarasa maganar ta na kwallan idanunsa da ke cikin nata.
dukkan hannayensa ya sa ya rungumeta tsam gami da tura fuskarsa cikin wuyanta, cikin fitar hayyaci ya ce “Ni ma ba a son raina hakan ta ke faruwa ba, sai dai ni ba na buƙatar mace a rayuwata dole wata rana za ta hana ni yin abinda ya dace, amma ni ban taɓa ƙin ki ba hasalima ko da yaushe ki na cikin Zuciyata!!!”

SHARE FISABILILLAH

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.

AN FARA PAYMENT

*©️INDO*

_______________________________
DATA SERVICE

*GARAƁASA Kar ku bari ayi ba ku💃🏼*

            MTN
500 MB  150
1GB  280
2GB   550
3GB  840
4GB 1,100
5GB 1,380

  AIRTEL
500  MB  160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB  1,450

           GLO
500MB  170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

   9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
………………………………..
WhatsApp Number or Call:  09079885632
_______________________

https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 20

                 ©️
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Wannan shine Last Free Pages*

LAST FREE PAGE
Da sauri ta ɗago  ta zuba masa blue eyes ɗinta ta na murmushi me matuƙar ƙara mata kyawu da jan hankalin me kallonta, cikin sassanyar muryar da ke ƙara sa shi fita daga hayyacinsa ta ce “Indai da gaske ka ke    ka yi min Alƙawarin za ka kasance tare da ni  har abada,  kuma za ka rabu da wadda ka Aura.”  idanunsa ne su ka ƙara girma, tamkar aradu ta rikito masa aka   haka ya ji saukar kalaman nata, laɓɓansa har karkarwa su ke yi wajen cewa “Impossible!         Razia idan ki ka rabani da Asma’u  tamkar kin rabani da garkuwar  rayuwata ne, ban na son rabuwa da ita kuma ba na so ta cutu, akanta na shiryawa komai  ko da mutuwa ce,  ta na da muhimmanci a rayuwata kuma kema ki na da shi,  zan so ku rayu a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba tare da cuta da  cutarwa ba.”
“Ba zan iya haɗa Mijina da kowace ɗiya ba, kuma ma ka rasa wadda za ka haɗani kishi da ita sai Bil-adam, ba ka nemi zaman lafiya ba, kuma ka na ji  ka na gani zan kasheta ko kuma na nakastata!!”
Ta yi maganar a fusace.
zafi da ƙuna kawai Zuciyaraa ke yi, ture ta ya yi daga jikinsa gami da juya mata baya cikin ɓacin rai ya ce “Tinda na fahimtar  da ke   kin kasa fahimta  zan ɗauki tsatstsauran mataki akanki da zarar kin cutar da ita,  ko meye ya sameta ki sani zan ninka shi akanki, ko kasheta ki ka yi sai na yi miki azabar da za ki gwammace ke ma mutuwa ki ka yi,   tinda na gaya miki gaskiya kin kasa fahimta.”

Ta na shirin yin magana Russlan ya diro a wajen, ransa a matuƙar ɓace,  ya na sauka ba tare da wani tunani ba ya ɗame kwari-da-bakar hannunsa   ya na shirin harbawa Razia,  wani gwauron tashi Akhiee ya yi  ya dira a kansa ya bangajeshi su ka faɗi can gefe su ka fara mulmulawa kamar ƙwallo, cikin sa’a  Akhiee ya yi nasarar ƙwace kwari-da-bakar ya yi wurgi da ita zuwa gefe, rai a ɓace ya ce “Me ta yi maka?”
Russlan ya tunkuɗeshi gefe sannan ya  miƙe ya na cewa “Sabida ta raina mutane   a dinga faɗa mata magana amma ita kamar shaiɗaniya?   yanzu gashi ta sa Uban Dawa sai faɗa ya ke yi mini a ganinsa ko me ta yi  laifina ne,  gwara kawai na harbeta mu je mu yi jinya  da wannan fitinar ta-ta.”
Dogon tsaki  Risslan ya ja kafin ya ce “Amma ai Matata ce ko? kuma wurina ta zo ba wani wurin ta tafi ba.”
“Waye ya bata izinin fita to?  kawai ka ƙyaleta  ta karɓi hukuncin abinda ta yi, ka riga ka san halinta  kaima.
“Ba fa zan bari ka cutar da ita ba,  laifi na yi mata kuma ta na da right  ɗin da za ta nuna ɓacin ranta,  ka je kawai zan dawo da ita da kaina.”
Cikin takaici Russlan ya ce “Sai ka  amsa Kiran Father kai ma nemanka ake yi.” Daga haka ya tashi sama  ya basu wuri.

