Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 65

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

65

Nihad na zaune dakin Mimi bayan azahar tana danna sabuwar wayar da Khalil ya siya mata, har ta kira Mumy da ya farooq da wayar don ya saka mata layi da credit a ciki, Mimi ta shigo dakin rike da ankonsu ita da Hanan ta diresu gefen gado, laces biyu ne sai super uku uku, Nihad dai sai kallon kayan take, Mimi tayi wani sigh tace “Ankon mu ne wannan…. Idan an siyo wani zan cire maki naki, Suhaila ma ba a kawo nata ba” Nihad tace “Ankon mene?” Mimi ta kalleta zata yi magana amma kamar warce ta tuna wani abu sai tayi shiru tana kallon Nihad din, can ta juya kawai ta harhada ankon ta saka a press dinta ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad ta ajiye wayar hannunta tana sake maimaita kalmar ankon da Mimi tace mata a zuciya, a hankali ta koma saman gadon ta kwanta. Khalil na zaune first parlor din Mami tare da Aunty Maryam, Mami kuma tana other parlon din nata tare da bakuwarta, Aunty Maryam tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace “Komai tace maka kar ka mata musu kayi ta bin ta da toh, amma gaskiya baza ka hadasu gida daya ba” Khalil dai yayi shiru bai ce komai ba, cause he don’t get why Mami is making issues complicated, Aunty Maryam tace “Yau saura kwana ashirin da daya cif cif, ita Nihad din ta sani??” Ya daga kai ya kalleta ya girgiza kai yace “Ban gaya mata ba gaskiya” Aunty Maryam tace “Aa ya kamata ka gaya mata, tun farko ma ya kamata ace ka sanar mata kana da yarinya da kayi ma alkawarin aure kaga zata san da maganar a kasa ba yanzu kawai taji sa kamar daga sama ba” Ya sauke ajiyar zuciya yace “Ko za ki mata maganan da kanki Aunty?” Aunty Maryam ta rike haɓa tace “Ehh lallai, wato ni ce ma zan gaya mata za a mata kishiya salon dai baiwar Allahn tayi ta kallona da shi, kai dai zaka sameta kasan yanda zaka gaya mata cikin lallami, akan dai taji a wani waje baka gaya mata ba, ba don Mami baxata fahimce mu ba da auren ma dagawa kawai aka yi sai zuwa nan da wata uku tunda ai an kai kudi, ita kuma kaga bazata yi tunanin don ba a sonta bane zaka sake aure, amma kuma naga bata da matsala, yarinya ce, kaga bazata wani damu da kishi ba sai nan gaba” Murmushi kawai Khalil yayi bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace “Allah kuwa bazata daga hankalinta ba yanda babban mace zata yi, she is too young for that” Khalil yace “Toh Aunty nan gidan zata yi ta zama kenan?” Aunty Maryam tace “Toh nayi ma Mami magana ka dauketa yau ku tafi kawai tace ai duk rana daya za su shiga gidan da Nadeeyah, kaga sai nan da sati uku kenan, to ya zan mata??” Da mamaki Khalil ya dinga kallonta, Aunty Maryam tace “Kasan idan Mami ta ce ga yanda take son abu to fa kawai ayi hakuri a bi ta da yanda take son din, that’s just it” Aunty Maryam tace “Ni dai zaka kai ni airport zuwa la’asar, kar kayi nisa” Yace “Toh yanzu idan kika tafi sai yaushe za ki dawo Aunty?” Aunty Maryam tace “2 days before the wedding in sha Allah” Yace “Toh Allah ya kai mu” Aunty Maryam tace “Ameen”
