Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 79

Sponsored Links

*💖 NIHAAD 💖*

*79*

 

Har suka kusa gida Nihad bata ce masa komai ba don tayi nisa duniyar tunanin da ta tafi, da ta tuna Khalil is getting married soon sai taji gabanta ya fadi sosai, amma idan ta duba yanda ta tsallake many challenges a rayuwarta sai taga wannan din ma she will scale through it, Allah zai tsallakar da ita, amma fa in ta tuna wannan challenge din is for ever sai taji duk jikinta yayi sanyi, may be Allah bai rubuta zata ji dadi tayi farin ciki a rayuwarta ba, daga wannan sai wannan, ba a wata daya sai taga sabon jarabawa, but Alhamdulillah for everything, ya ɗan kalleta yace “Baby we need to get some foodstuffs” Ta juya ta kallesa a hankali tace “Ohk” wani shopping mall ya tsaya suka shiga ciki a tare, siyayya suka yi sosai na kayan abinci da kayan shayi, sae varieties of drinks, duk dai wani abu da yasan za a bukata a gida sai da ya siya, ta zabi spices iri iri na girki, bayan yayi payment aka kai masu kayan gaba daya bayan booth din motarsa, ana kiran sallan magrib suka bar haraban mall din, still kafin su karasa gida sai da ya tsaya wani eatry ya siya masu abinci da drink. karfe goma saura Nihad ta fito daga wanka kenan ya shigo dakin da turarrukan wuta da Mami ta yi mata, ya ajiye mata su a kasa yana kallonta yace “Kin kunna heatern bandakin ne” Ta gyada masa kai tace “Na kunna” Ya nuna mata turarrukan wutan yace “To su wa ennan ya ake yi da su?” Murmushi tayi tace “Ci ake” Ya zaro ido yana kallonta, tace “Zaka ce baka san turaren wuta ba?” Ya shafa kansa yace “Can u pls make me a cup of tea after dressing up ki kawo min daki?” Tace “Ohk” Juyawa yayi ya fita daga dakin, sai da ta gama shafe shafenta, kafin kace me kamshi ya cika dakinta, ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta dau Hijab har kasa ta sa ta fito daga dakin, a tunaninta zata gansa downstairs zaune parlor amma bata gansa ba, ta wuce kitchen kawai ta daura masa ruwan shayin, bayan ta gama ta wuce sama da shayin, tana tsaye jikin kofarsa tayi knocking a hankali tare da sallama sannan ta bude kofar, tsaye ta gansa a dakin with short alamar he just took his bath too, banda kamshi me dadi babu abinda dakin yake ga sanyin Ac da har yayi yawa a dakin, bata karasa ciki ba murya can kasa tace “Ga shayin na gama” without looking at her yace “You can come in” Ta turo masa baki tace “Ni ban gama abinda nake yi ba fa” Ya buda ido sosai yana kallonta yace “Idan kin ajiye ba sai ki wuce ki ci gaba da abinda kike yi ba, i am not stopping you Love” Shiru tayi na few seconds sai kuma ta karasa ciki a hankali ta tafi har bedside drawer ta ajiye cup din shayin, sai kuma ta saci kallonsa taga kallonta yake, zata nufi kofa yayi saurin jawota ya matseta jikinsa yace “Ni kika ce ma cin turaren wuta ake yi ko?” Ta marairaice masa tana shigewa jikinsa tace “Toh kai baka san wasa ba, ni fa da wasa na gaya maka haka” Ya cire mata Hijab din jikinta murya can kasa yace “Noo, ban san sa ba, you have to tell me how i will start eating it when it’s not you….” Kawai gani tayi ya kashe switch din dakin, ya dauketa cak sai kan big bed dinsa, rungumesa tayi ta fara masa kukan shagwaba tana cewa “Ni dai a’a pls” Nan ta kara birkita mutumin…. Da asuba a nan dakin suka yi sallah tare saboda ruwan da aka fara tun karfe hudu saura har zuwa lokacin sallah bai tsaya ba, bayan sun idar ya juya yana kallonta taki barin su hada ido, murya can kasa yace “Good morning Heart” ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita a hankali ya dago kanta yana kallon idonta da ya kumbura, nan da nan hawaye ya cika idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi ya jawota jikinsa a hankali yace “I am sorry wife, i am very sorry” Ita dai bata ce komai ba sai hawaye