Akhiee  ya maida kallonsa kan Razia da ke durƙushe  ta na kuka magashiyyan,  a hankali ya taka zuwa gabanta ya durƙusa, tausayinta ya cika masa Zucuya taf,  cikin tattausar murya ya ce “Razia! gardamarki ce ta sa ki ke fuskantar ɓacin rai a kodayaushe,  ba kya jin magana gashi ba kya aikata abu me kyau,  Lokacin da za’a ƴantaki ya kusa amma a bisa wannan laifin da ki ka yi  na san dole Uban Dawa Zai Ƙara miki lokaci,  ba kya kiyaye ɓacin rai, ba kya ɗaukar shawara, ni a yanzu ba zan iya yin komai a kai ba don nima hankalina ya fi kwanciya idan aka killace ki, fitinarki ta yi yawa  musamman a yanzu da ki ka ƙara burkicewa,  ki tashi mu je.”
Ba ta iya cewa komai ba sai kuka, Zuciyarta tamkar ta tarwatse, ji take da Allah zai haɗata da Husnee a yanzu ba abinda zai hana ta kasheta in yaso sai ayi mata ɗauri me dalili.
Hannunta ya kama su ka ɓace daga wurin.

A Fadar Uban Dawa su ka sauka, yayinda Da yawa daga cikin ahalinsu sun taru a wurin su kaɗai ake jira.
Russlan da Arsalaan da Hidaya da sauran yara su na durƙushe a gaban Tafkeken gadon Sarauta na Uban Dawa,  anan Razia da Risslan su ka durƙusa su na miƙa gaisuwarsu.

Sai da lokaci ya ɗan ja sannan Uban Dawa ya yi gyaran murya ya fara da cewa ”Risslan Labari ya iso mana na cewar ka Auri wata Ƴar Bil-adam ba tare da iyayenta sun Amince ba,  meye dalili?”
Da sauri ya ɗago kansa cike da tsoron ta yadda Father zai Karɓi  Abin, Mother ya kalla cike da son ƙwarin guiwa daga gareta, ta sakar masa sassanyan murmushinta gami da lumshe idanunta .
Ƴar ajiyar Zuciya ya sauke gami da yin ƙasa da kai ya ce “Sabida ta na sona ne,  kuma idan ba na tare da ita komai zai iya faruwa da ita, shi yasa na yi hakan, a gafarceni Father.”
Uban Dawa ya jinjina kai cikin dattako gami da manyance ya ce “Ba ka yi tunanin hakan akwai kuskure  ba?”
“Ba na tunanin akwai kuskure a ciki, amma ban sani ba ko kun hango abinda ni ban hango ba.”
Father ya yi murmushi  hakan ya sa duk sauran na wajen su ka murmusa, cike da ƙauna da kulawa ya ce “Kar ka sake wani ya rabaka da Ita, nima zan so ganinku tare.”
Da sauri Razia ta ɗago rinannun idanunta ta zubawa Uban Dawa gami da cewa “Father!!” cikin kaɗuwa da tashin hankali.
Oum Razia ce ta yi saurin tarar numfashinta da cewa “Kul!!  kar ki ƙara sako baki cikin maganar manya.”
Uban Dawa ya ce “Razia ba sai kin neme ni ba ni zan nemeki da kaina domin kin yi mini laifi,  indai fa ba za ki koyi jin magana ba to ba za ki dena karɓar hukunci ba,  Yanzu kin ninkawa kanki Shekaru a ƙarƙashin Hukunci,  Arsalan  maza a maida ita.”  ya ƙarasa maganar ya na kallon inda Arsalaan ya ke
Razia ta ƙara rushewa da wani azababben kuka ta na magiya gami da bada haƙuri, amma  ba wanda ya ce uffan  har shi wanda ya yanke hukuncin, Akhiee kuwa rintse ido kurum ya yi don kuwa sam ba ya jin daɗin kukan nata.

