Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 26

Sponsored Links

Page 🖤26🖤

 

Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan.
Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba.
Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin.
Bombee kuwa ganin kowa ya dauke kansa daga kanta bai sake cewa komai ba,yasa ta tabbatar labarin data basun ya samu karbuwa a xuƙatansu,dan haka itama sai tasaki ranta,tareda ɗiban abincin karyawa ta shiga ɗaki, dama yunwa ce ta tasheta daga baccin.
Bata ƙarisa gama cin abincin ba sakeenah tashigo cikin ɗakin ɗauke da sallama,amma mutuniyar ko amsawa batayi ba,duk da tasan sakeenan ce.
“Hmmm sallamar ma bazaki amsa ba Bombee,mai yayai zafi haka?”
“Wutah…..wuta ce tayi zafi,mai ya kawoki wajena da sanyin safiyar nan?”
“Kutt yanzu ne safiyar kuma ma zuwa wajenkine laifi komai,…naji abinda yafaru tsakanin ki da mijinki,gabaɗaya gari ya ɗauka Bombee tadawo gida bayan kwanan ta ɗaya a gidan miji?”
“Wata tsiyar ce dan nadawo to,ina kema kikace mijina bana wani ba,mutanen garinnan allah suna shiga hancina da ƙudundune,ke kuma ga munafurfur shine kika taho da rawar ƙafa ki faɗamin ko”
Juya ido sakeenah tayi tareda hararar Bombee,haka kawai jininsu ya haɗu,amma ko yaushe Bombee cikin nunamata isa take a dole ta fita da wata biyar.
“Kaiii ke wallahi Bombee tsiyata dake wanda yadamu dake ma baki barshi ba,koda yake laifina ne danake biyemiki”
A zuciye ta tashi zata bar ɗakin,Bombee tayi caraff ta rike mata hannu tareda cewa.
“Keɗince shegen surutunki ya miki yawa,naji menene yakawoki toh wajena,nasan dole akwai dalili”
“Hmm wai kura ce zatace da kare ya maye,kawai zuwa nayi tayaki zaman jimami,duk da cewar ko kaffara bazanyi ba nasan da gangan kika lahanta goje badan yakawo miki farmaki ba ko kuma dan kina tsoro ba,dama kin shiryah hakan tun sanda kika yarda da aurensa”
“To kin sani miyasa kike sake tambaya dama”
“Saboda share tantama ne”
“Hmm wato dan kiji daɗin zuwa kice ita tafaɗamin da bakinta dagangan ta maujeshi”
“Hhhhhh kinsan bazanyi hakan ba,nidama duk shirin auren da akeyi nasan bakiyi kama da wacce zataje ta zauna ba,ki kallifah kayanki na gida,duka sunanan babu abinda ya samesu baki bayar dasu ba ko kin tafi dasu…….ahhh to kayan auren fah,kinsan tunda baki daɗeba dole zasu karbi abinsu”
“Hhhh daga baya kenan,jiya naje nayi ciniiki na karbi kuɗinsu,yau zasuje a matsayin barayi suɗau kayansu yanda na tsara”
“Innalillahi keee Bombee to idan goje yaƙi sakinki fah yazakiyi”
“Hhhhhhh lallai kema gara ce,to ko kudin hajji aka bashi nasan bazayyi gigin ƙin sakina ba,kijira kiga zuwan takardar tawa,ɗan iska yaje yagama akuyancinsa da wasu,kuma tsabar dan ya raina rayuwata yace zan buɗe masa cinyata?….shi a dole wai ga miji ahh ubangida kai,tauren banza tauren wofi,na tabbatar yanda nayi masa dukannan bazai ƙara moruwa ba ta wannan fuskar kan,shida haihuwa kuwa saidai yaga anayi,naga da yanda zai sakeyiwa ƴaƴan mutane ciki”
“Kutt waikina nufin kinsan komai dama tsiyace”
“Da a tunaninki bansani ba,me kika ɗaukeni ne,dan kawai nace bansani ba shiyake nuna bansani,ke karki dameni bacci zan koma,ki tafi naki harkar.
Zan zauna a gida na sati ɗaya,daganan naɗora daga inda natsayah”
Takarisa maganar tana hamma tareda sake miƙewa akan gadon.
Jijjiga sakeena tayi tareda ficewa a ɗakin,Bombee ta wuce duk yanda take tunani.