da take tana shessheka a hankali, dagota yayi ya kwantar da ita saman gadon ya ja mata duvet don garin yayi sanyin sosai, ya zauna gefenta yace “Get some sleep” Yana ta zaune gefen nata har yaga ta fara bacci wajen karfe shidda, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya sauka daga kan gadon ya dauke pray mat din da suka yi sallah yayi folding dinsa. Har da safe karfe takwas bata tashi ba, ya dau makullin motarsa ya fita zuwa pharmacy don siyo mata magani ya dawo gida, ko da ya shiga dakinsa bai ganta a ciki ba, ya fita zuwa dakinta jin wanka take a bandaki ya zauna dakin ya jira har ta fito, suna hada ido ta sunkuyar da kanta ta karaso kan gadon ta kwanta ta lulluba da duvet don sanyin take ji, ya koma kusa da ita yace “Maran ya daina ciwo gaba daya?” Ta kallesa ta gyada masa kai, ya dagota yace “I can also make u warm not only duvet” Yana fadin haka ya lullubesu da duvet din gaba daya yana rungume da ita, kamshinsa yasa taji warmth din, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace “But…. did you know i love you?” Lumshe ido tayi, shi ma yayi hakan yana jin sabon sonta na fizgarsa yace “Ina sonki, ina sonki my wife, fiye da yanda ni kaina nake zato… I want to be with u till death do us apart…..” As if whispering tace “Me too, i love u” Kissing dinta ya fara yi, duk da tsoronsa da ya cika zuciyarta amma bata hanasa ba, kuma daga karshe sai da tayi da ta sanin da bata hanasa din ba, haushinsa da taji na yanzu yafi na jiya da daddare, ya gaji da lallashinta ganin kamar tunzurata yake kara yi kawai yayi shiru ya kyaleta yana kallonta. Sai da ya sauko downstairs ya kalli agogo yaga har sha daya saura minti biyar, ya tafi kitchen ya hada mata shayi don shi kam babu abinda ya iya bayan wannan, ya kusa minti daya tsaye bakin kofar dakin ya kasa shiga kamar dai yana shakkarta, daga karshe dai ya tura kofar a hankali, durkushe ya ganta jikin gadon, ya karasa ciki da sauri ya ajiye shayin yace “Are you okay?” Cikin kuka tace “It’s paining me” Ya dagota ya zaunar da ita gefen gadon yace “I am sorry dear, pls ki sha Shayin ga magani na siyo maki nan” Da kyar ya lallabata ta sha shayin ƙadan sannan ya bata maganin da ya siyo mata daxu ta sha, tayi ta juye juye har kusan 12 kafin bacci ya dauketa, ya mike ya fita daga dakin zuwa nasa. Karfe uku na yamma bayan ya sa ta ci abincin da ya siyo mata ya sauko downstairs tare da ita, gaba daya baya jin dadin ganinta cikin yanayin da take ciki yanzu, and he promise him self zai kyaleta har sai ya gano cause of ciwon maran nata, ta zauna kan kujera tana kallon tv dake aiki, yayi kasa da murya yace “U are angry at me ko?” Taki ce masa komai, ya zauna gefenta yace “Kiyi hakuri plss ba laifina bane Baby” Ta wani kallesa, murmushi yayi ya ja hancinta yace “To mu je kiyi strolling compound for some minutes, you will feel better” Bai jira cewarta ba ya dagota suka fita daga parlon, yace “kin taɓa zaga Backyard din gidan nan kin ga flowers da na shuka maki kuwa?” Ta girgiza masa kai, yace “Ohk now, zan rufe idonki in kai ki har wajen and u chose the best flower da kika fi so, da kaina zan dinga watering din maki shi, sauran kuma masu aiki su dinga yi” Ta ɗan buda ido tace “Toh idan naje na fadi kasa fa?” Tun da garin Allah ya waye sai yanxu ta bude baki tayi masa magana, yaji dadin haka yace “Ta ya zaki fadi bayan ga mijinki, ain’t u secured when with me?” Ita dai bata ce komai ba, bayan sun sauka matakalan bakin entrance din gidan ya zaga ta bayanta ya tsaya ya rufe mata idonta a hankali da hannunsa, sannan ta tafiya a hankali yayi leading dinta har zuwa Backyard din gidan, ita dai tafiya kawai take amma a tsorace gani take kamar xata ji ta kume kanta da bango ko ta ci tuntube da wani abu ta fadi, sai da suka kusa wajen yace “Now, let’s stop here