Cikin sanyin jiki Mother ta ce “Father!  don Allah  a yiwa Razia afwa, wani lokacin Zuciya ce take ruɗarta da aikata abinda ba daidai ba.”
“Idan ba a nuna mata kuskurenta kuma ta yaya za ta fahimci yadda rayuwa take??,   idan ta gama hankalta babu me ƙara hukuntata; idan akwai wanda zai yi magana ana saurarensa.”
Miƙewa Akhiee ya yi gami da cewa “Ni kam zan fita ana nemana.”
Da kai kowa ya amsa masa, sannan ya fice.

Hajiya Laure Yau har ƙagara ta yi gari ya waye Sabida  mafarkin Boka Barore da ta ke yi, ko ta farka da zarar ta koma sai ta ci gaba.    Tin ƙarfe bakwai na safe ta ɗauki waya ta turawa Hajiya Saudah kira,  a ɓangaren Hajiya Saudah ma wayar ta na hannunta ta na shirin kiran Hajiya Laure ta sanar mata,  cikin sauri ta ɗauki kiran gami da kara wayar a kunnenta ta na cewa “Hajiya Laure kema kin yi mafarkin ne?”
Hajiya Laure ta ce “Hmm! na yi manaaa,,  ba me daɗi ba ma kuwa,  ai ni gaskiya mu shirya tin wuri mu je mu ji abinda zai ce don wallahi a tsorace nake.”
“To ai nima dai hakan take a nawa ɓangaren, har na ji ma ina tsoron zuwa wallahi don mafarkan da na yi ba kyau”  Hajiya Saudah ta faɗa murya ƙasa-ƙasa,  da sauri Hajiya Laure ta ce “A’ahh!  da ke mu ka je  da ke za mu koma, ni kinsan ba sanin kan abinsa na yi ba,   ko hanyar ba lallai in gane ba, kar kuma mu ƙi komawa ya yi mana wani mugun abin, don na lura azzalumi ne”  ta ƙarasa maganar cikin nuna tsoronta a sarari.
Ƙulululu!!!! cikin Hajiya Saudah ya  ƙara juyawa,  jiki na ɓari ta ce “Kuma fa haka ne, to ki shirya mu je da wuri.”
Da sauri Hajiya Laure ta ce “Ai tuni na shirya dama ke kaɗai na ke jira,  na fa cika da tsoro wallahi.
Hajiya Saudah ta kasa cewa komai sai ma katse wayar da ta yi   ta na sauke wani gwauron nishi,  yau ɗaya dai ta yi danasanin raka  wani wajen Boka Barore.

Dolenta  ta shirya,  Hajiya Laure ta zo ta zabareta su ka yi gaba, cikin su biyun ba a bambance wadda ta fi shiga  tsoro da firgici.