Mami na zaune parlonta da Aunty Maryam da dake rufe trolly dinta don la’asar din ya kusa Hajiya Amina ta shigo parlon, Ta zauna da fara’a, bayan sun gaisa tace “Ina amaryar, shiru shiru ni dai ban ganta ba tun da suka iso jiya, shine nace to ni bari in biyota” Mami tace “Ayya, ai ko nace Mimi ta kai ta ta gaisheku ke da Aunty Hassana tun dazu, ban san bata kai ta ba” Hajiya Amina tace “Allah sarki, ai ko bata kai ta ba, ita ma Aunty Hassanar dazu ta dawo ai” Aunty Maryam ta dago kai jin sai yau Aunty Hassana ta dawo daga Kanon, Mami tace “Allah sarki” Hajiya Amina tace “Ya muka ji da shirye shiryen biki kuma?” Mami tace “Alhamdulillah” Hajiya Amina ta mike tace “Toh Allah ya kai mu lokaci, dama dai cewa nayi bari in leko amarya” daga haka ta fita daga parlon, Aunty Maryam ta taɓe baki ta ci gaba da abinda take tana girgiza kai tace “Munafurcinsu dai zai kare masu idan kin bibiya Hassanar ce ta turo ta, in sha Allahu sai mun ji su kaca kaca a rana nan ba da dadewa ba kuwa” Mami dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, ta dau wayarta ta shiga kiran Mimi, Mimi na dagawa Mami tace “Dama baki kai ta bangaren Amina da Hassana ta gaishesu ba kamar yanda nace maki Mimi?” Mimi ta zaro ido tace “Ohh da na shiga dakin dazu na tarar bacci take, bari in duba yanxu Mami” Mami ta katse wayarta, Aunty Maryam tace “Shi kuma Khalil daga cewa ba jimawa zai yi ba ya bar ni shanye a nan gashi har lokaci ya kusa…” Mami tace “Ba ga driver ba sai ya kai ki mana, dole sai shi Khalil din” Aunty Maryam dai bata ce komai ba.
Mimi na shiga dakinta ta tarar da Nihad kwance amma ba bacci take ba, Mimi tace “Ki dau gyalenki mu je ku gaisa da stepmom dita Neehad” Nihad ta mike zaune, gaba daya bata da walwala tun dazu, Mimi na kallonta ta mike ta dau Mayafinta sannan Mimi ta fita dakin ta bi ta a baya, babu wani banbanci bangaren Mami da na Hajiya Amina sai dai Hajiya Amina parlor daya ne babba, tun da suka shigo Hajiya Amina ke kallon Nihad don ita fa duk zaman Nihad a gidan ba wai ta san ta bane, Nihad ta zauna kasa ta gaisheta da ladabi, Hajiya Amina ta amsa faram faram tana mata sannu da zuwa, Nihad dai bata dago kanta ba, bayan few minutes Mimi tace “Aunty Hassana ta dawo ko Mum?” Hajiya Amina tace “Bata dade ma da fita nan ba, ku je tana can bangarenta” Mimi ta mike tace “Toh bari mu je ta gaisheta” Hajiya Amina tace “Toh madallah” Nihad ta mike suka fita daga parlon, da sauri Hajiya Amina ta dau waya tayi dialing din number Aunty Hassana ta sanar mata ga su Mimi za su taho bangaren nata… Mimi na isa ta bude kofar parlorn a hankali, ɗan matsakaicin parlor ne shi ma dai ya hadu iya haduwa, amma bai kai na su Mami girma ba, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin Aliyu zaune parlon saman kujera daga kusa da bakin kofar parlon yana sanye da 3 quarter da polo, suna hada ido ta sunkuyar da kai, Mimi na ganinsa tace “Hi” Daga haka ta karasa can cikin parlon zuwa kofar bedroom din Aunty Hassana tayi sallama, Aunty Hassana tace “Waye?” Mimi tace “Mu ne, an zo za a gaisheki ne Aunty” Aunty Hassana tace “Ina zuwa” Dawowa cikin parlon tayi tana kallon Nihad da ta rakube waje daya a cikin parlon, duk ta ki sakin jiki, lokaci lokaci Aliyu dake danna waya yake mata kallon kasa kasa, Sai ga Aunty Hassana ta fito tana kallon Mimi tace “Sai kin wani rakota kamar za a cinyeta?” Mimi tace “Aa ai bata san hanyar ba” Aunty Hassana tace “Toh ai yanzu ta ga hanyar ko?” Mimi tayi shiru bata ce mata komai ba, can ta mike, sosai gaban Nihad ya