baby” Ita dai bata ce masa komai ba, taga ya zame hannunsa a hankali daga idonta, ta gwale ido tana neman flowers din, duk da akwai flowers din masu kyau a wajen amma idonta bai sauka kan komai ba sai kan cages har hudu dake wajen…. Juyawa tayi da sauri ta kallesa, ya wara mata ido yace “Hope za a janye Allah ya isan yanzu ko?” She was speechless, can kawai ta karasa inda cages din suke tana kallon kyawawan colourful birds dake ciki, wa enda ma suka fi nata tsada da kyau, ai kawai sai ta juya ta koma da gudy ta rungumesa tightly cike da farin ciki tace “Waoww wllh i love them so much, naji dadi sosai, are they for me pls?” Murya can kasa yace “Kin janye Allah ya isan yanzu?” Ta daga kai tana kallonsa da sauri kamar me son gano wani abu, zaro ido tayi ta koma baya hade da dafe kirji tace “Dama kai ne ka sakar min tsuntsaye na a gidanmu??” Ya karyar da kai yace “Ai ban san naki bane na zata na makota ne” Kawai sai ta fashe da dariya har da kyakyatawa ta durkusa wajen, ya dinga kallonta yana murmushi har cikin ransa yaji dadin dariyar nan nata, tayi dariyarta me isarta, ta mike tsaye ya jawota jikinsa murya can kasa yace “I love u so much dear” Ta kwantar da kanta kirjinsa tana murmushi ta lumshe ido a hankali tace “I love you more Hubby” Yace “Kin yafe min yanzu?” Tace “Baka min komai ba my dear, instead ni ce nayi maka” Tun daga ganin birds din nan Nihad ta dawo lively suka zaga gaba daya gidan da ita tana gaya masa how beautiful everywhere looks, sun kusa awa daya a compound din sannan suka shiga ciki shi ma saboda la’asar da ake kira, yayi alwala ya fita xuwa masallaci ita ma tayi sallan sannan ta shiga kitchen, tunanin abinda zata girka ta shiga yi, cause she don’t want him to be spending money buying food outside, cous cous tayi deciding ta hada masu with sauce, ko da ya dawo masallaci ya ganta a kitchen he was so surprise, shi fa kawai ya siya kayan abinci ne saboda ya kamata ya siya amma ba wai don yasa ran ta iya girki ba balle ta girka masu, bai gama kwasan mamaki ba sai da ta gama girkin wajen biyar da rabi ta zubo masu a tare, shi dai yasan da baya gidan bazai taɓa yarda Nihad ce tayi girkin ba ko duk jikinsa kunnuwa ne, wallahi yayi mamaki sosai, he never expect such taste from her food, sai yake jin kamar Maminsa ce ma tayi girkin tsabar dadinsa, ita bata wani ci da yawa ba amma shi kam ya ci har sai da ya kusa cinyewa, ya jawota kusa da shi yayi mata whisper a kunnenta, turo baki tayi ta rufe fuskarta a jikinsa don maganar tasa ya bata kunya, Yayi kasa da murya yace “Amma fa kin fi abincin by far…..” Suna ta zaune parlorn har aka kira magrib ya tafi masallaci ita kuma ta dau plate din abincin ta kai kitchen, basu taɓa zama su yi hira da Khalil ba sai ranan, they gisted about so many things har kusan karfe goma da rabi, daga karshe ya sa suka tafi bandaki suka yi wanka a dakinsa, ta gama shirin kwanciyarta ta kwanta saman gadon tayi lamo, bayan ya shirya shi ma ya kwanta kusa da ita, banda faduwa babu abinda gabanta yake, ya rungumeta ya kashe wutan dakin murya can kasa yace “Maran yayi sauki yanzu ko?” Tayi shiru bata ce komai ba don tun bayan da ta fara shan maganin bata jin ciwon kuma, duk iya daurewan da ya so yayi ya kauda kansa daga gareta yayi bacci amma ya kasa, sai juye juye yake amma bai yi attempting komai ba, can dai ta dago kanta a hankali tace “Are you okay?” Ya kasa ci gaba da daurewa kamar me rada yace “Plss…. I…” Sai kuma yayi shiru, rubbing his chest a hankali tace “You what?” Shkkn ta kara rikita al’amarin, she didn’t stop him ta daure duk da condition din nata, ganin she couldn’t hold it anymore daga karshe ta fara masa kuka, amma ya kasa kyaleta, daga karshe kuma ya dawo yana bata hakuri, bai yi baccin da yake ji ba sai da ya tabbatar she is okay, ya jira har