Muddassir na cikin driving kamar an tsunkuleshi ya gangare Motar gefe ya tsaya,  wayarsa ya zaro ya lallatsa  ya tura kira:
Sai da na farko ya katse wani ya shiga sannan aka ɗauka,  Bakinsa har karkarwa ya ke yi wajen cewa “Oga Dazginabu ina cikin tsaka me wuya fa”.
a ɗaya ɓangaren Dazginabu ya yi magana cikin kakkausar muryarsa wadda   ta ke nuni da rashin imani da tausayi da bushewar Zuciyarsa,  “Me ya faru??”
“Sahun Keke ya auri Ƙanwata, kuma wadda na fi ƙauna, ban san yadda zan yi ba wallahi”
“Hhhhhhhh!!”  ya shiga ɓalɓala dariya irin ta mugayen mutane,  Maddassir dai ya na saurarensa  har ya yi me isarsa  sannan ya tsagaita ya ce “Kar ka damu Mafaraucina, wannan dama ce ta zo mana wadda za mu ƙara wasa ƙwaƙwalwarsa, za mu dinga yi masa abinda bai yi tsammani ba  kuma ba zai taɓa zarginka ba,  yanzu ko me mu ka yi masa ruwa ta sha, zai dinga kallonka a matsayin yayan Matarsa, yayin da mu kuma za mu dinga cin dunduniyarsa,  ka ga ranar nan ya kashe jama’ata  to yanzu tinda haka ta faru  ka ci gaba daga inda ka tsaya ni kuma zan dinga tura masa wasu domin kawar da hankalimsa daga kanka.”  ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa “Ina Fatan kisan da aka yiwa yaran nan guda Biyu ya taɓa Zuciyarsa sosai.”
Muddassir ya ja wani dogon numfashi ya sauke shi tare da wata zazzafat iska me tiriri,  murmusawa ya yi cikin jin daɗin kalaman Ogan nasa,  shi da duk bai yi wannan tunanin ba, amma kuwa tinda abin ya zama haka ba shakka shi me goyon bayan auren ne ba zai so a raba su ba. da wannan tunanin ya ce
“Gaskya kanka ya na kawo wuta Oga!!”  Ya faɗa cikin sigar yabawa da koɗawa.
Dazginabu ya yi wata shu’umar dariya.

Muddassir ya ce “Ai nake gaya maka ba ƙaramin  tashin hankali ya shiga ba, har yanzu ban ƙara jin ko ɗuriyarsa ba, da haka za mu sabauta shi har sai ya haukace sannan mu kashe shi, lokacin Ƙanwata kuma za ta dawo hannunmu.”
Dazginabu ya ƙyaƙyata dariya cike da farin ciki ya ce “Yau duk  waɗanda su ka ba ni aiki akansa  za su sha kyakkyawan labari,  ka ci gaba da Fito masa a matsayin Yayan Matarsa  kuma  kar ka bari aiki ya buɗe.”
Muddassir ya ce  “Kamar an gama ne Oga.”
Da haka su ka yi sallama kowa cike da farin ciki da jin daɗi samun babbar dama a hannunsa.