fadi, ta dinga kallonta har ta nufi kofa ta fita, Aunty Hassana tana kallon Nihad tace “Sannu ko, bari a kawo maki ruwa” Daga haka ta nufi kofar parlon ta fita, Nihad da gabanta ke faduwa sosai ta kalli Aliyu taga still wani irin kallo yake mata, mikewa tayi da niyyar ficewa daga parlon, taga ya mike ya kulle kofar ya nufo ta yace “Munafuka, macuciya er cin amana…. Dama ashe duk yaudarata kika dinga yi a baya ban sani ba? Ki rasa wanda zaki aura a karshe sai makiyi na? And you are trying to make it look as if baki san hakan ba?” Nihad dake kallonsa zuciyarta na bugawa tace “Kai ban kiraka da munafuki ba sai nice zaka ce ma munafaka? Naga ai ban taɓa amfani da sunan mahaifin wasu a matsayin mahaifina ba, i never lied to you about who my dad is, hasalima har gidanmu na kai…..” Bata kai karshe ba ya sauke mata mari, ta dafe kuncinta da mamaki tana kallonsa babu ko kiftawa, yace “Sai kinyi da kin sanin sanina a rayuwarki, kuma duk sai na fanshe bata min lokaci da kika yi ta hanyar da baki taɓa zato ba wallahi, i am promising u this” Dai dai nan aka bude kofar parlon Aunty Hassana ta shigo rike da tray me dauke da kwalin lemo da glass cup, tana kallon Aliyu da sauri ta ajiye tray din hannunta tace “Me ke faruwa Daddy?” Kofa Nihad ta nufa da sauri hawaye na sauka idonta, Aunty Hassana ta gwalo ido ganin haka ta bi ta tana kiranta amma tuni Nihad tayi nisa, Aunty Hassana ta dawo parlon cike da masifa rai bace tace “Kai wani irin shashasha ne mara lissafi Daddy? Kai me yasa baka jin magana ne? Nace maka a sannu za a bi komai amma sai da ka yi mata magana? Toh yanzu ina kake son in bi ta in bata lemon nan fisabilillahi? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, baka kyauta min ba Daddy” Aliyu yace “Ke kika ga haka mum” Daga haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Hankali tashe Aunty Hassana ta kira wata long time frnd dinta Maimuna da ta hadu da ita zuwansu kano ta shige daki da sauri. Direct Nihad dakin Mimi ta koma ta zauna gefen gado hawaye na sauka idonta sai kuma ta fashe da kuka sosai, ko minti biyar bata yi da shigowa ba aka bude kofar dakin, Khalil ya shigo, da mamaki yake kallonta ganin kukan da take, sai kuma ya nufeta da sauri yana kallonta yace “What happened?” Hade kai tayi da gwiwa tana kuka sosai, ya zauna gefenta ya dagota hankali tashe yace “Talk to me plss an maki wani abu ne?” Tana shesshekan kuka tace “Aliyu slapped me” Khalil ya dinga kallonta ba ko kiftawa, as if counting his words yace “Aliyu slapped you?” Nihad ta gyada kai cikin rawan murya tace “Mimi ta kai ni mu gaisa da yan gidan shine muka hadu da shi a parlon warce muka je kano tare da ita” Khalil bai jira ya gama sauraronta ba ya mike ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, direct dakin Aliyu ya nufa that is almost 5 minutes walk daga dakinsu Mimi, a hanya ya ga wani vase din flower ya dauka yana ci gaba da tafiya kamar zai tashi sama, bai kuma hadu da kowa ba har ya isa part din Aliyu, dai dai nan shi kuma ya fito daga dakin sa babu wata wata khalil ya fasa vase din jikin bango ya caka masa da karfi a kafarsa, Aliyu yayi wani kara ya dafe bango da sauri yana zaro ido, kan kace me sai ga jini kamar an bude pampo, hakan bai sa Khalil ya fasa shakesa ba yana huci yace “Stay away from my wife, idan