tayi bacci kafin yayi baccin shi ma with sweet dreams of her. Tun da ya dawo masallaci sallan asuba basu koma bacci ba, tana jikinsa yana danna waya a hankali yace “Amma ya kike jin ciwon maran naki yanzu? Let me see if i should get another medicine for you” Ta girgiza kai tace “Ba kamar na shekaranjiya bane ciwon” Yace “Na jiya fa?” Tace “It stopped immediately” Yace “Kuma bai maki cikin dare ba?” Ta gyada masa kai, ya shafa gashinta yace “Alright love, we will be traveling to Zanzibar hope u will welcome this idea, sai mu yi like 3 weeks a can….” Nihad ta daga kai ta kallesa, yayi mata murmushi yace “I promise u will love it there wife” A hankali tace “May be some other time, kaga Abbana bai yi 40 days ba, sannan kuma ina son inyi settle down a nan so i can rest and practice my duties as a housewife, i am tired of going from one places to another, i will love to stay here for sometime…” Cikin sanyin murya yace “Haka ne, shikenan anytime u feel like wanting to go for holidays u can let me know pls” A hankali tace “Ohk and one more thing pls” Yana kallonta yace “I am all ears sweetheart” Bata yarda yaga hawayen da ya taru idonta ba cikin sanyin murya tace “I know u will be getting married soon, nasan ita budurwar ka ce warce ku ke tare tun ba yanzu ba, ni kuma Abbana ne yayi mana aure da kai It’s not as if i am ur choice or u had the intention of marrying me, so pls i am begging for Allah’s sake, do not use my past mistakes against me, that might affect me mentally, i have already gone through a lot in life do not break my heart pls I can’t endure it, sannan don Allah kar kace zaka hada mu gida daya ina rokon ka don Allah, i am saying this because i know u can afford it….” Bai ce mata komai ba yana jin yanda hawayenta ke sauka a jikinsa, ya rungumeta ya lumshe ido yana patting bayanta a hankali… Da yammacin ranan Khalil ya san Nadeeyah zata zo gidan yi ma Nihad gaisuwa but ya rasa ta yanda zai gaya mata cause shi yanzu da ranta ya baci gwara nasa ya ɓaci sau dubu, har dai Noor da Nadeeyah suka iso gidan bai sanar mata ba, sai bayan da ya gaisa da su a parlor sannan ya haura sama zuwa dakinta, kayanta ya sameta take gyarawa a press, ya zauna gefen gado yace “Su Noor sun zo” Nihad na kallonsa tace “With Mimi?” Ya girgiza kai kawai, sai kuma dai a hankali yace “With Nadeeyah” Sosai taji gabanta ya fadi tayi shiru tana kallonsa, yayi kasa da murya yace “Gaisuwa ta zo maki ba wani abu ba, don Allah idan kin fito kar ki nuna mata komai Baby, Nadeeyah is a very nice gal, bata da matsala and kinga sai Allah ya kaddara cousin dinki ce ma, nasan kinsan haka pls behave maturedly Wife” Nihad dai bata ce masa komai ba, ya mike yace “Kar ki bata lokaci ki fito pls” Daga haka ya juya ya fita, Hijab kawai Nihad ta dauka ta saka don skimpy dress ne a jikinta, har ta sauko kasa gabanta faduwa yake, bata dai yarda sun hada ido ba ta karaso cikin parlon ta xauna, Noor tace “Good evening sis” Nihad ta kalleta tayi murmushin karfin hali tace “Sannunku da zuwa” Nadeeyah tace “Ya karin hakuri?” Ba tare da Nihad ta kalleta ba tace “Alhamdulillah mun gode Allah” Nadeeyah tace “Allah ya ji kansa, Allah ya gafarta masa” Nihad tace “Ameen” Mikewa tayi at first Khalil ya zata sama zata wuce, ya bi ta da kallon mamaki, sai kuma ya ga hanyar kitchen ta nufa, ta dauko masu ruwa da lemo ta kawo ta ajiye masu sannan ta tafi ta debo abincin da ta girka dazu shi ma ta ajiye masu, ya ji dadin hakan da tayi, Drinks din kawai suka sha su ma kuma basu wani dade a gidan ba suka tafi don driver na jiransu a waje, Khalil ya bi ta har kitchen bayan taje ajiye tray din drinks din a hankali yace “Thank you Wife” Ita dai bata juyo ba balle tace masa komai amma Allah kadai yasan abinda take ji a ranta, and she is trying her best not to cry.