Hajiya Laurenku da Hajiya Saudarku  ana zaune gaban Boka Barore   wanda ya ke ta tuntsira dariya  da zarar ya kallesu.
Hajiya Laure sai Zare ido ta ke yi kamar an jiƙa Kuliya sannan aka zaneta,  jikinta sai wata  masharshara ya ke yi, cikinta  sabida yamutsin tsoro da ya ke yi har ta fara jin gudawa.
Cakk!!!  ya tsaya da dariyar sannan ya ce “Ya riga ya auretaaahhhhh!!”  ya ƙarasa maganar ya na wata sabuwar dariya har da nuna Hajiya Laure da yatsa, hakan ya bawa gudawar da ta fara matsota damar zillowa,  ta na so ta yi magana amma tsoro ya hana don ba ta san abinda bakinta zai furta ba, sai ido take zazzarewa da ka gani ka ga mara gaskiya.
Hajiya Saudah ce ta yi ta maza ta ce “Boka mun yi munanan mafarkai yau, sannan gashi mun zo  mun ji ka ce ya aureta ba mu fahimci me ke shirin faruwa da mu ba”
“Ita Yarinyar da mu ke bibiya ya riga ya aureta kuma ya na bata kariya da iyakar ƙarfinsa,  yanzu dama ɗaya ce garemu, iyayenta sun shigar da ƙararsa Kotu  don haka za mu yi duk wani ƙulli wanda zai sa Kotu ta raba Auren, da haka ne za mu fi jin daɗin azabtar da shi  mun san zai ji ƙuna idan wani abun ya sameta Hahhhhh!!”  ya ci gaba da dariyarsa ta rashin hankali gami da mugunta.
Hajiya Saudah ta ce “Mun shiga tara, To Boka wai dole sai ita  ba wasu da za’a  bibiya a ciki ko ƴan uwansa haka?”
“Babansu fa Malamin Muslimci ne sun riƙe ayoyin Allah ba za mu iya nasara akansu ba,  ta hanyar wannan yarinyar kaɗai za mu yi galaba akansa, kuma dole sai mun yi nasara, dole ne auren nan zai rabuuu!!”
cikin rawar baki Hajiya Laure wadda take jin tamkar ta fashe da kuka ta ce “A yi mana duba a ga auren zai rabu ɗin?”
Wata muguwar kururuwa ya yi  tare da baza hannayensa,  Su Hajiya Laure su ka toshe kunnuwansu sabida  amon muryar ta shi  da  ta karaɗe kunnuwansu har tsakiyar ƙwaƙwalwarsu.

Wani Haske ne ya bayyana a tsakaninsu wanda ya  kashe musu idanu  dole su ka ɓuɓɓuya a cikin gyalensu,  muƙit hasken ya ɓace sai Boka Barore zaune a mazauninsa,  bai jira sun yi magana ba ya fara cewa ” Mun samu Tabbacin dole sai sun rabu don haka za mu ci gaba da ƙoƙari, Kotu za ta raba su da temakonmu!!!  sannan shi ɗin Ba Mutum bane zai ma iya kasheta da kansa, kuma shi ɗin ya na da mata!!  kuma matar ta shi muguwa ce, zan tashi  Aljana Tsigai  daga bacci zan aikata wajen Razia za su zamo abokai ta yadda za ta ƙara zugata akan ta cutar da Kishiyarta,  waɗannan matakan su ne maƙurar Manuniyata, ku ajiye kuɗin sadaukarwa ga Aljanu ku tashi ku tafiiiiiiii!!!”
Hajiya Laure dai abin Duniya ya gama tsumata, ba ta iya ɗakko kuɗin ba ma sai Haj Saudah ce ta janyo jakartata  ta zube masa kuɗin da ta gani a ciki  sannan ta miƙe.

Da ƙyar da numfarfashi Haj Laure ta tashi sabida ƙafarta da ta yi wani mugun sanyi tamkar ba a jikinta take ba, ga gudawar da ta yi ta fara ɓata mata jiki,  da ƙyar da ƙyar take takawa tamkar ƴar shayi har su ka fito.
Sai a lokacim Hajiya Saudah ta lura da abinda ta yi  ta sanya sallallami ta na tambaya,  Da ƙyar Haj Laure ta ƙwaƙulo muryarta da ta maƙale ta ce “Tsoro ne ya sa ni sakin gudawa Saudah yanzu ina zan samu ruwa in gyara jikina?”  Haj Saudah ta ce “Wannan ai abin kunya ne Laure!  haba don Allah,  Daga kin tsorata sai gudawa?”
“Tashin hankali fa ba a sa masa rana, ina na yi zaton haka?  na riga na tsorata tin a mafarkin da na yi bayan haka ga shi yau da wasu alamu na firgirtarwa Boka ya zo mana,  ga kuɗina da nake ta  zuba masa, Allah ya sa dai a samu nasara a wannan karon”  ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka.