kuwa ba haka ba, ni ne doom dinka, i promise you” Yana gama gaya masa haka ya turasa da karfi ya juya ya bar wajen kamar wani soja…. Mimi ta fita da trolly din Aunty Maryam zuwa mota ta dawo kenan ta hadu da khalil tace “Yayanmu Aunty Maryam tana ta nemanka fa” Bai ce mata komai ba ya fice daga parlon, Mimi ta tafi ta gaya ma Aunty Maryam yana parking space yana jiranta….. Khalil na kai Aunty Maryam Airport ya dawo sai bai shiga gidan ba, yayi parking kofar gida yayi dialing number Mimi, Mimi na dagawa yace “Are you with me?” Tace “Yeah ina ji” Yace “I want you to come out now with Nihad but kar ki gaya ma Mami, zata siya abu ne a Supermarket” Mimi tace “Alright” Daga haka ta katse wayar, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta fito da Nihad, tun daga nesa yake kallonsu har suka karaso, yana kallon Mimi yace “Thank you” cike da damuwa Mimi tace “Yayanmu they just rushed Aliyu to the hospital now, i think ko kwalba ne ya fadi a kafarsa i don’t just understand, he is bleeding seriously” Khalil yace “Ohh really” Bai jira me zata ce ba ya bude gefensa yana kallon Nihad yace “Shiga mu je ki siyo abun” Nihad ta shiga motar, ya kalli Mimi yace “Za mu dawo yanzu but don’t say anything to Mami” Tace “Ohk” Yace “Noor fa?” Mimi tace “Noor na gidansu Nadeeyah” Yace “Ohk” Daga haka ta kulle motar ta koma cikin gida shi kuma ya bar layin, sai a sannan Nihad ta kallesa da damuwa tace “Me yasa zaka yi injure dinsa haka?” Yace “Saboda ya taɓa Nihad” Tayi shiru tana kallonsa, can ya girgiza kai yace “Dama i have been targeting him for so long, so this is just an opportunity that comes but once” Nihad da hankalinta ya tashi tace “Mimi said he is bleeding heavily” Khalil yace “Serves him right” ta daga kai da sauri ta kallesa ganin gidansa ya kawota, deep down her she felt happy saboda bata jin dadin zaman gidan nan nasu, bata son gidan har cikin ranta, ya sauka ya bude gate din ya shiga da motar ciki sannan yayi parking, da kansa ya sauka ya bude mata side din da take, ta sauke idonta sannan ta sauka daga motar, yana rike da hannunta suka shiga cikin gidan, sama ya tafi da ita, yana kallonta yace “Which room will u prefer amongst the room?” Nihad dai sai kallon dakunan take bata ce komai ba, yayi hugging dinta a hankali ta baya yace “Ko in zabar maki?” Still dai tayi shiru feeling him at her back, a hankali ta fara kokarin janye jikinta ya ki saketa dragging her closer to him, murya can kasa yace “Na zabar maki this one” Ta kalli dakin da yake nuna mata wanda yake kusa kusa da bangarensa na master Bedroom, rubbing her flat tummy yace “Kina so?” Kai kawai ta gyada masa, wasu abubuwa ya dinga yi mata ita dai bata hanasa ba sai kafafuwan ta ne kawai suka kasa ci gaba da daukanta, he could feel how fast her heart is beating, he noticed jikinta ba shi da wuyar reacting to stimulation, bata ankara ba sai ganinsu a bedroom dinsa tayi….