A satin Nihad hudu a gidan Khalil ya fahimci abubuwa da yawa game da ita wanda a da idan aka gaya masa bazai taɓa yarda ba, babban abinda ya burgesa ya kara narkar masa zuciya game da ita shine tsaftarta, she is neat in all aspects ba kuma na ganin ido ba, she is just neat in nature, sannan ko kaɗan bata da son jiki don kullum take gyaran babban gidan duk da su kadai ne a ciki, bayan ta gyara dakinta ta wanke bandaki sannan ta shiga nasa ma tayi hakan, ga kuma parlon kasa da kitchen, a ko da yaushe cikin kamshi me kwantar da hankali da zuciya zaka samu gidan, ya zata kawai na kwana biyu zata yi ta gaji ta watsar but sai yaga ba haka bane ways dinta ne tsaftace waje, bata son kazanta da gaske, another sweet thing is that she can cook varieties, tun daga abincin gargajiya, na zamani, snacks, infact all, ba kuma wajen kowa ta koya ba sai wajen Aunty Jamila, iya girkinta na kashesa da mamaki, he never knew she had all this qualities a baya, hakan ya kara masa sonta sosai ba kadan ba, ganin kansa yake the luckiest on earth da Allah ya mallaka masa ita a matsayin matarsa, he just love her dearly, wannan yasa a ko da yaushe duk sallan da zai yi yake saka Abbanta a addu’a don he gave him a gift that he could never have found else where, yana alfahari da ita a matsayin matarsa, duk bayan 3 days yake zuwa gida ya gaida Mami, idan Janar na nan shi ma su gaisa, kuma baya wuce awa daya a gidan kamar ana mintsilinsa, ko da wasa bai taɓa attempting din kai Nihad gidan ba don yana ganin Mami zata iya rike masa ita, shi ko a yanda yake ji yanzu yasan bazai iya rayuwa without Nihad ba, har tunani yake ta inda zai fara adjusting idan yayi resuming aiki. A yau Inna da Aunty Jamila da daya matar Alhaji Abubakar tare da Kamila suka iso garin Abuja da kayan lefen Nihad, Khalil bai sanar mata zuwansu ba kuma shine yayi masu jagora har zuwa gidan Janar, Mota uku suka taho da, daya na Farooq, sai Jeep din Alhaji Abubakar, da kuma na haya da suka yi chattering daga motor park, duk ukun kuma kayan lefen Nihad na ciki don akwatuna sha biyu ne, sai uban turaren wuta da Humra da Mumy tayi mata, Aunty Jamila kuma ta taho mata da products din KMZ, Inna sai salati take a zuciyarta ganin lafiyayyen anguwan da suka shigo duk sojoji ta ko ina, har dai suka isa gidan Janar, Inna ta kalli Aunty Jamila tana wuri wuri da ido tace “Nan din ma duk a cikin Najeriya yake Jamila?” Aunty Jamila tayi murmushi tace “Haba tun yaushe muka baro Najeriya Inna” Inna tace “Ko da naji, dama tun da muka sauka kan wani rubabben titi kafin Halilu ya isko mu nasan mun bar Najeriya na dai yi shiru ne kawai” Sosai Mami da Hajiya Safeenah, da wata kawar Mami suka yi welcoming dinsu dama an hada masu abinci iri iri da drinks, Sojojin suka dinga shigowa da akwatunan zuwa babban parlon gidan, bayan an gama gaisawa an cika masu gabansu da kayan ciye ciye su Mami suka bar parlon, Inna ta kalli Aunty Jamila tace “Sai da nace ku bari ko kala shidda ne in saka a akwatina aka ki aka ce sai dai kala biyu, to yanxu ga irinta nan, kun dai ga gidan nan ba irin gidan da mutum zai sa kaya daya ya wuni da shi bane, minti nawa ne kaya ya fara tsami a jikin mutum? Ni dai wallahi Habubakar bai kyauta min