Hajiya Saudah ta ce “Sannu to,     mu yi gaba ko za mu samu ruwa.”
Haj Laure ba ta ce kanzil ba ta ci gaba da jan ƙafa. Su na cikin tafiya  su ka yi arba  da wata wawakekiyar Rijiya,  Hajiya Saudah ta ce “ga ruwa ya samu, riƙe min jakata.”
Haj Laure ta karɓa ta na mutsiltsila idanu,  ba ta hana Haj Saudah zuwa wajen ba don kuwa ita tsoro ba zai barta ta je ba.

Haj Saudah na isa wajen ta kai hannu za ta taɓa  Gugan da ke ajiye a gefen Rijiyar ta ji an doka mata tsawa da wata irin murya me rarrabewa, sun kai sakanni biyar  su na jin muryar na yawo a dukkan kusurwoyin  wajen.
Ai Hajiya Laure ba ta san lokacin da ta fashe da wani mashahurin kuka ba,  Haj Saudah kuwa garin gudu har da tuntuɓe da shirin faɗuwa,  a memakon ta tsaya wajen Haj Laure   sai ta wuce ta nufi hanyar da za ta sadata da mota,  Ganin haka ya sa Haj Laure ta bita  bayan ta tattaro ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata ta fara gudu  jagwab-jagwab.

Sai da su ka isa wajen Mota sannan Hajiya Laure ta samu confidence ɗin bajewa a ƙasa ta na ƙara sakin wani kukann gami da cewa “Na shiga uku na lalace yau zan biyoka Alhaji Salisu, shi kenan tawa ta ƙare nima yau mutuwar zan yiiiihihihiii”  ta ja ƙarshen maganar gami da gaurayata cikin kukanta.
Hajiya Sauda kuwa haki ta ke famar yi  kamar Zuciyarta za ta yi tsalle ta fito ta baki,  Sautin kukan Hajiya Laure ne ya ƙara faɗaɗa  ta rintse ido kawai faɗi take “Ga su nan sun biyomu  Na mutu na lalace, Salisu gani nan gareka,  na shiga ukuuuuuuhh!!!!!”

Haj Saudah kuwa ta zama tamkar bishiyar da ta yi shekara da shekaru a wajen, hatta idanunta sun ƙame ta zubawa abinda ta ke gani ido da haka ta tafi shuuuu!!!! jikake yiffff!!!  ta faɗi ƙasa a sume………………

(Su Hajiya Laure yau an taɓowa kai😂 Oo! Ni INDO🤣)

Madarasatul-Nurool-Islam
Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa  da ke a Office ɗin Malamai, ya zuba tagumi, gashi dai a zaune amma hankalinsa ya yi balaguro,  tunanin Akhiee wanda ya kwana biyu bai gani ba yake yi, ko ranar da yazo makaranta zuwan ƙarshe sai dai labarin ya zo ya samu amma bai ganshi da idanunsa ba.

Sallama ake rafkawa a bakin Office ɗin amma sam bai ji ba har sai da aka buga ƙofa sannan ya yi zaram ya na rarraba idanu.
Wani Matashi ne da ke a ɗaya daga cikin gidajen Layin  yake ta ƙwalla sallama, sai da ya kuma yin wata sannan Sheikh Auwal ya amsa, gaishe shi ya yi cikin girmamawa sannan ya sanar masa cewar  wasu bayin Allah ne su ka zo neman shugaban makaranta wato dai Sheikh Auwal Ɗin.

Faɗuwar gaba asarar Namiji……… Sheikh Auwal na jin haka  ba tare da ya san dalili ba gabansa ya faɗi kwantsam!!!   amma da yake akwai taurin Zuciya sai ya daddafe ya ce “A sanar musu gani nan fitowa.”
Saurayin ya ce “To shi kenan!”  sannan ya juyawa  zuwa waje, bayan ya sanar  wa  Daddy da wanda suke tare ya wuce nashi wuri.
cikin tantama da shakku Sheikh Auwal ya fito, ganin Daddy ne ya sa Zuciyarsa ta ƙara tsinkewa.