A hankali Khalil yayi kissing din goshinta yace “Wake up, it’s almost Magrib….” Nihad ta bude Idonta, ya dagota zaune yana kallonta, yana son sanar mata maganar da Aunty Maryam tace ya gaya mata amma ya kasa don bai ma san ta inda zai fara ba, Yayi kasa da murya yace “Za mu tafi can gida yanzu” Sosai gabanta ya fadi jin abinda yace mata, ta kasa ce masa komai. Har suka sauka downstairs Nihad ji take kamar ta fashe da kuka, ya dau wayarsa da ya ajiye a parlon, nan ya ga missed calls din Janar har uku, sai na Mami kusan goma, shi gaba daya ya ma mance da wani abu da ya aikata sai yanzu da yaga kiransu, ya mayar da wayar aljihunsa yana rike da hannun Nihad suka fita daga gidan. Sai da suka isa gida Khalil yayi parking a layin yana kallon Nihad, kamo hannunta yayi a hankali, gathering all courage yace “Kin san kafin Abbanki ya hadani aure da ke ina da budurwata warce har da akwai maganar aure tsakanina da ita right?” Nihad ta daga kai tana kallonsa kamar bata fahimce abinda yake nufi ba, Ya lumshe ido ya bude amma ganin irin kallon da take masa kawai ya fasa ci gaba ya ja motar yana driving din a hankali, ana bude masa gate yayi parking a parking space, Nihad bata sake second daya a motar ba bayan ya bude lock din ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan, ya sauke ajiyar zuciya ya jinginar da kansa jikin kujeran motar. Sai da Khalil yayi sallah sannan ya shiga gidan yana ciro wayarsa dake ring a aljihu ganin Abbansa ne ya daga, Janar na gama maganar da zai masa ya katse wayar, Khalil ya nufi bangaren Aunty Hassana kamar yanda Janar din ya umarcesa yana bude kofar parlon ya ga Janar a tsaye, ga Aliyu zaune a kasa an nannade masa kafa da uban bandage wanda har yayi stain da jini, sai zufan azaba yake, Aunty Hassana na zaune parlon sai kallon kafar Aliyu take ta kankance ido zuciyarta na tafarfasa, Ga Mami a tsaye duk jikinta yayi sanyi, ko magana bata yi, Hajiya Amina ma na dakin sai girgiza kai take cike da alhini, Janar ya juya yana kallon Khalil cikin daga murya yace “I need an explanation to this Ibrahim” Khalil yayi shiru bai ce komai ba, Janar yayi masa tsawa yace “Magana nake maka” Khalil ya gyara tsayuwarsa jikin kofar yace “Tsautsayi ne, amma ba da gangan bane” Janar na masa wani kallo yace “Tsautsayi?? Shaye shaye ka fara da zaka kira hakan da tsautsayi? Where u out of ur mind” Khalil dai yayi shiru, can a hankali yace “Kayi hakuri” Janar ya hau zaga parlon fuskarsa a murtuke, Can ya juya ya kalli Khalil yace “Sai ka shirya gobe ka tafi Germany ka hadu da business partners dina na can” Aunty Hassana ta daga kai da sauri tana kallon Janar baki bude, shi kansa Aliyu kallonsa yayi da sauri, Khalil yace “Ohk” Daga haka ya juya ya fita daga parlon, Mami ta kasa dago kai don bata yi expecting jin abinda Janar ya fada ba, Aunty Hassana ta kasa daurewa cikin ɓacin rai tace “Yaya kasan kuwa illar da yayi ma kafarsa? Har fa ƙashinsa sai da ya tsage ya dagargaje” Janar ya kalleta yace “Sai a fita da shi waje a sake duba kafar….” Aunty Hassana na huci tace “Iya abinda zaka gaya ma ɗan ka kenan bayan illata min ɗa na da yayi?? Amma yaya ka bani mamaki, wallahi ka ban mamaki, iya matakin da zaka dauka kenan a kan wannan mugun raunin da Khalil ya ji masa??” Janar ya tsaya kallonta bai dai ce komai ba, tana girgiza kai tace “Toh wallahi baxan yarda ba, idan na yarda shegiya uwata da ubana suka haifeni, kafin in dau mataki dama sai na fara kiran duk family sun san abinda ake ciki, duk sai na bi na tura masu video din kafar Aliyu, Khalil ya nakasa min ɗa amma kai ta business dinka ma kake a Germany ko?? To wllh bazan yarda ba samm, sai inda karfina ya kare a wannan abinda Khalil yayi ma ɗa