ba, kafin dare ma sai in sanye kala biyun da na taho da shi ai” Hajiya Hauwa dai sai murmushi take, Aunty Jamila taki ce ma Inna komai, babu abinda Inna bata taɓa a abincin da aka ajiye masu ba, wani da ta ji taste din ba irin nata bane sai tayi maza ta mayar cikin warmer din tana gwaggwale ido, Mami ce ta shigo parlon bayan kusan awa daya, Inna ta mike tace “Hajiya a ina zan yi wanka in canza kayan haka kuma” Aunty Jamila ta kalli Hajiya Hauwa da ta saki baki tana kallon Inna da mamaki, Mami na Murmushi tace “Mu je sama Baaba” Inna tace “Naga ma an tafi da akwatin nawa can sama” Mami tace “Ehh yana can dakina” Inna aka bi bayan Mami ana daga shoulder sai kuma ta juya da sauri tana kallo Aunty Jamila tace “Ke jamila kin saka min sarkata da dankunne a cikin akwatin kuwa?” Aunty Jamila da tayi tagumi tace “An sa” Da sauri ta bi bayan Mami, Kamila ta tabe baki tace “Dama ai sai da Baffa yace kar a taho da ita, yanzu ai ga irinta nan” Khalil na ajiye su Aunty Jamila dama gida ya koma don tun safe ya baro gidan, hankalinsa duk ya koma can, yana shiga parlon kamshin turaren da ya doki hancinsa sai da ya sa shi zaunawa a parlon for some minutes yana bin ko ina da kallo, can ya mike jin alamar tana kitchen, ya shiga kitchen din miyar vegetable ya sameta ta gama hadawa, tuwon ma ta gama, rungumeta yayi ta baya yace “Baby wannan wani irin turaren wuta ne kika sa haka a gidan nan? Yafi ko wanne dadin kamshi” Tayi murmushi tace “Tohm tunda shi ma turaren wutan sai kayi santinsa to wata neighbor dinmu ce ta shigo ta kawo min dazu, tace min ordering dinsa tayi….” Ya wara ido yace “I bet from dubai, or… Saudi??” Dariya Nihad tayi tace “Aa fa a nan ne, A *Albaita-Al-sahal* tace min tayi ordering turaren” Yace “Then we will order ours too” Ta kashe gas din tace “Sure” Juyo da ita yayi yana kallonta yace “Guess what baby?” Tayi shiru tana kallonsa tace “What?” Yace “Da farko dai Abdallah yana hannun hukuma yanzu haka, after beaten blue black by soldiers…. That’s my papa’s handwork, and since he is involve in sha Allah nasan dole za a hukuntasa yanda ya kamata” Nihad da farin ciki ya cikata tace “Alhamdulillah, am so happy to hear this, maa sha Allah” For just a week now aka fara neman Abdallah bayan Khalil ya buda ma Janar abinda yayi, at first ya ki gaya ma Janar cause bai san ta yanda zai yi viewing issue din ba, kada ace duk gidan kuma basu da kamun kai ne, but sanin Janar na saka baki duk inda Abdallah yake dole sai an lalubosa a kasar, shine kawai dai yayi shahada ya sanar masa duk abinda ya faru though yasan Abbansa baya tunani negatively, Janar yaji tausayin Nihal sosai kuma yayi alkawarin za a hukunta Abdallah yanda ya kamata, ko sati daya bai yi da gaya ma Janar ba sai ga Abdallah a garin gombe an kamosa har zuwa garin Abuja bayan ya ci duka a hannun sojoji, Khalil yace “Ko da yake bazan gaya maki na biyun ba, zaki gani ne kawai da idonki” Bai jira cewarta ba ya ja ta suka bar kitchen din ya tafi sama da ita yace “I am pressed Baby” Nan da nan ta hade rai ta wani turo baki…..

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

 

*Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp 09084473900*

Leave a Reply

Back to top button