Bayan sun Gaisa Mutumin ya ce “Ko za mu iya ganin Muhammad Muhammad?”  Sheikh Auwal ya ce “A’a Kwana biyu ma bai zo Makaranta ba  yau ma bai zo ba,  Lafiya kuwa?” miƙa masa wani ɗan envelope ya yi gami da cewa “Daga Kotu, Iyayen Yarinya sun shigar da Ƙararsa akan Auren Ƴarsu da ya yi ba tare da sun sani ba, in ya dawo gida sai a bashi.”  cikin kaɗuwa Sheikh Auwal ya ce “Aure?? kuma Akhiee ɗin??”  Daddy ne ya yi saurin shiga zancen da cewar “Shi kuwa,  na kawo ƴata don ta yi Karatu amma  an ɓuge  ga Aureta,  maganar gaskiya ba zan ɗauka ba dole ne ya saketa.”
“Wai Husna?” Sheikh Auwal ya ƙara tambaya don tabbatarwa,  Daddy ya ce “Ita ɗin fa”
Sheikh Auwal kamar ya fashe da kuka, a sanyaye ya shiga basu haƙuri gami da rarrashi,  Shi dai Daddy kawai jinsa ya ke yi don kuwa gani ya ke yi duk da laifinsu don haka  ya ke jin haushinsu.

Har su ka yi sallama su ka tafi ya na ƙara jaddada musu ban haƙuri,  bayan sun tafi ya koma Office ya zauna. duk ya rasa abin yi,    ji ya ke inama ƙasa za ta tsage ya shige sabida tsabar kunya da takaici da baƙin ciki.

Husnee:
kwana biyu da ba ta fita ba sai ta ji tamkar ta shekara  da yake akwaita da son yawo.  Yau dai ta rantse sai ta fita don haka ta dinga kiwon Mommy da Amadu.  Ta na samun dama kuwa ta zumbuɗa Hijab ta fice, kai tsaye  ta nufi Makaranta duk da cewar da ƴar tazara tsakanin yankinsu da yankin makarantar amma yau ba ta buƙatar a kaita a Mota don ta san Direban nata zai hanata fita.
Ta na  cikin tafiya Tankar Yaƙi da Tawagarta su ka sha gabanta.

Ta na sanye da wani mugun ɗamammen wandon  Jeans  blue wanda aka tsatstsaga wajen guiwarsa sabida tsabar gayu,  rigar kuwa  ta ciki fara ce sol  itama ta mugun kama jikinta sai jacket da ta ɗora ita ma ta jeans, sai  farar  bandana wadda iyakacinta goshi, tsefaffen gashinta wanda ke ta zuba ƙyalli ya yi watsa-watsa kowanne ya kama gabansa, hannunta ɗaya a Aljihun riga ɗayan kuma ya na kusa da bakinta ta na zuƙar Wiwi ta na busawa.

Wani irin taku ta ke yi  me cike da izza, zarra, jin kai, ƙasaita,  tamkar ita ce  Queen Elizabeth.

Husnee ta kallesu ɗaya bayan ɗaya  ta ga zaratan ƙarti sai zaro mata na mujiya su ke yi su na huro mata hancika tamkar bujimayen shanu,  Zuciyarta ce ta fara tsallle tsoro da razani da firgici haɗi da tashin hankali su ka kawo mata ziyarar bazata.

JanKai ne ya kalli shugabar ta  shi  cike da ƙagarar  aiwatar da mugun aiki akan Husnee  ya ce “Ya kika ce Zinaru!  mu hau kanta ne ko kuwa??”

Jin haka ya ƙara ɗaga hankalin Husnee idanun nan nata kamar an danne tinkiya za’a yanka sun firfito waje tsuru-tsuru,  Tankar Yaƙi ta busa hayaƙi a ƙasaice ta ce “Saurin me ka ke yi,  ku kawo mini ita nan.”
Ta na faɗen haka su ka nufi inda Husnee take dama a tsakiya su ka sata, ba tare da tunanin ita mace ce  su maza ba haka su ka cicciɓeta ta na ihu ta na komai su ka direta a gaban Tankar Yaƙi.