na” Janar yace “Ni kike gaya ma maganganun nan Hassana?” A fusace tace “Na fada, ai ɗa bai fi ɗa ba, shekaru kusan ashirin baya haka nan yayi masa rauni a baya har yau taɓon na nan a bayansa, a wancan lokacin ma babu wani mataki da ka dauka banda asibiti da ka kai Aliyu, kawai ka dauki son duniya son jaraba ka daura ma yaro yana ta abinda ya ga dama ya zama terror har da su sace sace a lamarinsa, ohk don ba ubanmu daya ba shine zaka dinga fifita ɗan ka a kan ɗa na?” Janar ya gyada kai yace “Ki sameni parlona Hassana” Daga haka ya fice daga parlon nata, Aunty Hassana ta dinga bambami tana zage zage, babu abinda ta mance bata gaya ma Mami da tayi shiru tana kallonta, daga karshe ta fice daga parlon nata ta bi bayan Janar tana huci, dama ta saba fesa masu rashin kirkinta kuma ta zauna lafiya a gidan, babu yanda har shi Janar din ya iya da ita, ita abinda ya kona mata rai Germany da Aliyun bazai je ba sai Khalil, shine babban baƙin cikinta a yanzu, tana isa parlon Janar ta ki zama tace “Ina jin ka” Bai ce mata komai ba banda zaga parlon nasa da yake, bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace “Ki tattara komai naki ki bar min gidana yau ba sai gobe ba Hassana” Buda baki tayi tana kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, can tace “In bar maka gidanka kace?” Yace “Ehh ba sai gobe ba, dama da na duba wasu mugayen halayyenki a baya da yanda kika hadani da mahaifiyata har ta koma ga Allah, to da ko anguwan da nake bazan bari ki karaso ba balle ki shigo gidana har ki zauna zaman shekara talatin….” Aunty Hassana ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, yace “Ba hauka Ibrahim yake ba da zai raunata Aliyu haka nan kawai, they must definitely be something, they must be a reason….” Aunty Hassana na huci tace “Toh ai naga akwai cctv a gidan a duba mana a ga dalilin tunda goyon bayan ɗan ka kake Abubakar” Janar yace “Cctv din da ku ke kashewa ko wanne kike nufi a ciki? Hassana yau ba sai gobe ba ki bar min gidana kada in sa sojoji su fitar min dake, wallahi karfin zumunci kawai nake dubawa nake zaune dake banda haka a irin makircin da kika hada min a baya ko kusa da inda nake bazan bari ki zo ba” Wani murmushin takaici tayi tace “Ohk” Daga haka ta juya ta fice daga parlonsa, direct bangaren Hajiya Amina ta nufa, Hajiya Amina ta taso tace “Ya ake ciki yanzu?” Hassana tace “Ragowar kudin nan na wajenki zaki turo min yanzu” Hajiya Amina tace “Kudi kuma? Aa ni babu ko sisi a wajena, ai kudin sun kare” Wani axababben kallo Aunty Hassana ta jefa mata tace “Me din suka kare?? Miliyan 15 din nan da yayi saura fa nake nufi” Hajiya Amina tace “Aa, ni fa nace maki babu ko sisi a tare da ni” Aunty Hassana tayi mici mici da ido tace “Kan uban can, to kuwa zan maki rashin mutunci, ni zaki ce ma babu ko sisi?” Hajiya Amina tace “Yau ga ikon Allah, kudin haihuwa suke ne, kwanaki kin san sa na tura ma sadiya miliyan 3, to dama ai shikenan ya rage a kudin ko bakya lissafi ne??”

 

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

 

 

Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba’a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da ‘Nihad pack’ 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

Ga number da za a tuntuba kamar haka. +2347065525409

Leave a Reply

Back to top button