Lokacin da suka isa asibitin su daayi sun ɗan tada goje da pilo,ana zubamasa ɗan ruwan shayi a baki yana sha.
Sannu da jiki mlm Ahmadu yayimasa,ya amsa daƙyar,inna daayi kam ko kallon sa batayiba.
Dan sandan ne ya matso inda goje yake tareda cewa.
“Goje yanzu muka dawo daga gidan su matarka,ga surukinka nan ma kana gani,munyi mata tambsyoyi da dama,amma a yanda ta bamu labarin abinda ya faru,alamu ya nuna cewa batasan komai dayake faruwa ba dangane da zaman aure. Tace mana tunkarota kayi kana ce mata zakayi mata irinna sauran matan datakejin labari,wanda hakan yasaka ta shiga cikin tsoro ta farmakeka domin kare kanta. Saboda a baya taga yanda matan daka lalata suke shiga cikin wani hali na damuwa,kuma yanda ake bawa mata labarin fyaɗe,abune da ake nuna musu mutuwa ce kawai tafishi.
Shin dagaske ka farmaketa ko kuwa”
“Ehh to lokacin dana dawo gidan ina cikin fushi ancemin tafita da safe,to…..shiyasa nace mata inna fara babu wanda zai iya ƙwatarta a wajena,na nufeta domin nasaka ta jin tsorona,daga nan bansan miyasa ba ina dabb da kaiwa hannuna kanta saijina nayi a wata duniya daban ina juyawa”
Ajiya zuciya ɗan sandan yasake tareda cewa.
“Alamu yanuna kenan labarin data bayar da gaskene,sannan koda ankaita kotu baza’a ɗaureta ba,saboda an tabbatar batada masaniya gameda abinda yake cikin aure,wanda iyayenta sun amsa cewa hakan laifinsu ne. Sai nabiyu kuma ta kaimaka farmaki ne domin kara kanta daga fyaɗen da take tunanin zakayi mata”
“Amma kowa yasani tunda matata ce,ai ba fyaɗe zanyi mata ba”
“Eh kowa yasani,amma ita da batasan komai ba akan auren bata sani ba,laifi nakane goje,dana iyayenta kuma. Dan haka mlm Ahmadu zai biya komai daya danganci maganin ka har ka warke”
“Wannan zancen banzane,wacce bata san komai bane zata iya wannan aika aikar,zancen nan dasake,inma mlm Ahmadu cin hanci yabaka domin ka faɗamana haka to bazan yadda ba”
Jauro ne yasaka hannunsa akan kafaɗar inna daayi tareda cewa.
“Kinga kibar wannnan kumfar bakin,babu wani cin hanci haka zancen yake”
“Huuh haka kam,Dan Allah kuyi haƙuri da abinda yafaru mlm jauro,haƙiƙa abu bayyi daɗi ba,saidai babu yanda za’ayi tunda yafaru,yanzu zancen gida nakawo kuɗin da akayi zan bayar,ayi hakuri dan Allah.
Yarinya kuma kozata koma gidanta ba yanzu ba saitasan komai tukunna”
Tun kafin mlm Ahmadu yagama bayanin dayake goje ya zare ido tareda cewa.
“Wacce yarinyar kake zance,banason sake ganinta a rayuwata,wannan ba mutum bace,in aurena ne dayake kanta ake haɗani da ita,to na sake ta saki dubu ma idan anayi,bana som hanya tasake haɗani da ita ta arziƙi saita ɗaukar fansa”
Hannu Inna daayi takai zata rufe masa baki,amma ta makaro ya aikata abinda take gudun.
“Kai shashashan inane,karka manta fah yanzu tamaida ka musaki wanda bazai ƙara haihuwa ba,daka saketa wacece kuma zata zauna dakai,amma da ka barta ina dole ta zauna dakai. Yanzu kuwa zataje tafara sabuwar rayuwarta hankali kwance”
Kuka inna daayi tafashe dashi tareda cewa.
“Burina shine naga kayi aure ka haihu,amma wannan burin yanzu yakau har abada babu shi. Zabin daya ragemin shine naje na tattaro ƴaƴan daka raba a titi na riƙe,dan sukaɗai yanzu suka rage,wani bazai zo ba………wannan yarinya kwai tsinanniya,bantaba zaton idan ka aureta nakasa ka zatayi ba,ita ma dolene taga karshenta aradu”
Ganin fallashe fallashen da inna daayi take tana kuka ne yasa mlm jauro jijjiga cikeda takaici,jan su mlm Ahmadu yayi waje suka gama tattaunawa,daga nan zance ya wuce,aka bar goje da wahalalliyar jinyah.