Zabgegiyar wuƙarta me kama da Adda ta karɓa a hannun Jankai ta goge ta sannan ta zubawa Husnee idanunta da su ka koma launin ja,  cikin  murya me ƙunshe da manufofi da dama ta ce……………………………

Akhiee,   Ɗan-Bakwai ne  ya miƙo masa wayarsa da take ta tsuwwa, ya karɓa bayan ya  ɗaga kiran ya sa a saman kunnensa,  a ɗaya ɓangaren me kiran ya ce “Ni ne dai Abokin gabarka Inspector Khalil,  ina zarginka da aikata kisan kai na wasu Ƴan Yara guda biyu  bayan ka yi musu Fyaɗe  kai da yaranka,  ba wanda zai aikata hakan sai kai.”
Cikin Nutsuwa Akhiee ya ce “Aikin ne ka rasa da za ka biyo ta bayan gida kuma?? Ka san ina yin ɓarna da yawa, ko za ka iya yi mini ƙarin bayani?”
“Sunan Ɗaya Zakiyya Ɗaya kuma Farhana, an tsinci gawarsu kuma bincike ya nuna sai da aka yi lalata da su sannan aka kashe su, ɗaya a ciki ma har da ƙwaƙule mata ido,  Ba wani kwalo-kwalo da za ka yi mini na san kai  ne ka aikata, kuma mu na nan mu na ƙara bincike akanka.”

Akhiee ya ja tsaki kafin ya ce “Shashashan banza”.
A fusace IP Khalil ya ce “I’m Police fa ni zaka gayawa maganar banza?  wallahi ka guji shigowa hannuna sai ka gane kurenka wallahi, har ni za ka cewa shashasha??  I will arrest you wallahi”
“Faɗi da Hausa”  Akhiee ya faɗa cikin salon rainin hankali, ai kuwa IP ya ƙara haurowa da Masifa da faɗe-faɗe ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Sai da ya gaji ya yi low sannan Akhiee ya ce “In kun shirya kamani ɗin ina jiranku da kai da iyayen gidan naka, in ka tashi zuwa ka tawo da IG ma.”
daga haka ya katse wayar ya na mamakim Sharri irin na ɗan-adam, an kashe masa Mutanen sannan za a ɗora masa sharrin aikatawa.

Waya ya ɗauka ya kira Rahma don jin Halin da Farhana ta ke ciki don ya san in su ka gane ta na raye ma wata sabuwar gwaramar ce.
Rahma ta na ɗagawa cikin Muryar kuka ta ce “Dama yanzu na ke son kiranka Ɗan Manya”
”Why”
Cikin dauriya ta ce “Ita ma Farhana Allah ya yi mata rasuwa”.  “What??  Farha is dead??” ya faɗa cikin kaɗuwa da razani.
Sake fashewa ta  yi da kuka ta na cewa “Yes! kuma na yi imani da Allah ita  ma haɗa baki aka yi da Likitoci su ka kasheta…………….

LAST FREE PAGES

(Mutanen Akhiee da na Husnee zan gani ko zan iya Ƙidaya adadin Ƙaunar da za ku nuna musu  ta hanyar jin labarinsu har ƙarshe😍)

ƘARSHEN FEJIN KYAUTA

Na Kuɗi ne….
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP  500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632

LAST FREE PAGE
_______________________________
DATA SERVICE

*GARAƁASA Kar ku bari ayi ba ku💃🏼*

            MTN
500 MB  150
1GB  280
2GB   550
3GB  840
4GB 1,100
5GB 1,380

  AIRTEL
500  MB  160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB  1,450

           GLO
500MB  170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

   9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
………………………………..
WhatsApp Number or Call:  09079885632
_______________________
*©️INDO*

Leave a Reply

Back to top button