Cikin ƙankanin lokaci zancen Bombee ta lahanta mijinta a daren farko ya karaɗe garin gembu,kowa sai mamakin labarin yake.
Ita kuwa Bombee yakan ko kaɗan bai dameta ba,dan dama da gangan tayi hakan saboda tasaka tsoron son aurenta a zuƙatan mutanen garin.
Aikuwa tayi nasara,dan tundaga wannan lokacin koshi mlm Ahmadu bakinsa yayi mutt dayi mata zancen aure.
Zuwa jeji kuwa wajen su inno bata fasaba,sukansu basuji daɗi abinda tayi ba,amma ya zasuyi macece da ba’a sakata tayi saitaga dama.
Babu abinda yafi damun Daneji da lamarin sai yanda Bombee tabata kunya a gaban ƴan uwanta,suka zama ganau ba jiyau ba akan abinda Bombee tayi.
Har kusa sati guda da faruwar hakan Daneji bata kalli inda Bombee take ba,saboda takaicin abinda tayi. Tana sane da fushin da innartata take da ita,duk da yana damunta amma ta basar,dan tasan zata hucene nan da wani lokaci.
Tana tsaye a bakin gadonta tana shirin fita Daneji tashigo ɗakin cikin ɗaure fuska.
“Ina zaki da yamman nan?”
“Uhm zan ɗan……”
“Jeji zakije koh,kafin ki tafi jejin bani kuɗin kayan ɗakinki da kika siyar,zan mayar wa ubanki kudinsa”
“Inna ni ban……”
“Nima ƙarya zakiyimun kaman yanda kikayiwa mutane lokacin da kika kashe mijinki a tsaye,a tunaninki bansan duk abinda kikeyi ba,harda zuwanki wajen maharbi uwaisu ba,nice nacewa inno Ta dunga saka ido akan ki.Hmmm nifa na haifeki Bombee mai zaki boyemin dangane da rayuwarki.
Ba wannan ne yakawoni ba,ke yashafa wannan rayuwarki ce,amma kuɗin kayan dakin kam banaki bane bani su nan”
“Dama inna kin…kinsan…..amma ina baki fadawa baba ba ko?”
“Meyasa zan faɗamasa,mekike nufi,sai na buɗe bakina na tozartaki a duniyah bayan wanda kike ciki. Nima ba auren da akayimiki nakeso ba,sanann kowa yasan halin goje ya cancanci fiyeda haka,amma ba goyon bayanki nake ki aikata wani irin sa ba.
Ki kulada duniyah dakuma wanne mutane zaki fuskanta a duk inda kike,jikina yana bani rayuwarki bazata tsayah iyah garinnan ba,zaki shiga duniyah da nisa,dan haka idan hasashena yabbata ki dunga tunawa mutunci yafi kuɗi,sannan ki maida Alkhairi idan akayi miki,kuma ki tuna abu uku.
Duk da bawani sanin mutuncin kanku kikayi ba,ku tuna cewar ke musulma ce kuma macece sannan kuma bafulana,kinuna asalinkin a ko ina”
Ƴar dariyah Bombee tayi,haka halin innar tata take,tana yimata hanya a cikin duhu tana takawa batareda tasani ba,….ko dabbar da aka haifa yau kuka take ƙoƙarin yi na neman uwarta,ko ɗan banza yana san uwarsa,komin ƙarfinka wajenta zaka nufa in duniya tayi maka zafi,Allah yamu ikon kyautatawa iyayenmu,idan ƙasa ta binne idanuwansu kuma Allah yayi musu rahama da jin ƙai.
Ciro kuɗin Bombee tayi a ƙasan kayanta ta miƙawa Daneji,karba tayi ta ƙirgasu tareda kallon Bombee.
“Komai zakiyi a duniyah kisani Sata bata bawa mutum daraja,ki samu naki koda kuwa ta wuyane,karki dauƙi na wani,kisa a ranki kinfi ƙarfin hakan,saikiga zuciyarki da sane da abin hannun mutane”
Ɗaga kai Bombee tayi cikeda jin daɗin maganar mahaifiyar tata,wanda lokaci guda tayi musu matsugunni a cikin taswirar rayuwarta.

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button